Free chapter 路 Read without an account
CHAPTER 21
*HARAMTACCIYAR GADA.*
_*{Ha蓷uwar rayuka da 茩addara ta tattara wuri guda.*馃敟馃挃}_
*NA*
*HAFSAT MUSTAPHA ('Yar Mutan Naija).*
*SADAUKARWA GA UWAR茒AKI NA: HAJIYA ZAINAB AHMAD (Hajiya Mama). Amincin Allah da ni'imominsa su tabbata a gareki Uwata.*
*BOOK 1*
*Page 21.*
Sai da su Yallabai suka shige 蓷akin da aka kwantar da Saffy kafin Jidda ta waigo ta dire idanunta a kan kofa, sai sauke numfarfashi take, tana ji kamar zata shi蓷e.
Cikin 茩arfin hali ta ja jiki zuwa kan doguwar bench da ke nan kusa da ita ta zauna sannan ta ha蓷e cinyoyinta ta kifa kanta a kai.
Saffy na ganin shigowar tawagar mutane ta yi saurin mi茩ewa zaune, idanunta ya sauka kan Yallabai. 茦irjinta ya yi wani irin 蓷okawa, nan take tsananin kwarjininsa yasa ta ji gaba 蓷aya tana neman rasa natsuwarta.
Dakyar ta samu ta daidaita natsuwarta, kamar wacce aka tsikara da allura ta mi茩e da sauri ta jawo hijabinta tana 茩o茩arin sanyawa, a lokaci 蓷aya firirin hancinta na sha茩ar da蓷a蓷ar kamshin tsadaddun turarukansu masu sanyi daya ba蓷e ko ina.
A karo na biyu ta sake kai kallonta garesu.
"Sannunku da zuwa."
Ta furta sannan ta saddar da kai kasa sabida wani irin kwarjinin Yallabai da ke neman kashe mata ido.
Abokansa, Alhaji Nasir da sauran su ne suka amsa mata cikin fara'a suna tambayar jikinta, amma shi Yallabai uffan bai ce ba sai kura idon da ya yi kan 蓷inkin da aka mata, nan take ya ji wani sabon tausayinta ya 蓷arsu a ransa.
Su Alhaji Nasir suka zauna kan doguwar kujeran da Saffy ta tashi akai, shi kuma Yallabai sai daya kwashi mintina kusan biyar kafin ya jawo stool da Chef Ali ya ajje masa sannan ya zauna yana sauke ajiyar zuciya wannan karon kansa a kasa. Dakyar ya iya kai hannu ya zare farin glasses 蓷insa sannan ya sake 蓷aga kai ya sauke jikakkun idanunsa a kanta.
"Baiwar Allah ki yafe ni, I'm sorry you went through all this because of me."
Abun mamaki ruwan hawaye ya balle kan fuskar Yallabai. Abun ya ba Alhaji Nasir da sauran abokansa mamaki matu茩a, domin duk wanda ya san Yallabai ya san ba kowane abu ne ke iya karya masa zuciya har ya zubar da hawaye ba.
Saffy ta bu蓷e baki za tayi magana amma ta kasa sabida kukan data ji yana neman taso mata, hakan yasa ta za蓳i yin shiru.
Ganin kamar babu hanki a tare dashi yasa ta nufi inda tissue paper yake, ta 蓷anyi rolling sannan ta yanka ta nufe shi ta mi茩a masa.
茒agowa ya yi yana kallonta.
Ta ce"Kar蓳i ka share hawayenka, ina so dani da kai mu 蓷auka cewa abin da ya same ni mu茩addari ne daga Allah."
Sosai ta burge abokansa, shi kansa ya ji da蓷in yarda da tayi da 茩addara.
Dr. Anderson, likitan dake kula da lafiyanta ne ya yi gyaran murna bayan ya lura da yanayin da duk suka shiga don itama 茩walla ne cike idanunta amma gudun kar su gane yasa take sa tissue tana sharewa da wayau.
Ya dubi Yallabai ya ce"Ranka ya da蓷e kana so ka mayar mana da aiki baya fa, ji bi yadda kake sa patient 蓷inmu zubar hawaye."
Ya furta yana dariya, kowa ma dariyan ya yi har Saffy. Daga haka likita ya fita ya bar su.
