Free chapter · Read without an account
No Surrender!
by NorthernAngel · His Rose
4:30 PM, Galado Manor.
Kusan awa ɗaya kenan Hajiya Sauda da iyalanta suna zazzaune a parlourn farkon shigowa wing ɗin Yemma. Tunda aka koro su a wulaƙance daga gidan Zara suka yo nan ɗin, har yanzu basu sa Yemma a idonsu ba. Yar ɗakinta, Hajiya Mai Gado ce kawai ta samu nasarar shiga ciki, ta hau har saman ɓangarenta inda tun lokacin ba su sauko ba balle Yemma ta fito su ganta. A saman kuwa, suna zaune a private lounge ɗin Yemma ita da Hajiya Mai Gado, suna kashewa suna binnewa. Duk yadda aka yi tun daga shigarsu gidan Zara, Hajiya Mai Gado tiryan-tiryan ta hau ba wa Yemma labari daki-daki. Gyada kai kawai Yemma take yi tana sauraron ta har ta gama, ranta na wani irin mugun tafasa. Bayan kusan awa ɗaya suka sauko ƙasa, sai dai Yemma ba ta fito babban parlourn da su Hajiya Sauda ke zaune ba—saboda sun mugun ba ta haushi gami da takaicin halin rashin aji da tazubar ɗin da suka nuna a matsayinsu na surukan Galado. Kallon Hajiya Mai Gado tayi, tace a kira mata Rahama. A can parlourn kuwa, Amal ce ta doka wani uban tsaki mai tsawon gaske. "Mommy, gaskiya na gaji! Ashe haka kike zuwa gidan nan ana wulaƙanta ki?! Gaskiya ni kam tafiya za na yi!" Rahama ta amshe zancen cikin takaici: "Ni ma wallahi tafiya zan yi Amal! Kuma gidan ubana zan tafi saboda na gaji! I am sick and tired of how these people are treating us! Mutanen nan kwata-kwata ba su san darajar mutum ba. Wallahi gidan ubana zan koma..." Ta ƙarasa maganar tare da sake fashewa da wani irin kuka mai tsananin raɗaɗi da kuna. Hajiya Turai ce ta yi magana ƙasa-ƙasa tana waige-waige. "Wai ku me ya sa kuke haka ne, Rahama?! Kwata-kwata ba ku da ɗa'a da tsari! Yanzu daidai ne ku riƙa irin wadannan maganganun a cikin gidan surukai?! Musamman ke Rahama, ki iya bakinki! In mun fita sai ki yi duk maganganun da za ki yi. Kuma babu inda zaki je, kina nan daram! In kika tafi ai ta ji daɗi ita tsinanniyar... Ai kin yi mata abin da take so ke nan!" Hajiya Saudah ta gyaɗa kanta a fusace tana cewa, "Faɗa mata dai, Turai! Babu inda zaki je, zama daram a gidan nan—har da haihuwa! Ai wasan yanzu aka fara shi. Daga yau kin daina raga mata! Ita ɗin banza, yadda take takamar ubanta wani ne, ke ma naki uban wani ne! Duk abin da ta yi miki ki rama, babu abin da zai faru! In kin koma gida ina kike so insa raina? Gaki ga Surayyah.. haba! Da surutun makiya zanji ko da me?" Ta ƙarasa maganar cikin ɗaga murya da karkarwa, tana goge hawayen tsantsar ɓacin rai na bakin cikin da Zara, Zafar, da kuma ita kanta Yemmar da ta shanya su take ciki. Sam ba su taɓa fuskantar irin wannan cin mutuncin da wulaƙancin a dukkan rayuwarsu ba! Daidai lokacin, Hajiya Mai Gado ta leƙo babbar ƙofar tana faɗin, "Ke, Rahama... Taso." Haɗe rai Rahama ta yi tamau kamar ba za ta tashi ba, sai da Hajiya Turai da Hajiya Sauda suka daka mata tsawa a tare. "Tashi mana! Me kike yi ne haka?!" Da sauri ta miƙe tana goge hawayen da ya bushe a fuskarta. Kanta har wani azababben sarawa yake yi domin gajiyar da ke jikinta, ga zafin buguwar da kanta ya yi a ƙasa yayin kokuwarta da Zara, ga kuma wata masifaffiyar yunwa da ke cin cikinta—sakamakon weight gain supplements ɗin da take sha wanda ba ƙaramin cin abunci yake sanya ta yi ba. Tana