Free chapter · Read without an account
Chapter 37
SULTANIM
Na
Mss Samher
Instagram mss_samher
Tiktok mss_samher
Wattpad mss_samher
Page37
Duka jakan kayan ta hautsina idanu waje take kallon kayan kamar zata saki kuka, duk ciki bata ga wata suturar arziƙi da zata sanya ba, daga night gowns ɗin har sauran kayan sawan dake ciki, ta ɗan jima tsaye tana tunanin mafita, yayin Faruq ke lura da ita amma yayi kamar be ganta ba.
Da ƙyar ta zabo wata a ciki wadda a ganinta tafi ko wacce dama, irin wannan mai 8 piece ɗin ce, dusty rose color sai anyi mishi ado da bakin lace, dogon wando da kuma rigansa ta ɗauka, kafin ta maida saura kayan cikin jakar ta koma toilet.
“Hasbunallahi wani’imal wakeel” ya furta a fili sanda ta bacema ganinsa, wayoyinsa ya ciro da aketa kira ya kashe gaba ɗaya bayan yaga mai kiran nashi.
Gaban mirror dake cikin banɗakin ta tsaya tana kallon kanta, iya kyau rigar tayi maya kyau matuƙa, ita kanta taga hakan, sai gaba ɗaya babu sirri, don ƙirjinta ya fito sosai ta sama da tudunsu komai ana gani.
Ɗan ƙaramin tsaki taja tunawa da ko hijab bata shigo dashi ɗakin ba, damara ne ya faɗo mata dan haka ta saki murmushi ta jawo sabon towel ta rufe jikinta sannan ta fito
Bata kalla inda Faruq ɗin ke zaune ba tayi hanyar barin dakin har ta kama handle ɗin koma taji yana faɗin
“Hey you, sai ina kuma?” Daram taji gabanta ya faɗi, amma cikin ƙarfin halin data ara ta yafa ma kanta batare data juyo ba tace
“Ɗakina zan koma.”
“For your information, we’ll be together every night from now on, forever.”
A hankali ta juyo dan tabbatar da abinda kunnuwanta ke jiye mata, a cikin idanuwanshi nata idanun suka sauka, kasa jurewa kallonsa yasata janye nata idanun
“Gashina ya jiƙe kuma banaso na kwanta dashi a haka.” Tayi maganar tana turo bako, dan ta fara gajiya da al’amarinsa.
Cikin natsuwa ya miƙe ya isa gaban dressing mirror yaja kujeran, ya kuma buɗe wata drower dake gefe ya ciro hair drayer, sai daya seta komai sanan ya dubeta
“Madam bismillah ko” zuwa yanzu kam mamaki Faruq ɗin yake bata, bata da wani zabin daya wuce takowa a hankali ta zauna kan kujeran kamar yadda ya buƙata.
Towel ɗin tana rufe jikinta ya cire, farin bayanta da fararen damtsenta ya bayyana ga idanunsa, lumshe idanunsa yayi kafin sannu a hankali ya fara busar mata da gashi, cikin natsuwa Faruq ya gama gyara mata gashin ya kuma kama mata shi waje guda daga kasan kanta sannan ya shige banɗaki bayan ya ɗau towel ɗin data fito dashi
Kamar wata gunki haka Nadrah ke binsa da kallo, tana kuma ƙara mamakin yadda ya iya gyara mata gashin dan ko ita ta gyara baya kai haka, da wannan tunanin ta tashi ta maida komai inda taga ya ɗauko, ba jimawa shima yafito
A hankali ya zame ya zauna kan lallausan sofan dake gefan gadon, yana jin wani abu na tsarga masa mai tsananin ƙarfi cikin kowacce jijiya da hanyar jinin dake jikinsa, bai taba jin wani abu da idanuwansa suka jarabtu da kallo irin yarinyan nan, tun yana tuhumar kansa da ƙaryata kansa har yagaji ya fara gasgata zaton zuciyarsa, idan ya tuna da alkawarin da yayiwa wa kansa sai yaji ƙaramar natsuwa ta ziyarce shi, bayaso komai ya shiga tsakaninsu sai ya tabbatar ta fara jin wani abu game dashi, saboda bazai mata dole.
Cikin jikinsa ya janyota bayan ya kashe wutar ɗakin yana sinsinar ƙamshin jiƙinta, lakwas tayi tana sauraran duk wani abun da yake a zuciyarta kuwa karata duk wani adduan da yazo ranta takeyi.
“Calm down, ba abun da zan miki” ya faɗa can ƙasan maƙoshinsa saboda yadda yaji jikinta ya fara rawa.
Ta ɗauki lokaci mai tsawo tana karantar numfashinsa har sai data tabbatar yayi bacci sannan ta samu natsuwa, a hankali itama bacci mai cike da natsuwa ya ɗauketa.
