Free chapter · Read without an account
Fuska biyu angel and Boss
CHAPTER 2️⃣1️⃣
ZAYYAD
“Ka makara, Zayyad.”
Muryar ta fito daga duhun corridor ɗin.
Zayyad ya tsaya cak.
Idanunsa suka kafe kan duhun da ke gabansa.
Hannunsa ya shiga aljihunsa a hankali, yana neman wayarsa.
“Waye kai?”
Shiru.
Sai wata dariyar ƙasa ta fito.
Zayyad ya matse haƙoransa.
“Ka fito.”
“lokaci baiyi ba.”
Kafin ya ƙarasa, mutumin ya jefa wani abu ƙasa.
Tak!
Zayyad ya kalli abin.
Karamin envelope ne.
Ya sunkuya ya ɗauka.
Amma da ya ɗaga kansa—
Babu kowa.
Ya bace.
Zayyad ya buɗe envelope ɗin.
A ciki akwai hoton Sabreen.
Amma wannan karon…
an rubuta a bayan hoton:
“ABIN DA KAKE ƁOYEWA SHI, ZAI KASHE KA.”
Zayyad ya daɗe yana kallon rubutun.
Sai zuciyarsa ta buga da ƙarfi.
“Sabreen…”
Ya juya da sauri zuwa ɗakinta.
---
SABREEN
Sabreen tana zaune a gefen gado.
Laptop ɗin yana gabanta.
File ɗin da ke ɗauke da sunan RABI.mp4 yana kan screen.
Amma bata iya dannawa ba.
Hannunta yana rawa.
Sai ƙofar ɗakin ta buɗe.
“Angel.”
Sabreen ta ɗago kai.
Zayyad.
Ta sauke numfashi.
“Zayyad…”
Ya shigo ya rufe ƙofar.Idanunsa suka tsaya a kanta.
Ya lura da yadda take rawa.
“Me ya faru?”
“Ban sani ba…”
Ya matso.“Me kika gani?”
Sabreen ta nuna laptop ɗin.
“Wannan.”
Zayyad ya kalli screen ɗin.
Da ya ga sunan file ɗin—
Fuskarsa ta canza.
“Kar ki buɗe, Me yasa?”Sabreen, ki saurare ni.”
“Me yasa ba zan buɗe shi ba?”
Ya yi shiru.
Ta kalle shi sosai.
“Saboda akwai wani abu a ciki da zai fallasa ka?”
Zayyad bai amsa ba.
Idanunta suka cika da hawaye.
“Tun farko kana ɓoye min abu.”
“Ba don in cutar da ke ba.”
“To me yasa?”
Zayyad ya matso kusa.
“Saboda ina tsoron abin da zai faru da ke idan kin san komai.”
“Ni kuma ina tsoron abin da zai faru da ni saboda kana ɓoye min komai.”
Ta juya kamar za ta tashi.
Amma Zayyad ya kama hannunta.
Sabreen ta tsaya.
“Zayyad…”
Ya kalli hannun da ya riƙe.
Sai ya sake shi a hankali.
“Sorry.”
Muryarsa ta yi sanyi.
“Amma…”
Ya ɗago idanunsa zuwa nata.
“Ba zan iya tsayawa ina kallon ki kina shiga hatsari ba.”
Sabreen ta kasa magana.
Zayyad ya ƙara:
Kin san me ya fi bani tsoro?”
Ta girgiza kai.
“Ranar da zan kira ki…”
Ya yi shiru na ɗan lokaci.
“Ki kasa amsawa.”
Sabreen ta kalle shi.
Zuciyarsa ta ƙara bugawa.
“Ranar da zan zo wajen ki…”
Muryarsa ta yi rauni.
“Na tarar babu ke.”
Ya yi murmushi mai ɗauke da ciwo.
“Wannan ne tsoron da nake da shi.”
Sabreen ta sauke idanunta.
“Zayyad…”
“Hmm?”
“Kar ka fara.”
“Me?”
“Wannan maganar taka.”
Ya yi murmushi kaɗan.
“Romance?”
Sabreen ta kalle shi da haushi.
“Eh.”
Ya yi dariya ƙasa-ƙasa.
“Okay.”
Amma kafin ya janye—
Sabreen ta matso kusa da shi saboda tsoro.
