Free chapter · Read without an account

Chapter 29

by Umma mustapha · WA ZAI FUSKANCE NI??

WA ZAI FUSKANCE NI??
BOOK 1
Umma Mustapha
@umsarArewapen
Wattpad: Umma Mustapha
PAGE 29
Akwana a tashi, har su Nihla suka kammala jarabawarsu. Dalibai kowa yana ta shirye-shiryen tafiya gida, domin wannan dogon hutu ne da za su samu bayan kammala zangon karatu.
Washegarin ranar ne su Nihla za su tafi gida. Da daddare, Irfan ya zo mata sallama. Suna zaune a cikin mota, wayarsa tana hannun Nihla tana buga game.
"Hafsat."
Irfan ya kira sunanta.
" Akwai wata magana da nake son mu yi, tana da muhimmanci sosai."
Jin abin da ya faɗa ya sa Nihla ta tattara nutsuwarta wuri guda, ta ajiye wayar gefe tana sauraron sa.
Irfan ya yi shiru.
Kamar yana jin wani irin nauyin kalmomin da yake shirin furtawa. Ya ɗan sauke numfashi, sannan ya kalli Nihla.
Zuciyarsa tana bugawa da sauri, amma ya san ba zai iya ci gaba da ɓoye abin da ya dade yana zuciyarsa ba.
Bayan ɗan lokaci, sai ya furta:
"I love you with all my heart."
Nihla, wadda har yanzu kanta yake ƙasa tana wasa da hannunta, da jin kalmar sai ta dago da sauri. Kalmar ta zo mata a bazata.
Ta zuba masa ido sosai, kamar tana son gano ko wasa yake yi mata ne.
Amma babu alamar wasa a fuskarsa.
"Kina mamaki ko?"
Ya ɗan yi murmushi.
"Da gaske nake, Hafsat. Ina sonki, kuma ina son in aure ki. Don Allah, ki ba ni wannan damar, please."
Ya ƙarasa maganar cikin sigar roƙo, idanunsa a kanta.
Nihla kuwa tamkar an lika mata bakinta. Ta kasa furta ko wace irin kalma. Kallon sa kawai take yi, yayin da maganar da ya faɗa take ta maimaituwa a cikin zuciyarta.
Ina sonki... Ina son in aure ki.
Maganar so abu ne mai nauyi, musamman idan ta zo maka a bazata daga wanda ba ka shirya jin hakan daga bakinsa ba.
"Talk mana, please."
Ya sake katse mata tunani.
Nihla ta sauke ajiyar zuciya, ta ɗan muskuta ta gyara zamanta.
"Ba ni da abin cewa ne."
"Ke ce kike da abin cewa, saboda gaba ɗaya maganar a kanki take."
Nihla ta ɗan yi shiru, kafin ta ce:
"Dokar kula saurayi tana ɗaya daga cikin dokokin da aka saka min a gida."
"Ba zan takura miki ba. Zan ba ki lokaci ki je ki yi shawara."
Ya ɗan yi shiru, sannan ya ƙara da cewa:
"Abin da nake so ki sani shi ne, Irfan yana mutuwar sonki."
Bayan ya faɗi hakan, bai ƙara magana ba.
Ya miƙa hannu zuwa bayan kujerar motar, ya janyo wata leda, sannan ya ɗora mata a kan cinyarta.
Nihla ta kalleshi cikin mamaki, tana neman ƙarin bayani.
"Naki ne, tsaraba ce. Babu yawa."
Ta so tace masa baza ta karba ba, amma ganin yanayin fuskarsa da yadda gaba ɗaya yanayinsa ya sauya, sai ta yi shiru.
"Na gode."
Shi ma bai ce komai ba.
Nihla ta ɗan kalleshi, sannan ta tambaya cikin kulawa:
"Me yake damunka? Na ga gaba ɗaya mood din ya sauya."
"Babu komai."
"Don Allah, ka faɗa min. Na ga kamar akwai wani abu."
Ta faɗa tana nuna kulawarta a gare shi.
"Karki damu, ba komai."
Ya ɗan kalli agogon da ke hannunsa.
"Ki shiga gida. Na ga dare ya fara yi."
Nihla ta ji jikinta ya yi sanyi. Ta buɗe ƙofar motar ta fita, amma maimakon ta shiga gida, sai ta tsaya a wuri tana jiran ta ga tafiyarsa. Leƙo da kansa yayi ta window ɗin motar.
"Ki shiga gida mana."
Nihla ta kalleshi.
"Ina son ganin tafiyarki ne. Ba zan bar wajen nan ba sai na ga kin shiga."
Dole Nihla ta juya ta nufi cikin gida.
Amma zuciyarta ba da daɗi. Ta kasa fahimtar abin da ya sauya yanayin Irfan haka kwatsam.
Ko a cikin maganganun da na faɗa akwai wadda ba ta dace ba?
Tambayar ta ci gaba da yawo a zuciyarta.
Da wannan tunanin ta ƙarasa cikin 
ɗakinsu.
