Free chapter · Read without an account

DA JININSA NAKE RAYUWA

by Sayyid · DA JININSA NAKE RAYUWA

A hankali ya buɗe idanunsa da yaji sun yi masa nauyi sakamakon shigar marin da yaji, wani irin jiri yana ɗibarsa cike da girmamawa ya ce.

“Hajiya gani.”

Harara ta sake watsa mai kamar wadda ta gansa a karon farko, cikin wuci ta ce.

“Al Qaseem! Al Qaseem, sau nawa na kira sunaka?”

Kansa yana ƙasa ya ce.
“Biyu Hajiya.”

“To karka bari na kira na uku, domin kwata kwata bazan kira shi da alheri ba, tun ina maka magana da hausa ka fita sabgar waccan mitsiyaciyar yarinyar nan ta wajen Bilki, idan har ba haka ba wallahi zanyi maka abin da baka taɓa tunani ba.”

Shiru ya yi ba tare da ya ce komai ba, bai san aina Hajiya ta ji wannan maganar ba, yaso Daddy ne da kansa ya yi mata maganar gashi taji, shi bai da matsala da ita tun da har Daddy ya ce ya nemi yardar Husna ai angama magana, shi dai kawai zai lallaɓata ne, yasan Daddy yafi ƙarfin duk wani taurin kai nata, ita kanta ba zata ja da maganar Daddy ba, ba tare da ya ce mata komai ba har ta gama hayagagarta ya miƙe ya fice, yana fita ta zauna ya haɗe kai da gwiwa, ina zata sa ranta ɗanta da yake a nutsi ta ci buri a kan sa shine zai ƙare a kan waccan ‘yar, dangin Bilki sun ƙwace komai kenan? A fili ta furta.

“Allah Ka tsinema Bilki, da zuri’arta, har Hajiya babbarma, kishiya ai kishiya ce.”
Sai kuma taja wani dogon tsaki, ta rasa inda zata sa kanta duniyar gaba ɗaya ta yi mata zafi, yanda ta ci dogon buri a kan Al Qaseem, chaɓ. 

Al Qaseem na fita daga ɓangarensu ya yi ɗakinsa, yana shiga ya faɗa kan gado ba tare da ya cire ko takalmin ba, wata irin tsawa yake jin kansa na yi tamkar zai tsage gida biyu, kalaman Hajiya sun sanya masa tsoro da firgici, ya yi tunanin yanda take yawan yi mai zancen aure zata yi farin ciki idan ya kawo mata Husna ya ce zai aura, sai dai yaga akasin haka, amma kuma yana kyautata zaton inda ta sami labarin an bata ba daidai ba. 

Hannu ya sa ya sake dafe kansa da ke wani irin sara masa da ƙarfin, ji yake kamar ƙwaƙwalwarsa ce zata fashe, dole ya samawa kansa lafiya ta hanyar dakatar da duk wani tunanin da yake yi. 


09:30pm.
Alhaji Musa Ɗankaka da kan sa ya shigo ɓangaren Mimi, ganin yau ita ce da shi amma bata samu shigowa ba ya san dole ba lafiya ba, duk da ya yi waya da Leemah ta sanar da shi ta dawo gida amma ya san hakan ba shine zai hana Mimin zuwan ba, yafi tunanin ƙafar ce ta matso mata.
 
Lokacin da ya shiga falon ya yi daidai da lokacin da Ashraf ke shirin zama, shima shigowarsa kenan yaje ɓangaren Abba baya nan shine ya yo nan, shi kuma Abba sai da ya fara zuwa wajen duka matan nasa, nan ne ƙarshe. 
Abba yana shigowa duk suka miƙe suna gaidashi har da Husna, bayan sun gaisa ne Husna ta miƙe zata shiga ciki ya ce.

“Zo nan Asma’u.”
Dawowa ta yi ta zauna kanta na ƙasa, bai fara magana da ita ba ya ce da Mimi.
“Ƙafar ce?”
Kai ta gyaɗa masa, ba iya ƙafar bace har da ɓaci rai da yadameta, shi ya sa ta ce da Ashraf lallai yazo ya sameta gida tana so su yi magana. 

