Free chapter · Read without an account
Page 21: A house of old wounds
Saboda kukan da Dua ta kwana tana yi, sai zazzabi ya kama ta, har suka isa Kaduna, zazzabin bai sake ta ba
Da suka iso wani babban gida a unguwar Kinkinau, suka yi horn, aka zo aka buɗe gate ɗin sannan suka shiga cikin gidan da motar, Nan Amrah ta buɗe ƙofar motar ta fito da gudu, cike da murna ta nufi cikin gidan
Ƙarar shigowar motar ce ta sa Granny ta fito domin tarɓar jikarta mace tilo, aikuwa suka yi clashing a hanya, kowa cike da farin cikin ganin ɗayan
Dua kuwa tana cikin motar, tana jin matsanancin ciwon kai. Idonta a rufe yake, har bata san sun iso ba sai da ta ji ƙarar fitan Amrah, sai ta realize cewa sun iso kenan, ta buɗe ƙofar motar, ta ga hanyar da Amrah ta bi, ita ma ta fara bi step by step, tana tracing har ta isa ƙofar parlour, ta yi sallama da calm voice sannan ta shiga, ta durƙusa har ƙasa
“Granny ina wuni? Mun sameku lafiya?”
Ta ɗan kalle ta “Lafiya”
Sannan suka ci gaba da hirar da suke yi ita da Amrah, Dua kuma ta rakube a edge ɗin parlour
Driver ɗin da ya kawo su yana jira, amma da ya dade ya ji shiru har ya gaji, sai kawai ya yi deciding ya kwashe kayansu daga boot ya kai musu ciki, sannan ya yi musu sallama ya kama hanya. Da ya isa ƙofar parlour ya yi sallama “Wanene?” Granny ta tambaya
“Driver ɗin Daddy ne fah” Amrah ta amsa
“Hajiya driver ne. Na kawo musu kayan su, kuma na zo mu gaisa sannan mu yi sallama”
“Toh… toh… toh, karaso mana”
Ya shiga, sannan suka gaisa ya yi musu sallama ya kama hanya
Granny ta dakawa Dua tsawa
“Ke, wata irin mara tarbiyya ce? Ya shigo muku da kayan ma, ya yi miki kokari, amma kin barsu a nan dan mutane su shigo su gani, ko ke baki iya ɗaukar abu ki kai ciki ba? Toh lalle Zahra ta yi kokari da wannan mugun halin naki”
Ta tashi, duk jikinta ba ƙwari “Ina zan kai su Granny?”
“Dan uwarki ɗakin zaki kai”
Haka ta kwashe kayan ta kai ɗakin da aka nuna mata, duk daga ƙafar da ta ɗaga sai ta ji kamar kanta zai sage gida biyu
Duk sun hallara a dining area domin su ci lunch, Ummi tun tafiyar Dua take jin hankalinta bai kwanta ba, shi ne ma ya sa take ta share Mummy, Aryan ma kusan tunani ɗaya suke yi, Duk tunaninsa yana kan yadda zaman Dua zai kasance a wannan gidan, yasan Granny ba ta kaunar ta, sai dai gwamma kakansu na miji baya hantaranta
Duk suna yi lunch ɗin, amma kowa da abin da yake sake-sake a ransa Mummy kuwa tana jin cewa wannan shi ne daidai. At least Dua ta yi missing wishes ɗinta, balle tafi Amrah
Housemaid ɗin Granny ta gama shirya abinci ta ajiye a dining sannan ta wuce domin ta alerting ɗinsu, Granny ta shiga ciki ta sanar da Alhaji cewa food is ready suka fito tare, sannan ta kwalawa Amrah kira
“Idan kin gama wanka ki fito mu ci abinci, ga Alhaji ma har ya fito”
“Toh gani nan, daman I’m almost done” Amrah ta amsa
Ta fito ta zauna kusa da Alhaji tana ba shi labari. Lantana housemaid ɗin Granny, ita ta yi serving ɗinsu sannan suka fara cin abinci Alhaji ne ya fara magana “Hajiya, ina ita ɗayar yarinyar?”