A wannan lokacin ne aka ji wata ƙara daga corridor.
Krrrrrr…
Sabreen ta firgita.
Ba tare da tunani ba, ta kama rigar Zayyad Wanda a bazata yaji saukar hannunta akan kirjinshi Amma seya nuna baigani ba saboda abinda ke gaban su.
Zayyad ya kalleta.
Hannunta na riƙe da shi sosai.
Zuciyarsa sai buga take
Wannan ƙaramin motsi nata ya sa duk abin da yake ƙoƙarin ɓoyewa yake kokarin tashi daga zuciyarsa.
Ya kalli fuskarta.
Sabreen a tsorace take.
Amma ba ta sake shi ba.
A hankali ya ɗaga hannunsa ya kare ta.
Yana mai hugging dinta sosai saboda ganin yake tamkar za a rabasu
“Ki yi shiru.”
Ta ɗaga kai.
“Zayyad…”
“Ina nan.”Muryarsa ta yi ƙasa saboda Shi mutum ne mai mugun feeling duk yanda ya Rabi mace to sai yanayin sa ya canza.
“Babu wanda zai taɓa ki.”
Yafada in a cool voice!
Ta kalli idanunsa.
A wannan lokacin Zayyad ya kasa ɓoye abin da ke zuciyarsa da kuma na gangar jikinsa.
“Sabreen…”
“Hmm?”
“Ni…”
Sai kuma Ya tsaya.
Yana so ya faɗi kalmar Amma yanaji tai masa nauyi a baki
Hakan ya haɗiye ta.
Sai ya ce:
“Ni ba zan iya jure rasa ki ba.”
Sabreen ta saki rigarsa a hankali.
“Kar ka ce haka.”
“Me yasa?”
“Saboda bana son ka ɗora min wannan nauyin.”
Zayyad ya yi shiru.
Sai ya janye kansa.
“Okay.”
Ya yi ƙoƙarin murmushi.“Ba zan tilasta ki ba.”
Sabreen ta kalle shi.
A karon farko ta ga wani irin ciwo a idanunsa.
Sai wayarsa ta yi ƙara.
TRRRR…
Ya duba screen.
Unknown Number.
Ya ɗaga.
“Hello?”
Shiru.
Sai murya ta fito.
“Ka riga ka faɗa mata.”
Zayyad ya tsaya cak.
“Waye kai?”
“Ka sani.”
“Me kake so?”Muryar ta yi dariya.“Ita nake so.”
Zayyad ya kalli Sabreen.
Fuskarsa ta canza.
“Idan ka taɓa ta—”
“Too late.”
Kiran ya katse.
Zayyad ya tsaya kamar wanda aka daskarar.
Sabreen ta kalle shi.
“Me ya ce?”
Bai amsa ba.“Zayyad?”
Ya ɗaga idanunsa.
“Ki tsaya a bayana.”“Me ya faru?”
“Sabreen…”
Muryarsa ta yi tsauri.
Saboda wani irin kishi da ya rufe Shi lokaci guda.
“Mutumin nan yana cikin gidan.”
Yafa fuska babu walwala
A dai-dai lokacin kuma sukaji
ƙarar ƙofar gidan ta buɗe.
Sabreen ta kalli Zayyad.
Zayyad ya kalli corridor.
Sai suka ji takun ƙafa.
Tak…
Tak…
Tak…
Yana ƙara kusantowa.
Zayyad ya matse hannun Sabreen.
“Kar ki motsa.”
Amma kafin su ga wanda yake zuwa—
Wata murya ta fito daga duhun.
“Zayyad…”Ya gane muryar.
Idanunsa suka firfito saboda da tsoro da mamaki.
Sabreen ta tambaya:
“Waye?”
Zayyad bai iya amsawa ba.
Domin muryar ta sake cewa:
“Na san inda ka ɓoye takardar…”
“Kuma na san dalilin da yasa kake ƙoƙarin kare Sabreen.”
Zayyad ya tsaya cak.
Sabreen ta kalle shi.
“Wace takarda?”
Zayyad ya rufe idanunsa na ɗan lokaci.
Asirinsa ya kusa fitowa fili…
To be counted…
MISS NASIR ♥️ ✍️