Free chapter · Read without an account
Unfiltered Chaos
by NorthernAngel · His Rose
A ɓangaren su Hajiya Sauda kuwa, suna zazzaune a parlourn har lokacin. Hajiya Mai Gado da ƙanwarta Hajiya Turai na zaune gaban center table, sai zabgar high-end pastries da gassasshen naman ragon nan suke yi suna ta faman hira da su Umma Deeza hankalinsu kwance—saboda a cewar Hajiya Mai Gado, ai gidan ɗansu ne! Hajiya Sauda ce dai iced mocktail kawai aka zuba mata take sha a hankali, yayin da ƴarta Amal ko kallo ba ta bi kayan ciye-ciyen da aka jera musu ba, tana ta faman shan ƙamshi. Kusan mintuna talatin kenan cif da shigar Zara da Rahama ciki, amma ko motsinsu ba a sake ji daga ɓangaren ba. Dai dai lokacin aka tashi daga sallar Juma'a, su Hajiya Mai Gado suka soma shirin tafiya gida domin gudanar da tasu sallar, sai dai kash—Rahama ba ta fito ba tukunna, gashi basa son tafiya su barta. Ana cikin haka ne aka yi sallama daga daga bakin ƙofar shigowa, duk da riga an zuge frosted glass door ɗin amma ba a ƙaraso ciki ba. Amsawa su Umma Deeza suka yi da sauri cikin fara'a saboda muryar Mu'azzam da suka jiyo. Shi ya fara tura ƙofar ya shigo, yana ɗan ƙarewa mutanen dake parlorn kallo a tsanake, kafin ya kalli Anne yana faɗin, "Anne, Zafar ne zai gaishe ku." Cikin hanzari ita da su Umma Deeza suka amsa da, "Ah ah, to shigo da shi mana... Bismillah!" Juyawa ya yi—wanda sai a lokacin ma ya lura da zamansu Amal da mahaifiyarta Hajiya Sauda. Ɗan mamaki abin ya ba shi, amma bai nuna komai a fuskarsa ba. Ya ci gaba da takawa zuwa bakin kofar yana cewa, "Zafar, come in." Daga haka ya sake juyowa ya dawo kusa da Umma Deeza ya zauna, tare da kama hannunta a tsakanin nasa, sannan ya hau gaishe da manyan mutanen gurin a taƙaice. "Ina wunin ku?" Kafin ka ce me, Hajiya Sauda ta fi kowa zakewa da hanzarin amsawa. "Lafiya lau, son! Ya kwana biyu?" A taƙaice ya amsa mata da, "Alhamdulillah," ba tare da ya sake maida kallonsa kanta ba. Sannan ya amsa gaisuwarsu Amal da ke ta faman fito da gaba ɗaya fara'arta. Aunt Oma ya kalla ya hau gaishe ta tare da tambayarta ina Mommy Amadi ta amsa sanda tana ciki tana hutawa ne. Daidai lokacin, Zafar ya shigo falon da sallama a bakinsa, muryarsa a ƙasa soft and smooth. Amsa masa sallamar aka hau yi ta kowace kusurwa, yayin da Amrah ta tashi daga one-seater sofa ɗin da take zaune ta koma kusa da Anne ta zauna domin ba shi wuri. Ƙarasowa ya yi ya zauna cikin nutsuwarsa. Hajiya Sauda kuwa, sai zabga fara'a da washe baki take tana yi masa sannu da zuwa cike da girmamawa kamar wani uban dakinta. Matuƙar mamakin ganin Hajiya Mai Gado Zafar ya yi a cikin gidan. Yau ɗin ma a karo na biyu bai shaida Hajiya Sauda ba, har sai da idonsa ya fara sauka kan Hajiya Mai Gado. Ya sake juyowa ya kalli Hajiya Sauda da Hajiya Turai a tsanake—sai a lokacin kwakwalwarsa ta harbo masa mahaifiyar Rahama ce, kuma ya tuno maganar da suka yi two days cewa zasu shigo duba Zara suyi mata barka. Bai kawo komai a ransa ba, kai tsaye ya hau gaishe da su Anne cike da tsantsar girmamawa da biyayya. Daga nan ya maida gaba ɗaya hankalinsa kan Aunt Oma yana ɗan janta hira akan danta (adoptive son) wanda tun kwanaki yayiwa Zara maganar ta hadashi da Zafar he has a business proposal, toh haihuwar Jasmine ita ta dakatar da komai. Matuƙar mamakin irin sakewarsa da sakin fuskarsa a gurin dangin Zara ne ya kama Hajiya Mai Gado—don kuwa ita dai a gabanta bai taɓa sakewa kowa ba da wannan buɗaɗɗiyar fuskar haka ba. Amma gashi tun daga shigowarsa falon yake ta zabga hira da su hankali kwance, ya gama magana da Aunt Oma ya kuma basu labarin Jasmine da yadda take ta girma cikin ƙanƙanin lokaci kamar ba cikin incubator take ba. Daga nan kuma sai musu ya sarfe tsakaninsa da Mu'azzam—wanda ke tsokanarsa a kan wai Umma Deeza duk ta rame tun zuwanta gidan Zara, dan haka ya kamata ta koma gidansa ta huta. Nan take Zafar ya karɓe zancen cike da babatu, yana kafe a kan babu inda za ta je, domin