Dr. Haseeb ya ce"Daddy da gaske fa so kake ka mayar mana da aiki baya." Ya fa蓷a a wasance.
Yallabai ya murmusa ya ce"Haseeb, ku yi hakuri kowannemu na da yadda yake ji a ransa ne."
Su Alhaji Nasir suka ce"Haka ne, Allah dai ya kiyaye gaba." Aka amsa da "Ameen."
Dr. Haseeb ya musu sallama don akwai wani aiki da ke gabansa kuma jiransa ake.
Saffy ta dube shi ta ce"Thank you so much sir."
Haseeb ya murmusa ya ce"You are welcome ma! Allah ya 茩ara miki lafiya ya kuma kiyaye gaba."
Ta amsa da "Ameen." Daga haka yasa kai ya bar 蓷akin gashi har zuwa wannan lokacin Saffy bata san cewa shi mijin Samha, uwar蓷akinsu bane.
Ko da Dr. Haseeb ya fita, sam bai gane cewa Jidda ke zaune ba saboda hankalinsa baya wajenta, yana tunanin aikin da zai yi ne.
Dariyarsu da Jidda keta ji sosai ya 茩ara daga hankalinta, sai ta ji kamar ta fa蓷a 蓷akin domin ta ga abin da ke faruwa. Haka dai ta dunga tausar kanta don already ta riga ta kai wuya, 蓷auriya kawai take, haka kawai take ji a jikinta Saffy na neman 茩wace mata secret husband 蓷inta.
Har Dr. Haseeb ya fito ya tafi bata sani ba saboda ta dukar da kai, zuciyarta na tafarfasa. Bata san cewa tana da zafin kishi ba sai yau.
Fitowar su Alhaji Nasir ne yasa tayi saurin 蓷agowa a tsorace don bata tsammaci fitowarsu da wuri haka ba. Sun gama dubiyarsu sannan suka sallami abokinsu suka fito sabida zuwa su kama harkokin gabansu.
Idanun Alhaji Nasir direct a kan Jidda ya sauka, yanayinta ya tabbatar masa da lallai tana cikin damuwa. Duk kusancinsa da Yallabai bai san cewa ya yi auren sirri ba. Abin dai an yi shi ne a 蓳oye kamar yadda Jiddan taso.
Har sauran sun yi gaba, shi ya ja da baya yana
"Baiwar Allah lafiya kike kuka kuwa?"
Ita sam bata ma fahimci cewar hawaye idanunta ke tsiyayar wa ba sai da ya yi magana a sannan ta ankara. Gabanta ya yi wani irin bugawa da 茩arfi, da sauri ta kai bayan hannu tana goge fuskarta, da disasshiyar murya ta ce"Ba komai, lafiya lau nake."
"Lafiya ce za tasa mutum zubar hawaye haka? Duk wanda ya ganki ya san kina cikin damuwa."
Ganin zai addabeta da tambayoyi yasa tayi maza ta ce"Ina tausayin halin da yar'uwata take ciki ne har ban san idanuna na tsiyayar da hawaye ba."
"kina nufin yarinyar da aka illata a fuska da ke kwance a wannan 蓷akin?"
Da sauri ta daga masa kai "Eh, yar'uwata ce."
Kuka ya ci mugun 茩arfinta wanda ita ka蓷ai tasan ainihin abin da ke damunta bayan Allahn daya halicce ta, amma wani zai yi tunanin ko tsananin tausayin Saffy ne yasata wannan kukan.
Cike da tausayawa Alhaji Nasir ya rausayar da kai ya ce "Yi hakuri ki bar kukan nan, haka Allah ya 茩addara mata, fatanmu a yanzu Allah ya bata lafiya."
"Ameen." Ta furta dakyar.
Kuka ne tayi shi kasa-kasa amma sosai ya ta蓳a Alhaji Nasir, sauran abokan da suka fahimci kamar baya biye dasu suka waiwayo, nan suka gan shi tsaye kusa da Jidda har ma yana 茩o茩arin bu蓷e jakar kudinsa da zai kai banki ya yi deposit na ku蓷in kasuwancinsa. Ya sa hannu ya ciro bandir 蓷aya ya mika mata.