zunbure-zunburen baki gami da ɗan jan ƙafa ta isa inda Hajiya Mai Gado take tsaye. Wani razanannen kallo mai cike da takaici Hajiya Mai Gado ta watsa mata, kafin ta gyaɗa kanta a hankali tana cewa, "Biyo ni." Tuni Rahama ta sha jinin jikinta, domin da alama ta tabbata Hajiya Mai Gado ta jiyo duk wani kalaman da suke ta faman zazzagawa a ƙasa. Cike da matsananciyar fargaba da zulumi, ta soma gudanar da addu'a a zuciyarta gami da roƙon Allah ya sanya kar Hajiya Mai Gado ta kai ƙararta wajen Yemma. Suna shiga cikin second parlour ɗin Yemma, suka hango Yemma a can nesa tsaye kusa da lafiyayyar ƙofar glass ɗin da ke sadarwa da tangamemen garden ɗin gidan. Cikin ƴar hantara gami da salon ƙasaita, Yemma ta ce, "Ta yi sauri mana Mai Gado! Ya take tafiya haka ne?!" Cikin rawar jiki da firgici, Rahama ta soma sauri har tana yin tuntube wajen ƙarasowa inda Yemma ke tsaye. Yemma kuwa, ko ɗigon kallo ba ta sami dama watsa mata ba; kawai ta juya ta soma takawa da hanzari tana faɗin: "Biyo ni." Daga haka suka fice zuwa faɗaɗɗen garden ɗin gidan, inda kai tsaye suka doshi hanyar da za ta sadar da su zuwa wing ɗin Baffa...
A ɓangaren Zara kuwa, misalin ƙarfe 7:00 na dare tana zaune a alfarmance cikin lounge ɗin suite ɗinta ita kaɗai tana having dinner ɗinta—wanda lafiyayyan, gassasshen salmon fish ne aka shirya mata shi salam, tare da steamed quinoa da dafaffun ganyayyaki mai cike da nutrients na musamman domin maida ƙarfin jiki bayan haihuwa, da boiled ostrich egg ɗin da aka yanka mata shi ɗan kaɗan a gefen plate ɗin, sai kuma wani herbal and energizing fruits smoothie na musamman da ake haɗa mata. Wayarta tana maƙale a hannunta, babu abinda take yi sai ƙwadarawa Zafar kira tun yamma har aka yi Magriba. Domin kuwa lokacin zuwansu duba baby Jasmine tuntuni ya yi, amma shiru babu shi babu alamunsa, gashi kuma kiransa take bil-haƙƙi amma sam ba ya picking. A karo na ba adadi, ta sake danna lambarsa bai ɗaga ba, sai kawai ta juya ga kiran business number ɗinsa. Ita ma wayar ta shiga, sai dai ba ta tsammaci zai ɗaga ba; kawai ta sa a ranta idan ta gama cin abincin bai zo ba, to ita za ta sa Lamidi ya kai ta gidan asibitin kawai. Amsawar da ya yi wa wayar ne ya ba ta mamaki gaske. A speaker ta sanya wayar gami da ajiye ta a gabanta, ɗan haka ji kawai ta yi muryarsa ta amsa a cikin faddaddan lounge ɗin: "Princess..." Ya faɗa in a greeting form. Sunkuyar da kanta ta yi gami da ƙankance idanunta kan wayar, ta amsa ciki-ciki, "Baka ganin calls ɗina ne?!" Alamar tafiya take jiyowa ta tsantsar sauri daga dayan ɓangaren wayar. Cikin wata saƙaƙƙiyar murya mai nauyi ya ce, "Apologies, baby. I had to head out of town unexpectedly and accidentally left my phone in Mu'azzam's car. I'm heading back as we speak." Haɗe rai Zara ta yi tamau, tana jefa masa tambaya a fusace, "Ina kaje?!" Wata zafaffar sigh mai ƙara ya ɗa saki daga bakinsa, kafin ya ce mata, "Ibadan." Wani irin hade rai tayi, "Ni dai gaskiya tafiya ta zan yi! How are you literally going to leave town when you know we have a daughter that is in an incubator and needs us every single day?! Like, what kind of reckless, irresponsible behavior is this?!" Ta ƙarasa maganar cike da masifa da ɗaga murya. Wata lafiyayyar ajiyar zuciya ya sake saukewa cikin nutsuwa, yana cewa, "Zara, please