Free chapter · Read without an account

Page 20: The journey to Kaduna

by Hauwa Jibrin Sulaiman · The Unwanted Daughter

7:00pm, sai ga kira ya shigo wayar Amrah. A lokacin tana gaban closet tana duba kayan da za ta saka. Ta ciro riga da wando ta ajiye a kan gadonta, sannan ta je ta ɗauki wayar

“Hello, just additional two minutes please” Ta aje wayar ta fara saka kayanta, bayan ta gama, ta gyara kanta, ta ɗaure gashinta da ribbon, ta ɗauki ɗan kwali ta ɗan rufe kanta, ta saka high heels, ta feshe jikinta da turare sannan ta ɗauki jaka

 A ɗayan hannunta kuma wayarta take rike da shi

Dua duk tana kallonta, tana son yi mata magana, amma tana tsoron abin da zai biyo baya gashi gobe tare za su yi tafiya, ta rasa abin da za ta ce mata, sai dai tana mamakin sabon halin Amrah

Da Amrah ta zo fita, ta ce mata
“Make sure ba wanda zai san na fita, okay?”

Dua ko kallonta ba ta yi ba, balle ta bata amsa, Amrah ta buɗe ƙofar ɗakin ta ɗan leka parlour, Da ta ga babu kowa, ta sauko a hankali, tana ƙoƙarin fita daga parlour sai ga Fatima ta fito daga kitchen,  Amrah ta daka mata harara, sannan ta fice

Hibbah ta kira Ummi, da Ummi ta ɗauka sai ta ce“Hope muna da nasara?”

Hibbah ta ɗan yi shiru kafin ta ce,
“A maganar sa, nothing seems like zai ce Dua ba za ta je ba. But yadda muka rabu, idan ba matarsa ta canza masa ra’ayi ba, toh tabbas ba za ta je ɗin ba, I know him”

Ummi ta sauke ajiyar zuciya “Do well please, tausayin yarinyar nake yi”

“Shi yasa bayan rasuwar Aneesa na so in ɗauke ta. Saboda nasan Aneesa ba shiri suke da Zahra ba, kuma nasan ba za ta iya riƙe mata ’ya ba idan ba makirci bane” Suka ɗan yi hira na wasu mintuna kafin suka yi sallama

Amrah na fita, kai tsaye ta nufi motar da ke jiranta. Da ya gan ta, ya yi saurin fitowa ya zagaya ya buɗe mata ƙofar gaba

“Princess, irin wannan kyau haka?”
Amrah ta yi murmushi ta shiga, Shi ma ya zagaya ɗayan gefen ya shiga, ya tada motar suka bar anguwan.
Kai tsaye club suka wuce, da suka shiga, ta hango Rumaisa, nan take ta tafi suka rungume juna

“Let’s get in” ya ce , suka shiga ciki
Jack ya jawo Amrah jikinsa suna hira, sannan ya fara zukan shisha

Rumaisa ma ta ɗauka tana zuka sai Jack ya miƙawa Amrah “try it”

“No”

“It’s nothing, just a flavor” Bayan sun samu sunyi convincing ɗinta, daga ƙarshe ta yarda ta fara zuka ita ma, bayan wani lokaci suka yi sallama da Rumaisa, suka kama hanya, kai tsaye mall suka wuce, ya yi wa Amrah siyayya sannan ya kai ta gida ya sauke ta

Da ta shiga gidan, kai tsaye ɗakinsu ta wuce, ta ajiye kayan da aka siyo mata a mall, sannan ta nufi ɗakin da Sultan yake ta yi knocking, amma shiru, ba a amsa ba, kuma ba a tambayi waye ba sai ta murɗa handle ɗin ta shiga

Da ta shiga, sai ta ga babu Sultan a ɗakin, ta kusa fita kenan sai ta ji motsin mutum daga toilet, sai ta dawo ta zauna a kan gadonsa tana jiransa.
Bayan wasu mintuna sai ya fito, da ya gan ta, ya tsaya cike da mamaki
“Hey, lafiya?”

“Sure! Kawai am here to say goodbye, kasan gobe ne tafiyar namu, and I’m not pretty sure zamu haɗu gobe”

“Ai toh da kin tsaya a parlour then call me, ai zan zo”

“Bayan ka canza min, you have totally changed towards me yanzu. Ko gaishe ka nayi, amsawar ka za ta sound somehow”

“I’m just moody that’s why, but now, I’m sorry”

“Ya wuce, what’s new?”, Sultan ya kalle ta “Where is Dua?

Amrah ta harare shi, ta ɗan murɗe baki “Oho”

Sultan ya girgiza kai, yana mamakin rashin kunyarta “Safe trip, Goodnight”

“That’s all?” Ta tambaya tana tsare sa da kallo, 

Sultan ya fusata kamar mai aljanu ya ce “Out!” 

Idonta ya kawo hawaye, ba ta ƙara magana ba, ta yi saurin fita daga ɗakin

A ransa ya ce,
Yanzu idan Ummi ta gan ta a ɗakina, yaushe zan fara mata bayani? Bayan dazu ma ta gama yi min warning and worst part of it babu Kaya a jikinsa amma ita bata san kunya ba

Dua yau ta tashi da matsanancin baƙin ciki, ganin komai yana faruwa saboda rashin mahaifiyarta ne ya sa za a tura ta inda take ganin za a halaka ta, ta yi ta tunanin tafiyar har ta kasa riƙe kanta, sai ta fashe da kuka

A cikin gidan kuma shirye-shirye ake yi, Mummy ta sa a sauko da kayan da za su tafi, duk da ana hutu, yau da wuri aka gama breakfast saboda tafiyar Amrah da Dua

Daddy ya ce kowa ya fito ayi breakfast. Kowa ya hallara a dining room, amma Dua ba ta cikin su. Ummi ta lura da hakan, amma babu wanda ya damu da rashin zuwanta “Wai ni kam ina Dua ne?”