"Ga wannan ba yawa dubu 蓷ari biyu ce kwa 茩ara a ku蓷in magani, I'm sorry na baki cash instead of transfer." Ya furta yana 蓷an murmushi.
Bin hannunsa da ke rike da bandir 蓷in kudin Jidda ta yi da kallo bakinta sake. Ba wai bata saba ri茩e kudin daya ci uwar wannan bane, ita dai kawai mamaki take na irin 蓷aukakar da Saffy ta samu a lokaci 蓷aya wajen Yallabai da mutanensa.
Dole yasa tayi zargin akwai wani abu tsakaninsu amma koma menene ya faru ita ta ja ma kanta tunda ita taki bari ya bayyanawa kowa ita sabida tsananin gudun abin da zai biyo baya take.
Ganin tana 蓳ata masa lokaci ga abokansa na jira yasa ya dire bandir 蓷in kudin a gefenta.
"Allah ya bata lafiya."
Ya fa蓷a sannan ya yi gaba ya sami sauran, suke tambayarsa ko ita wacece? Ya yi musu bayanin cewa ai yar'uwar Safiyya ce.
A can 蓷aki bayan fitar su Alhaji Nasir, Yallabai ya bi Chef Ali da kallo na yadda yake addana ledoji na kayan dubiyan da su Alhaji Nasir suka kawo, carton na madarar gwangwani, carton na malt sai kuma kayan marmari. Ita kanta Saffy sai mamakin irin wannan 蓷aukakar da ta samu take, ga can kuma waje an ba Jidda ku蓷i duk sabida ita amma bata sani ba.
Idan ta tuna cewa wai Yallabai ne mutumin da suke tare a daren jiya har suka samu sa蓳ani kafin mahaukaciyar matarsa ta bayyana ta illatata sai kawai ta murmusa.
Mutumin da take ta admiring, mutumin da take burin zama ma'aikaciya a gidan abincinsa har Muwadda ke mata yanga har tana gindaya mata wani shara蓷in banza, sai gashi wai shine a gabanta yana fuskantarta.
Ta samu damar ganinsa a saukake, amma fa gaskiya ne ganinsa kam sai an shirya, tunda kafin ta samu wannan damar sai da aka kusa hallakata.
Duk da dai ta wahala matuka, kuma ba haka aka so ba amma kuma sosai tayi farin cikin ganin wani abin ya yi sanadin ganinsa a kusa da ita. Kuma irin 蓷aukakar da ya yi mata yasa har take jin a ranta laifin matarsa a wajenta ya ragu amma duk da haka sai tasa ta gane cewa ita 蓷in 'yar iska ce ta bugawa a allon sha.
Sai ta tabbatar ta koya mata darasin da ko nan gaba akace tayi ma wata makamancin abin da tayi mata, za ta ji tsoron aikatawa.
Bayan Chef Ali ya gama addana komai, Yallabai ya murmusa ya ce"Weldone Aliyu! Aikinka na kyau, Allah ya saka muku da alheri."
Chef Ali ya ce"Ka cancanci ayi maka fiye da wannan hidima Ranka ya da蓷e."
Sai a yanzu Yallabai yake tuna Jidda, ya manta dazu da suka yi waya tace masa tana asibitin, duk da ya zo yaga sakon data turo masa kan illata Saffy amma bai 蓷auki abin serious ba.
"Ina Alkhairi?"
Ya yi tambaya yana kallon Chef Ali kasancewar yasan haka yake kiranta.
Chef Ali ya 蓷an susa kai ya ce" Tana waje, ni na hanata shigowa ganin da tawagarka kazo and again ina tsoro kar wani abin ya sameta tunda ita aka so cutarwa amma mistakenly tsautsayi ya fa蓷a a kan ita wannan."
Ajiyar zuciya Yallabai ya sauke ya ce"Karka damu babu abin da zai sake faruwa in sha Allah, je ka bata izinin shigowa."
"Ok sir"
Bayan fitarsa Yallabai ya dubi confused Saffy da tayi shiru tana tunani don ta fahimci ita wacce ake kira da Alkhairin ne aka so cutarwa sai tsautsayi ya fa蓷a kanta.