a cewarsa nan ɗin ya fi gidansa kyau da jin daɗi nesa ba kusa ba! Haka dai suka riƙa musunsu cikin masha’a ana ta faman dariya a falon. Har da Amrah data sa baki tana goyon bayan Zafar, sakamakon ikirarin da Mu'azzam ke yi na cewa wai Zara na wahalar da Umman. A gefe guda kuwa, jikinsu Hajiya Sauda ya riga ya yi masifar la'asar—ganin yadda aka share su aka manta da zamansu a falon kamar ma ba su nan a gurin. Hatta su Aunt Oma da Anne duk sun haɗu suna taya su Muazzam, suna cewa ai idan ya ɗauke Ummansa su ma sun wadatar da Zara tsaf. Hajiya Mai Gado dai sai bin kowa take da idanu tana gyada kai cike da tsantsar al'ajabin yadda Zafar ya saki baki bil-haƙƙi yana ta faman zuba hira, sai kare matarsa yake yana kafewa a kan babu inda Umma Deeza zata je ai dan su tazo. Ita dai Umma Deeza sai dariya take yi tana sa baki jefi-jefi, amma a can ƙasan zuciyarta cike take da matsananciyar kewar aminiyarta Maryam—tana ji a ranta ina ma tana raye ta ga wannan ranar itama, wai yau Zaran ta ce ta haihu har a ke wannan taron a gidanta! Ita kuma Hajiya Sauda da mutanenta, suna tsaka da shirin mikewa domin tafiya, sai suka tsinci muryar Muazzam yana tambaya a tsanake. "Sanyi, ina Zara?" Kafin Anne ta ba shi amsa, Hajiya Sauda ta rigayi kowa cafke maganar cikin sauri. "Zara tana ciki tare da Rahma... Sun shiga bedroom ɗinta ne wai za ta nuna mata wani abun gyaran gashi. Suna can dai..." Tun shigowar Zafar falon, sai a lokacin ya damƙa mata dukkan hankalinsa gaba ɗaya, yana jin abin da take faɗa kamar a mafarki ko a almara. Idanunsa kawai ya ƙafe a kanta—ba ya ko ƙyaptawa—baki da hanci a buɗe. Mu'azzam ne ya katse shiru da tsoron da ke neman mamaye wurin, inda ya faɗa cikin ƙasa da murya tone na ayar tambaya. "Tohh...?" Ganin yadda Zafar ya gyara zama, idanunsa cike da razana yana ƙyallara wa Hajiya Sauda kallo, ya sa Hajiya Turai yin saurin sa baki domin neman daidaita al'amura. "Wallahi ai ba komai… Gashin Rahmar ne ka san tabarakallah... Zaran tana ta yabawa, shi ne fa tace mata tana da wata straightener, su shiga ɗaki ta nuna ma..." Ba ta ma ƙarasa da maganar ba, Zafar ya miƙe tsaye a kan ƙafafunsa cikin zafin nama kamar wanda aka tsakura da allura. Cikin wani irin sauri ya nufi hanyar private suite ɗin Zara. Kafin ka ce me, ya riga ya kutsa kai cikin lafiyayyen lounge ɗinta, ya shille kai tsaye zuwa babbar ƙofar bedroom ɗinta. Yana ƙarasowa tafe da numfashi a sama, ya murɗa handle ɗin ƙofar—sai dai ya ji ta a kulle gam, deadlocked! Wani gigitaccen salati ya buga a cikin zuciyarsa gami da gumi mai sanyi da ya soma karyo masa, yanzu ita Zara yaushe tayi lafiya da karfin rigima? Ita har ta manta halin da suka fito? Idan wani abu ya same ta fa? Kuma so take ta takalo masa Yemma yana zamansa? Cikin bacin rai ya hau dukan ƙofar yana ƙiran sunanta cike da tashin masifa. "Zara, unlock this door this instant! Do you hear me? Open it now!" Haka ya riƙa pounding ƙofar bil-haƙƙi cike da fargabar kar reshe ya juye da mujiya tunda ba lafiya ce ta isheta ba, amma ko alamar akwai mai numfashi a cikin ɗakin babu. Mu'azzam ne ya biyosa ciki shima cikin mamakin yanda ya taho nan din. Shigowa yayi ya karaso bakin kofar yana tambayarsa, "Wai me ke faruwa ne?!" Zafar ya juyo da fuskarsa da ta riga ta sauya launi, ya kalli Mu'azzam cikin wata irin nutsuwa ya fada mai, "She locked it! The door is completely deadlocked from the inside!" Shiru Mu'azzam ya yi yana jefa wa ƙofar kallo cikin daskarewa, sai a lokacin shima kansa wani babban alarm ya hau ƙara da sauri a cikin kwakwalwarsa. Sai a lokacin ya fahimci
