Free chapter 路 Read without an account

25

by Anisa Muhammad Yahaya 路 NUFIN ALLAH


馃挄 NUFIN ALLAH 馃挄 
By
Anisa Muhammad yahaya 


Page 2锔忊儯5锔忊儯


A shawarma king yatsaya ya siyar musu sanan suka cigaba da tafiya 

A karkasara gidan Anty yake, basu suka isa ba sai after magriba daman ba da wuri suka fito ba kuma sunyi tsaye tsaye

A kofar gidan yayi parking be shigar da motar shi ba, Ahmad yayi parking a bayan shi

Fitowa sukai har ya Ahmad 蓷in, itama Jalila fita tayi, ta bude motar zata fita ne yayi saurin sa lock

Kallon shi tayi taga ya wani maze kamar bashi ya saka ba

"Yahh ban fita ba fah" tayi maganar a 蓷an shagwa蓳e tana kallon shi

"Baki bani card 蓷ina ba" shima ya juyo yana kallon ta 

Kai ta kawar ta dauko card 蓷in nashi a jakar ta ta mi茩a mishi dan ita tama manta 

Kara yunkurin bu蓷e handle 蓷in tayi yace

"Hanky" gefen ta ta duba ta gan shi ta dauko shima ta mi茩a mai

Hannun nata ya kalla sai kuma ya amsa still ita yake kallo, Amman itama ta 蓷an ha蓷e rai, saboda jinta take wani iri a gurin Barin ma yanda ya kafe ta da idanu

Ajiyar zuciya ya 蓷an sauke yace 

"Ki 蓷auka ledan dake 茩asan kafanki ki tafi da shi naki ne, 蓷ayan Kuma ki basu Ashraf" ya fa蓷a yana cire lock ya ta蓷a motar alamun yana jiran ta fita

Mamaki ne ya kamata tunda taga sanda ya ba Jalila ledan shawarman sai tace
"Ni kuma"

"Eh" ya fa蓷a yana 茩ara ha蓷e rai dan karma ta 茩ara tambayar shi

Itama ganin haka yasa tayi mai godiya ta 蓷auka tayi waje dan bata ga face 蓷in cewa bazata amsa ba

"Ah ah inasu baban nawa, maisa basu shigo ba, ko batare kuke ba" Anty dake zaune a parlour tana kallo tayi maganar 

Gaisheta sukayi fareedah tana cewa

"Yah Ahmad yace wai a kawai wani abu da zaije yi a office in suka shigo yasan baza su fito da wuri ba gashi dare yayi Amman wai zasu zo musamman"

"Okay nifa ince dan Amma tace su zasu kawo ku"

 "Addahhh!!!" ashraf dake zaune kusa da anty ganin su ya taso da gudu yana rungume fareedah 

"Na da蓷e banganki ba Adda nayi missing dinki"

"Nima haka boy, yakake, ina ya majeed"

"Ina lapiya, yana sama bara in kira miki shi" ya fa蓷a yana 茩o茩arin fara gudu yaje sama ya kira majeed, Anisa tace

"Ni ai bakayi missing dina ba ka manta dani ko ashuu nah??" tana 蓷an kwa蓳e fuska kamar gaske

"Laaa addah ai banganki ba addah reedah kawai na fara gani shi yasa"

"Daman ina zaka ganmu ga favorite sis ta zo" nabila tayi maganar tana aika mai hararar wasa

"Kaii adda dagaske ita na gani fah kawai sai yanzu na ganku"

"Kaidai kasani kira mun mutumi na nima tunda kai baka ganmu ba sai yanzu" Jalila ta fa蓷a tana zama kusa Anty

"Wai ina kuka je ne naga kun da蓷e baku iso ba dan amma tace tun kukayi laasar kuka fito Amman se yanzu nake ganin ku, ina nan ina medile'' 

"Mun 蓷an tsaya a ShopRite ne fah anty su yahh sun mana siyayya" fareedah ta fa蓷a tana 蓷aga ma Anty ledan hannun ta

"Aikam sun kyauta,sai kutashi kuje saman ku ajje kayan"

Toh suka ce Anisa ta mi茩a mata na 蓷ayan hannun ta tace '' ya Faruq yace abasu majeed'' suna mi茩ewa sukayi sama

Da kallo ta bisu tana fatan Allah cigaba da 蓷aurar da zumuncin nan haka, daba dan ma anty shaheeda da addah abida suna neman raba kan yaran ba ai da ba haka ba

Tunda sun nuna su baso suke yaransu na zuwan musu ba, su kuma da suke barin nasu yaran suna zuwa ba suce karsu zo ba Amman sai su ringa musu kora da hali

Shi yasa suma suka kyale tunda ba'a dole tunda ba sa so sai su kyale su, ko da iya haka ne zumuncin ya isa tunda su basa so ayi da nasu yaran

"Wai ke wanan extra ledan fah tun muka shigo na ganshi a hannun ki" fadin Jalila tana janyo ledan kusa da Anisa

"Yahh ne fah ya bani"
"Wani yayan??" suka fa蓷a kusan tare suna zare ido dan sun san dai a motar ya Faruq ta zauna, Amman basa tunanin dai shi, saboda ya Faruq fah ya Faruq ne

"Shiya bani da zan fito yace wai nawa ne"

Budewa suka fara yi kamar wa蓷anda aka aike su

Perfumes,skin care products,hair products da sweets, biscuits, chocolate da ice cream

"Keee wallahi zato na yanzu dai yazama hundred percent sure, bara kuga" Jalila ta fa蓷a tana janyo wayar ta dake kusa da nabila 

"Yauwa zancen zan miki na 蓷azu daman yana raina sister" fareedah ta fa蓷a tana washe baki kamar gonar auduga

Videon da ta musu 蓷azun ta nuna musu 

"Awwwwn!!!" Nabila da fareedah suka fa蓷a

"Wallahi You two make the perfect couple, ke Black beauty shi 蓷an fari" fa蓷in fareedah 

"To mukuma fah, bamuyi making perfect match ba ni Black shi Black" fa蓷in nabila tana wani juya ido cike da shau茩i

"Ke fah bakida kunya nifah yanzu in law dinki ce Amman kike wannan rashin kunyar a gabana" fadin Jalila 

"Tabb waya ga ai abinda yafi haka ma zanyi a gabanki, kunyar ki na me zan ji" fa蓷in nabila 

"Su in law manya, muga me kuke gani" Anisa ta fa蓷a tana kwace wayar hannun fareedah 

"Kutty see ayaushe kika yi wannan taasar" tayi maganar tana ri茩e baki

Dan idan ka kalli videon sai kai tunanin wasu love birds ne barin ma yanda take wani shagwa蓳a yana wani mata magana da taushashen murya ya mi茩a mata hanky


_____________________
By
Anisa Muhammad yahaya 馃尯

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.