Free chapter · Read without an account

DA JININSA NAKE RAYUWA

by Sayyid · DA JININSA NAKE RAYUWA

A fusace ya taso daga kan dinning ɗin, ba wata wata yana zuwa ya tsinkawa Husna wani zazzafan mari wanda ya sa ta ga wasu taurari na yawo a sama, kafin ganinta ya ɗauke na wasu ‘yan sakanni ya dawo, lokacin da ganinta ya dawo Ashraf ya sa ƙafa ya tattake kayan wutar ta fara mutuwa sai hayaƙi da ƙauri. Husna kam ko alamar hawaye ba ta yi ba sabida yanda marin ya shigeta, babu ƙarya tun da take a rayuwarta ba a taɓa yi mata dukan da ya shigeta ba kamar wannan, ji take ma tana son yin kuka amma idanunta sun ƙeƙashi sunƙi fitar da hawaye. 

Da gudu ta yi cikin ɗakin da take zaune, tana shiga ta faɗa kan gadon ta fara sakin wata nannauyar ajiya zuciya, sai da ta daɗe a haka sannan hawaye ya fara zuba a idanunta, suma ƙwalla ce ba wani dogon hawaye ba. 
Dolenta ma tabar masa gidansa chaɓ, ai bata ga ta zama ba, dan wannan marin ya haifar mata da wani zazzafan tsoronsa, da kuma wata ɗimemiyar tsanarsa, a fili ta ce.
“Allah Ka sakamin.”
Haka ta yi bacci tana jin raɗaɗin marin a fuskarta, washe gari da safe kam har ƙarfe sha ɗaya bata fito ba, sai da ta tabbatar ya fita ganin sha ɗaya ta yi, dan ita bata ma tantance wace rana ce, bare tasan yana fita ko baya fita. 

Lokacin da ta fito babu kowa a cikin falon hakan ya bata damar fita, ko a wajen ma tana murɗa handle ɗin ƙofar ta buɗe, sai da ta sauke jiyar zuciyar farin ciki sannan tasa kai ta fita, mai gadi na mata magana ta watsa mai harara ta buɗe ƙofar ta fita da kanta, tana fitowa ta ce.
“Ina zan iya wannan masifar gidan chaɓ, in Allah Ya yarda na gama zuwa gidan nan har abada, ai daman ba gidan ubana ba ne.” 
Ta ƙarasa maganar tana murguɗa baki, hanyar ta fara bi tana tafiya kaman zata ta tashi sama, har Allah Ya kawo ta bakin titi, sai da tazo bakin titin sannann ta tuna babu ko sisi jikinta, maimakon ta tausayawa kanta sai ta fashe da dariyar rashin sanin mafita, a hankali ta fara taka ƙafa zuwa babban titin Kabuga, tana cikin tafiya taji an yi mata horn, kamar ba zata tsaya ba sai kuma ta tuna abin da ke gabanta, tsayawa ta yi tana sauka ƙasa daga kan titin aka buɗe motar aka fito, wa zata gani idan ba Al Qaseem ba, ɗan wajen Hajiya Kubrah wanda kwanaki ya biyota Dade ta ce mata ɗan uwan Ashraf ne. 
“‘Yan mata ina zaki haka?”
Murmushi Husna ta yi, sannan ta ce. 
“Yaya Al Qaseem ina kwana?”
“Lafiya ƙalau Husna.”
Ya faɗa cikin sanyin murya, dan shima muryarsa sanyi ne da ita kamar ta Ashraf, ganin ta yi shiru ya ce.
“Ina zaki?”
“Gida zan koma.” 
“wanne gidan?”
Ya faɗa yana mamaki, dan shi ya ɗauka ta dawo gidansu ne ta gama zaman a nasu gidansu, kwanaki da ya tambayi Dade ce mai ta yi ina ruwansa, ya san kuma Mimi bata nan, to ko gidan Ashrfa tazo tun da dai ya san nan ne unguwar da Ashraf yake, shima wani abokinsa ne ba lafiya yazo duba shi, sabida yana so an jima zai je Abuja shi ya sa yazo da safen nan.
“Gidan Mimi.” 
“To shigo na mayar da ke mana, nima ai can zani.” 
Ba musu Husna ta shiga motar, dan dama neman na Allah take, idan bata shiga tafiyar ƙafa ce zata ce, kuma ita bama zata iya kai kanta gidan ba. Suna cikin tafiya ya ce.
“Mimi ta dawo kenan?” 
“Bansaniba wallahi, amma ko bata dawo ba zan zauna wajen Dade.” 
Gyaɗa kai kawai ya yi, bai son shiga abin da ba a sa shi ba, amma dai zai so sanin alaƙarta da Mimi, tun da shi bai santa ba. 
“Mimi kakar ki ce?” 
Girgiza kai ta yi, sai ta ce. 
“Yayar Mamana ce.” 
“Okay.” 
Ya faɗa sabida baya son cika ta da surutu, itama taja baki ta yi shiru har suka ƙarasa gidan, shi ya ɗaukar mata jakar har cikin part ɗin Mimi, tana shiga ta ci karo da Leemah zaune tana faman latsa computer, ƙasa Husna ta durƙusa ta ce.
“Yaya Leemah ina yini?”
“Yana ganki, ko yau Mimi zata dawo?”
Yaya Lemmeha ta tambayi Husna, girgiza kai Husna ta yi ba ta ce komai ba. 
“Ko ‘yar iskar ce ta gwada miki halin nata?” 
Husna ta yi shiru, Yaya Lemmah ta ce.
“Allah ya kyauta, shi ya dawo da ke?”
“A'a, bai san na tawo ba baya gidan.”
Husna ta faɗa tare da ta shi, Yaya Leemah ta ci gaba da aikinta wani sabon project take shiryawa. 