“Allah Ya ƙara sauƙi, ai tun da naga banganki ba na ce to jikin ne, yaushe zaku koma wajen likitanan?”
“Sai nan da sati biyu.”
Mimi ta faɗa, sannan ta sake cewa.
“Kun yi magana da mijin Halima ne?”
Girgiza kai ya yi, kafin ya ce.
“Ya rubuta mata takarda, to neman me zamu yi masa? Mu ce ya mayar da ita ko me? Tun da har yana ganin ya yanke hukunci da yaga ya dace ba shikenan ba, nifa babu wata yarinya da zamanta zai dameni, da suje su hulaƙanta gidan aure gwanda su dauwama a gabana.”
Shiru Mimi ta yi, dan ita batasan abin da zata ce ba, amma ita bata ga amfanin zaman gidan ba, Alhaji ne ya sake cewa.
“Mun yi magana da Al Qaseem, ya sanar da ni sun daidaita da yarinyar wajena Husna ko? Na ce masa wannan ai ta kwana gidan sauƙi, tun da Malam ya damƙamin ita ai anyi mai wuyar, ko kin san da maganar?”

Husna ji ta yi kamar ta tashi ta gudu, sabida wata irin kunya data kamata, shi kam Alhaji babu ruwansa mutum ne mai matuƙar wayewa, abubuwa dayawa bai damu da su ba, zai iya zama tare da surukansa ya yi hira idan har yana dasu, duk da yana da ilimin addini kuma yana da riƙo da addini, amma wannan wayewar ta taɓa mu’amalalsa dayawa. 

“Eyh Alhaji, nima na samu labari amma ai ga Husnan anan ko?”
Mimi ta faɗa tana nuna Husna da ta yi tsuru tsuru, Leemah ji ta yi ranta ya ɓaci sabida ta san wannan abun ma ba mai faruwa ba ne, dan Hajiya Kubrah ba zata taɓa barin faruwar hakan ba. Ashraf kam wani abu yaji banbarakwai, haushin Al Qaseem ya cika shi, duk da daman ba magana suke ba, kuma shine abokin tsamarsa a duk gidan, basa taɓa zama inuwa ɗaya, haushin da Al Qaseem ya bashi shine ya rasa wa zai aura sai wannan yarinyar? Ya yi me da ita, yarinyar da bata san komai ba sai rashin kunya sai fitsira, ko makaranta ta gagara kammalawa, tasa rashin kunya a gabanta.
Ga tsabar rashin kunya ma tana zaune ake maganar aurenta, wani dogon tsaki yaja wanda sai da ya jawo hankalin Husna, karaf suka haɗa ido da shi ya sakar mata wani mugun kallo ya ɗauke, sai da ya ɗauke kai sannan itama ta bi shi da harara. Leemah ce ta ce.
“Ni kam Daddy wannan kasan ai abu ne da bazai yu ba, kasan Hajiyarsu ba bari za ta yi ba.”
Murmushi ya yi mata irin na manya, sannan ya ce.
“Da yake ita ke da haƙƙin aurar da shi ba? A yanzu ma da na baro wajenta bata yi min maganar ba, saɓanin Hajiya Babba ma da ta yi murna da maganar har tana cewa ta ɗauki nauyin kayan lefe, tun da Hajiya Babba tasan maganar, kinga kuwa itama ta sani.”
Abin da bai sani ba, Hajiya Kubrah ba ta yi tunanin yasan maganar ba, shi ya sa ta zaɓi yin shiru. 
“Ke Halima mene naki a ciki? Magana ce fa ta iyaye, kuma kinsan duk gidan nan babu wadda zata ja da abin da Alhaji ya faɗa, sannan ai sai ki sanyawa Husnan wani abu a ranta.”
Mimi ta faɗa tana hararar Leemah, Daddy ne ya sake cewa.
“To ita yarinyar sun sasanta ɗin ne? Sabida ina son ayi komai cikin sati biyu, bayan an ɗaura auren kafin ta tare ina son miƙama Malam ita da igiyar aure a kanta kamar yanda ya buƙata.”
Wani sanyi Husna taji ya mamayeta, ashe ana yin auren ma gidansu zata koma, tabbas Al Qaseem ya zama haske a rayuwarta, Allah Ya tabbatar musu da alheri, ya bar ƙauna a tsakaninsu. 
Maganar Mimi ce ta katse mata zancen zucin da take yi, jin tana ambatar sunanta tana faɗin.
“Ita dai Husnan bamu yi magana da ita ba, amma nasan suna tare da shi, zancen aure ne bansani ba ko amincewarta ya yi magana da kai, Husna.”
Mimi ta ƙarashe da kiran sunanta, Husna ta kalli Mimi ta yi ƙasa da kanta, Mimi ta sake cewa.
“Da amincewarki ne Al Qaseem ya yi maganar aure da Alhaji?”
Shiru Husna ta yi, ta kasa ko ƙwaƙwaran motsi wani irin kunya take ji.

