Free chapter · Read without an account
Chapter 43/45 End
SULTANIM
Na
Mss Samher
Instagram mss_samher
Tiktok mss_samher
Wattpad mss_samher
Page43/45 END
Ƙarfe huɗu da wasu mintuna na yammacin ranan laraba su Zahra suka iso gidanta.
"Ina fatan dai Ya Faruq bai nan?" Zahra ta faɗa tana ɗan fidda idanu gami da watsa idanunta a babban falon gidan haɗi da kallon stairs ɗin, murmushi Nadrah tayi tana kaɗa kai
"Allah ya shiryeku, to baya nan" ta amsa musu kai tsaye.
"Au to, dama wai don mufi sakewa ne" ta faɗi tana dariya.
Zaina tace “indai Yaya da wannan matar tashi ne, yanzu ma kina iya ganinshi” ita dai Nadrah murmushi kawai tayi tunda tasan gaskiya suke faɗa, yanzu Faruq bashi da tsayayyan lokacin dawowa ko yaushe da yaji ganinta kawai zaka ganshi.
Ɗinkin bikin Hisham suka kawo mata tunda ranan juma’a ne ɗaura auran. Atamfa ne da kuma wani fabric material mai kyaun gaske, fabric ɗin gobe za’a sakashi na event ɗin mothers day, sai atamfar kuma na ranan friday.
Ɗinku nan sunyi mata kyau matuƙa, Mami ta kira tayi ma godiya sosai tunda ita ta siya duka kuma ta biya har kuɗin ɗinkin.
Basufi minti talatin da zuwa ba sai ga Hanifa da Ameerah, nan sabuwar hira ta ɓarke tsakaninsu.
Sun jima sosai suna hira dan har sai bayan magrib tukunna driver yazo ɗaukar su Hanifa, su kuwa su Zahra sai wajan ƙarfe tara na dare Mahmud yazo ɗaukarsu lokacin Faruq yana gida, yayi mamakin ganin Mahmud yazo ɗaukarsu amma dai bayyi magana ba har suka wuce.
Washe gari tun ƙarfe biyu saiga Faruq ya dawo gida, dama tun kafin ya fita ya faɗa mata babu wani mothers day ɗin da zataje.
Sam sam bataji shigowarsa ba sai tsintar kanta tayi jingine a ƙirjinsa ya zagaye ta da ƙugunta, ya sanya hannuwansa saman lafaffen cikinta ya kuma ɗora kansa saman kafaɗarta yana leƙen abinda take dafawa, da muryar dake wanzar da soyayyah a zuƙata yake faɗin
“Guess what? Goben ma fa kawai zan barki ki fitanne badan raina yaso ba amma please ki kula, ina da tsananin kishi Allah, look after yourself for me” sai ya sake mannata cikin jikinsa sosai kamar zai maidasu abu daya, muryarsa can ƙasa
“I LOVE YOU Chubby am” gaba ɗaya kalamansa sun kashe mata jiki kawai saita kasa ci gaba da yanka ball papers ɗin da takeyi akan chopping board, tana riƙe dai da wuƙar kawai a hannunta.
Sakinta yayi daya lura da haka sai ya zame ya dawo gabanta ya karba wuƙar ya fara yayyanka mata har yadda ya iya ya mata mamaki.
Kusan shi ya tayata dukka aikin sukayi suka gama tare, tun cikin kitchen ɗin ya zuba ya fara kaiwa cikinsa itace mutum ta uku a duniya da yakejin daɗin abincinsu fiye ma da yadda ransa yakeso, da ƙyar ya iya kaiwa falo ya zauna tayi serving nashi.
Daɗin sai ya masa yawa ya dinga jinsa yana yawo a wani gajimaren farinciki, yana ci yana kallon fuskarta har ya kammala.
Ɗaure da babban towel ta fito a wanka bayan ta baroshi a falo yana waya, a natse ta ƙarasa closet ɗin tare da fara neman kayan da zata saka saboda yanayin garin akwai ɗan zafi.
Shigowan Faruq yasa ta waiwayowa tana dubansa, ganin ya nufo inda take kai tsaye sai ta shagwaɓe fuskarta tana kallonshi.
Murmushi kwance akan fuskarshi “Why the face? Just wanna feel your....."
Sai maganar bakinsa ta katse, saboda tuni yakai hannuwansa inda ya nufa, kafin tace komai ya janye towel ɗin dake jikinta, sai tafara ƙoƙarin zamewa amma inaa, ya saka dukka hannuwansa biyu ya riƙeta sosai ta bayanta, cikin ƙanƙanin lokaci ya fara birkita mata kwanya saƙonnin da yake aikema ƙwaƙwalwartata sun girmama, sai ya zare kansa daga ciki yana dubanta da idanuwansa da suka sauya launi
"Please ki sanmin ɗan kadan, no more any pain.....i promise.....i promise Cubby" ya faɗa a ɗan ruɗe saboda yadda hankalinsa yayi gaba.
Bata jin dadi idan taganshi a gabanta cikin kwantar da kai yana roƙanta akan hakkinsa, a hankali ta gyada masa kai tana lumshe idanu, cak taji ya sureta yana cewa
“Thank you sunshine, thank you" ya azata a tausashe saman gadon ya maye gurbin bargon yana sanyata tsakiyar ƙirjinsa gami da sake lullubeta da wata tattausar soyayya mai tsayawa a ruhi da kuma gigita hankali.