Da asuba yana fita sallah itama ta tashi ta wuce ɗakinta, koda ya dawo bai nemeta ba system ɗinsa ya kunna dan ya ƙarasa aikin daya fara jiya saboda yau zayyi amfani dashi a office.
Da wuri ya shirya ya fice shiyasa koda ta tashi da safe basu haɗuwa ba, haka dai ta gyara gidan fes har ɗakinshi, tea kawai ta haɗa saboda yau wani irin kasala takeji a jikinta.
**********
Tun ƙarfe biyar yaso baro company ɗin amma zaman da yayi da ma’aikatansa daya ba aikin duba gidansa ya tsayar dashi, duk da ba wani aiki ne mai yawa ba amma yafiso ya zama daga nan ɗin akayi dan bayason matsala ko kaɗan, shiganshi office ɗin kenan Hisham ya shigo office ɗin ya kuma miƙa masa file ɗin hannunsa
"Ga sauran agreement din nan ka duba, idan komai yayi sai ka sanya hannu munata loosing opportunity dinmu, bansan a kwanakin nan me yasa ka kasa concentrating akan aiki ba, haka jiya ƙiri ƙiri baka shigo ba is there any problem?"
"Nop" ya amsa masa a taƙaice
"Okay....i hope so" Hisham din ya faɗa shima yana
miƙewa, bai sake komai ba suka fito tare suna tattaunawa.
Tun ƙafin ya ƙarasa bangaransu ya haɗu da Zaina take faɗa masa Nadrah na sashen Mami, dan haka yana shiga wanka yayi yana fitowa kuma suka haɗu da Dady suka wuce masallaci.
Tun daga nesa ya kasa kaucewa kallota, sanye da atampa ɗinkin riga da skirt wani irin sonta na ratsashi, tayi masa kyau matuƙa, dama sallah duk suka shiga itace dai tafito yanzu tunda har Faruq ya gama cin abinsa da Zahra tayi serving nasa.
Su suna cikin main falon suna hira Mami ta sako, gun Faruq ta ƙarasa dake ƙishin giɗe a ƙayataccen waiting falon dake can gefen dining ɗin
“Umar yaka zauna nan kai kaɗai kuma?” Tayi tambayar tana zama a ɗaya daga cikin kujerun.
Idanunsa dake lumshe ya buɗe kafin ya gyara zamansa
“Bakomai Mamina”
“Alhamdulillah kuma dama kai na sakko nema ai, Nadrah zata zauna a nan kafin ka kammala gyaran gidan, akwai shirye shirye da zamuyi” tayi maganar tana maida hankali sosai dan son karantar yanayinsa.
“Meyasa kuma Mami, wani irin shiri zakuyi da dole saita zauna nan.” Yayi tambayar da wani irin yanayi dashi kanshi bai san ya bayyana ba.
“Naga nan da can ɗin duk ɗaya ne babu wani banbanci, ɗazu nasa ta haɗo ƴan kayayyakin sawanta, ko kana da matsala da hakan”
“Shikenan Mami” ya faɗa yana kai dubansa wajan da Nadrah take, Mami batabi ta kansa ba ta miƙe zuciyarta fes cike da hamdala annashuwa da samun gamsashshiyar natsuwa.
Ɗakin daya kasance na Zaina ne kafin su koma kwanan ɗaki ɗaya ciki suka gyara ta shiga
Kayan jikinta ta cire ta ɗaura towel ta shiga wanka, bayan ta fito tayi tsaye gaban mirror tana goge ruwan jikinta ta ja dressing chair ta zauna tana qoqarin fara shafa mai
''Amma fa yau garin kamar da zafi, ki shafa kaɗan kada zafi ya dameki”
A tsorace ta waiwayo, yana kwance abinsa akan gadon nata hankalinsa kwance kamar a dakinsa yake, sanye yake da t shirt fara tal mai gajeran hannu sai three quater shima din fari ne tas, ga kuma jallabiyarsa daya cire a gefe
A hanzarce ta miƙe da gudu ta koma cikin banɗaki, tsaye tayi jikin ƙofar takaici ya cikata data bi jikinta da kallo, yanzun gwanin kallon mutane tasan ya gama ƙare mata kallo
Daga cinyarta ne kawai zuwa ƙirjinta a rufe amma ko ina na jikinta awaje yake, koda ta leƙa yana kwance bashi da niyyar tashi, danne dannensa ma yake a waya abinsa
“Idan zaki fito ki fito abinki, ni zuwa nayi na tambayeki, ba abinda kike tunani bane”
“Ya Faruq Mami fa, dan Allah ka tashi ka tafi, kada wani yazo ya ganka”
“Saboda ga kwarto ko? Ya faɗa yana murmushi mai sauti da tunda tasan Faruq bata taba ganin yayishi ba.……