Free chapter · Read without an account

Chapter 28

by Umma mustapha · WA ZAI FUSKANCE NI??

WA ZAI FUSKANCE NI??
BOOK 1
Umma Mustapha
@umsarArewapen
Wattpad: Umma Mustapha
PAGE 28
Sanye take da doguwar rigar abaya a jikinta, ta yane kanta da mayafin abayar, tana riƙe da ƙaramin carpet a hannunta. Ganin fitowarta ya sa Irfan ya fito daga cikin mota, ya karasowa wajenta.
Hannu yasa ya karɓi carpet ɗin, akan wani ɗan tudu da ke ƙofar gidan ya shimfiɗa carpet din. Nihla kuwa ta sa ido tana kallonsa. Ba ta san dalilin da ya sa wani lokaci take jin kunyar Irfan, tare da wani irin nauyinsa idan tana gabansa ba. Ba ta cika haɗa ido da shi ba.
Bayan ya gama shimfiɗawa, ya ɗago ya kalleta.
"Karaso ki zauna."
Ba ta yi musu ba, ta ƙarasa gefen carpet ɗin ta zauna. Shi ma ya zauna daga ɗayan gefen.
"Ina wuni?"
"Lafiya lau."
"Kin daina kukan?"
Nihla ta sunkuyar da kanta ƙasa tana murmushi, ba tare da ta ba shi amsa ba.
A daidai lokacin Fatima ta fito daga cikin gidan, hannunta ɗauke da ƙaramin tray. Ta ajiye shi a gabansu. sannan ta gaida Irfan.
Ya amsa mata tare da cewa
"Ba ki tambayi mutumin ba?"
Ya faɗa cikin sigar zolaya.
Dariya Fatima ta yi, sannan ta ce:
"Ai mun yi waya da shi. Ya ce ba zai samu damar zuwa ba."
Daga haka ta koma cikin gida.
Nihla ta janyo jug ɗin sobo gabanta, ta zuba a cup, sannan ta miƙa masa. Irfan ya karɓa, ya yi mata godiya.
Daga nan kowa ya yi shiru.
Shirun ya ɗan yi tsawo, har Nihla ta kasa jurewa. ta katse shi ta hanyar tambayar sa.
"Ka ce idan ka zo za mu yi magana, amma ga shi ka yi shiru."
Irfan ya kalleta, sannan ya ɗan ɗaga gira.
"Har yanzu ba ki cire abin daga ranki ba kenan?"
"Ba haka ba ne, kawai dai ni tsoro nake ji wallahi. Kar gobe mu shiga makaranta, a aika security su tafi da mu."
Maganarta ta ba shi dariya. Sai da ya murmusa kafin ya amsa.
"A cikin makarantar nan, wa ya isa ya tinkare ku? Maganar ta wuce. An kashe case ɗin."
Nihla ta kalle shi da mamaki.
"Kamar ya? Ni ban gane ba. Ka fito ka yi min bayani."
"Iya bayanin da zan iya miki kenan."
Kafin ta sake sako wata magana, ya yi saurin cewa:
"Mu ga wayarki."
Ba tare da tunanin komai ba, Nihla ta miƙa masa wayar.
"Cire min password ɗin."
"Ni wayata babu password."
"Ki ce wayar masu gaskiya ce."
Ya faɗa yana taɓa screen ɗin wayar.
"An ba ni damar shiga ko'ina."
Murmushi Nihla ta yi, gami da gyada masa kai.
Kai tsaye Irfan ya shiga gallery ya fara kallon hotunanta. Wasu hotunan nata ne ita da Fatima, wasu kuma ita da 'yan gidansu. Yana cikin kallon ne sai wani hoto ya ja hankalinsa.
Ya ɗauko hoton da Nihla ta yi tare da Hafiz, ya kalleta.
"Waye wannan? Na ga kamar kun fi yin hoto tare da shi."
"Yayana ne, sunansa Hafiz."
Amsar ta motsa wani abu a cikin zuciyarsa, yayin da wani tunani kuma ya sake bijiro masa.
Nan take ya kawar da tunanin daga ransa, ya ci gaba da kallon sauran hotuna da bidiyon da ke cikin wayarta.
Bayan ya gama, sai ya koma kan contact ɗinta. Ya duba number ɗinsa, ya ga ta yi saving number ɗin da:
IRFAN - my friend.
Ya ɗan tsaya yana kallon sunan na ƴan daƙiƙu, sannan ya miƙa mata wayar.
Nihla ta karɓa, ta ajiye ta gefe.
Bayan ɗan lokaci, sai ya lura tana ta bige-bige, alamar sauro na damunta. Ya kalleta sannan ya ce:
"Ki tashi ki shiga gida."
Ta ɗan kalleshi.
"Kar sauro ya cinye ki."
Ya san ko ya ce mata su koma cikin mota, ba za ta yarda ba. Shi ya sa be yi mata magana ba.
Daga nan suka yi sallama. Nihla ta shiga gida, shi ma Irfan ya koma motarsa ya tafi.
Bayan ta shiga gida, Fatima ta fara tambayarta yadda suka yi da Irfan. Ita ma hankalinta ya ƙi kwanciya, tun da lamarin ya faru take cikin damuwa. Amma Bata samu wata gamsassiyar amsa ba. Haka dai suka haƙura suka kwanta, kowa da abin da ke sakawa a zuciyarsa.
Washe gari da safe, suka shirya suka shiga makaranta domin suna da test ɗin da za su yi. A tsorace suka shiga cikin makarantar, sai dai har suka je suka fito babu abin da ya faru.
Haka dai aka ci gaba da lallabawa, har suka fara exam ɗin second semester.

Umsar ✍️ 
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.