Kaman yadda yayi mata alƙawarin kuwa babu wani sauran zafi data fuskanta, saima tarin kunya da ya barta da ita saboda yayi ta koya mata abubuwa yana sanyata tana responding masa saƙonninsa, abinda ya basu wani irin dare mai matuqar ƙayatarwa, daren daya sake narkar da kowannensu ya kuma sukurkutar masa da tunani, ya sake dasa musu so da ƙaunar juna mai tsanani.
Ko bayan komai ya kammala cikin jikinsa ya matseta tsam, idanunsa a rufe yake cewa
“Mu sa wannan kyakkyawar tafiya ta dawwama har abada, zan cigaba da ƙaunarki har zuwa numfashina na ƙarshe” wani irin abu taji yana sulalewa yana kwaranya a kwanyarta, ta gyaɗa masa kai a hankali ta lumshe idanu tana jinta a wata duniya ta daban, dama haka soyayya take? Ko kuwa itace Allah ya bata miji mafi nagarta da iya soyayyah.
*FRIDAY*
Shi da ita dukkaninsu a shirye suke tsaf, ita cikin material ne a jikinta sai kuma ta sanya babban hijabi, shi kuma cikin ƙananun kayane akwai inda zasuje da Hisham kafin lokacin ɗaura auran.
Tsaye take shima haka tana rungume tsakiyar ƙirjinsa suna musayar ƙamshin turarukansu, kowannensu ji yake kamar bazai iya tafiya yabar ɗayansa ba, cikin wata murya yace
"Shall we?" Ta gyaɗa masa kanta a hankali.
“Okay chubby.....but, inason naji kalma ɗaya daga bakinki, me yasa kikemin rowarta? baki taba gayamin ba" sai data ɗaga kai ta kalleshi
"Inaso kice i love you Umar Faruq" murmushi tayi tana cusa kanta sosai cikin ƙirjinsa, kunya takeji tun jiya ya gama sakwarkwatar da ita gaba ɗaya
"Please say it, ko kuma kawai a fasa fitar nan" kanta ta girgiza tana sauke ajiyar zuciya, tana jin yadda zuciyarta keta azalzalarta kan ta faɗa ɗin, cikin wata irin murya dake dauke da sauti na daban tace
"Ina sonka, ina ƙaunarka...i so much love you Ya Faruq"
Wani irin sauka maganarta tayiwa zuciyarsa daya sakasa sake wani irin murmushi me kyau da sauti daya sakasa janyota jikinsa yana haɗe kirjinsa da nata ya sakar mata murmushi me kyau daya sakata kasa dauke idanuwanta akansa ya kalli bakinta kafin ya maida idanuwanta cikin nata yace
“Matar Umar, da gaske daga zuciyarki ne?” yayi maganar yana shafa gefen fuskarta, saita jinjina masa kai cike da kwarin gwiwa, tana jin dadin kasancewarta a ƙirjinsa, akwai wata nutsuwa mai tarin yawa tattare da gurin.
“A moment forever etched in my heart, ke ce mafi kyawun ɓangaren rayuwata, thank you so much Chubby.” Da ƙyar suka yakice juna ya dauketa sai gidan Mami, bai shiga ciki ba saboda kiran da Hisham keta masa dama kuma Mamin tana can gidan su Hisham ɗin already.
Tun ta shiga gidan suka dameta da tsokana, irin wannan soyayyah haka Anty Nadrah, kinyi wani fresh sai kyau kike ƙarawa, saita sharesu saidai tana ta murmushi, saboda ita kanta tasan jiyan tabar mata abubuwa masu yawa da bazata. Su Zaina kuwa haka tayi haƙura da tsiyar da suketa mata har suka haƙura sukayi shuru.
Wuraran ƙarfe sha biyu da rabi duk suka shirya driver ya kwashesu zuwa gidan hajiyar Hisham, gida ya gama cika da ƴan uwa da abokan arziki Aunty mama, Hanan dama sauran yaran.
Dawowansu kenan daga reception ɗin da suka haɗa na bayan ɗaurin aure, saida suka tsaya a masallaci sukayi sallah la’asar sannan ƙalilan daga cikinsu suka taho gidan.
Yana tsaka da waya suka fito ita Zahra da Ameerah, ta glass ɗin dake jikin mota ya hangota, duk da bai juyo ba amma yana ganinta sosai sai ya lumshe idanunsa sannan ya sake buɗesu, yana ci gaba da ƙare mata kallo ta glass din ba tare data sani ba, har suka iso inda yake bai juyo ba bare yayi alamun ya gansu, saidai duk wani taku nata akan idanunsa ta saukeshi, kusantowarsu yasashi faɗin
“Let’s talk later” ya zame wayar daga kunnasa ya jefata a aljihu.
Ita sam bata ma lura dashi ba hankalinta yayi wajan Mahmud wanda dama dalilinshi ta fito daga ciki, magana yake musu su kuma sai dariya sukeyi saboda yadda yake ta sakin layi, babu wani tsammani taji an damƙi hannunta tare da soma janta batare daya ce da ita komai ba.
Da kallo duk suka bisu har ya isa ga motarsa ya buɗe gaban motan ya sanya ta a ciki sannan ya zagaya ya shiga ɓangaran driver, basu kama cika da mamaki ba sai da Faruq yaja motar ya bar cikin gidan da wani irin sauri wanda hakan ya soma ɗan jawo hankalin jama’ar dake harabar gidan.
