Free chapter · Read without an account
The fear😳
INUWAR ƘADDARA 🖤
Book 1
Page 2✍️
Meelah Bazata
Bayan shigarsa ɗakin nasa, ya maida ƙofa ya rufe. Kallo Ammah ta bi shi da shi har sai da ya shige, sannan ta ɗaga hannu sama ta ce, “Allah ga Sayyid ɗina, ka shirya min shi, ka sa ya gano gaskiya, ka raba shi da wannan harkar.”
Duk da yana da ɓangarensa musamman a gidan, amma wani lokaci yakan zaɓi ya kwana a cikin ɗakin mahaifiyar tasa. Itama tashi ta shiga zuwa ɗaki, sai dai har zuwa lokacin ba kwanciya ta yi ba, alwala ta yi ta sake hawa kan sallaya tana ci gaba da kai wa Allah kukanta, akan Allah ya shirya mata Sayyid, ya ƙara kare mata Rooman ɗinta.
Shi kuwa bayan shigarsa ɗakin nasa, ko takalman ƙafarsa bai cire ba, haka kuma bai canza komai ba, ya faɗa kan gadonsa, tare da bingirewa ya fara bacci.
Da asuba kiran sallar farko ya tashi. Duk iskanci irin na Sayyid, baya wasa da sallah, haka baya shaye-shaye, amma bayan waɗannan duk wani abu da ya danganci daba to yana gaba-gaba,idan kuwa akazo harkar fadan daba,toh shine agaba ,haka bangaren jagaliyanci.
Ko da ya ko da yaje masallaci, a can ya haɗu da yayyen baban nasa su uku, babu wanda ya kalleshi, a ciki domin sun san halinsa. Shi kuwa dama Kawu Manu yana ganin sa da gudu ya juya ya koma masallacin domin ya san akwai jikakka a tsakanin su. Shi kuwa Madugu girgiza kai kawai yayi yana kwafa a ranshi, faɗi yake, “In kere na yawo, zabo ma na yawo.”
Ko da ya koma gidan bai koma part ɗin Ammah ba, kawai part ɗinsa ya nufa domin a ranar kam babu zaman lafiya sai ya ɗaga hankalin kowa. Kuma baya so Ammah ta hana sa abin da yayi niyya, hakan yasa zai bari sai ta fita saboda yau akwai inda za ta fita duba mara lafiya, ita kuma Rooman yasan makaranta zata tafi.
Ko da gari ya waye ya yi haske, ya fito cikin shigarsa ta kullin. Kallonsa na tsayawa yi, tabbas yana da siffa irin ta ban tsoro kam,saboda yanayin idanuwansa. Sai dai kyawunsa, inaga shine abin da yake ba mutane tsoron. Fari ne, saidai ba sosai ba, amma tabbas za a kira sa da fari, saidai yafi kama da irin Buzaye nan ko kuma Larabawa. Idanuwansa manya ne sosai, shine abin da inaga yake ba mutane tsoron a game da shi har basa iya haɗa idanu da shi. Haka kuma ƙwayar idanun nasa ba baki bane, ya sirka da launin ash color. Yana da saje sosai wanda ya kawata ɗan ƙaramin bakinsa wanda yayi ja sosai, kamar ya shafa lipstic. Haka gashin girar sa mai yawa ce sosai kamar yadda gashin kansa yake. Akwai wata katuwar tabon sara daga gefen girar sa da hagu, wacce ita ce ta ba da wani salo na musamman a fuskar tasa.
Jikin sa babu alamar sara ko suka, kwata-kwata, yadda fatarsa take kyalli da sheƙi har wani ɗaukar ido take. Babu ta yadda zaka kallesa ka danganta sa da ɗan daba, saidai fuskar sa ɗin ita ce tayi kama da ta ’yan daban, saidai akira sa uban daba,duba da yadda take a daure tamau babu alamar rahama bare kuma sassauci.
Karensa Rocky, bakin kare ne, gashi jibgege yadda kasan kura, haka yake, gashi tsawon sa ya kai ƙafa huɗu. Babu wanda baya tsoron Rocky a gidan saboda yadda Madugu yake sa shi hukunta masa mutanen gidan.
Rooman ita da Ammah sune kadai wannan kare yake shatawa layi,domin wani lokacin in Rooman zata fita shine yake rakata,ita ta riga ta saba da karen,kuma dama ko da babu karen,babu wanda ya isa ga tunkari suk inda take bare kuma ya nemi cutar da ita domin kowa yasan kanwar madugu ce.