Jidda na jin cewa Yallabai ya bata izinin shiga, da sauri ta mi茩e ri茩e da bandir na ku蓷in da Alhaji Nasir ya bata. Amma kafin ta shiga 蓷akin sai ta jefa ku蓷in cikin jaka.
Da sauri ta shige har tana bangaje Chef Ali da ke tsaye bakin 茩ofa, ya yi maza ya daka tsalle ya koma gefe.
Chef Ali ya girgiza kai yana "Allah sarki ita dai wannan haka kawai na ji ina tsananin tausayinta."
Bai koma ciki ba ya zauna kan bencin da ta tashi sabida ya basu damar ganawa a tsanake. Chef Sam ya tafi kar蓳o lunch na rana koda Yallabai yazo bai same shi ba.
Daga bakin kofa Jidda ta tsaya tana kallonsu, ita dole so take ta karanci yanayin kowanne amma ta kasa gane komai.
Saffy na ganinta ta washe hakora don zuwan Yallabai yasa gaba 蓷aya ta manta da wata Jidda. Shigowarta yasa ta tuna cewa tunda ta fita waya bata komo ciki ba.
"Meet my sister Yaya Jidda."
Saffy ta fa蓷a tana murmushi idanunta kan Jidda da ta maida kofa ta rufe a hankali.
Tun kan ta karaso wajensu ta ga Yallabai ya yi murmushi ya ce" Ni kuma meet my khair, ita ce wacce kika ji na bada izinin ta shigo."
Zumbur! Ta mi茩e tsaye tana "Tohhh! Yaya Jidda fa? Dama ita ce alkhairin taka?"
"Kwarai kuwa! sai dai naga kamar baki da sanin kakkafar alakar da ke tsakaninmu tunda abin sirri ne kuma ita taso a 蓳oye."
Saffy ta ha蓷iye abin da ya tokare ma茩oshinta kan tace"Ko kai ne ta fa蓷a min kunyi auren sirri da shi amma naki yarda da zancen?"
Kafa蓷unsa ya daga yace"Ban ma san kun tattauna da ita akan hakan ba, kuma ni dai ba zaki ji mutuwar sarki a bakina ba. Ba don abu haka ya faru da ke ba, bazan zauna anan ina fayyace miki komai ba."
Saffy na kokarin magana, Jidda tayi saurin daka mata tsawa" Safiyya ya isheki haka da musayar yawu da kike da mijina, i think i have tolerated enough. Tabbas shine mutumin da kika gani kwanaki a gidana har na fa蓷a miki cewa munyi auren sirri da shi amma kika ki yarda."
Gaba 蓷aya jikin Saffy ya mutu, tsananin mamaki ma ya hanata magana.
"I want to address something clear."
Duk suka zuba mishi ido suna jiran abin da zai ce. Sai daya kwashi kusan 40secs sannan ya fara magana.
"Jidda zan sake fa蓷a a gaban yarinyar nan, ba nemanta nake ba don na ga kin 蓷auki lamarin da zafi har da turo min text da ba sai na bayyana abin da kika turo ba."
Yaki fa蓷ar abin da ta turo saboda baya so ya haddasa rikici a tsakaninsu.
Nan ya kwashe labarin ha蓷uwarsu da Safiyya, abin da ya faru tsakaninsu har zuwa kan illar da matarsa tayi mata, sai a sannan Jidda ta iya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya.
Sai da Yallabai yasa Chef Ali ya shigo sannan yake gaya musu an ci su Haj. Nafeesa taran miliyan 蓷aya da rabi, don haka idan an sallameta sai taje polis station tasa hannu sannan ta karba ku蓷in tare da wani nata.
A 茩arshe ya 蓷ora da"Ni kuma zan bada 2m sabida a kaina tsautsayin nan ya sameta. Idan an ha蓷a duka ya kama milyan uku da rabi, nasan in sha Allah zasu isa kula da lafiyarta."
Tuni Saffy ta manta da halin da take ciki, Cike da farin ciki ta duka har kasa ta fashe da kuka tana godiya"Ranka ya da蓷e Wannan ai kudin sana'a ka bani, nagode kwarai da wannan lukutin kyautar da kuma tsaya min da kayi ka 茩wato min hakkina, Really appreciate you sir."