“Oho, mata da bakin hali, halama ta koshi”
“Ai baku kirata ba, toh taya zata san zamu fara? Naga sai da kika bimu kika kiramu”
Sai ya kalli Amrah “Ke, tashi ki je ki kirawota”, Amrah ta amsa da “Toh”
Ta tafi ɗakin da Dua take, dan nan suka sauka ciki, ta ce “Hypocrite, Alhaji is calling you” Sai ta juya ta fita
Dua kuwa da ƙyar ta iya tashi. Ta fito zuwa parlour hannunta riƙe da kanta, ta durƙusa sannan ta gaishe su Alhaji ya kalle ta “Lafiya kuwa? Ko wani abu ne yake damunki?”
“Zazzabi ne da ciwon kai yake damuna”
“Oya zo ki zauna ki ci abinci sai ki sha magani ki kwanta ki huta, ki yi bacci zaki ji kin warsake, stress ne na tafiya”
“Toh, nagode”, Granny ta harare ta, suna cikin cin abincin ne Alhaji ya tashi “Ni dai na koshi, bari na ɗan amsa waya”Sai ya bar wajen
Hajiya ta kwalawa Lantana kira, bayan ta zo, sai ta kalli Dua “Ke, dago ki ji ni da kyau”
Ta kalli Lantana “Ke kuma Lantana, kin san jiki da jini, dole watarana kana bukatar hutu, toh ke Dua, daga yau har ku koma gida, ke zaki na komai na cikin gidan nan, Lantana sai kina nuna mata wasu abubuwan da ba ta sani ba”
“Toh in shaa Allah” Dua ta amsa a hankali
Lantana ta kalli Hajiya “Amma Hajiya, baki ganin aikin nan zai mata yawa? Kuma kamar yarinya ce… Ni ma kuma kin ga aikin nan nawa ne”
“Toh, zauna sai ki ci gaba da gaya min abin da ya dace da wanda bai dace ba, shashasha bar nan gun”
Suna gama cin abinci, Granny ta kalli Dua “Ke ai sai ki tashi ki fara aikin ko? daga yanzu ne zai fara”
Dua kamar zatayi kuka “Granny, please and please ki barni, wallahi anjima zanyi, yanzu kuma jiri nake ji”
Kawai Granny ta sa sallati, har da guntun hawaye “Yanzu yarinyar nan, ban isa in sa ki abu ki yi ba sai ki ce ba zaki yi ba? Tunda ke ba yar aiki na bace?”
Dua ta sake buɗe baki tana kallon ikon Allah, ashe ganin Alhaji ne ya sa Hajiya take yin wannan sharri
Alhaji ya kalli Dua “Ke, tashi ki shiga ciki ki sha magani, In kin sha sai ki kwanta”
“Toh nagode, Allah ya amfana” Ta tashi ta shiga ciki
Hajiya kuwa ta fara faɗa, tana shiga nan, ta fita can
“Ai duk abin da yake yi dama so yake ’yar ƙaramar yarinya ta raina ni”
Da ya gaji da jin masifarta, sai ya kalle ta “Hajiya, kin san me? Nasan kalar son zuciyarki, wanda a baya kika kusa sani na shiga halaka, Nasan idan kin yi maganar gaskiya da na ƙarya, kuma maganar da kika ce ta faɗa miki, kar ki manta hali zanen dutse ne fa, yarinyar nan ba zata taɓa faɗa ba”
Tun da ya fara magana ta sake baki tana kallansa “Wato saboda ita yau zaka fara kirana da makaryaciya ko? Saboda ita ko?”
“Tsaya na gaya miki abin da nake son faɗa miki, kar ki manta, Irfan zai zo gidan nan ya yi one week, so kar ki ce ban faɗa miki ba” Ya juya ya wuce
Ta fara faɗa “Toh wallahi bazai yiwu ba. Gwara ka faɗa masa ba mu da kayan abinci, ya yi zamansa gidan uwarsa ko kuma kakarsa, to dan kawai yana jikan yayarka ne kawai sai yana wani zuwa mana? Idan jikan ne, gashinan an kawo maka Amrah, Yayarka fa da ko son nawa bata taɓa yi ba, yar tata da ta yi aure ta aura mai kuɗi sosai, ba ta taɓa kawo mana ziyara ba, Sai kawai a kawo mana ɗanta? Inaa, bazai yiwu ba”