“Ran maza ya ɓaci, nima fa wallahi ban kula dashi” cewar Zahra tana dariya.
Ameerah tace “nidai na ganshi amma ganin yana waya yasa kawai na share, kuma banyi ma tunanin ya ganmu ba”
“Nidai kar kishinsa yasa ya illatamin ƙanwa dama na lura dashi tun ba yanzu ba” Mahmud ya faɗa ranshi a ɗan bace.
“Haba kai kuma ranka ya daɗe, why the attitude? Yayana is the best husband ever yasan me yakeyi”
“And me” ya tambaya yana kallonta.
“The best boyfriend” kawai duk sai suka sa dariya.
Tunda ta shiga motar baice komai da ita ba sai gudu da yake shararawa, tana kuma jin yadda yake sauke numfashi da kuma ajiyar zuciya lokaci bayan lokaci haɗi da fidda wata iska daga bakinsa, da alama ransa a bacen yake duk sai taji babu dadi cikin ranta.
Sau kusan uku yana satar kallonta ya zaci zata nuna damuwa ko wani abu da yayi kama da haka akan gudun da yakeyi, amma sai yaga kamar ma batasan me ya faru ba abinda ya sake ƙular dashi ya dinga hadiyar zuciya shi ɗaya yana lumshe idanunsa haɗi da buɗesu.
Tun a gate security suka fara miƙa gaisuwa yana amsa musu da hannu saboda ba'a cikin yanayinsa yake ba, motar tasu ta shige zuwa cikin katafariyar harabar gidan suka tsaya a parking space.
Yana gaba tana biye dashi har suka isa ɗakinsa ya wuce batare daya mata magana, can ƙasan ranta sai takeji babu dadi sam, abinda ya ɗauke walwalarta itama gaba ɗaya, ɗaki ta shiga dan tayi wanka saboda tasan bazai kuma sake fita da ita a yau ba.
Tana zaune a balcony ɗin dake ta bayan ɗakunansu saman wani luntsuma luntsuman sopa da aka ƙawata wajan dasu, bayan ta shirya sai ta zabi tazo wajan ta zauna gabanta littafine take karantawa sai murmushi takeyi, musamman Ameerah ta kawo mata shi ranan da sukazo gidan.
Sosai hankalinta yayi gaba yana tsaye a bayanta bata sani ba hannuwansa cikin aljihun wandonsa, yana sanye da shirt mai gajeran hannu wadda ta zaune ta lafe a jikinsa, ta kuma fidda ƙirarsa na cikakken namiji.
Ji yake kamar ya dauketa ya hadiyeta, wani irin zazzafan so ne yake shigarsa zuwa kowanne sashe na jikinsa, sai ya fara takawa sannu sannu har zuwa bayanta, ya tsaya sannan ya miƙa hannunsa ta gefan kafadarta ya ranƙwafa faffaɗan ƙirjinsa yana gogar bayanta, ya sanya tafin hannunsa ya rufe rabin littafin.
Cak ta tsaya da karatun murmushi akan fuskarta, sai ga ɗaga kai a hankali ta waiwaya tana dubansa, take idanuwansu suka sarƙe waje ɗaya fuskokinsu gab da juna, numfashinsu ya fara gauraya waje guda kusan lokaci ɗaya kuma a tare kowannensu yaɗan lumshe idanunsa tare da buɗewa, Faruq ɗin baice komai ba, sai ya sanya ɗaya hannun nasa ya zare littafin ya ajiye, sannan ya saka hannuwansa biyu ya ɗagata cak ya kuma ɗorata saman table ɗin dake tsakiya, ya kuma maye gurbinta akan kujeran ya zauna a kai, ya matso dab da ita kamar zai shige cikinta, ya kwashi ƙafafunta ya ɗorasu saman cinyarsa.
Da kallo yabi ƙafafun nata farare sol babu digon komai a kai sai na baƙin lalle, hannu yasa ya fara mata tausa sannan cikin murya mai sanyi ya soma magana
“Am sorry for what i did earlier, bansan yadda zan canza kaina ba wajen ɗaukar duk abinda zuciyata ta gamsu da ta soshi da mugun muhimmanci ba, wallahi dan ma yayanki ne amma da saina sauke masa haɓarsa tukunna zan bar wajan dake”
Maganarsa ta ƙarshe ta bata dariya, fara’a sosai bayyane kan fuskarta har dimple ɗinta na nunawa
“Fear enough Ya Faruq, wannan fateemahr taka ce kai kaɗai”
“You deserve a gift, bari in baki” bata ƙara wani tunani ba ya miƙe tsaye ya sunkuceta, ta cikin balcony din ya buɗe ƙofar glass ɗin suka zarce bedroom dinsa.
Wani irin hot romance ya dinga aje mata da wasu kisses masu zafi, wani saƙo me nauyi da tsayawa a rai ya dinge ajema kowacce gaba ta jikinta, sun jima a haka kafin su nutsa duniyar ma'aurata, wadda suka jima da tsarata haɗi da killaceta da wasu irin abubuwa masu sanya abokin rayuwarka ya tsaya maka a rai.
Tana zaune gaban mirror yana busar mata da kai da hand drayer, ɗaure take da towel wanda ya ɗan zame kaɗan yana nuna fararen ƙirjinta da kuma tudunsu ta sama abinda yake yawan tafi da hankalinsa kenan, shima towel ɗin ne ɗaure a ƙugunsa, yana busar mata da kan idanuwanta na saman faffaɗan ƙirjinsa da ko yaushe yake burgeta, yana ɗaya daga cikin abubuwan dake sanya mata natsuwa idan ta kalleshi.