Ta tarar da Fatima ta yi shirin kwanciya. Don haka ta sauya kayanta zuwa na bacci, sannan ta kwanta a gefen Fatima.
Fatima, wadda ke riƙe da waya a kunnenta, ta ɗan waiwayo tana kallon Nihla. Nan take ta lura cewa tun shigowarta ba ta da kuzari, yanayinta da kuma mood ɗinta sun sauya.
"Bani minti biyu, zan kira ki," ta faɗa, tana mai katse wayar.
Kusa da Nihla ta dawo ta zauna.
"Me yake faruwa ne? Kin fita da karsashi, kin dawo da sanyi a jiki. Wani abu ya faru ne?"
Ta faɗa, idonta a kan Nihla.
Nihla ba ta so ta faɗa wa Fatima abin da ya faru. Amma Kuma ya zama dole ta fada mata Dan tana buƙatar shawara. Wataƙila Fatima za ta iya gano ko a cikin maganganun da ta yi wa Irfan akwai inda ta yi kuskure, har hakan ya sa yanayinsa ya sauya.
Ta tashi daga kwanciyar, sannan ta zauna. Ba ta ɓoye wa Fatima komai ba. Ta ba ta labarin duk abin da suka tattauna da Irfan, tun daga lokacin da ya bayyana mata soyayyarsa har zuwa yadda suka rabu.
Ta ƙarasa maganar tana tambayar Fatima ko akwai inda ta yi kuskure a cikin amsar da ta ba shi.
Fatima ta yi shiru.
Ita fa taga ƙoƙarin Irfan da har ya dauki lokaci me tsawo ba tare da ya furta sirrin da ke cikin zuciyarsaba. Ya ɗauki tsawon lokaci yana ɓoye abin da yake ji, amma yanzu ya fito fili.
Ta san tun farko za a zo wannan gabar, Kuma ta san cewa za a sha fama da Nihla.
"Ki ba ni amsa, gami da shawara," Nihla ta katse mata tunani.
Fatima ta sauke ajiyar zuciya, ta kamo hannun Nihla ta riƙe.
"Zan fara da tambayar ki ne kafin na ba ki shawara."
Ta kalli Nihla sosai.
"Nihla, kina son Irfan ko ba kya sonsa?"
Nihla ta ɗan yi shiru kafin ta amsa:
"Fatima, ko da ina son shi, babu wani amfani, tunda ga dokar da take kaina."
"Har yanzu ba ki ba ni amsar tambayar dana Miki ba"
Ta ɗan matsa kusa da ita.
"Kina son Irfan ko ba kya sonsa?" Fatima ta sake maimaita tambayar.
"Ni ba na son shi. Kallon aboki kawai nake masa."
Fatima ta ɗan kalleta.
"To, ki sanar da shi gaskiya, kar ya ci gaba da ɓatawa kansa lokaci. Gwanda ya sani tun da wuri."
Nihla ta fara girgiza kai.
"Ba zan iya buɗe baki in ce masa bana son shi ba."
"Saboda me?" Fatima ta jefa mata tambayar.
"Saboda tarin alkhairansa a gare mu. Yana da kirki sosai, kuma ina jin daɗin abota da shi. Ya taimake mu a rayuwarmu ta makaranta. Da wane ido kuma zan kalleshi in ce masa bana sonsa?"
Ta ƙarasa maganar kamar za ta yi kuka.
Fatima ta ɗan yi shiru, tana kallon fuskarta.
"Nihla, kina son Irfan."
Nihla ta kalleta da sauri.
"Me ya sa kika ce haka?"
"Saboda duk wasu alamomin soyayya sun bayyana a tattare da ke. Kin daɗe da faɗawa komar so ba tare da kin ankara ba."
Nihla ta ci gaba da kallonta, amma ta kasa magana.
Fatima ta ɗan matse hannunta.
"Da gaske nake, Nihla. Duk wanda ya kalli alaƙarku, zai san akwai soyayya a ciki, duk da ba ku bayyana wa junanku ba."
Nihla ta sunkuyar da kanta, kalaman Fatima suna ratsawa cikin zuciyarta.
"Kiyi shawara da zuciyarki. Ki bi abin da zuciyarki take so. Ke ce ya kamata ki zaɓa wa kanki abin da ya dace, ba wani ba. Ni dai na haska miki hanya, zaɓin yanzu yana hannunki."
Nihla ta yi shiru. Kalmomin Fatima sun bar mata wani sabon tunani da ba ta shirya fuskantarsa ba.
"Ya kamata mu kwanta, saboda gobe da wuri za mu tashii," Fatima ta faɗa bayan sun gama tattauna maganar.
Da haka kowacce ta kwanta.
Amma Nihla ba ta samu nutsuwa ba. Idanunta suna kallon duhun ɗakin, yayin da tunani ya cika fal cikin zuciyarta.
Kalaman Irfan da na Fatima suka ci gaba da yawo a cikin kanta.
"I love you with all my heart..."
Sai ta lumshe idanunta, kalmar ta ƙi barin zuciyarta.
Umsar ✍️ 
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.