Free chapter · Read without an account

Chapter 41

by Hauwa’u Abdurrasheed · SULTANIM

SULTANIM
      Na
Mss Samher

Instagram mss_samher
Tiktok mss_samher
Wattpad mss_samher


Page41


Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke bayan kiran sallar asuba ta farkar dashi, don sake haɗuwar jikkunansu waje ɗaya kunnashi ya soma yi, musamman tudun qirjinta da ya tokareshi da kyau kai kace da gayya tayi hakan, numfashinsa ya fara canzawa tare da bugun zuciyarsa, ya lumshe idanunsa yana jin yadda take sauke numfashi a hankali cikin galabaita da gajiya, yana tausayinta bazai iya sake taɓata ba taci wahalar daya kamata ace ya barta ta sake hutawa da kyau, da yaji abun yana neman fin ƙarfinsa sai ya zare jikinsa daga nata, ya sanya mata pillow cikin bacci ta kama pillow ɗin da hannunta da kyau murmushi yayi yadda tayi da fuskarta a haɗe kamar idanuwanta biyu ya bashi dariya, ya gama saara mata wajen shagwaɓa da raki.


Alwala ya shiga ya ɗauro,abun sallah ya shinfida ya gabatar da sallah ya tsaya sosai akai yana fuskantar ubangijinsa, ya masa baiwa a rayuwa cikin wannan rintsin rayuwar da mata na gari ke tsada da wahala.


Tun data sallarshi ta farka amma bata motsa ba, a hankali take shaƙar tattausan ƙamshinsa daya kama jikinta, ƙamshin da babu abinda yake tuna mata sai daren jiya, abubuwan da suka faru suka runga dawo mata sai ta dinga jin komai kamar a mafarki, kwanyarta ta dinga tuno kalaman da bakinsa suka dinga furta mata, sai ta sauke ajiyar zuciya me nauyi ta kuma lafewa akan gadon.
Shiya taimaka mata tayi alwala tazo kuma tayi sallah, sannan suka koma bacci.


                  A hankali ta fara buɗe idonta tana kasa kunnuwanta, Jin shuru ya tabbatar mata da baya ɗakin kwata kwata, don haka ta miƙe ta zauna sosai tana kallon lokaci ƙarfe kusan sha ɗaya da rabi na safe.

Zaune tayi tana tunanin ta yadda zata miƙe ko ina ciwo yake mata a jikinta, cinyoyinta kamar ba nata ba duk da ya ragu ba kamar daren jiya ba, sai ta yanke shawarar ta sake shiga banɗakin ta haɗa ruwan zafi ta yiwa kanta yadda yayi mata jiya.

Tana zuro qafarta ƙafa taƙi bata haɗin kai sai ta narke gaba ɗaya zuciyarta na karyewa, kada dai ace ya illatata gaba ɗaya ba zata sake moruwa ba? take ƙwalla ta cika mata idanu suka fara bin kuncinta, dai dai lokacin daya turo ƙofar ya shigo.

Fes fararen idanuwansa da suka sake wani haske suka sauka a kanta, yana sanye da wata tshirt wine color da baƙin wando, sai tattausan baƙin gashinsa daya sake sheƙi cike a kansa, ya sake wani fresh dashi jikinsa na fidda rikitaccen ƙamshin nan nasa.

Ƙasa tayi da kanta tana jin inama bata farka ba yayin da shi kuma murmushi yakeyi mai ƙarawa fuskarsa kyau da haiba, takowa yaci gaba dayi zuwa gabanta, yana ayyana yadda zai dasa zazzafar soyayyarsa a ranta, soyayya me zafi irin wadda yake burin ginawa a rayuwar auransa, soyayyar da zata zama abar kwatance, ya riga daya gama sallama mata rayuwarsa saboda haka bayajin akwai wani abu da zai musu shamaki a tsakaninsu.

“Good morning Chubby am" ya faɗa da wata murya dake cike da shauƙi, shauƙin da tunda ya tashi har ya fita ya dawo shine a zuciyarsa, wani irin unforgettable night da bazai taba shafewa a rayuwarsa ba muddin yana numfashi.