don't start. It’s an incredibly short flight—it's barely a thirty-minute trip. Just give me sixty minutes and I will be back at the estate to pick you up." Turo baki ta yi cike da rashin haƙuri da alamar gundura, "Whatever! You have exactly one hour. If you're not pulling up by then, I'm literally hitting the road by myself." Daga haka ta datse wayar ba tare da ta jira amsarsa ba. Abincinta ta ƙarasa ci a tsanake, bayan ta kammala kuma ta miƙe ta shige dressing room ɗinta ta hau shiri. Bayan ta gama kimtsawa tsaf, ta fito lounge ɗin ta dauki removie, ta kunna TV ta zauna ta hau kallo—tana yi tana jefawa tsadadden agogon hannunta kallo lokaci zuwa lokaci.
Kira ne ya shigo wayarta, tun kafin ta dubi screen ɗin ta ɗa saki murmushi domin ta riga ta san ko waye, daman yanzu take tunanin yanda yau ya shafa mata lafiya. Ai kuwa tana dubawa ta ga Roman din ne. Picking ta yi, bayan sun gaisa ta tambaye shi jikinsa, ya amsa sannan ya hau sanar mata yanzu su Vicky da Sam suka bar wajensa, kuma sun ce nan gidanta za su zo. Amsa masa ta yi da cewa ta sani, saboda ta yi waya da Susan tun da safe ta sanar mata za su shigo su dukkaninsu yau da dare. Daga haka dai suka fara gudanar da hira da shi suna labari, inda take masa tambayoyi a tsanake game da inda yake da zamansa yanzu da kuma harkar aikinsa. Wasu abubuwa dake daure mata kai game da rayuwarsa kawai yake gaya mata, amma nata da lokacin zurfafa tambayiyin ta ya barshi sai sun hadu face to face. Sai wajen ƙarfe 9:20 na dare kiran Zafar ya sake shigowa wayarta. Sallama tayi da Roman sannan ta miƙe ta koma ciki ta ɗauki Fendi handbag ɗinta ta fito. Cooler ta ɗauko ta sanya breast milk storage bags ɗin a ciki, sannan ta sauka ƙasa tana kumbure-kumbure. Ace tun ɗazu ya je yayi zamansa?! Da ba don tana son magana da shi mai muhimmanci ba, da wallahi ba za ta jira shi ba! Yanzu idan abincin Jasmine ya ƙare a asibitin kuma ba su kai ba fa? Haka dai ta ringa takawa tana mita da masifa ita kaɗai har ta fito babbar harabar gidan. Zafar, da ke zaune a cikin motarsa yana hangota ta fito, ya buɗe ƙofar ya zagayo domin buɗe mata wajenta tun kafin ta ƙaraso. Sai dai tana ƙarasowa, kafin ta shiga motar ya tsaida ita gaba ɗaya gami da tsare na da idanu yana ƙare mata kallo, da mamakin ganin jallabiya mai hula ce kawai ajikinta yasa yace, "Wait a minute... What exactly are you wearing right now?!" Dama tun farko fuskarta a haɗe take tamau, ɗan haka ba ta ce masa uffan ba. Hannunsa da ke manne a jikin ƙofar motar ya tare mata hanya, ta sa nata hannun ta janye shi gently, sannan ta shige motar ta zauna. Shiru ya yi a tsaye, ya daskare yana bin ta da kallo ta glass ɗin motar. Jin shirun ya yi yawa ya sa ta ɗago fuskarta ta kalle shi, calmly ta ce masa, "Oga, please, if you're done admiring the view, close the door. My daughter's feeding time is non-negotiable and we are already late." Gyaɗa kansa ya yi a hankali, sannan ya rufe mata ƙofar motar ba tare da ya sake furta komai ba. Daga haka ya zagaya ya shiga mazauninsa na driver, ya tada motar suka fice a guje suka bar cikin gidan. Shiru ne ya mamaye ciki da wajen motar, sai dai bai dore na tsawon lokaci ba. Suna fita daga ƙofar estate ɗin, Zara ta juyo ta kalle shi kai tsaye, tana tambayarsa, "When are you giving that girl