Sai da Husna ta kwana biyu sannan Mimi ta dawo, Husna ta kasa mantawa da marin da Ashraf ya yi mata, daga lokacin da ta zauna ta yi shiru babu abin da take tunawa sai zafin marin da ya yi mata. Lokacin da Mimi ta dawo gida taga Husna ta yi masifa kamar ta ari a baki, a waya ta kira Asharf ta ce masa lallai lallai yazo gida tana nemansa, haka Dade lokacin da ta shigo ta sami labarin wai Husna ta kwana biyu a gida itama ta yi masifar kamar ta ari baki, lokacin da Ashraf yazo ya gaida Mimi yafi sau biyar bata amsa ba, tun anan ya fuskanci ranta ya ɓaci, a lokacin Husna na cikin ɗaki ma bata san yazo ba. 
“Muhammad Ashraf shine asalin sunanka ko?” 
Mimi ta faɗa rai a ɓace, ɗaga kai ya yi ya kalleta muryarsa na rawa ya ce. 
“Mimi ki yi haƙuri.” 
“Ina tambayarka, so nake kasanar dani nice na haifeka ko kuma matarka Jamila?” 
“Dan Allah Mimi ki yi haƙuri, wallahi yarinyar ce bata ji, kuma wallahi na yi wa Jamilam faɗa sosai da sosai.” 
“Wallahi Ashraf sai na nunawa matarka nice na haifeka.” 
Tana faɗin haka ta tashi ta shige ɗaki, shiru Ashraf ya yi kwata kwata bai gane abin da take nufi ba, amma ya san tabbas abune mara daɗi zata yi masa, wanda bazai so ba. 

Bayan wata biyu.

Zaune take a garden ɗin gidan da yake daga can baya, tana sanye cikin doguwar riga ta atamfa, hankalinta yana kana tsuntsayen da ke wasa a saman wata ƙaramar bishiyar a cikin garden ɗin. 
Gaba ɗaya Husna ta mayar da garden ɗin wajen zamanta, baka taɓa ganinta a cikin gida sai dai idan aiki zata yi ko wani abu, a yanzu ita ce ke yin girki a part ɗin Mimi, Dade ma ta koma part ɗin da zama gaba ɗaya ma. 
Mimi da kanta ta kai Husna wajen Alhaji Musa tin da suka fuskanci lamarin Abba bana wasa ba ne, ta faɗa masa zaman da Husna ta yi a gidan da kuma abin da Abba ya faɗa, Alhaji Musa yaso kiran Abba tun da daman yana da lambarsa, amma Dade ta ce lallai yaje ya same shi ƙafa da ƙafa. Alhaji Musa mutum ne mai sauƙin kai uwa uba kuma mai biyayya, haka ya taka har gida ya sami Abba, bayan sun gaisa da Abba ya sanar da shi yazo bawa Abba haƙurine, amma Abba ya rufe ido ya ce ya shifa yana kan bakansa, a wajenma ya ce shi ya barwa Alhaji Musa Husna baya son sake ganinta har sai lokacin da ta san mutuncin kanta, ranar da ta zama matar aure. 
Alhaji Musa ya ce ya amshi Husna ya kuma gode, ta zama ‘yar sa.

