Free chapter · Read without an account

Chapter 36

by Hauwa’u Abdurrasheed · SULTANIM

SULTANIM
      Na
Mss Samher

Instagram mss_samher
Tiktok mss_samher
Wattpad mss_samher


Page36


Fara kiraye kirayen sallar magrib ya sanyashi miƙewa ya shiga ɗaki ya ɗauro alwala ya tafi masallaci, dama tagama komai har gyaran kitchen ɗin zamansa a falon ya hanata fitowa dan a takure take sosai, tana jin fitarshi ta fito ta shirya abincin a dinning ta shige ɗakinta.


         Sai bayan isha suka shigo gidan shi da Dady daya dawo daga tafiya yammacin ranan, sashen Mami suka wuce duka, falon Dady suka samu sauran kasancewar idan Dady ya dawo daga tafiya suka zauna su ɗanyi hira a falon nasa.

Su kaɗai suke cin abinci banda Faruq dake ta aikin danna wayarsa dan za’a zuba masa yace a’a, Mami ta dubeshi da murmushi akan fuskanta tace

“Yau lafiya dai bakaje office ba?”

“Lafiya kalau Mami kawai hutawa nakeso nayi” ya bata amsa batare daya ɗago ba.

“Hakan yana da kyau” ta faɗa tana faɗaɗa murmushinta.

Dady dake sauraransu yasa tissue ya goge bakinsa 
“Umar iyalin naka babu wata matsala ko?”

Cak ya tsaya da abinda yakeyi ya waiwayo ya kalla Dady da shima kallonsa yakeyi yana tsumayen amsarsa

“Alhamdulillah bakomai.”

“Ma sha Allah, Allah ya ƙara muku zaman lafiya, ya maganar karatunta yana nan dai ba?”

“Eh Dady” ya amsa a taƙaice, shima Dady kansa kawai ya jinjina ya kuma jin natsuwa a tattare dashi.

Falon ya ɗauki shiru na wani lokaci kafin Faruq ya ɗanyi gyaran murya tafin hannunsa cikin sumar kanshi yana safa ƙeyarsa

“Dady zansa a ƙarasa sauran abun daya rage na gidana inaso na koma”

A tare suka ɗago kai suna kallon Faruq ɗin dan maganar tashi ta basu mamaki, Dady yace

“Gaskiya Umar nayi farin ciki dajin wannan zancen daga bakinka, ko gobe ka shirya ka ɗau matarka ku tafi Allah ya muku albarka”

“Badai gobe ba ya shirya a natse muma ai akwai shirin da zamyi” cewar Mami.


Bece komai ba ya niƙe dan dama abin da yakeso ya faɗa kenan, yayi musu saida safe ya fice, Mami kuwa da kallo ta bishi tunani daban daban na yawo a cikin kanta.



                Zama yayi kan dining ɗin yayi shiru yana tunanin abunyi, kiranta yakeso yayi amma besan ta ina zai fara ba, Fateemah Nadrah sunaye biyun sukazo ranshi lokaci guda, kansa ya girgiza yana jan guntun tsaki, sai kawai ya miƙe ya nufi ɗakinta

Karo suka kusayi da ita tana ƙoƙarin fitowa bece da ita komai ba ya kamo hannunta suka dawo falon, kujera yaja ya zaunar da ita kafin shima ya zauna, ita kam idanu kawai take rabawa tana kallon saban salon da Faruq ya samo


“Naci abinci” ta faɗa a hankali kanta a ƙasa tana danna yatsun hannunta

“Ni kuma banci ba” ya bata amsa yana kallonta

Sai ta mike ta buɗe warmers ɗin  tayi serving nashi, ƙamshi me daɗi ya gauraye wajan, har sai da yaja iskar data kwaso ƙamshin har cikin huhunsa dan yawunsa ya fara tsinkewa, tana shirin barin wajan ya riƙo hannunta 

“Seat” 

Bamusu ta zauna bugun zuciyanta na ƙara ƙarfi, yanayin fitar numfashinta na chanza, Faruq bai kuma kallonta duk da yana ankare da yanayinta, sosai yaci abincinsa ya kuma kora da coconut drink ɗin data haɗa, ganin ya gama hakan yasa ta tashi ta tattare wajan

“Haɗamin ruwan wanka” ya bata umarni karo na farko a rayuwar auransu.


Kamar ƙafafunta ba zasu iya ɗaukanta ba haka ta jasu tayi ciki, a jikin bangon toilet ta jingina bayanta bayan ta kunna ruwan tana jiran na ɗumi ya sauko, ajiyar zuciya take saukewa akai akai.

Ta gama haɗawa ta juyo ta kama handle ɗin da nufin buɗe ƙofar sai ya rigata shigowa, sanye da trouser da fara qal ɗin singlet kamar ba’a sanyawa a jiki, ta ɗauka zai matsa mata ne sai taji ya maida ƙofar ya rufe dole ta janye da baya har ya shige idanuwanta na kallon ƙasa, dan bazata iya kallonshi a haka ba tsoro yake bata, gaba ɗaya damatsansa a mummurɗe suke dake nuna yadda ya kware wajan motsa jiki, daga hanuwansa zuwa ƙirjinsa duka sun bayya

Ya zare singlet ɗin da tayi saura a jikinsa, da saurinta ta ƙara gaba tana ƙoƙarin buɗe kofan, ta saka hannu ta murɗa ƙofan amma tajita a rufe batasan kuma ya akayi ya rufeta ba

Tashin hankali, sai taja da baya ta sake jingina da bangon zuciyarta na wani irin bugawa cike da fargaba, to wanka zaiyi tana cikin banɗakin kome yake nufi da ita gashi yaƙi ya mata magana, miyan bakinta ne ya ƙafe ganin yana zare wandon jikinsa, ta rasa wanne ɓangare zata kalla saboda ko wani side na banɗakin mirror ne,  saita rufe idanunta hawaye na taruwa cikinsu.