irin danyen aikin da hatsabibiyar yarinyar ta shukawa Rahama da iyayenta. Cikin sanyin jiki shima ya ƙarasa jikin ƙofar ya soma duka yana ƙiranta. "Rose, come on! Are you in there?! Unlock this door right now!" Nan ma shiru babu amsa, sai shiru kawai ke fita daga ɗakin. Haka suka riƙa dukan ƙofar suna ƙiran sunanta. Kafin ka ce me, har Umma Deeza—wadda hankalinta sam bai kwanta ba tun ɗazu—ta biyo bayansu cike da fargaba. Haka suka taru a bakin ƙofar suna ta bugu cikin tashin hankali, kafin daga baya Zafar yace yana zuwa, zaije bangarensa. Daga can ciki kuwa, a daidai lokacin da Zafar ya ƙaraso bakin ƙofar ya fara knocking bil-haƙƙi, a daidai lokacin ne Rahama ta ƙwalla wata gigitacciyar ƙara gami da miƙewa tsaye jikinta na wani irin rawa da kyarma. Cikin rawar murya da tsantsar razana take kallon Zara, tana faɗin, "What did you do?! Oh my god, what have you done, you fucking bitch?!" Ta ƙarasa maganar tana tura Zara baya da wani masifaffen ƙarfi, wanda hakan ya sa Zara ja da baya sosai har tana buguwa da glass cabinet ɗin da tsadaddun perfumes ɗinta ke jere a kai. Cikin ɗan mamaki Zara ta ɗago tana kallonta—har lokacin da heavy-duty shears ɗin da yankakken gashin Rahama a maƙale a hannunta. Rahama dai ta riga ta gigice gaba ɗaya, sai ihun gaske take zabgawa tana shafa kan nata da ke guntule. Sake isowa inda Zara take tsaye ta yi, ta sa hannu biyu ta kama wuyan silk camisole ɗinta, tana sake maimaitawa cikin tsananin hauka. "Look at what you did to my hair, you psychopath! How dare you cut my hair?! Wallahi sai na kashe ki yau!" Zara, da ke bin ta da wani calm, ice-cold kallo, tayi magana cikin sanyin murya tana kanne ido daya. "Saki mun riga." Ƙin sakinta Rahama ta yi, tana ƙara damƙe wuyan rigarta tare da fara ƙoƙarin ƙwace shears ɗin da ke hannun Zara da hannunta guda. Cikin warning tone Zara ta sake cewa, "I said get your hands off my clothes. Seriously, don't push me to do something that'll make everyone look at me like I'm the heartless one here." Rahama dai na ta ƙoƙarin ƙwace scissors ɗin, yayin da Zara ta riƙe shi gam a hannunta. Haka suka riƙa kokuwa a tsakiyar glam room ɗin, Rahama na wani irin gurzar kuka kamar ranta zai fita saboda tsantsar takaici ga kuma karfinta da Zara tayi obviously. Tura ta Zara ta yi baya kaɗan, trying her absolute best kar ta ji mata wani ciwo. Cikin ko-in-kula ta ce, "Ki fitar min a gida! I'm warning you, don’t you ever come near me or try me like this again." Ina! Idanun Rahama sun riga sun rufe da wani masifaffen rage; ta sake nufo Zara gaba ɗaya ta hau kokuwa da ita tana ƙoƙarin ƙwace shears ɗin ko ta halin ƙaƙa. Tura ta Zara ta sake yi—wannan karon da iya dukkan ƙarfinta—wanda hakan ya sa Rahama faɗuwa ƙasa tim! Sannan kanta ya bugu da karfi ta kuma buge heavy ring light ɗin da ke ajiye a can gefe ya fadi kasa. Wani sabon ihu Rahama ta sake bugawa tana ɗago kanta da ya daki ƙasa da ƙarfi. Zara dai ko kallo ba ta bi ta da shi ba, ta wuce zuwa bakin ƙofar tana faɗin, "Kin gani ko? You don't want to see that side of me, trust me. I will literally beat the living shit out of you." Daga haka ta nufi hanyar fita, sannan ta juyo tana kallon inda Rahama ke zaune a ƙasa ta dafe kanta idanunta a runtse, da alama tana cikin matsananciyar azaba. Cikin wata calm, cold voice Zara ta ce, "Zo ki fita..." Cikin ƙarfin hali da kukan azaba, Rahama ta faɗa da ƙarfi, "Wallahi babu inda zan je sai na rama! You're not getting away with this, wallahi!" Zara ta gyada kanta a hankali, muryarta a lafe, "Okay, bet. Go ahead." Daga haka ta koma gaban Rahama, ta sunkuya tana miƙa mata shears ɗin hannunta. "Gashi toh. Tashi ki rama." Cike da wani ƙarfin hali da zafin rai, Rahama ta karɓi shears ɗin daga hannun Zara, sannan ta miƙe tsaye ta nufo Zara cikin zafin nama. Tana ƙarasowa ta ɗaga scissors ɗin ta ɗaura shi gab da gashin Zara! Sai dai kafin kaifin scissors ɗin ya kai ga sauka a kan gashin, Zara ta sa hannu guda ta tare hannunta, tare da murɗe hannun da wani karfin gaske—wanda hakan ya sa Rahama sakin wata gigitacciyar ƙara saboda tsananin zafi! Tura ta Zara ta sake yi da ƙarfi; wannan karon, custom island ɗin glam room ɗin ya daki ƙugunta da ƙarfi, yayin da hannunta kuma ya tunkuda display bust ɗin da ke ɗauke da tsadaddun short hair wigs a gurin, komai ya warwatse a ƙasa! Cikin zafin murya