"Ina kwana?" Ta fada cikin girmamawa, bai amsa mata ba sai ya duƙa a gabanta, wata kima da daraja ya bata a rayuwarsa, ba ita kaɗai ba hatta Mami da iyayanta wanda ko saninsu bayyi ba, hannayensa ya zura ta ƙasan fuskarta sannan a hankali yace

“Get up, lemme help you” 
Fuskarta a narke irin na wanda ke shirin sakin kuka ta langabar da kanta gefe guda, ya fahimci abin da take nufi sai kawai ya miƙe a hankali yasa hannu kamar daren jiyan dai a tausashe ya ɗauketa ya nufi banɗakin da ita, yana tafe yana kallonta duk da ta cusa fuskarta a ƙirjinsa.
Bai sanyata dole kan cire kayanta ba amma ya tsaya ya gasata kamar jiya taji kuma ɗaɗin jikinta ƙwarai, fita yayi ya barta dan tayi wanka.

Manyan towel guda biyu tayi amfani dasu, ɗaya ta ɗaura a ƙirjinta ɗayan ta lullube kanta, baka ganin komai sai kwantacciyar sumar gaban kanta.

Yana tsaye ya waiwayo idanuwansa a kan fuskarta, sai yaga fuskartan itama tayi fresh kyakykyawar farin fuskarta na sheƙi na ɗaukar hankali, ya nufota a inda take tsaye daga gefan ƙofar banɗakin, tana tunanin ta yadda zata shirya yana cikin ɗakin, tunda an kawo mata komai nata tun a jiyan.

Idanuwanta a kansa kamar yadda nashi yake a kanta wani abu mai ƙarfi yaji yana fusgarsa zuwa gareta
Tsoro ya hanata motsawa daga inda take gani take kamar wani abun zai sakeyi mata, ya karanci tsoronta sai ya saki murmushin gefen baki har ya isa kusa da ita ya kuma manneta zuwa cikin ƙirjinsa.

A tare suka saki ajiyar zuciya yayin da yaci gaba da sauraren bugun zuciyarta yadda yake gudu da sauri sauri da alama akwai tsoro tattare da ita

A hankali ya zura hannayenta ya zagaya dasu zuwa bayansa ta yadda zata rungumeshi shima haka ɗin yayi, ya zagaye hannuwansa ta bayanta abinda ya ƙara musu kusanci sosai, tsahon wasu mintuna sannan ya jata a hankali, suka dinga takawa kamar me koyon tafiya


Gaban mudubi ya tsaidata, sannan yaja mata kujera ya kuma zareta daga jikinsa yace

"Seat here" a hankali ta zauna tana rintse idanunta saboda yadda wajen har yanzu yake mata ciwo, tsananin tausayinta na ƙara lullɓe zuciyarsa.


Man shafawar ya ɗauko ya bude ya dora saman mirror ɗin, ya lakato ya ɗaga tattausan tafukan hannunta da kallo da suke jazur saboda tsabar fari har wani kwanciyar jini sukayi, ya lakata mata man sannan yace

"Lemme help you" sai ya koma daga bayanta ya fara shafa mata a baya.


Idanunta ta lumshe kawai zallan mamakinsa dake addabar zuciyarta ko wani daƙiƙa na raguwa, gaba ɗaya kamar wani Faruq aka sauya mata duk ya kwance gaba ɗaya.

Wasu abubuwa taji suna mata yawo dukka jikinta, tana iya kallonsa ta cikin madubin yadda gaba ɗaya yanayinsa ya fara canzawa, tsoro ya sake cikata ta riƙe kukanta wanda ke shirin ƙwace mata, idan yace zai sake wani abu da ita ta tabbatar mutuwa zatayi.

Sosai ya dinga ƙoƙarin controlling kansa bayan ya gama shafa mata sai ya ɗauko hand drayer
Tsaiwa yayi shi da kansa yana kallon fuskarta ta madubi bayan ya gama gyara mata gashin ya kuma kame mata shi da band, fuskarta ta fito fayau kuma tayi wani irin fes idanunta sun sake girma da haske, sai ya sunkuya yayi kissing tsakiyar kanta yana lumshe idanunsa.
Ɗakin ya bari bayan yasata ta shirya ta fito ta sameshi su karya.


Cikin natsuwa ta shirya tsaf cikin wata crystal fabric, fabric ne mai matuƙar tsaɗa da haɗuwa amma sai akayi masa wani irin simple ɗinki daya ƙara fitar da ainahin kyawunshi, duguwar rigace amma sam babu hayaniya a tattare da ɗikin, sunyi mata kyau sosai, tattausan murmushi ta saki lokacin data dubi kanta a madubi, sai ta tsinci kanta da sanya kwalli da kuma lipgloss.