“Tun da ta yi shiru yana nufin da amincewarta.”
Alhaji Musa ya faɗa, Husna dai bata ce komai ba, shi kam Ashraf mamaki yake ya tabbata yarinyar nan bata da kunya, kuma abin da ya ɗaure masa kai bai ji anyi zancen karatun ta ba, amma ana na aure ta nuna tana so, karatu ta ce a’a, kuma ya san shima Al Qaseem ɗin ba mai da hankali zai yi a kan karatunta ba, tun da shima ba wani son karatun yake ba, shi kam zai ga yanda za ayi rayuwa da jahilci, tsaki yaja ciki ciki yana mai jin haushin kansa ko me ya sa ma ya damu da lamarin karatun nata ma oho. 
“Ta shi ki shiga ciki.”
Mimi ta faɗa, ba musu Husna ta miƙe har tana harɗe ƙafa ta shiga ciki, tana shiga ta faɗa kan gado ta fara sauke wata ajiyar zuciya, lamarin ya yi mata daɗi mussaman da aka ce ana ɗaura auren gidan su za a kaita.

 Waya ta ɗauko Alhaji ta fara kira, bugu ɗaya ya ɗauka yana faɗin.
“Baki yi bacci ba?”
“Tukunna dai, kasan me?”
Kamar tana kallonsa ya girgiza kai, kafin ya ce.
“Sai kin faɗa.”

“Na kusa dawowa gida, nan da sati biyu ma.”

“Dan girman Allah fa?”

“Wallahi.”

“Abba ne ya yarda?”
Alhaji ya tambaya.

“A’a, aure zanyi.”
Sai da ta faɗa kuma taji wani nauyi ya danneta, dan bazata ce kunya ba tun da ita dai ba kunyar faɗar magana ce da ita ba, amma ta auren nan ta yi mata nauyi. 

“Wa zaki aura?”
Shiru ta yi bata ce komai ba, ya sake cewa.
“Wa zaki aura, ina tambayarki?”

“Yaya Al Qaseem.”

“Waye haka?”

Ya tambayeta, daman tasan ba lallai ya san shi ba tun da basu da wata alaƙa da su, ko sunzo nan ma wajen Mimi ne kawai, kuma ma ba zuwan suke ba albarkacin Husnan ne ma suka zuwa yanzu. 
“Ɗan gidan Hajiya Kubrah ne, abokiyar zaman Mimi, ƙanin Yaya Nusaiba ne amma an ce ya ɗan girman wannan Ashraf ɗin.”
Har cikin zuciyarsa yaji daɗi, yasan baza a taɓawa Husna mutumin banza ba, amma bai sani ba ko tana son sa ko za ta yi aure ne kawai sabida ta dawo gida, cikin yanayin kulawa ya ce.

“Husnah.” 
“Na’am.”
Ta amsa, ya yi gyaran murya sannan ya ce.
“Kuma kina son sa ko zaki yi aure ne sabida ki dawo gida?”

“A’a, nima ina son sa fa, kuma ya ce zai barni nazo gida sai na yi wata ɗaya sannan za ayi bikin.”

“To Allah Ya sanya alheri, bari na sanar dasu Yaya Abdul, har da Mama ma.”

“A’a kar ka sanar da Mama, Mimi zata yi mata magana.”

“Toh shikenan amarya.”
Ya faɗa tare da katse wayar, tashi ya yi ya fito ɗakinsu Yaya Abdul duk ya sanar dasu, kowa yaji daɗi kuma sunyi addu’ar Allah Yasanya alheri.

Washe gari. 
Husna bata sami saƙon da take samu daga Al Qaseem ba, abin da ya yi matuƙar tada mata hankali, gashi kuma ta kira shi wayar aka she, gaba ɗaya hankalinta ya tashi matuƙar tashi har ya kasa ɓoyewa a fuskarta, Dade na ganinta ta san abin da ke damunta amma ta yi banza da ita, a yanzu hankalin Dade ya yi ta koma Wudil, wannan ƙarin hasken da malaminta ya sanar da ita ya ɗaga mata hankali sosai, kuma tana son zuwa gidan Ashraf amma bata san me zata ce ba, sabida gudun kar ayi mata wani gani na daban, sau ɗaya suka taɓa zuwa gidan ita da Mimi da Hajiya Babba tun daga nan basu koma ba, kuma matar ma ba zuwa take ba sai da babban dalili, to yanzu rana kwatsam ta ce zata je ai za ayi mata wani kallo na daban, amma ita dai tana kyautata zaton Jamilar ce ke da ciki, tun da ta duba ko ina bata ga wani ƙari ba. 