Hisham tun yana kiransa yana masifa har yayi fushi dalilin dayasa yaketa sauri kenan gashi an fara kiran sallar magrib
“Oya sauko ki shirya, don idan naci gaba da ganinki a haka komai yana iya faruwa” yayi maganar yana ajiye hand drayer ɗin, tun tana jin kunya idan yayi wani maganar har ta soma sabawa saboda da ta lura hakan dabi’arsa ce sam bayajin kunyarta.
Har ta miƙe ya kuma riƙo hannunta
“Chubby kin kashe min jiki, will you help me get ready?” girarta ɗaya ta dage masa kamar yadda yake mata kana ta kashe ido tace
“Why not”
Kai ya girgiza fuskarsa ɗauke da murmushi
“Lallai a shirye kike Chubby, irin wannan kashe ido haka, get ready for the second round idan na dawo.”
Hannu tasa ta rufe fuskarta tana dariya, ba wani ɓata lokaci ta gama shiryashi ta hanzari yayi kissing nata kafin ya bar ɗakin dan yasan Hisham ya gama cika dashi.
Wani irin weekend mai bada kala sukayi, weekend ɗin da tunda yazo duniya baijin akwai wanda ya fishi dadi a wajensa.
Ranan monday dolensa ya shirya ya fita da wuri tunda Hisham na hutu kuma akwai Schedule sosai a company.
Da rana Nadrah ta samu kiran Umma a wayarta har biyu, da zallar mamaki take kallan wayar kafin ta danna bin kiran, daga can ɓangaran Umma ta amsa tare dayin sallama cikin girmamawa suka gaisa sannan Umma ta soma magana
“Abbanku ne yake sanar dani abubuwan arziki kyautar mota dama saban gidanki da kuka koma, shima Mahmud haka, Allah ya sanya alkairi Allah kuma ya ƙara muku zaman lafiya”
Umma ta cigaba da cewa “Dan Allah Nadrah kiyi haƙuri da duk abun dana miki, haƙiƙa nasan ban kyauta ba, na mu’a malanceku da mummunar dabi’a daga ke har iyayanki wanda basu taremin komai ba, sai dan wata dukiya da Allah ne mai bada shi, nayi saurin haɗa Baffah da Nafisat dan gudun kada Abbanku yace zai aura masa ke, sai gashi ubangiji ya zaɓa miki wanda ko da a mafarki naga hakan ya faru zan ƙaryata kaina ɗari bisa ɗari, kwana biyu ya ɗauke ni kafin na samu ƙwarin gwiwar kiranki, duk da kalan wulakanci da zangwamar dana miki hakan bai hana ubangiji yayi miki ni’imar dani ko ƴaƴana bamu da ita ba, wallahi daga zuciyata nake neman afuwarki Nadrah harma dana su Aminatou idan zai yiwu”
Numfashin data riƙe tun soma maganar Umma ta sakeshi a hankali kafin cikin sassanyan murya tace
“Umma ni babu abun da kikamin amma idan ma akwai na yafe miki, maganar su Mama kuma kinsan babu wanda yake da ikon yafe haƙƙin wani, kawai abu mafi mahimmanci shine kin canza wannan kaɗai ya wadatar kuma nayi farin ciki”
“Nagode Nadrah, Allah ya ƙara miki zaman lafiya a gidanki, Allah kuma ya jiƙan mahaifanki” daga haka Umma ta sauke wayar tanajin nauyin da zuciyarta yayi yana kwaranya a hankali.
Nadrah kuwa adduar da Umma tayi na ƙarshe shine ya zauna mata a kai, dan ko lokacin rasuwarsu bata tabajin ta buɗe baki tayi addua kamar haka ba, tana fatan Allah yasa hakan ya ɗore da tafi kowa farin ciki.
*************
Gida ne suka taru suka ginashi cike da ni'ima ƙauna soyayya da kwanciyar hankali, wanda tsabar kula da haƙƙin juna wanda Allah ya ɗorawa kowannensu, kowa na ƙoƙarin sauke haƙƙin ɗan uwanshi a kansa kuma ya ƙara da kyautatawa wadda Allah ke sanyata tsakanin ma'aurata.
Manzon Allah SAW yace
“Mafificinku shine wanda ya fi kyautatawa iyalansa, kuma sanan yace “ni ne mafi alheri ga iyalina”
Kamar yadda Faruq ya sake tabbatarwa kanshi yayi dace da macen ƙwarai wadda har abada bazai iya rabuwa da ita ba, haka itama Nadrah anata ɓangaren tabbas babu shakka Faruq kyautar Allah ne, hikimar ubangiji bata da ƙarshe, a yayin data rasa iyayanta take da tabbacin kuma zama tare da Umma bazai taɓa mata daɗi ba sai auran Faruq ya raba ta da duk wata damuwa ya kuma sadata da mutane masu ƙaunarta, yanzu gashi da tayi haƙuri komai ya wuce.
***************
BAYAN WATA UKU
Haka rayuwa taci gaba da tafiya musu cikin hikima ta ubangiji, cike da farin ciki da yalwar arziƙi, tsantsar ƙauna da fahimtar juna a tsakaninsu.