wannan karon, Zara ta fara magana idanunta sunyi jawur. "Make one more reckless move and I swear you will receive the beating of your life! Do I look naive to you? No, you thought I was dumb, right? Yeah, that's it—you really thought I was dumb! You genuinely thought you could infiltrate my territory and claim my husband without paying a heavy price for it. You only got lucky because my hands were tied with my pregnancy when you sneaked in, because under normal circumstances, you wouldn't have survived a week. But your grace period is officially over because you have my undivided attention now. This conflict has only just begun! Today I took your hair; tomorrow it'll be something far more devastating to your entire existence. I won't rest until you voluntarily run out of this arrangement with your own two feet. Shege ne zai fasa ni da ke! Just sit back and watch me completely dismantle your life while the whole Galado family stands by and watches in absolute silence. Not even the mother-in-law who smuggled you into this estate can do shit to me!” Daga haka ta juya ta isa bakin ƙofar glam room ɗin ta sake buɗewa, tana faɗin, "Zo ki fita! If I reach the count of three and you're still in my space, I promise you I am fetching Zafar's clippers from the bathroom and shave your entire head bald—including your eyebrows." Daga haka ta fara ƙirga cikin ɗaga murya. "One..." Ta ba ta space na kusan minti ɗaya, sannan ta sake cewa, "Two..." Rahama ta miƙe a zuciye ta nufi gaban vanity mirror, ta janyo mayafinta ta lulluɓe kanta tsaf domin ɓoye ainihin ɓarnar da aka yi mata. Daga nan ta juyo ta nufo Zara; tana ƙarasowa bakin ƙofar ta tsaya, suka kafawa juna idanu. Cikin kukan da take har sannan, Rahama ta ce, "Wallahi wallahi, sai na nuna miki ni ba Salma ba ce! Kuma zama daram a cikin gidan nan—har da ƴaƴa ma! You can either choke on your own bitter heart and die, or you can pack out if you can't handle it! If your husband actually loved you and was truly wrapped around your finger, you’d make him divorce me, or at least stop him from stepping foot in my house! You’re just a toxic, psychopathic bitch who doesn't even know God! Jahila kawai!" Daga haka ta ɓangaje Zara da ke tsaye tana ɗan tabe baki cike da rainin hankali. Ta fice a fusace ta nufi babbar ƙofar master bedroom ɗin, har lokacin kukan tashin hankali take zabgawa ba ƙautautawa. Cikin hanzari Zara tabi bayanta, ta shige gabanta zuwa bakin ƙofar, ta hau unlocking ƙofar da kanta ba tare da ta ce mata uffan ba. Daga waje kuwa, a daidai lokacin da Zafar ya juya zai nufi ɓangarensa domin duba ko master key card din gidan zai iya bude kofar, sai suka ji ana unlocking ƙofar ta ciki. Cikin hanzari ya juyo ya dawo bakin ƙofar idanunsa kyafe. Ana gama buɗewa, kafin ma Mu'azzam da hannunsa ke kan handle din ya mirda ƙofar, aka riga shi mirdawa ta daga ciki. Tana buɗewa, sai ga Rahama ta fito kamar wadda aka hankado ta daga wuta, har lokacin wani irin kuka mai ban tausayi da raɗaɗi take zabgawa. Nan fa wurin ya kacame da hayaniya da cakuɗewar tambayoyi na: "Mene ne? Lafiya?! Me ya faru?!" A daidai lokacin sai ga Aunt Oma itama ta shigo suite ɗin sakamakon jin shirun ya yi yawa. Rahama dai ƙoƙarin ƙwace kanta take daga riƙon da Umma Deeza ta yi mata tana ta tambayarta abin da ya faru. Daga nan idon Rahama ya sauka kan Zafar da ke tsaye a gurin kamar an dasa shi, ya ƙura wa bakin ƙofar ido yana jiran ya ga ta ina Zara za ta ɓullo. Da wani irin ƙarfi Rahama ta bige hannun Umma Deeza, ta ƙarasa gaban Zafar da hanzari ta faɗa jikinsa, tare da sake fashewa da wani irin kuka mai tsananin ban tausayi da ban tsoro. Aunt Hannah ce ta fito daga ɗakin da ke cikin parlourn na Zara—wanda nursery ne aka yi wa baby Jasmine, inda yanzu ma wasu kayanta da suka iso cikin dare ne ta shiga ɗakin tana jerawa a closet. Fitowarta ke nan ta ji marayan kuka da hayaniyar da ke tashi daga ƙofar dakin Zara, cikin hanzari ta ƙarasa