 Tun daga wannan lokacin Husna ta cire rai da sake zuwa gida gaba ɗaya rayuwarta ta canja ta zama wata shiru shiru ko magana yanzu Husna bata ƙaunar yi, bata taɓa tunanin akwai abin da zai rabata da gidansu da ‘yan uwanta ba sai gashi ta jawa kanta bisa taurin kanta, gashi a gida Abba ya ce bai hanasu waya da Husna ba ko gaisawa, amma bai yarda su dinga zuwa gidan da niyar sunje wajenta ba. 
Hakan ya rage musu zuwa gidan sai su kwashe sati ɗaya, biyu ba suje ba. Wannan rashin ganin ‘yan uwan nata yana cikin abubuwan da suka canja Husna daga Husna mai taurin kai da tsiwa zuwa Husna mai shiru shiru, a yanzu abubuwa da yawa Husna zata gani ta yi banza bata tanka ba, gaba ɗaya komai ya fice mata a kai, ta gwammace ma ta zauna a garden ɗin nan tana kallon tsuntsaye. 
‘Yan ajinsu sun yi candy sun bar Munjibir, ita kuwa tana zaune ta ce ba zata koma makaranta ba, Said Kibiya tazo itama kuma taje Kibiya bikin yayar Said Kibiya, anan suka haɗu da Ali Kaita sabida itama tazo daga Katsina, daga bikin Ali Kaita ta biyo Husna gida ta yi kwana ɗaya washe gari Mimi tasa driver ya kaita har Katsina. 
Su kansu sunyi matuƙar mamakin ganin Husna ta zama shiru shiru, babu ruwanta da hayaniya kamar ba Husna mafaɗaciya ba, gwanda ma su ta sake sunyi hira sosai da sosai, amma ga sauran ‘yan makaranta Husna sai ta zama abun kallo, dayawa sun ɗauka jinyar da ta yi ne ya sauya ta. 

Tun da ta zauna a garden ɗin yau ta haɗe kai da gwaiwa, fuskarta a duk ta nuna rashin jindaɗi, tana ta faman tunanin yadda rayuwa ta sauya mata. Duk sanda ta tuna kalaman mahaifinta na cewa ba ya son sake ganinta matuƙar ba a gidan aure ba, sai ta ji tamkar ruwan zafi ake sheƙa mata a ƙirji. Wannan rashin tabbas din da take ciki na makomar rayuwarta, haka wani lokacin takan ɗan tuna kalaman cin mutunci da Jamila ta jefa mata, duk da takan jima ba ta tuna ba, amma yau duk abubuwan sun haɗu sun caɓe mata, tana son gidan tana son komawa gida, tana son ganin Abba, wani lokacin idan abubuwa suka haɗarmata sai ta ɓuya ta yi ta kuka gaba ta ji duniyar ta yi mata ƙunci.
​​A daidai wannan lokacin ne Al Qasim ya taho, shigowarsa kenan gidan ya daɗe a Abuja kusan sati uku, yana sanye da farar shadda yana tafe yana danna waya, Idonsa ya sauka a kan Husna da ke zaune waje ɗaya tamkar wata marainiya.