Murmusawa kawai ya yi yana mamakin yadda ta nuna tsananin farin cikinta a kan kudin, kuma ambaton yin amfani da kudin tayi sana'a ya matukar birgeshi, ko da gani yarinyar za taso dogara da kanta.
"Yaya ki tayani godiya."
Jidda da tuni tayi mutuwar tsaye tayi saurin dawowa hayyacinta don ba karamin mamaki ne yake neman sumar da ita nan tsaye ba.
"An gode, Allah ya saka da alheri."Ta fa蓷a ba tare da ta dubi inda yake ba, a lokacin ta nemi wuri ta zauna don ji take kafafunta ba zai iya ci gaba da 蓷aukarta ba.
Kamar daga sama ta ji ya ce"To, ke kuma wani kyautar zaki ma yar'uwar taki tunda a kanki aka cutar da ita?"
Yallabai ya fahimci babu wata dangantaka ta jini data ha蓷asu shiyasa Jidda ke nuna kishi. A ganinsa kawai yar'uwa ce da bariki ta ha蓷a su.
Jidda ta yi 茩o茩arin 蓷anne zuciyarta jin wani abu na neman taso mata, ba tare da wani dogon tunani ba ta bu蓷e jakarta ta zaro bandir na kudin da Alhaji Nasir ya bayar, dama dai tana da niyyar bata ha茩茩inta amma tunda ya kasance so ake itama ta fitar da wani abin ta bayar, kishin daya turnike zuciyarta yasa ta ji sam ba zata iya cire ko ficika ta ka蓷a ma Safiyya ba.
Mi茩ewa tayi ta dire 200k 蓷in a gefen Saffy ta ce"Tunda 茩aramin 茩arfi gareni, ga 200k nan kiyi maneji, Allah ya 茩ara lafiya ya kuma kiyaye gaba."
Wato a maimakon ta nuna ku蓷i ne daga Alhaji Nasir, sai kawai ta nuna taimakonta kenan. Saffy ta mata godiya sosai.
Suna nan sai ga Jami'ai biyu da aka turo domin duba jikin Saffy. Sai da zasu wuce 蓷aya daga cikinsu ya ce"Idan aka sallameki kina iya zuwa ki kar蓳i ha茩茩inki na ku蓷in da aka ha蓷a miki tare da wani naki."
Godiya ta musu kamar ta goyasu tsabar farin ciki.
Babu jimawa Yallabai ya bar asibitin, duk da Jidda taso su sake 茩ebancewa amma bai bata fuska ba.
Likita dai ya tabbatar da nan da kwana biyu za a iya bata sallama, amma sannu a hankali ciwon zai warke, sai dai fa akwai alamun zai bar mata ta蓳o, hakan ya 茩ara daga hankalin Saffy da kuma jin a ranta dole ta 蓷au fansa, haka nan ba zata ta蓳a barin Haj. Nafeesa ta tafi free ba.
******
Samha na biyan ku蓷in taranta ta bar station a gurguje don ta je tayi magana da CP a waya domin yasa baki a sake mahaifiyarta. Ita sam bata ma zaci za a 茩arbi ku蓷in tara a hannunsu, ita duk a tunaninta tsabar 茩arfin connection da take da shi zai sa komai yazo musu da sauki.
Sai gashi sau茩in da aka samu kawai shine sassautawa Mummy hukuncinta da akayi, wato ba a yanke mata hukuncin zuwa gidan gyara hali ba illa tarar da kawai aka cita.
Sai dai kuma duk wannan namijin 茩o茩arin da Samha tayi akansu, sam Mummy taki shiga taitayinta, gani take kamar sun riga sun kubuta har take iya kallon tsakiyar idon DPO tana gaggaya masa magana son ranta, gashi yanzu ta bashi haushi yasa an mayar da ita cell. Ta bar Samha da wahalar neman mafita kuma dole dai CP 蓷in zata sake kira kuma tasan sai ya bukaci a 茩ara masa wani ihsanin kafin ya kuma tabuka wani abin.
Ga ku蓷in da za a bashi 蓷in ma duk a cikin aljihunta zai fita, ga 蓷an sandan daya taimaka musu suka yi magana da CP a waya, shi ma sunyi al茩awarin biyansa bayan sunyi free, ta san kuma Mummy ba biya za tayi ba duk ita za tayi settling 蓷insa don Mummy akwai ta da kiyashin cire ku蓷i.