domin ganin abin da ke faruwa. Tana ƙarasowa, ita ma ta tarar da cakwakiya; har lokacin tambayar Rahama ake me ya faru, yayin da Aunt Oma ke daka wa Zara tsawa—wadda ke ɗan leƙo kanta daga cikin ɗakin—tana cewa ta fito ta yi bayanin abin da ya faru. Cikin sauri ita ma Aunt Hannah ta gauraya tana tambayar: "Mi ka hwaruwa ne?!" Shi dai Zafar, kamar an dasa shi a wurin ba ya motsi. Bai rungume Rahama ba, haka kuma bai ce mata uffan ba. A hankali ya sa hannunsa ya zare sharsharan mayafin abayar da ke kanta—wanda ke rufe da gashinta—nan take asiri ya tonu, guntun gashin da aka aske ya bayyana radau ba sauran doguwar jelar gashi! Umma Deeza, da idonta ke kanta, ta saki wani uban salati da ya sanya kowa daskarewa a wurin, wanda hakan ya maida hankalin kowa kanta. Cikin wani irin tsantsar shock, Aunt Oma ta furta, "Jesus Christ..." slowly, sannan ta juya ta kalli Zara da ke ɗan leƙo kanta tana kallonsu daga cikin ɗakin kamar barauniyar da aka ritsa. Mu'azzam ne cikin zafin murya ya ce, "Zo nan, Zara! Step out of that room!" Cikin hanzari ta maida kanta ciki tana turɓune fuska ta ƙi fitowa. Ba don Umma Deeza da ke tsaye a bakin ƙofar ta ba wa ƙofar baya ba, da rufe ƙofar za ta yi tasa lock. Umma Deeza ce ta juya tana kallon cikin ɗakin ita ma, ta yi magana da rawar murya. "Me kikayi haka, Zara?! What is wrong with you?! Why did you do this to her?!" Rahama dai har lokacin sautin kukanta na tashi cikin wani irin kuna da takaici. Cikin tsawa Aunt Oma ta yi mata magana. "Pụta ebe a ugbu a! Ị naghị anụ ihe?!” A ɗan razane Zara ta fito, saboda Aunt Oma na ɗaya daga cikin mutanen da take shakku tun tana karama, shi ya sa ma tun farko ta labe a ciki. Kowa idonsa na kanta gaba ɗaya, banda Rahama da kanta ke manne a ƙirjin Zafar tana rusa kuka mai ban tausayi. Zara ta fara bin kowa da kallo guda-by-guda har suka haɗa ido da Zafar. Kallon ta yake shi ma with a completely blank expression—ba ka isa ka ce ga abin da ke ransa ba, kawai dai tsaf yake bin kowane move nata da kallo. Aunt Hannah tayi magana cikin gayya. "Ya aka yi ɗan gashin nata ya zama haka? Me ya faru, Rose?!" Zara dai na tsaye ta yi folding arms ɗinta a ƙirjinta, ta ɗan kalli Aunt Hannah sannan ta ɗauke kanta gefe guda tana turo baki cike da taurin kai. Cikin wata gigitacciyar tsawa, Mu'azzam ya ce, "Ba magana ake miki ba?! Don't tell me you committed this petty act!" A wani irin zuciye, Zara ta juya da sauri ta nufi cikin ɗakin za ta koma ta rufe kanta. Umma Deeza ce ta yi saurin tare ƙofar, cikin muryar da babu alaman wasa ko kaɗan a ciki ta ce, "Turn right back around and answer your brother's question this instant!" Girgiza kai Zara ta yi, sannan cikin ɗaga murya da ke cike da raɗaɗi ta fara magana. "No, Umma, I refuse to justify myself to him! I owe absolutely no one an explanation. If he is so deeply concerned about her well-being, he can ask her directly. It is blindingly obvious that her feelings matter more to him than mine. I literally just walked out of that room, and not a single soul has asked if I'm okay—including my own brother! But honestly, I shouldn't even be surprised. You didn't even have the balls to question your own cousin when he decided to go marry your ex-wife's sister! Everyone was totally fine with it, and you all expected me to just sit back and take it. I was pregnant, for God's sake! And not one person from their family tried to put a stop to this madness. No one stood up for me!" Cikin zafin muryar Mu'azzam ya katse ta da kaifin harshe. "Don't you dare displace your husband’s betrayals onto me, Zara. Zafar is an autonomous man. If he chooses to cross ethical lines by marrying my ex-wife's sister, I have absolutely no jurisdiction over his choices. Ko kuwa ke yarinya ce har yanzu da sai na shigar miki faɗa?! Why don't you confess to Umma right now how many times I begged you to choose your peace and walk away?! You chose to internalize that trauma during your