Suna zuwa daidai ƙofar part ɗin Ammah, ya kalli Rocky da yake biye da shi, yace, “Faka anan.”
Aikuwa take karen ya ja ya tsaya yana muzurai.
Shi kuwa sallama yayi ya shiga falon na Ammah. Rooman ce sanye cikin shigar uniform ɗinta na makarantar Islamiya, kasantuwar yau Asabar, makarantar bata da nisa sosai da gidan, can saman layi ne.
Tana ganinsa fuskar ta ta washe da murmushi tace, “Yaya, jiya ina ta jiranka, baka dawo ba. Akwai aikin da aka bamu a makaranta, amma yanzu na riga na yi.”
“Ki yi ki gama ki tashi mu tafi makarantar,” ya faɗa hakan yana karasawa gurin Ammah ya zauna a kusa da ƙafafunta.
“Ammah barka da safiya, ya haƙuri da halin SAYYID ɗinki?”
Murmushine ya kawata fuskar Ammah, ta saba da gaisuwar ta yaron nata, kullun sai ya tambaye ta ya haƙuri da halinsa.
Gashin kansa ta shafa cikin kulawa tace, “Sayyid ɗina ai ɗan albarka ne, nasan ko dan Rooman ɗin sa wata rana zai canza, daga wannan Sayyid zuwa Sayyid da nakeso.”
“Ammah, bakyajin haushi na wai? Kin san fa sai kina haƙuri da ni, amma Allah wallahi babu wanda zai taɓa ki na kyale, wallahi Allah...” Duk da yadda yake maganar, amma cikin taushi take fitowa daga bakinsa zuwa ga mahaifiyar tasa.
“Shikenan naji, Ubangiji Allah ya shirya min kai, yanzu amma ba ahaka zaka raka Rooman ɗin makaranta ba ko? Kuma dai kasan tsoronka sukeyi, don Allah Sayyid ka rage wani abu, ko murmushine ka dinga ɗanyi, amma wannan daure fuskar dole kowa ya dinga tsoronka. kalli yanzu kiri-kiri saboda kai Leenah ta daina shigowa gidan nan. Don Allah Sayyid ka gyara.”
Kara daure fuska Sayyid yayi jin sunan Leenah da Ammah ta ambata, shi baiwan santa ba,amma ya san wacce ammah take nufi,sannan yace, “Ai in na ƙara ganin waɗannan siraran ƙafafun nata a gidan nan, Ammah, sai na karya mata su. Sai baki kamar na ɗan tsuntsu, fitinanniya m,kuka kawai ta iya. Na taɓa dukan ta ne da in ta ganni kamar taga Shaiɗani, bari ma na ƙara ganin ta,” ya faɗa cikin jin haushi, domin ya tsani yadda yarinyar tana ganinsa take firgita, wani lokacin har suma ta taɓa yi tsabar tsoro, shiyasa yake jin haushin ta.
“Ke kuma sai ki yi sauri ki tashi mu tafi, uwar iya cin abinci kamar kina cin duniya,” ya faɗa yana hararar Rooman domin haushin ta yake ji yadda take kawance da waccan aljanar yarinyar.
“Ni dai ban ce kayi mata komai ba, nasan halinka, in ba haka ba zan bata maka rai. Ai ko baka yi mata komai ba, wannan halin naka ai shi kaɗai zai sa a dinga tsoronka,” Ammah ta faɗa hakan yayin da suke mata sallama suka fita, yana riƙe da hannun Rooman.
Hanyar gate ɗin gidan suka nufa. Gida ne babba sosai, kuma kana ganin tsarin gidan kaga na masu kuɗi ko kuma waɗanda suka yi tashen kuɗi.
A ƙafa suka fita, sai a lokacin na sake kallon unguwar. Tabbas babu gidan da ya kai sa girma, gidajen ne na masu rufin asiri da kuma na takalawa. Layin yana da tsawon wanda kuma ba laifi yana da faɗi, gidaje ne a duk ɓangarori biyun, wani na kallon wani.
Suna fitowa, karen sa Rocky yana biye da shi a bayansa, ga Rooman da ya riƙe hannunta, ɗayan hannun nasa kuma riƙe da jakar makarantar ta.