Sun fara karatu a ɗaya daga cikin manyan jami’ar dake garin Abuja, duk da makaranta ɗaya suke dasu Zahra amma lokutan shiga aji ya banbanta saboda course ɗinsu ba ɗaya bane, inda ita take karantar gynaecology.
Mahmud da Musty tuni sun gabatar da kansu har manya sun shiga maganar an kai kuɗin aurensu, haka itama Ameerah inda zata aura yaran ƙanin babansu, Hanifa ce kawai babu a ciki dama itace ƙaramarsu.
*************
Kamar kowanne lokaci kafin dawowar Faruq da awa ɗaya ta kammala komai, haka yauma take ga Nadrah, bayan ta kammala ayyukanta ta faɗa wanka lokaci ta ɓata mai yawa gaban madubi tana tsara kwalliya kana ta fidda wata sexy fitted long gown, doguwar rigar fara ce sol mai zanen furanni masu launin ruwan hoda, tana kuma ɗauke da siraran hannu tayi mata kyau matuƙa, bayan rigar kusan rabinsa a buɗe yake, kusan kullum shigar Nadrah kenan don ƙa'idar Faruq ce, bata sanya manya kaya sai idan zasuyi baƙi ko da rana idan baya nan, amma ko dawowar rana yayi tofa sai anmasa kwalliya da shigarsa ya gani kana zai koma, saidai ko idan zasu fita unguwa wannan kam harda hijabinta.
Ta sake duban kanta ta tabbatar komai yayi daidai, ita kanta tayaba irin kyawun da tayi, ta rasa me yasa take ƙara wani kyau tare da cika har wani kumatu ta ƙara, ta sake fesa turare sannan ta fito.
Shigowarshi cikin falon yayi dai dai da saukowarta, tunda ta taho din ya zuba mata idanu ko ƙiftawa bayayi, a kullum kwanan duniya sake ninka masa ƙaunarta ake cikin zuciyarshi, har ta ƙaraso bai sani ba sai data sa bakinta ta hure masa ido tare da shigewa jikinsa.
Ya saki murmushi yana mai saka hannunsa ta bayanta
“You seem really tired hubby, gaskiya idan sukayi wasa zamuje hutu, akan me za’a ɗinga wahalarmin da Ya Faruq ɗina” tayi maganar a shagwaɓe.
Ajiyar zuciya ya saki yana murmushi
“Sosai kuwa Chubby, amma wai.. Chubby ina da tambaya” yayi maganar yana bin ko ina na jikinta yana shinshinawa saboda irin ƙamshinta dake gigita shi.
“Ina jinka Hubby” tayi maganar itama tana kallonsa cikin ido.
“How can i stop loving you this much, yana neman ya hallakani fa” dariya ta ƙyalƙyale da ita tana sake narkewa cikin jikinsa
“Saidai a ƙara maka wani a kan wanda kake min, so nake kayita sona over and over again, saboda ni ina da tabbacin bazan taɓa iya daina sanka ba”
“Wayyo Allah zuciyata” ya faɗa yana dafe daidai zuciyar tasa, cak ya ɗagata suka haura sama.
Ya sani a bisa al'adarta kafin ya dawo ta haɗa masa ruwan wanka don haka ya wuce da ita banɗakin kai tsaye, tuni ido ya soma raina fata don ta gano ƙarshen zancan, yau kam kwalliyarta saidai ta sake wata, da sauri tace da shi
“please masoyi ka saukeni, zan tayaka ma wankan”
Dariya ta bashi ya dubeta irin salon da tayi mana ya kwaikwaya
“Kin riga kin makara masoyiya” yana gama faɗa ya sanyata tsundum cikin bathtube sannan ya fidda kayan jikinsa ya bita ciki, sai da suka gama shan ƙaunarsu kafin suyi wankan su fito.
Yana baje saman tatausan carfet ɗin falon Nadrah tana hidimar zuba masa abinci don a ƙasa yafi cin abinci, sanye yake da gajeran wando shi kaɗai ne jikinsa sanyin AC na ratsashi, ta riga ta saba da kallo irin na Faruq indai yana kusa to fa dukkan idanunsa na kanta, bata damu ba hasalima jin dadin hakan takeyi don yana sanya shi farin sani, ba macen data isa ya tsaya yana kallonta to ita ɗin halaliyarsa zata hanashi more kallonta, ya faɗa mata ba sau ɗaya ba kallonta na jefashi cikin nishaɗi.
Sai data lakuce masa hanci sannan tace “Hubby am”
“Chubby am” ya faɗa yana murmushi, ta tura masa plate ɗin abincin wanda ke ɗauke da lafiyayyen waina da yayi kyau ya tashi, tayi pairing nashi da miyar taushe wadda tasha tantaƙwashi da naman sa da manshanu.