pregnancy; no one martyred you. But martyrdom is not a license for malice. Pain does not justify you to turn into a violent, petty criminal. If the weight of this polygamy is too much for your mental stability, then walk away! But I will never coddle you while you project your rage through these malicious, unhinged tantrums. I refuse to stand by and watch you compromise your integrity by acting out like a complete lunatic!" Sai a lokacin Zafar ya motsa daga daskarewar da ya yi. A hankali ya zare Rahama daga jikinsa, sannan ya kalli Zara da ke tsaye a bakin ƙofa gaban Umma Deeza tana ta ƙoƙarin maida hawayenta. Cikin wata calm, authoritative voice ya ce, "Go inside." Wani zafaffen kallo ta jefa masa mai cike da masifaccen kishi, ta buɗe baki za ta yi magana, sai dai kafin ta kai ga furta uffan, Zafar ya katse ta da cold voice dinsa. "Not another syllable. Walk through that door and go inside." A hankali Umma Deeza ta matsa daga bakin ƙofar, sannan ta sa hannu ta janyo Zara suka shige ciki tare. Suna shiga, Zafar bai yi wata-wata ba; ya ƙaraso bakin ƙofar, ya sa hannu ya janyo ta ya kulle gam daga waje. Daga haka ya juyo, idanunsa na ƙeƙashe a kan Mu'azzam. "I will advise you to step back and stay entirely out of my marriage. You just got finished declaring that she isn’t a child, meaning if she ever decides to walk away from me, she has the autonomy to do so—but the reality is, she is still right here by my side. She chose to stay under my roof. So stop overstepping, stop trying to plant seeds of doubt in her mind, and stop trying to orchestrate her exit from the life we are building." Daga haka ya kalli Aunt Hannah da Aunt Oma, cikin muryarsa ta natsuwa da sa girmamawa ya ce, "Please, let’s just drop this subject right here. What’s done is already done, and pressuring her or demanding explanations will only worsen her mood and trigger another defense mechanism. Let us just give her space to breathe and leave the rest to God... Allah ya shiryata." Duk suka amsa da “Amin” cikin matukar sanyin jiki. Daga haka ya maida kallonsa kan Rahama da ke gefe tana kuka, ya fara mata magana cikin fada. "You wanted a reaction from her, right? Well, congratulations, you got it! In broad daylight, you and your family thought it was a brilliant idea to pull up to my home just to antagonize my wife, right? Well, look at the results. You finally got the reaction you were fishing for. So wrap that cloth around your head, collect your family, and clear out of her property immediately." Bai jira amsa ko nuna tausayi ba, ya nuna mata babbar ƙofar fita alamar ta fice yanzu-yanzu. Wani irin marayan kuka mai sauti Rahama ta fashe da shi—wanda sai da ya firgita kowa a gurin! In banda Aunt Hannah da ke tsaye cikin tsantsar farin ciki da murna a zuciyarta, har Aunt Oma ma ta ji daɗin matakin da Zafar ya ɗauka; dama haushin Zaran da ta ji a farko shi ne kar danyen aikin da ta yi ya ja mata matsala da mijinta. Da gudu Rahama ta fice daga suite ɗin jikinta na wani irin azababben kyarma. Zafar na ganin fitarta, ya kalli Aunt Hannah da ke tsaye, ya fara magana cikin ƙasaitacciyar muryarsa ta umarni, "Please deadlock the entrance to this suite right now. If those people refuse to leave the premises and start causing trouble, order the staff to escort them out. Tell the guards to unleash the dogs if anyone makes a reckless move. Just do not let any of them into this sector." Aunt Hannah sai gyada masa kai take yi, tana matuƙar ƙoƙarin danne tsantsar farin ciki da annashuwar da ke maƙale a zuciyarta. Daga haka Zafar ya kalli Mu'azzam yace, "Muje." Ɗan shiru Mu'azzam ya yi a tsaye, saboda tunanin masifa da rigimar dake shirin ɓarkewa yanzu da zarar Rahama ta ta faɗawa iyayenta dake can parlour. Amma kuma da ya sake auna lafuzzan da Zafar ya jefa wa Rahamar ɗazu, sai ya ga ai tsantsar gaskiya ya faɗa mata! Sam ba domin Allah suka tattaki suka zo gidan nan ba—kawai dai sun haɗu da