Kamar wani sakarai ko kuma yau ya fara ganinta haka ya saki baki yana kallonta, kallon kallo sukai ma juna kafin ta janye kallonta daga kansa.
Yana zaune a katafaran falon wanda shine hawa na biyu a cikin gidan, an ƙawatashi da luntsuma lutsuman royal furnitures masu ɗaukar hankali.

Manyan kulolin data gani saman table ɗin dake tsakiyar falon yasa tadan waiwaya ta dubeshi, ya fahimci me take nufi hakan ya sashi faɗin

“Oya come, Auntie mama ce ta aiko dashi" yayi maganar da mayen kallon nan nasa, ƙasa tayi da kanta sannan ta fara takowa a hankali har ta isa gareshi

 “You’re genuinely stunning Chubby am” Yayi maganar yana zaunar da ita a gefenshi, murmushi kawai tayi masa amma har zuciyarta tana ƙaunar wannan saban Faruq ɗin.

Suna cikin yin breakfast ɗin wayarsa tayi ƙara alamar shigowan kira, sai ya duba me kiran ɗan murmushin dake fuskarshi take ta ɗauke gaba ɗaya, ya tsani duk wani abun da zai haɗashi da Swafiyyah, blocking numbern yayi sannan ya gogeta gaba ɗaya daga wayarshi.

Duk yadda ta zata zai barta ne ta huta ita kaɗai hakan bai samu ba, don ko falon ƙasa Faruq bai sake leƙawa ba tare suke sallah dama komai, don hatta da girkin dare yana tare da ita a kitchen, waya ce a hannunsa yana duba saƙonni amma kuma ya kasa ya tsare da idanuwansa, gaba ɗaya ya aza mata wani nauyi baya minti uku cikakke bai ɗago ya dubeta da idanuwansa ba, duk sai tabi ta ruɗe ta kuma gaza sakewa


Haka dai da taimakon shi suka kammala girkin
Bayan sallan isha suna zaune Nadrah na kishin kiɗe a jikin Faruq, sau biyar Hisham yana kiransa yana katsewa, a ƙarshe ya amsa wayar amma sai ya sanyata a hands free ya ɗorata saman cinyarsa, idanuwansa akan fuskarta yake faɗin

“Kaga malan, wai anya lafiya kuwa?”

“Gaskiya ne mutumina, tun da safe nake kiranka amma sai yanzu Allah yayi, kana ma tunanin aikinka kuwa?”

“A inda nake yanzu ko Mami nasan zatamin uzuri, so faɗa me kakeso da sauri malan”

“Allah ya baka haƙuri, ya kamata ka shigo office gobe akwai files ɗin daya kamata ka duba” ya faɗa yana tun tsirewa da dariya.

“Nan da kwana uku in sha Allah, just take care of everything” daga haka ya yanke wayar.

Murmushi kwance saman fuskan Hisham, bai san wata kalar godiya zai wa Allah ba, Alhamdulillah shine kawai abun da yake iya maimaitawa.


Da daddare bayan ya sanyata ta gasa kanta tana tsaye bayan ta fito amma taƙi kallonsa, sai ya ƙaraso gabanta ya ɗora hannunsa saman nata 


“Meyasa bakison kallo na? I don’t like it this way please, ni da nakeso nan kusa ki haifamin twins.” Karon farko da murmushi mai cike da kunya ya ƙwace mata, sai ta juyo ta cusa kanta a ƙirjinsa tana murmushi, kafin kuma ta zare jikinta a nasa, binta yayi da kallo baiso hakan ba yaso ne su ɗan jima a tsaye ko hakan zai rage masa zafi.

Duk yadda yaso dauriya daren ranar ya kasa, dole ya sake kai kansa gareta saidai yadda ta dinga masa kuka cike da tsoro yasa ya haƙura, ya sanyata a ƙirjinsa yana sauke ajiyar zuciya kamar zai shiɗe, shi da ita dukka sun dauki dogon lokaci kowannensu baiyi bacci ba, saidai duk da haka ta rigashi yin baccin.