Tana nan tsaye bakin titi tana neman 蓷an sahu da zai kaita gida tunda an sallami direba daga aikinsa.
Daga bayanta ta ji ance"Malama ina zuwa? Kin manta ki biya ni ha茩茩ina?"
Tana juyowa tayi ido biyu da wannan 蓷an sandan da suka yi amfani da wayarsa wajen kiran Cp. Sai a lokacin ta tuna cewa ba a bashi ha茩茩insa ba.
"Dan girman Allah kayi hakuri na sha'afa ne, amma meye amfanin lambar waya dana baka? Sabida ka nemeni ne tunda bai dace muyi maganar ha茩茩inka anan ba gudun shiga matsala."
Sai a lokacin ya tuna da cewar ta bashi lambar waya da zai sameta tun a daren jiya daya gama musu aiki.
Hakuri ya bata sannan ya juya da sauri ya koma cikin station.
Wucewarsa keda wuya, ta samu 蓷an sahu dayake hankalinta a tsananin tashe yake, ko tsayawa tantance yanayin keken ba tayi ba ta afka ciki.
Sai da suka fara tafiya take gaya masa inda zata sauka, gidanta take so ta wuce direct, duk da taso zuwa gidansu ta kwashi kayanta amma sai taga rashin dacewar hakan, maganar fitowar Mummy ake a yanzu amma dole sai ta isa gida sannan ta nemi CP a waya.
Sun yi nisa sosai har ta fara jin da蓷in iskar da ke bugarta, nan da nan bacci ya fara 茩o茩arin fizgarta, kawai sai ta ji an 蓷an tabota ana"Hajiya mun iso inda zaki sauka."
A gigice ta bu蓷e ido amma kafin ta kai ga magana kawai ta ji an sha茩a mata abu a hanci, daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba.
Matashin da ke zaune tare da ita a baya ya kwanto ta jikinsa yana fa蓷in "Alhamdulillah yau ta shiga hannu, kai kira mana Don KB." Yake gayawa mai tukin adaidaitan.
Bai yi wata wata ba ya zaro wayarsa ya latso Don KB, hannunsa 蓷aya na tuki 蓷ayan kuma ri茩e da waya.
Yana dagawa ya ce" Oga kace alhamdulillah."
Murmushi Don KB ya yi ya ce" Menene ya faru?"
"Kai dai kace alhamdulillah."
"To alhamdulillah."
"Yauwa! Yau dai fafatuka ya 茩are don yau Allah ya bamu sa'a Samha ta shiga hannu."
"Kai haba don Allah da gaske kake?"
Don KB ya fa蓷a har da daka tsallen murna.
"Maganar da nake maka yanzu haka tana hannu, akwai wani jami'i da muka samu ha蓷in kansa ya bamu tabbacin za a sallami ita Samha a yau amma ban da mahaifiyarta. Shi ne tana fitowa station, muka ga bata samu abin hawa ba sai muka ja keke wajenta kuma cikin sa'a sai ta shiga kasan ba wayo gareta ba, bamu tsaya 蓳ata lokaci ba muka sha茩a mata hankerchief daka bamu."
"Wow! Good job, yanzu ku kaita wannan gidan, nima gani nan tafe zan sameku a can."
"Toh Ok."
Ya kashe wayarsa sannan ya 茩ara gudun adaidaitan.
Bayan gama wayarsu, DON KB ya fashe da wani irin mugun dariya yana murza two colour beard 蓷insa, sai da ya yi dariya mai isarsa sannan ya gimtse fuska ya ce"Samha yau kin shiga hannu kuma wallahi sai kin biya bashi. Zan tabbatar da na 蓷auki fansa a kan rayuwar 'yata da kika lalata."
_kayyasa! Ana wata ga wata, wanene kuma DON KB? Wacece 'yar tasa dake rayuwa a GIDAN MATA?Kuma wani fansa yake ikrarin zai 蓷auka kan rayuwarta da aka lalata?_
_Jama'a Saffy ta 蓷aukaka fa馃ぃ ku tayani lissafin nawa ta samu. Tsakanin ita da Haj. Nafeesa wa zai yi nasara?_
**Gobe free page zai 茩are in sha Allah.**