her divorce?" Kamar wanda ke jiran tambayar, kai tsaye ya ba ta amsa a taƙaice, "Ba rana." Kamar dirar mikiya ta ji maganar ta sauka a kunnuwanta. Wani nauyayyen shiru—a suffocating silence—ya sake ratsa tsakaninsu. Can ta sake cewa da shi, "And why is that?" Idanunsa na kan titi, ya amsa, "Because I am simply obeying my mother's orders." Wani soft, amused laugh Zara ta saki mai cike da rainin hankali, kafin ta gyara zamanta, ta juyo da gaba ɗaya hankalinta da kallonta kansa. Cikin light, dangerous voice ta ce masa: "That's funny... because your mother can't stand my presence. If you're such a dutiful son, why didn't you show her that same obedience and throw me out?!" Sai a lokacin ya juya ya jefa mata kallo guda mai nauyi, sannan ya sake maida hankalinsa kan titi. Jin ya yi shiru ya ƙi amsawa ya sanya ta sake magana da dan karfi wannan karon. "Don't ignore me! I asked you a question." Girgiza kansa ya yi a hankali, ya ce, "I'm completely done having this conversation with you." Bai ma gama sauke numfashi ba ta katse shi. "Why? Because you are a total hypocrite and a coward who satisfies his own desires, and then hides behind the lie of 'obeying his mother'?! No, bro... you are done playing me like this. You're not getting away with it this time. It is either you give that girl a divorce, or you let me go!" Amsa ya ba ta cikin wata nonchalant, unbothered voice, "If that's what you want, it can be arranged." Ɗan murmushin tsantsar rainin wayo ta saki, tana cewa, "Which one are you arranging, sweetheart?" Cikin dai wannan muryar tasa ta ko-oho, ya sake cewa, "Letting you go, obviously." Zara, da ke ɗauke da wannan kaifaffen murmushin a fuskarta, ta amsa, "Fine! Let's lay the terms on the table. Since you lack the spine to make a real choice, I will make this incredibly easy for you. From this exact second, there is going to be zero peace for you and that little shadow you call a wife. I am never letting you spend a single night under her roof again. And the moment you realize you can't handle the pressure? Hand over my divorce paper, and I will exit your life gracefully." Tun da ta fara maganar yake girgiza kansa a hankali. Bayan ta kammala, ya yi wani light chuckle na takaici gami da cewa, "Yaro man kaza..." Daga haka ya juyo ya kalle ta sosai, ya fara magana. "Zara, Zara... wallahi ki shiga hankalinki. You see that thing you're looking for—that reaction you keep trying to pull out of me? You’re going to find it much faster than you think, I promise you. Just keep testing me. This little warpath you've got yourself on? Stay on it. Don't look back, just keep pushing... because it is the quickest way to unlock the side of me you really don't want to see. We are going to get there eventually." Da wani cute, killer smile a fuskarta take bin sa da kallo; duk zare idonsa da threats ɗinsa ko ɗigon dar bai shiga jikinta ba. Yana gama maganar, ta ɗaura yatsunta biyu a kanta ta sara masa kamar wata soja. "Aye aye, captain... let's see what you've got then!" Daga haka ta juya ta zuge glass ɗin ƙofar motar ƙasa, ta hau kallon high-end side of Lagos ta window. Gyaɗa kansa kawai ya yi shima, ya maida cikakken hankalinsa kan tukin da yake yi. Har suka ƙaraso harabar asibitin, babu wanda ya sake cewa ɗan uwansa ƙala...