Ita kuma ta jawo wani cup na plastic tare da abun zuba sugar ta buɗe ta fara haɗa garin kwaki da suger da soyayyar gyada, cak ya tsaya yana dubanta ita kam batasan yana yi ba har wani tsinkewa yawunta yake kamar wadda taga wani abun dadi, sai da ya kira sunanta sannan ta ɗago kai, ganin yadda fuskarsa ta canza ya sanya jikinta yin sanyi, don ko kusa bata ƙaunar ta zama sanadin bacin ransa
“Amma ya mukayi da ke jiya? kika cemin sha'awarsa kike na barki kika ci kayanki, bazai yiwu ba gaskiya”
Tuni qwalla ta cika idonta, saboda idan taci abincin ji take kamar numfashinta zai ɗauke, wani lokaci sai tayi amai takejin dadi ba bata lokaci hawaye suka fara sauka saman fuskarta
Idonshi ya runtse don babu abin daya tsana kamar gani hawayenta
“Ya salaaaaam daga magana sai kuka kuma?matsonan muci abincin ko yaya ne idan muka gama sai ki faɗamin kalan abincin da kikeso ni kuma zan nemo miki shi, amma wanann hawayen ƙona min zuciya yake” ya fada yana daga mata hannu alamum ta taho, ba musu ta matso jikinsa tana goge hawayenta cike da son ta faranta ransa ta fara cin wainar sai dai ko guda ɗaya bata cinye ba amai ya taso mata, da sauri ta miƙe ta shige toilet tun tana yinsa tana fidda abincin da taci da garin da tasha dazun har ya koma bata iya harar da komai, gaba ɗaya hankalinshi a tashe yake gani yake shine sila da ya takura mata, bai samu nutsuwa ba sai da yaga bacci yayi gaba da ita, duk son da yakewa wainar kaɗan ya iya cin.
Cikin baccinsa ya dinga jin ƙamshin girki da sauri ya farka yana ya mutse idanunsa, kenan ita ke aikin girki a kitchen ƙarfe takwas na safe? da hanzari ya diro daga gadon
Tsayawa kawai yayi yana kallonta tamkar ba ita ta gama sheƙa amai jiya ba, tayi kwalliayarta tayi kyau kamar ka saceta ka gudu, ta gyara gashinta yayi kyau sosai.
Ji tayi kawai an rungumeta ta baya sai ta saki yar ƙaramar dariya
“Hubby ka bani tsoro.”
“Nima ai kin bani tsoro Chubby, ke da baki da lafiya ina ke ina shigowa kitchen fisabilillahi.”
Waigowa tayi suna fuskantar juna, murmushi ɗauke a fuskokinsu yana zagaye da ƙugunta, ta shafi sajensa sannan tace
“ina mai tabbatar maka idan za'a saka tsere sai na wuceka.” dariya ya saka ya sumbaci kumatunta
“babu musu don naga alama, wai Chubby meye sirrin ne? Amma ba damuwa nasan me zanyi”ya faɗa yana kashe mata ido.
“Me zakayi?”
Kallonta ya tsaya yi batare daya bata amsa ba, sai ta zame jikinta daga nashi tana cewa
“Ka gani ko? shi yasa idan ina abu mai muhimmanci banso kazo ka riskeni, don sawa kake in manta da kowa da komai ciki harda kaina”
Shi ya ƙarasa haɗa kayan karin tana tayashi da wasu abubuwan.
Bayan sun gama sukayi wanka ya sata ta shirya wai akwai inda zata rakashi.
*************
Tafe suke a motar gunun sha’awa hannunsa guɗa ɗaya yana cikin nata yana shafawa a hankali suna kuma taɓa hira, kallomsa tayi bayan taga inda ya kawota.
“Me zamuyi a asibity kuma”
“Nasan me yake damunki mana, kwana uku kenan kukkun sai kinyi amai, bakisan yadda hankalina ke tashi bane shiyasa, oya fito muje”
Bai jira amsarta ba ya fito daga motar sannan ya zagayo ya buɗe mata ɓangaran da take, haka ta fito tana turo maki suka nufi cikin asibityn.
Kai tsaye office ɗin Dr. Farida ya wuce, abokiyar karatunsa ne sun san juna tun da daɗewa.
Cikin mamaki Dr. Farida take kallon Faruq yadda yake mata mayani abun dake damun matarsa cike da damuwa, bayan ta gama rubuce rubucenta ta ɗauki sample ɗin jini tace su jirata tana dawowa.
Bayan mintuna sha biyar sai gata ta shigo murmushi akan fuskarta
“Congratulations Archi, you’re going to be a dad in sha Allah.” Duk idanu suka zubawa Dr. Farida, Faruq gani yake kaman tana masa wasa ne ko kunnuwansa basuji masa da kyau ba.
"Really?" Kai ta jinjina masa tana murmushi.
"Pretty sure, yanzu zamu iya zuwa ayi scanning don a tabbatar da lafiyar komai, watanninsa da kuma expected date of delivery ɗinta"
“Alhamdulillah alhamdulillah" shine abun da Faruq kawai yake maimaitawa, ya waiwaya ya kafe Nadrah da ido kamar zata ɓace, itama su take kallo kamar batama cikin hayyacinta.
Batare da ɓata lokaci ba suka isa ɗakin scanning cikin ƙwarewa ta fara aikinta, hoton tayin jarirai biyu radam ya bayyana kan fuskar na'urar, tsura ido sukayi shida Nadrah ɗin suna kallon ikon Allah.
“Amma gaskiya Archi nayi mamaki, ciki wata huɗu amma daga kai har ita babu wanda ya fahimci hakan”
Zamewa yayi a hankali zuwa gaban Nadrah sai ya zauna gefanta fuskarsa na fidda murmushi, ya taimaka mata ta zauna sosai
"Congratulations to both of us Chubby am" binsa tayi da kallo tana murmushi.
"Kizo gida ki duba parking lot na gidan duk motar data yi miki ki dauka, shine tukuicinki".