daidai da su ne. Domin kuwa ita Zaran ba kanwar lasa ba ce, tsantsar rashin sani ne kawai ya kawo su. Gyada kai Mu'azzam ya yi a hankali, sannan ya yi gaba abinsa, Zafar na biye da shi a baya suka fice daga bangaren. Koda suka fitowa zuwa babbar parlourn saman, tuni rigima da hayaniya mai masifan sauti ta riga ta kaure a wurin! Hajiya Sauda babu abin da take yi sai masifa da kutuntuma ashar. Su Mommy Amadi data fito, Anne, da Amrah kuma na tsaye a gefe guda sai bin su da kallo suke yi, har lokacin fuskokinsu ɗauke da tsantsar shock na ɓarnar da aka yi. Hajiya Mai Gado ce ta fara hango fitowar Zafar. Cikin hanzari ta numfasa tana ƙwalla masa kira da babbar murya, sai dai ko kallo guda bata samu daga gare shi ba—ya shile ta can gefe kamar bai san ana hayaniya a falon ba. Cikin sauri ya shige elevator ɗin gidan ya danna alamar sauka ƙasa. Mu'azzam kuwa, hankalinsa a kwance ya nufi lafiyayyun staircases ɗin gidan ya soma taka daya a hankali yana sauka. Turus Hajiya Mai Gado ta yi a daskare, tana bin Zafar da wani irin kallon al'ajabi gami da mamakin yadda ya shige elevator ya barta tana biye dashi tana kira. Cikin tsantsar tashin hankali da fargabar abin da ke shirin faruwa, ta hau lalubar lambar Yemma a wayarta cikin rawar hannu domin sanar mata. A ciki kuwa, tuni Aunt Hannah da Aunt Oma suka fito falon suka hau musayar yawu da su Hajiya Sauda. Kafin ka ce me, gagarumar rigima ta ɓarke a tsakiyar lafiyayyen parlourn, inda hatta Amal da Rahama suka hau sarfe-sarfen ashar gami da zazzaga cin mutunci, balle kuma iyayensu da suka cire sauran mutuncin da ke fuskokinsu. Bala'i ne ya kaure ba ɗan ƙarami ba a cikin gidan—akan wai lalle sai a bar su sun sa ƙafa sun shiga ɓangaren Zara! Su dai su Aunt Hannah suna tsaye ram da su a ƙofar gaban hanyar, ba su ba su damar wucewa ba. Hajiya Mai Gado kuwa na manne a kan waya ita da Yemma—wadda ke can gida tana jiyo dukkan gaba ɗaya wainar da ake toyawa ta wayar. Maids kuwa tuni suka shigo gidan su kusan su shida, suna ƙoƙarin korarsu da fitar da su waje a tsanake, amma har mari da haure-haure iyayen ke kai musu. Da ba don ma suna tsoron abunda zai biyo baya ba da tuni sunkai duka amma suna sane da cewa itayen Muazzam Galado da iyalan Amadi ne suke fada da su. Kawai dai masifa suke yi ta hauka! Suna cikin wannan gigitaccen hayaniyar sai ga jami'an tsaro (securities) na gidan sun ƙaraso shigowa gadan-gadan. Dama can Zafar ya riga ya yi zargin irin wannan halin da za su nuna, shi ya sa ya ba da umarnin a turo su cikin gidan da gaggawa. Duk da haka ba su fita ba; ba abin da suke yi sai zage-zage da furta kalaman rashin mutunci suna cewa in an isa a fito musu da Zara. Kusan tsawon awa ɗaya cif suna wannan cin mutuncin da tashin hankalin. Sai da suka tabbatar dai babu mai barinsu su taka kafa ciki ballema suka Zaran, sannan suka juya akalarsu zuwa ga fara fashe-fashen fitilun da tsadaddun kayan parlourn. Wannan karon tuni Mommy Amadi da ke zaune a gefe ta miƙe tsaye a fusace, ta taka musu birki tare da musu kashedin cewa duk abin da suka kuskura suka fasa a gidan, to wallahi sai ta kullesu a gidan yari taga mai fito dasu a kasarnan! Ba ma su samu nasarar fasa komai ba saboda securities ɗin da suka tare ko ina suka hanasu kwakkwaran motsi ma. Daga nan kuma securities ɗin suka fara turusawa gaba suna tura su zuwa waje. Daman da farko suna ƙyalewa ne saboda sun san surukan gidan ne suma, amma da suka ga abin nasu ba na girma da arziki ba ne, sai suka hau tura su zuwa waje a wulaƙance—wani irin abin kunya ga duk wani mai tunani da ya san ko su wanene! Hajiya Mai Gado ita dai ba ta shiga faɗan kai tsaye ba; tana manne da waya da Yemma tana ba ta labarin kowace motsi na abin da ke aukuwa. Dan haka yanzu koda securities ke tura su waje gaba ɗaya, tana biye da su ne a baya kawai tana kwarara wa Yemma bayanin gashinan ansa ana musu korar kare. Ita kuwa Amal, har sai da ta kai ga ta sha azababben mari a hannun ɗaya daga cikin