Free chapter · Read without an account

Chapter 7

by Nanamaryama · KANWAR SHEHU

بسم الله الرحمن الرحي






Page 7

Aunty ta ce Please ku shiga ciki ganin zuwa...

   Tafiya sukai yana aaka abubuwa marasa iyaka a cikin zuciyar sa, ya ce sister kada kisa Komi a zuciyar ki kinji ko?

Uhmm big bro "Alhaji ne fa ya ce muje bai gane mu ba, wayyo Allah na!"

Lallashinta abeed ya ke tayi, tana kuka baiwar Allah...

  Ɗakin "Aunty suka shiga suna jiran ta zo tai masu bayani, minti 10 ta ƙara a palon ya gama faɗa mata maganganu masu zafi ya tafi, tabi bayan su sister ta kasa ɓoye damuwar ta baiwar Allah tana shiga Abeed ya taso ya kamo hannunta ya zaunar da ita gefen gado ya ce aunty mai ke faruwa ne a cikin gidan nan? Tun ranar da muka dawo na lura da akwai matsala amma kin ce min ba haka ba, wannan abin da ya faru yau ya isa a s🦋
anar damu komi gaskiya!" 


        Kuka ne ya ci karfin ta tara mai ke mata daɗi ita dai tasan dai, alhamdulilah komi tana dashi wanda za'a gani a jikin macce a ce ana so Masha Allah Amma "Alhaji" ya juya mata baya kamar tsohuwar mayya, ta ce ku kwantar da hankalin ku bakomi fa!.. 

              Hmmm kawai Abeed ya faɗa tare da tashi firij dake ɗakin ya dauko mata ruwan sanyi ya ce tasha, amsa tai ta sha tana mai addu'a Allah ya kawo karshen wannan abu..

        **

    Yana isa gida ya fara bala'i ya na faɗar magana shi wannan yarinyar zata mara tabbas sai ya yi maganin ta a cikin wannan lokacin, gwaggo ta ce'' jibo zo kaji wata magana dai mai daɗi to?" 

          Banzan kallo ya watsa mata tare da faɗin mai zan ji ne, mutun yana cikin ya zai za'a wani kira sa , ya ce tunda ba zaki faɗa ba sai nazo barshi..!

        Budar bakin ta ta ce" nasan yadda za'a yi kasa mu jawahir amma kana min wulaƙanci sai an jima ta shiga cikin ɗakin ta"

          Da sauri ya bita sai ki ce min maganar mutuniyar ce ba wai ki shiru ba' to yanzu dai ina sauraron ki kawai ban na sha...

        Cikin zuciyar ta ta ce yaro bai san wuta ba sai ya taka, ta ce kana san ta dai kai aurenta zaka yi ko?

    Eh man kin san yarinyar ita kala ce wallahi gashi ba ta bilicin irin na sauran mata baƙaƙe, yarinyar dai tayi sosai gwaggo!!

         To abinda da nake so da kai, wannan yawan zuwa gidan ka rage sa kuma kadai na duk wani abu da kasan za'a ce ba'a so don Allah, sai ka ga yarinyar ita ma ta faɗa ta ka jibril kaga fa yanzu abokan ka wasu har da yara biyu akwai masu huɗu ma, don Allah ka nutsu ka kwantar da hankalin ka za ka samu" jawahir" in Sha Allah amma ta wannan hanyar da ka ɓullo ba zai baka ita ba gaskiya...!

      Kai kuma fa kinyi gaskiya "gwaggo za'a gyara kawai ma an gyara!" 

              *
Duk wani abin buƙata na matafiya ya samo saboda ranar Monday zasu tafi, suna zaune a palo shi da Aunty ya ce'' amma aunty mai ke faruwa ne nifa gidan duk jin sa nake ba daɗi because Alhaji bai mana yadda muka saba da shi na rasa ya zan yi?''

      A jiyar zuciya ta sauke tare da faɗin ina tunanin dai laifi muka masa amma tun lokacin da kuke garin su jadda ya canza min na bashi hakuri amma dai bai ce komi ba, illa bakar magana da yake min na rasa gane kan sa nima.


      Ya ce" Aunty Abinda ya sa nace haka ko saboda ji ranar da muka dawo ai bamu haɗu ba sai washe gari ji korar da ya mana sai nake ganin kamar dai ba lafiya yake ba!''


      Hmmm kawai ta faɗa, suna cikin Maganar ne ya ƙarar massage ta shigo wayar ta, ta duba ƙwalla ce kawai ke zuba Cikin idon ta wanda hankalin Abeed ya tashi sosai ganin mahaifiyar sa na kuka ya ce Aunty mainene? Ko na bata maki rai ne Aunty don Allah ki yafe min Please!

      Abeed bakai bane, amma don Allah mu cigaba da addu'a kaji rayuwa tana iya canzawa ko yaushe wallahi....

          Wayar hannun ta ya ɗauka sakon da ya gani ne yai matuƙar gigita sa an rubuta da babban baƙi kamar haka..

     SO MADAM KIYI HAKURI INA SAN KI AMMA DA NATAHO WAJEN KU GABA NA FADUWA YAKE WALLAHI, DAGA YAU KAR KI KARA SA GIRKI DANI MUMMY ZATA RINKA MIN PART DIN KI WARI YAKE NE BANSO YANZU BAKI GYARA, GA KUDI NAN A ACCOUNT NA SA MAKI SAI KU MANAGE NAGODE Yana gama karantawa ya ce wallahi ba zamu yarda ba taya haka zata faru??

          Kwantar da hankalin ka yaro, zauna mainene ba zai faru ba? Shi din ba mahaifin ka bane? Don ya min haka kasani ko laifi na ne? Bana so wani abu ya haɗa ka da shi na laifi kaji kaga dai Monday zaka tafi yau sauran kwana biyu to a rabu lafiya!.

      Kuka Abeed yasa saboda yasan bata da laifin komi a ciki, part ɗin ta kuma tana gyarawa sosai amma zai ce haka, tabbas akwai lauje cikin naɗi...



     Mummy ce ta shigo part ɗin ko sallama babu ta ce'' mara miji ya hakuri?''

Murmushi Aunty tai tare da faɗin alhamdulilah!

         Mummy ta ce........

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.