              
                Dukka kwanaki ukun da suka biyo bayansu kusan begenta ya dingayi, bai sake neman komai daga gareta ba saboda ta jigata a hannunsa


duk kuwa da cewa kawaici kawai yakeyi da kuma ƙoƙarin kame kansa, amma yana ji a jikinsa har yanzu bata sake masa jiki yadda yakeso ba, yanata ƙoƙarin ganin yabi kowacce hanya data kamata da zai dasa mata soyayyarsa a ranta amma baiga alamun komai ba daga gareta, saidai shi ɗin ya yadda da kansa ya kuma tabbatar babu macen da zata iya tsallake tarkonsa.


A hankali take buɗe idonta kamar mai tsoron cin karo da wani abun, fes ta saukesu akan Faruq dake kwance yana fuskantar ta, idanuwansa a rufe numfashinsa na sauka a hankaki, so take ta miƙe amma zuciyanta ta kasa bata haɗin kai, kyakkyawar fuskansa take kallo sai taga ya ƙara wani kyau da yana baccin.

Ta ɗauki tsawon mintuna tana kallonshi sannan ta tashi a hankali ta shiga banɗaki.

Wanka tayi ta shirya cikin  doguwar rigan atamfa wadda ta kamata daga sama daga ƙasa a buɗe, ta mata kyau sosai.

Breakfast ta shirya mai rai da lafiya kuma a ɗan hanzarce gudun karya makara, kammala shirya dinning ɗinta kenan taji an rungumeta ta baya 

“So am really living, i hope you will miss me” 
Saida Nadrah tayi da gaske sanan Faruq ya bar gidan bayan ya karya, don harya fara cijewa kan zai ƙara extra kwana biyu, ta dai samu ta lallaɓashi ya wuce.


Haka ta yini ita kaɗai cikin wannan katafaran gidan, lokaci zuwa lokaci ta kan kalli agogo tana kuma duban ta inda Faruq ɗin zai ɓullo, yau kawai da suka ɗauki awanni ba kusa da juna ba sai takejin tayi kewarshi matuƙa.


Ƙarfe shida ta fito daga wanka ana ta shiye shiryen kiran sallah magariba, a haka ta ƙarasa gaban madubi ta tsara kwalliya mai cike da tsari bayan ta mulke jikinta da nau'in turaruka basu ɗaukar hankali, gaban wardrobe ɗinta taje ta buɗe cike da tunanin wacce shiga zata yima, ta jima tana nazari kafin daga bisani ta fidda wata gown mai bala'in kyau, ash ce wadda aka mata ado da jajayen dutsina da kuma furanni, ta gyara gashinta tayi masa kanta ɗaurin v shape da jan ɗankwali, fashion ta saka na jajayen dutsina take ta fito gaba daya kamar wadda aka sauya
Babban hijabi ta saka ta tada sallah, tana idarwa ta sake duba lokaci ta cire hijabinta ta sake gyara ɗaurin nata kana ta fito falon, burner ta kunna dake lunguna na gidan duka ta sake sa turaren wuta.



                Tsayawa yayi tabayanta yana kallonta a hankali ya ƙaraso gareta hannayansa ya buɗe ya saƙalo wuyanta faffaɗan ƙirjinsa a daidai kanta ya kusanto da bakinsa ga kunnenta cikin calm and soft voice ɗinsa yace

“hey you! I miss you.

Juyowa tayi ta zubawa fuskansa ido shima ita yake kallo fuskanta ɗauke da murmmushi tace” Yay…. 

Yatsan daya ɗaura saman labbanta ya hanata ƙarasawa, idanunsu cikin najuna yake faɗin
“banasan sunan nan, a chanzamin wani.”

Manyan fararan idanuwanta da sukafi komai tasirantuwa a gareshi ta lumshe tanajin soyayyanshi yana ratsa duk wani tsoka da jinin dake jikinta.

Rungumota yayi a jikinsa, idanshi a kanta yake faɗin

 “You’re everything I’ve ever wanted, you complete me in every way, you’re more than enough, I LOVE YOU.”

Kallansa ta ɗago tayi da kyau, idanta da tuni sun ciko da hawaye, saita ƙara shigewa jiƙinsa tanajin wani irin annashuwa na ziyartan zuciyanta.

Hannu yasa ya ɗago fuskanta murya a sanyaye yace

“I’m really sorry for everything, for the pain, for making you feel like less.”

Shuru tayi kamar yadda shima yayi shirun tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi……

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.