Ya Leemah ce ta fito cikin shirinta, tana sanye da wata baƙat abaya ta yi rolling da wani baƙin mayafi na abayar, tana saƙale da wat cream clour ɗin jaka, takalminta ma cream clour ta yi kyau sosai, damam ita ‘yar wanka ce. 

“Halimatu ina zakije kike wannan saurin haka?”

“Ofis mana Dade.”
Ya Leemah ta bawa Dade da amsa, turo baki Dade ta yi gaba, aikin malamin Hajiya Babba yana ci a kan Leemah ta wajen zaman aure, amma har yanzu an gagara cire mata son wannan campanin, ba kamar lokacin da aka yi aiki a kan Ashraf ba, lokaci ɗaya ya ce ya ajiye aikin ba zai ba, amma ita da zarar ta dawo gida to bata da aiki sai zuwa ofis, ɗan taɓe baki Dade ta yi kafin ta ce.

“To ba zaki iya zaman iddah ba?”

“Ina Idda ta mana Dade, amma wannan ai wajen aikine ba wai yawon gararanba a gari ba ko?”

“Hakane kuma, wai kuwa ya labarin ‘yar uwarki ne Nusaiba, shiru”

“Tana lafiya Dade, bakwa yin waya ne?”

“Ta ina zamu yi yarinya daga ina mata zancen kar ta biyewa ɗabi’ar yahudawa taƙi haihuwa, shine ta daina magana da ni.”

“To kema Dade ai haihuwa na Allah ne, kuma suna iya ƙoƙarinsu Allah ne bai basu ba.”
Ya Leemah ta faɗa, sannan ta ce da Husna.

“Husna, ki ce ma Mimi na fita. Na shiga tana bacci, bana son tashinta.”

Murmushin yaƙe Husna ta yi, sannan ta ce.
“Tam Yaya, Allah Ya kiyaye.”

“Amin, amin.”
Ya Leemah ta faɗa tare da ficewa, motarta ta shiga ta nufi babban kamfaninsu na ƊANKAKA GLOBAL ENERGY & LOGISTICS LTD
Ya Leemah na fita Dade ta ce.

“Ke kam Me yake damunki hakane? Naga yau tun safe kina ta wani ɓata rai.”
Murmushin yaƙe Husna ta yi, sannan ta ce.

“Babu komai Dade.”
“Ki faɗa min mana, ko da Al Qaseem ɗin ne ya yi miki wani abu, ko auren ne ba kya so?”

“A’a fa, ba haka ba ne Dade.”
“To menene?”
Shiru Husna ta yi, Dade ta matsa mata sai ta faɗa mata abin da yake damunta, husna ta sanar da ita ba su yi magana da Al Qaseem ba ne, taɓe baki Dade ta yi kafin ta ce.

“Ke kuwa a haka zaku yi auren? Yanzu ace tun jiya baku yi magana ba ki kasa nemansa kuna gida ɗaya? Wannan ce kulawar soyayyar? Maza ta shi kije part ɗinsu ki duba ko yana lafiya.”
Shiru Husna ta yi, sabida ita tafi kowa rashin kunya sai taje wajen mahaifiyarsa ta ce tazo duba shi, tun zamanta gidan bata taɓa zuwa wajen Hajiya Kubrah ba, gwanda ma Hajiya Babba taje sau biyu ko uku.

“Bafa wajen mahaifiyarsa nake nufi ba? Ko kija nufin baki san inda part ɗinsa yake ba?”
Gyaɗa kai Husna ta yi, Dade ta ce. 

“Kina fita nan, akwai wani ƙaramin coridor to ai kina yin nan zaki ga wata baranda to nan ne ɗakinsa yake. Maza ta shi kije.” 

Miƙewa Husna ta yi, ranta gaba ɗaya baya so, amma Dade ta tunzurta tana kwantata mata wajen a kan taje shine nuna soyayya da kulawa.
Husna na fita Dade ta ɗauki wayarta, ta danna lambar Hajiya Kubrah, bugu ɗaya ta ɗauka tare da yin sallama, Dade sai sa ta duba taga babu kowa kusa da ita, sannan ta ce.

“Maza maza ga yarinyar nan ta nufi ɓangaren Al Qaseem zata je duba shi, ki yi maza kije ki yi musu kwaroroto kice tana zuwa wajensa kinga babu ta yanda za ayi musu aure, kuma dole tabar gidan a yau.”



Legendspen-Sayyid
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.