Sosai farinciki ya kama Dr. Farida, godiya tayi masa sosai sannan suka bar asibityn bayan kammala musu abun daya dace.
*************
Zaune suke gaban Mami kusan mintuna ashirin kenan sai kallo kallo sukeyi tunda suka gaisa babu wanda ya sake magana kuma da alama akwai ta a bakimsu, ta sake ɗagowa karo na biyu ta dubesu
“uhmm idan kun shirya yimin magana sai ku dawo, yanzu dai inaga ku tashi ku tafi kawai.”
Mutsu mutsu ya shiga yi kana cikin inda inda yace
“Mami daga asibity muke”sai ya miƙa scanning ɗin da akayi. shuru Mamin tayi tana nazari scan ɗin, babu shakka ta daɗe tana yiwa Nadrah kallon mai cikin, jin shiru babu wanda yayi maganar daga ita har shi ko twins ya sanya itama ta tsuke bakinta ta bisu da addu'a.
Tsantsar farin ciki da murna wajan Mami ba’a cewa komai
“Allah ya shiryeku, ciki wata huɗu wannan da a ƙauye kuke sai Allah , yaron Mami will soon be father of twins, Allah ya inganta mana”
Tashi Nadrah tayi ta barsu a wajan, dan shi kanshi Faruq ɗin sai soshe soshe kawai yakeyi.
Sai can dare Faruq ya ɗauketa suka wuce gida.
A hanya tace tanason cin cake ya tsaya a wani babban bakery shi kaɗai ya shiga ita kuma ta jirasa a mota, baifi minti goma da shiga ba ta hangoshi ya fito da hanzarinsa sai sauri yakeyi, bata gama tantance me yake faru ba budurwar data biyoshi da gudu tasha gabanshi.
“What the hell is happening to you Faruq? Me kake nufi da kar nayi embarrassing kaina?” Swafiyyah ta faɗa cikin tsananin tashin hankaki.
Ta gefenta yake ƙoƙarin wucewa amma babu tsammani yaji ta riƙe masa hannu, cikin tsananin bacin rai ya ɗaga hannu ya wanke fuskarta da mari, tun a cikin wajan ya mata gargaɗin ta rabu dashi amma taƙi sauraransa, ta tsaya bashi labarin ta samu hutun ne tazo ganinshi tunda tana ta nemansa a waya bata samu, ransa ya gama ɓaci gaba ɗaya, cikin kaushin murya yace
“I’ve been trying to control my self amma sai da kika ƙureni, I’m happily married, ki fita harkata kije kici gaba da rayuwar da kika zaɓa ma kanki, rayuwar dake tattare da ɓata da danasani, wallahi ina ƙara gargaɗanki idan kika kuma shiga gonata saina saɓa miki” daga haka ya wuce ya barta tsaye dafe da kumatun ta zuciyarta na bugawa, kenan yasan abun da takeyi shiyasa yayi avoiding duk wata hanyar da zai haɗa ta dashi.
Wani kallon ƙurilla me ɗauke da mamaki da kuma
fargaba Swafiyyah ke bin Nadrah dake zaune gaban mota ta haɗe girar sama data ƙasa, zuciyarta na ƙiyasta mata wannan ce matar Faruq kenan?, she's very beautiful, tana da wani irin kyau daya daki zuciyar Swafiyyah ya kuma kashe sauran ƙwarin gwiwan dake tare da ita gaba ɗaya.
Tafe suke a hanya babu wanda yayi magana, zuciyarta har wani tafarfasa yakeyi kukan da take ta ƙoƙarin dannewa ne ya kwace mata, sosai take kuka har tana shiɗewa.
Shima ransa a ɓace yake amma kukan da takeyi ne sam mazai iya jura ba, guri ya samu yayi parking sanan ya jawota jikinsa, kuka takeyi tana kuma turesa da iya ƙarfinta sosai ya riƙeta cikin ƙirjinsa yana shafa bayanta harta fara sauke ajiyar zuciya.
A hankali ya ɗago fuskarta sai yaga bacci ma tayi, gefen wuyanta yayi kissing kafin ya tada motar yaci gaba da tafi.
Ba ita ta farka ba sai ƙarfe goma na dare shima amai ne ya tada ita, kafin ta fito Faruq ya haɗa mata tea, tasha ta haɗa da cake ɗin daya siyo ɗin sai hararansa kawai takeyi, kamar yadda batayi magana ba shima sai ya taɓi yayi shiru ɗin kawai, yana ta ƙoƙarin lallaɓata.
*************
Cikin lokaci ƙanƙani labarin cikin ya karaɗe dangi, wani irin murna da farinciki suka tsinci kawunansu, Umma na falon Abba tana gyara masa lokacin da Mahmud ya kira Umma yake sanar da ita a fakaice, ta sulale ta zauna tana ambatar sunan Allah, Abba ma yayi farin ciki sosai matuƙa.
Ɓangaran Dady ma hakan take, gata dai kam ba’a ma maganarshi a nan wajan.
Mami harda kukan farin ciki, ckin sigan zolaya Dady yace da Mami
“Ashe dai Aishatu anason samun jikoki, harda kuka haka?, Faruq din dai shine na gaban goshin dai.”
**********
Sosai ya dinga tsokanarta tare da lasafta mata burikansa akan cikin, burikan nasa masu yawa ne har ta gaji da tayashi lissafawa, sun jima a jikin juna suna wata irin hira dake haifar da sabuwar soyayya da kuma shaƙuwa ta musamman, idan tayi magana sai yace dumin babyns yakeji.