Rufe idanuwan nata ya bashi damar kallonta san ransa, ba abinda yake ƙara tsole idanunsa irin ƙirjinta dake cike sosai, ya kuma zauna ta cikin rigar saboda tattarar roba da akayi mata daga sama, lallausan murmushi ya kwace masa abunda ya ƙarawa fuskarsa kyau, abinda yake daɗewa beyiba kenan, yaga ta turo baki gaba komai nata burgeshi take duk da kuwa yana kallon yarinta sosai a tattare da ita, zai san yadda zayyi yasa tafara sanshi koda kuwa rabin abin da yakeji a zuciyarsa da gangar jikinsa game da ita ne

Yadda hancinta ya cika da ƙamshin body wash ya tabbatar mata da wanka yakeyi, lallai maza basu da kunya shine abin daketa yawo a kwakwalwarta, tana nan tsaye bata motsa ba kamar yadda bata buɗe idanu ba, kawai ji tayi ya janyota cikin jikinsa gaba ɗaya yayi mata rumfa da yalwataccen ƙirjinsa, ya matseta sosai cikin jikinsa wani numfashi mai nauyi yana ƙwace masa batare daya shirya ba, wani irin haɗuwar jiki ya samu da ita irin wanda bai taba ba a rayuwarsa


Rasa abinda zatayi yasa gaba ɗaya ta ƙanƙameshi ta cusa kanta cikin ƙirjinsa saboda ruwan dake dukan kanta, hawayen da take boyewa suka sauka suka tadda fatarsa, dagata yayi kadan daga jikinsa yana duban fuskarta data danyi jaa, ya lumshe idanuwansa da suka fara sauya kala saboda wani abu dake harbawa a kowanne sashe na jikinsa, siraran lips dinta na motsawa a hankali, sai ya sanya fuskarta a tsakiyar tafin hannunsa yana ci gaba da kallon labbanta, baya jin yau zai iya shanye komai da komai


Shi kansa baisan yadda akayi ya tsinciki labbansa saban nata, yadda ya zacesu haka ya samesu da wani irin dumi da kuma sulbi, abinda ya sake tabashi kenan ya kuma haukatashi sai yayi amfani da harshensa ya buda bakinta sannan ya zura harshensa a ciki.

Wasu irin zafafan kisses dashi kanshi bai san ya iyasu a duniyarsa ba ya ɗinga bata, ciki da wajen bakinta ba inda bai tsotse ba da zafi zafinsa yake aiwatar da komai, yanayin daya bayyana har cikin fitar numfashinsa dake sauka saman hancinta


Gaba daya ta gama rudewa jikinta duka ya ɗauki rawa kamar wadda zazzabi ya kama, wani irin baƙon yanayi ne da batasan dashi ba bata kuma taba kawowa zai risketa ba, ta sanya hannunta itama gaba ɗaya ta kama kansa ta riqe tana son janyeshi daga fuskarta saidai bata da wannan kuzarin, ta rasa yadda zata rabashi da kanta kamar ma sake shige mata yake, sai kawai ta saki kuka

A hankali ya tsare bakinsa daga nata lokacin da komai ya fara sakinsa, amma har lokacin yana rungume da ita, bakinsa yaki saitin kunnanta cikin wata karyayyan murya yace 

“Thank you” sakinta yayi sannan ya ƙara ɗauraye jikinsa, ya jawo ƙaramin towel ya goge kanshi kafin ya ɗau wani ya ɗaura saman waist ɗinshi, dubansa ya mayar kanta tana tsaye idanu a rufe ta naɗe hannayanta duka biyun a ƙirjinta alamar sanyi takeji dan kayanta sun gama jiƙewa.

“Wanke jikinki ki fito” daga haka ya buɗe ƙofar ya fice, a hankali ta buɗe idanunta tabi ƙofar daya fita da kallo, bata da wani tsabin daya wuce hakan dan sanyi ya fara shiga jikinta.


Ta ɗauki tsawon lokaci tsaye ɗaure da towel tana tunanin yadda zata fito ya ganta a haka, tana tsaka da wannan tunanin ta tsinkayo muryan Faruq

“Inaga saina shigo toilet ɗinnan ko…..”

Ai bai gama rufe bakinsa ba sai gata zuruf ta fito sai raba idanu takeyi, murmushi ne ya subuce masa ko wani motsinta yana samun ƙarin dalilin daya kamata ya ɗinga tuna mata itaɗin matarsa ce.

“Ga kayan danazo miki dashi ki zaba wani kisa aciki” sumi sumi ta wuce wajan jakar daya nuna mata, yadda take tafiya kamar wata robot.……..

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.