Free chapter · Read without an account
020
by Kansa'u Bello · MEERAH
*MEERAH*
*020*
Juyowar da Nawaz ya yi da nufin gyara zamansa, sai idanunsa a cikin na Ajmal da ya bar abin da yake yi ya tsare shi da kakkaifan kallon da ya saka shi duƙar da kai ƙasa babu shiri yana kama kansa.
Ɗan tsai Ajmal ya yi da idanunsa a kan Nawaz ɗin yana son tantance ainihin abin da yake nufi da kallon da ya ga yana binta da shi ɗin, har da ƙarin murmushi irin na yaudarar nan.
Zai kuwa saka ido ya ga iya gudun ruwansa, don ba zai bari yana kallo a kai matakin da zai hure wa ƙaramar yarinya kunne ba. Taimako dai ya taimake ta kuma sun gode, sannan za su ba shi tukucin abin da ya yi, alaƙar ta tsaya daga nan.
Shi kaɗai yake saƙa waɗannan zantukan da zuciyarsa, har bai ji isowar Meerah gabansu da ajiye farantin da aka shirya ruwa da juice haɗi da kofuna a kai ba. Sai saukar muryarta da ya ji tana ce masa.
"Good evening Yaya." Kame fuskarsa ya ƙara yi sosai sannan ya amsa, wanda hakan ya saka ni ƙunƙuni a zuciyata nake gulmar 'yau ƴan baƙin halin ne a kusa.' Bai san ina yi ba don aikin gabansa ya ci gaba da yi ba tare da ya sake ɗagowa ya kalli kowa a cikin mu ba. Yaya Sultan ne ya kalle ni ya ce.
"Auta baki gane shi ba ne." Ya yi maganar yana nuna min Nawaz da nake jin idanunsa ƙasa-ƙasa a kaina, juyawa na yi inda yake nace.
"Sannu da zuwa, an yini lafiya."
"Lafiya lau Alhamdulillah." Ya amsa min fuskarsa ɗauke da kyakkyawan murmushi, sannan ya ɗora da cewa.
"Yaya jikinki? Ina fata dai babu abin da ke damunki?."
"Alhamdulillah, na warke." Na ba shi amsa sannan na ƙara yi masa godiya sosai a kan taimakon da ya yi min.
"Da ace waccen ranar ba ka zo a kan lokaci ba, to da ban san halin da rayuwata take ciki ba a halin yanzu, na gode sosai da karamcin da ka yi min ba tare da sanin ko wacece ni ba." Na furta maganar a hankali ina kallonsa fuskata ɗauke da murmushi. Shima murmushin ya saki ya ce.
"Kar ki damu, in sha Allah babu abin da zai faru da ke, you are safe." Ya faɗa min cike da kulawa.
"AMEERAH!!!!!." Razananniyar tsawar da Ya Ajmal ya daka min ta saka ni rufe bakin da na buɗe da shirin yin magana, har da toshe shi da hannuna.
Idanunsa nake kallo waɗanda suka yi wata irin kaɗe wa da ɓacin rai.
"Wuce ciki!!." Ya ƙara furta a zafafe yana nuna min hanya, ai da gudu na miƙe har ina cin tuntuɓe na nufi cikin gida hawaye na malala a saman fuskata.
Ajmal kuwa sai da ya kwashe kusan mintuna biyar yana ƙoƙarin dai-daita kansa sannan ya ɗago ya fuskanci Nawaz ya ce.
"Mun gode sosai da taimakon da ka yi mana, sai dai hakan ba zai ba ka damar da za ka shiga cikin rayuwarta da wata manufar ba. She is still young, saboda haka bana son wata alaƙa da ban ta yi ƙoƙarin ƙulluwa a tsakaninka da ita." Ya ƙare maganar yana ɗauko bundle na 1k guda biyu a aljihunsa ya ajiye a gabansa.
Gyara zama ya yi ya saka idanunsa sosai a cikin na Nawaz ɗin da ya kasa jure kallon sai da ya janye nasa idanun da ƙyar yana jin tsananin kwarjinin da idanun Ajmal ɗin suka yi masa.