Musamman Umma ta tura mata Talatu a cewar yaro ɗaya ya aka ƙare balle biyu, gara wani babba ya kasance a kusa.
Tun ranar da Talatu ta iso gidan ta koma ƴar kallo hakanan ta dinga kame kanta waje ɗaya, saboda gaba ɗaya Faruq ɗin ya kunce mata tunani, ashe haka yake? wata irin wutar soyayya ke tashi cikin gidan, saidai cikin salo da ban sha'awa da kuma ƙayatarwa, ya ɗauki kulawar Nadrah gaba ɗaya ya aza a wuyansa, abinda Talatu kawai keyi kula da gidan da kuma girki.
Ta fannin Nadrah kuwa sai yanzu tasan meye ainihin ma'anar gata, tako ina lelenta akeyi Umma ko yaushe tana kira, Auntie mama tayi nata ga kuma Mami.
Ko yaya Nadrah ta motsa sai a kawo mata cafka, ta ko ina gata da kulawa take samu, ba abinda Nadrah keyi saidai taci abinda ranta keso tasha abinda ranta keso, duk da cikin yazo mata da laulayi sosai, amma tana samun sauƙi saboda akwai masu ɗebe mata kewa.
Saidai fa duk yadda gidan yakai ga mutane da zarar oga Umar Faruq ya dawo zai ɗauke abarsa ya wuce ɓangaransa da ita, ita kanta Nadrah ƙorafi take masa ya dinga hutawa yaji da aikin office kawai amma yakance
"Da da hali zan ajjiye komai ne nayita rainon cikin nan har sai randa kika haihu.”
Tako ta ina babu abinda zata cewa Allah sai godiya, cikin lokaci ƙalilan Allah ta’ala ya canza mata rayuwarta gaba ɗaya, bata da wani sauran ƙunci ko kuma damuwa kwata kwata.
*************
Lokaci me tsayi suka ɗauka a cikin yanayin da daƙyar ya isa samun yar gamsuwar da zai iya
riƙe kansa ya dawo daidai yana sauke numfashi me zafi a kirjinta sbd rungumeta da
yayi tsamtsam yana kwantar da kansa a kirjinta idanuwansa a lumshe.
Itama lafewa tayi a jikin nasa kanta na kwance a nasa kan dake kirjinta ƙamshin gashinsa me daɗi yana shiga hancinta, ta lumshe ido tana jin tsantsar kaunar ƙamshin da jinsa har cikin ranta.
Bayan sun samu tsarki suna zaune a falor Nadrah na saman cinyar Faruq sai loda masa abinci takeyi.
Spoon ɗin takai bakinsa tana cewa
“Haaaa” cikin wata muryan daya sakasa buɗe bakin yana fidda tattausan murmushi.
Zuba masa abincin tayi kaɗan tana kallansa, a hankali yake tauna abincin har ya haɗiye yana ƙin dena mata kallan dayake mata.
“Dan Allah Ammin twins ki barni haka, na ƙoshi fa.”
Kunnansa ta kama da ƙarfi har sai daya saki ƙara sanan ta sake
“Na faɗa maka banason sunan ai, sai kace wata tsohuwa”
“Shikenan masoyiya na bari, amma ni banga komai a sunan ba, idan kinaso ki kirani Dadyn twins har kyauta zan baki” yayi maganar yana shafa cikinta daya ɗan fara fitowa.
“That girl in the bakery, she most be Swafiyyah right?” Tayi tambayar yanayin fuskanta na canzawa.
“Hmmm Chubby why now? Wallahi kinga baki bini bashin rantsuwa amma na rantse miki da wanda raina ke hannunsa ko tunawa da ita banayi, banaso na zaƙe da sai nace miki I HATE HER.”
“I just decided to, har da wani riƙe maka hannu saboda iskanci” ta faɗa idonta cike da kwalla.
Rungumeta yayi tare da kissing goshinta tattausan murmushi akan fuskarsa
“Kinsan menene?” Kai ta girgiza tana turo siraran labbanta, sai da ya sumbaci lips ɗin nata sannan yace
“Idan kika cire Mamina kece mace ta biyu da matsayin da babu mai irinsa a gareni, I love you, and i want to spend the rest of my life with you.”
“And, i also want to spend the rest of my life with you.” Ta faɗa kyawawan fararan manyan idanunta cikin nashi, da wani irin murmushi mai narkar da zuciya.
TAMMAT BIHAMDILILLA
Alhamdulillah a nan na kawo karshen littafin SULTANIM (my queen), kurakuren da nayi a ciki Allah ubangili ya yafe min, I dedicate the book SULTANIM to all my FAN, thank you so much for the support thank you for bearing with me, thank you for the encouragement and prayers always.
I am glad i got a chance to interact with such beautiful souls and finally SULTANIM conversation group Ya Subhanallah, naji dadin mu'amala da ku, kuma zan yi kewan ku fiye da tunanin ku,
HAFCEIY, Ummeeeterh, khadija adam, Aisha, Halima bature, sadee, shatou_y, salima musa gambo, ruqayyahtou, sadee, kitchen by hibbatu, leemerh_bintu dalha, I wish i can mention all ur names here sai dai i can't, thank you soo much my people for being patient with me daga farkon SULTANIM har zuwa yau da muka yi page ɗin karshe, I LOOOOOOORRRR YOU.……..