Mummy ta ɗaga kai “Bakin hali take da shi, shi ya hana ta fitowa”

Ummi ta juya zuwa wajen Fatima “Fatima!”

“Na’am Ma”

“Ki kira min Dua”

“Toh”

Fatima ta wuce ɗakin, ta samu Dua a dunkule a gefen gadonta “Dua, kizo ku yi breakfast”

Sai ta lura da yadda take kuka
“Subhanallah! What’s wrong with you, Dua?”

Kamar an buɗe mata ƙofar kuka ne, Dua ta ƙara fashewa da kuka
“Fatima ban son zuwa Kaduna, Ni nasan irin wahalar da zan sha, they all hate me extreme, ban san me nayi musu ba”

Da ƙyar Fatima ta shawo kanta
“Ummi na kiranki a dining”

Dua ta shiga toilet ta wanke fuskarta sannan ta sauko, tun daga kan stairs Ummi ta kura mata ido, Idonta sun yi ja, kuma sun kumbura “Subhanallah! What’s wrong with you, Dua?”

Duk suka juya suna kallonta, Ummi, Aryan, Sultan da Abbah, vabu wanda ya ji tausayinta kamar Ummi, Mummy kuwa ta tabe baki

Dua ta ƙaraso ta zauna kusa da Ummi sannan ta gaishe da kowa, Ummi ta fara magana

“Yau ɗin su waye ne za su yi tafiyar?”, Aryan ya amsa “Dua da Amrah”

Ummi ta kalli Alhaji Muhammad
“Dua tana da musabaqa ne, kuma kun yi accepting za ta attend, toh me yasa kuka chanza ra’ayi yanzu?”

Mummy ta amsa “Saboda mun ga ya dace mu canza, naga Kaduna za su tafi ne, ba wata duniyar ba, I don’t see why zan tura Amrah alone, da sai ku ce bana adalci a tsakaninsu”

Aryan ya shiga maganar, duk da ya san da ƙyar zai wanye lafiya da Mummy

“Then why not Dua ta zauna, Mummy? Tunda kinga ita ma ba son tafiyar take yi ba”

Mummy ta fusata “Dan ubanka! Manya na magana kana sa baki, Ita Dua ce tace ba ta son zuwa?”

Dua ta sunkuyar da kanta ƙasa tana girgiza kai, Ummi ta ce

“I mean, Amrah ba Islamiyya take zuwa ba, ita mai ƙoƙarin karatu, kuma sai a hana ta? This is not fair at all, mtsww”

Abbah ya yi mata alamar ta yi shiru, Aryan ya sake cewa

“Dua, ba kina cikin masu zuwa Germany ba? Wanda aka ba scholarship? Toh ai next week ne za su tafi, and you know ba ki nan”

Ummi ta kalli Mummy “Daman banda Islamiyya, school ma sun bata scholarship ne?”

Mummy ta ɗauki mock ɗin da ke gefenta ta wurgawa Aryan

“Ka wuce ɗakinku! Duk nan kaji me sa baki a maganar ne sai kai, mara kunya”

Ummi ta kalle ta “Then why?”

“Saboda tarbiyya muke bata, haka kurum za mu tura ta wata ƙasa without knowing how things will be there? Balle abu ya same ta, a zo ana ganin laifinmu”

Ummi ta girgiza kai “Naga ke kaɗai aka tura uwa duniya da sunan karatu? Ita kuma yarinyar da kowa ya san tana da addini, ba wani abu za ta yi na rashin tarbiyya ba, and at least she’s not alone, akwai masu kula da su a can, amma har za ku yi complain? Kuringa wa kanku faɗa mana”

Dua da ta ga duk saboda ita ake ta wannan maganar, sai kawai ta koma ɗakinta

Amrah kuwa ta bita da kallo, Ummi ta kalleta “Mark my word, shi da na kowa ne, ba ku san what tomorrow holds ba”

Around 9:00am, driver ya karaso ya shigo har parlour, ya kwashi kayan da za su tafi da su ya saka a mota. Sai ga Mummy ta fito tare da Amrah
Dua kuma ta sauko daga sama ta wuce ɗakin Fatima, bayan sun yi sallama, tana fitowa sai ta haɗu da Aryan, ya bata hakuri sannan suka yi sallama

Ta wuce wajen Ummi, nan ma suka yi sallama, Abbah ya yi mata nasiha, ta ce “Na gode”

Ta tashi za ta tafi, sai Sultan ya ce
“Ni ba za a yi min sallama ba?”

Gaskiya Dua ba ta lura yana wajen ba
“Am sorry, ban kula kana nan ba ne” Suka yi sallama

Sai a lokacin Ummi ta ce
“Kafin ku dawo, mu ma in shaa Allah za mu tafi”

Dua ta riƙe ta“No Ummi, please karku tafi”

Da ƙyar Ummi ta lallabata sannan ta kama hannunta suka fita

A nan Dua ta ce “Mummy, mun tafi”
Saboda suna gaban Ummi, Mummy ta amsa

“Yauwa ’yar Albarka, Allah kiyaye hanya, Idan akwai wani abu, kira ni, ku sanar da ni”

Suka shiga mota Daddy ma ya fito suka yi musu bye-bye, su ma suka musu fatan sauka lafiya
Aka buɗe gate ɗin, suka fita, suka kama hanyar Kaduna

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.