Itama Rooman ɗin ɗan matsakaicin gidan da yake kallon gidan nasu take kallo, gida ne na daidai talaka mai rufin asiri, gate ne green a ƙofar gidan.
kawar tata take jiran taga ta fito,somin kuwa tasan bata wucewa sai ta jira ta.
Yarinyar da ta fito daga cikin gidan tana kallon ƙofar gidan su Rooman ɗin, domin a yanzu ta daina biya wa Rooman makaranta, sai dai ita tazo saboda tsoron Madugun, ba ita kaɗai ba, kaf unguwar babu wanda yake yadda su haɗa hanya da shi sai yayanta Farooq.
Tana ganinsa ta juya da gudu tare da sakin jakar ta, muryarsa ta tsinkaya yana faɗin, “Kina komawa sai na sa Rocky ya cinye waɗannan ƙafafun kamar sillen ƙara,” ya faɗa yana zafga mata harara kamar zai cinye ta.
“Yaya, don Allah ka daina mata magana, wallahi tsoron ka take, kuma kaga mun yi latti,” ta faɗa tana marairaice fuska.
Shiru yayi bai sake cewa komai ba. Ita kuwa Rooman ta ƙarasa ta ɗau jakar ta Leenah tare da kama hannunta, har lokacin jikin ta rawa yake sosai kuma bata ɗago idanunta ba, kamar a jikin wuta take haka take jin ta, gaba ɗaya girmansa ya cika gurin. Allah ya sani, ita dai ko Mala'ikan Mutuwa bata tsoro kamar yadda take tsoronsa, tun ranar da ya shiga gidansu ya zane babban yayansu.
Matar sa yake duka, gata mutuniyar kirki, shi kuma ba shi da kirki. Haka zai yi iskancin sa, kuma in ya dawo gidan ya kama matar yayi mata duka, wani sa'in har tsakiyar layin yake janyota yake duka.
Aikuwa ranar hakan ta faru akan idanun Sayyid. Hakan yasa ya shiga har cikin gidan a gaban ’yan unguwa da suka taru, lokacin Leenah ta dawo daga makaranta kenan. ’Ya’yansa guda biyu ya sa suka daga masa shi, sai da ya cire masa riga sannan ya zane sa gaban kowa. Bayan ya gama zanesa ya sa shi tsallen kwado tun daga farkon unguwar har zuwa ƙarshen ta.
A wannan rana mutane da yawa sun ji daɗin abin da yayi, wasu kuma basu ji daɗin hakan ba, suna ganin ina ruwansa. Bai bar sa iya nan ba, sai da ya haɗa sa da Rocky, irin yadda ya yayyaga jikin Yaya Musa, sai da yayi sati ɗaya a asibiti. Tun daga wannan rana ta ƙara jin tsoron sa fiye da zato.
ita gaba daya girman sa ma tsoro,yake bata,haka idanuwansa gani take kamar aljani ne shi din,bare kuma wata rana da ta dawo daga maranta suka ga ana fada awata unguwa ,yadda ya dinga sarar wani mutun da wuka ranar saids tayi fitsari a wando, domin agabanta mutumin ya fadi ya mutu.
Ba yadda ta iya, haka suka shiga gaba, shi kuma yana binsu a baya. Duk wanda ya gansu sai ya canza hanya, domin shi kallo ma ka bari, idanunsa ya haɗu da naka ka jarraba kanka.
Ko da suka je makaranta, a bakin gate ɗin yasa Rocky ya tsaya, shi kuma ya shiga a bi bayansu. Tsit makarantar tayi, domin kuwa duk wanda ya gansa sai ya gudu ya buya ko kuma ya canza hanya.
Yana kai su ƙofar ajin nasu har malami ya shiga a cikin ajin. Malamin ya saba da ganin Madugu saboda ya sha rakota zuwa makarantar. Sai da ya kai ta har gurin zamanta ya zaunar da ita, sannan ya koma gurin malamin yace, “A musu afuwa, sun yi latti,” yana faɗin hakan ya sa kai ya fita a cikin ajin.
Kowa sauke ajiyar zuciya yayi, haka malamin bai ce komai ba ya ci gaba da yi musu darasi.
Shi kuwa yana fita, bai yi hanyar gida ba, domin akwai inda zai je. Yana dawowa kafin lokacin Ammah ta fita, alkawari ya ɗauka yau sai ya yi rashin mutunci a gidan.