jami'an tsaron sakamakon neman kawo raini da tayi masa, sannan ta nutsu ta shiga taitayinta. Daga nan kuma Hajiya Sauda ta maida masifar faɗanta gaba ɗaya kan wannan security ɗin a tsakiyar makeken compound din gidan. Da hayaniyar ta gauraye faɗaɗɗen compound ɗin, tuni Zara da ke zaune a saman lafiyayyen terrace ɗinta ta miƙe tsaye tana isa bakin gurin, ta hau kallon dukkan abin da ke aukuwa da idanunta cike da kwanciyar hankali da nutsuwa. Suna tsaka da wannan cin mutuncin, kafin ka ce me, tuni gigantic attack dogs ɗin gidan da ke can bayan gidan a ɓangaren Zafar suka fito a guje sakamakon hayaniyar da suka riƙa jiyo gidan yana amsawa. Ai kuwa suna ƙarasowa cikin compound ɗin, ba su yi wata-wata ba suka nufe su gadan-gadan suna haushi gami da gurnani kamar zakuna! Kafin ka ce me, kowa ya tarwatse a rude! A taƙaice dai, su Panther ne suka kori su Hajiya Sauda daga gidan cikin wani irin mugun guje-guje. Ita kuwa Hajiya Turai, tsabagen masifaffen tsoro, komawa cikin gidan ta yi a guje ta labe kitchen, har sai da securities suka dauke karnukan bayan kowa ya watse a compound ɗin, sannan wata maid ta samu ta fito ta fice daga gidan gaba ɗaya, hawayen takaici da sauran kunya sharkaf a fuskarta! Ranar dai haka aka yi ba daɗi a cikin estate ɗin, sai dai sam babu wanda ya sani an estate din—kowa sha'anin gabansa kawai yake gudanarwa. In ka ɗauke mutanen da abin ya shafa kai tsaye, sai kuma Hajiya Yemma da idan ranta ya yi dubu, to ya gama ɓaci matuƙa da abun da Zara ta aikata. A ɓangaren gidan Zara kuwa, bayan an gama watsar da su Hajiya Sauda waje a wulaƙance, hankali kwance suka sauko suka zauna a babban parlourn kasa suka hau hira gami da kwasar dariya kamar sam babu abin da ya faru! Saboda su ko takan zage-zagen rashin ɗa'ar da su Hajiya Sauda suka riƙa jera wa ba su bi ba; korarsu kawai suka rikayi daga gidan, balle kuma Mommy Amadi da ko a jikinta, ba ta ma jin abunda ake fada a cikin harshen hausa. Zara ita ma tuni ta fito daga bangarenta ta sauko ita da Umma Deeza, suka zauna cikin mutane suka hau hirar abin da ya auku. A tsanake, cikin sanyin murya da salon makirci, Zara ta hau sharara musu ƙaryar—wai Rahama ce ta fara tsokanarta har ta tunzura ta, shi ne kawai ta ɗauki shears ta guntule mata gashin! Anne ce ta girgiza kanta tana gyara zamanta, ta fara magana a tsanake. "Yanzu dan Allah da ace mutanen ƙwarai ne, ba sai a zauna a yi magana ta fahimta ba? A matsayinmu na manya, mu saurari bayanin yaran duka biyu, mu ba mai gaskiya gaskiya, sannan mu kuma mu yi wa ɗiyarmu hwaɗa tun da an yi musu laihi kam. Amma su sam ba su gaji mutunci ba ashe! Kawai suka hau baci kamar wasu tsohhin ƴan tasha!" Aunt Oma ta amshe zancen da hanzari. "Yo mene ne su in ba ƴan tasha ba?! Ai kina ganin mutanen nan, kinsan ilimi da tarbiyya sun yi ƙaranci a tare da su wallahi! Ji dai maganganun da suka ta yadawa sa'ad da suka shigo—har da cewa wai Zara ta dawo gidanta gudanar da jego, kamar ba haihuwar fari ba!" Umma Deeza ta karɓe zancen tana wani murmushin ƙasaita. "Har da wai ta tashi ta tafi ƙar mijinta ya dawo ba ta nan! Sai ga miji na zuwa ya rikice daga jin Mu'azzam na wa Zara faɗa. Tuni ya ƙorata waje, har Allah ya ƙara!" Nan fa suka hau kwasar dariya gaba ɗayansu har da Zara. Cikin dariya Amrah ta sa baki: "Ai ni tun farko na san ba zai yi komai ba wallahi... Gashi dai Rose ta aske ɗan gashin da yake sawa a miƙar masa!" Aunt Hannah ta fashe da wata muguwar dariyar keta tana fadin, "Ai kin yi mun daidai wallahi, Zara! Ni uwar ita tahi ba ni mamaki... Kina gani kinsan ba don Allah ta zo barkan nan ba. Wai su marasa mutunci!" Haka dai suka riƙa gudanar da hirar cikin tsantsar murna da annashuwa suna dariya ransu fes—musamman Zara da ke ta faman tsare tsaren yadda za ta tare Zafar kafin lokacin zuwansu duba Jasmine ya yi, domin ta tsara masa nata side of the story ɗin tsaf a nitse dan daga yau ya dena kwana gidan Rahama sai dai in ba sunanta Zara Amadi ba...