​Dakatawa Al Qaseem ya yi ya ɗan tsaya a nesa kaɗan da ita, ya ƙura mata ido cike da tausayawa. Yana ganin yadda kafadar ta ke motsawa alamar kuka take yi a hankali.
​Ya shafa sajen fuskarsa da hannunsa na dama, sannan ya tako a hankali har ya ƙaraso kusa da ita, ya zauna nesa kaɗan da ita, dan babu wata alaƙa da zata ba shi damar zama kusa da ita.
​"Sannu Husna..." Muryarsa ta fito a hankali cikin sanyi da taushi wadda ta sanya Husna zabura ta ɗaga kanta da sauri, dan bata ji wani mosti a kusa da ita ba.
​Ganin wanda ke tsaye a gabanta ya sanya ta hanzarta goge hawayen fuskarta tare da ƙoƙarin gyara zamanta. Ta duƙar da kanta ƙasa cikin jin kunya ta ce. 
"Ina yini, Yaya Alkasim..."
​"Lafiya lau Husna," ya amsa mata cikin sanyin murya. Yana kallon fuskarta, kallo ɗaya ya yi mata ya san da damuwa a ranta, bai san zaman me take yi anan ba, amma ya san bana daɗi ba ne, wani irin murmushi ya yi mai sanyi, sanna ya ce.
​"Kada ki damu da komai a rayuwa Husna. Kowane ƙalubale da kika gani a rayuwar ɗan adam, yana zuwa ne domin ya gwada jarumtar da ke tare da shi. Nakan kula da ke lokaci zuwa lokaci kamar zuciyarki na ɗauki da nauyi mai yawa, to ki yi haƙuri ki miƙa komai ga Allah, shi yawan tunani baya haifar da komai sai cutarwa.”

​Husna ta yi shiru, zuciyarta ta harba da ƙarfi. Rabonta da ta ji wani ya yi mata magana cikin yanayi irin wannan na tausayawa itun lokacin da take gida tare da iyayenta. Wannan kalaman na Alkasim sun shiga har can cikin tsakiyar kanta.
​Alkasim ya saka hannu a aljihun rigar da ke jikinsa ya fito da wata ‘yar ƙaramar alewa ledar ta kaɗai ɗaukan ido take yi, ya tsuguna kusa da ita yanda idonsa zai kasance cikin nata idon ba tare da ya taɓa jikinta ba, ya miƙa mata alewar sannan ya ce.  

​"Na san ba lallai kin iya ci abinci ba a yanayin da kike ciki. Amma wannan alewar tana rage ɗacin da mutum ke ji a bakinsa lokacin da yake cikin damuwa, na baki ne ki sha ko saki ji sauyin ɗanɗano a bakinki, sai kuma ki tashi ki shiga ciki, nasan Mimi bata san kina nan ba, ba kya ganin garin yamma ne, kuma yanayin damuna ruwa zai iya sauka kowanne lokaci.” 

​Husna ta kalli alewar, sannan ta ɗaga idonta ta kalle shi. Idanunsa cike suke da tsantsar tausayawa da kulawa ta gaskiya, babu wata alamar raini ko neman alfarma a ciki, muryarta na rawa ta ce. 
​"Yaya Alkasim... Nagode," 
​"Kada ki ce godiya gare ni Husna. Muddin ina gidan nan, babu wani abu da zai sake jefa ki cikin damuwa ba tare da na tsaya miki ba. Ki sani cewa kina da abokin shawara a kowane lokaci."

Yana faɗin haka ya miƙe tsaye, sannan ya yi mata alama da itama ta tashi, ba musu Husna ta tashi, ya ce. 

“ki huce kin ji.”
Kamar mara laka a jiki Husna ta fara tafiya, shima ya juya ya yi ɓangarensu, haka kawai yake jin yarinyar a cikon zuciyarsa, shi dai aure baya lissafinsa amma yarinyar na burgeshi har ya kan jima zai so ya zauna tare da ita su fahimci juna.
​Husna na riƙe da alewar a hannunta tana nufi part ɗin Mimi, a karon farko a cikin watannin nan, ta ji wani irin ɗumi da kwanciyar hankali sun ratsa tsakiyar ƙirjinta. Maimakon fuskar Uncle Dee da take yawan tunani lokacin kuka, sai kawai fuskarta ta kawo mata yanayin murmushin Alkasim da kalaman da ya gaya mata "Muddin ina gidan nan, babu wani abu da zai sake jefa ki cikin damuwa. .."
​Ta buɗe alewar ta saka a baki, tana jin yadda zaƙinta ya shafe ɗacin da ke bakinta, daidai lokacin da zuciyarta ke fara gina wani sabon sauyi game da wanda ke da muhimmanci a rayuwarta.



Legendspen-Sayyid 
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.