Guntun murmushi Ajmal ya yi da gefen baki wanda Sultan dake kallonsa ne kawai ya iya gane hakan.
Ɗan ranƙwafa wa ya yi daga zaunen da yake yana ƙara kame fuska sosai yace.
"Ga wannan tukuci ne na ɗawainiyar da ka yi a asibiti, sannan Barrister zai zo ku yi magana da shi, domin ana buƙatar ganinka a Kotu gobe. Za ka bayar da shaida ne a matsayin wanda komai ya faru a gabansa." Yana kammala faɗa ya miƙe ya ɗauki laptop ɗinsa ya nufi ɓangarensu.
Daga Nawaz ɗin har Sultan idanu suka bi Ajmal ɗin da shi har sai da ya ɓace wa ganinsu sannan suka kalli juna suna sauke ajiyar zuciya. Murmushi Sultan ya sakar wa Nawaz ɗin sannan ya gyara zamansa ya ce.
"Ka yi haƙuri fa haka halinsa yake yana da zafin zuciya, amma sai dai shi ɗin mutumin kirki ne. Kawai dai ba shi da yarda da kowa ne a kan Meerah." Murmushi Nawaz ɗin ya saki shima ya ce.
"Babu komai Wallahi, kar ka damu." Suna cikin wannan tattaunawar ne Barrister ya ƙaraso yana basu haƙuri kan zuwan da ya yi late. Ƙara tattaunawa suka yi da Sultan ɗin tare da Nawaz don Ajmal ɗin bai sake fitowa ba.
Koda Sultan ya miƙe da niyyar tafiya wasu kuɗin Sultan ya ciro ya haɗa da wanda Ajmal ya ajiye ya miƙawa Nawaz ɗin haɗi da sake yi masa godiya. Murmushi Nawaz ya saki yana mayar da kuɗin gaban Sultan ya ce.
"Duk abin da na yi don Allah na yi mata shi, ba don samun sakamako a wurin ku ba." Yana kammala faɗa ya miƙe ya tafi ba tare da ya ko juya ya saurari kiran da Sultan ɗin ke yi masa ba.
Da kallo Sultan ya bishi yana mamakin halayen su duka biyun da ke da banbanci sosai. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ba Barrister hannu suka yi musabiha ya miƙe ya shige ciki shima. Shima Barrister tafiya ya yi nashi uzurin.
*Meerah....*
Yanda na tafi da gudun nan ban tsaya ko ina ba sai a jikin Momy da ke zaune saman kujera tana danna waya, ina zuwa na faɗa jikinta ina fashe wa da kuka.
"Subuhanallah! Auta lafiya kuwa? Me ya faru?." Ta yi min tambayoyin tana ɗago ni daga jikinta. Cikin kuka na ba ta amsa da cewa.
"Ba Ya Ajmal ba ne ya yi min tsawa ya ba ni tsoro." Na yi maganar ina turo baki cike da shagwaɓa.
"Kai Allah ya shirya ki Meerah, ni na yi tunanin ma wani abin ne ya biyo ki kike irin wannan gudu da kukan." Momy ta faɗa cike da jin-jinawa shirmen Meerah. Bintu da ta kawo wa Momy ruwa ne ta yi dariya da cewa.
"Ai Hajiya ƙarama har yanzu jinta take tamkar wata ƙaramar yarinya."
"A hakan kuma sai son girman tsiya ba, da an yi magana sai tace ƴanmata ce ita ɗin a hakan." Momy ta faɗa bayan ta sha ruwan.
Murmushi kawai Bintu ta yi ta ɗauki gorar ruwa da Cup ɗin da Momy ta sha ta nufi Kitchen don ta mayar.
★★★
Washe gari aka shiga Kotu kamar yanda aka saka rana, kasancewar shari'ar ta manyan mutane ce yasa ake yinta a killace iya su da abin ya shafa kawai.
Ba a wani jata da nisa ba aka ƙarƙare domin duka hujjoji a bayyane suke ciki har da Nawaz da ya bayar da shaida, sannan da CCTV footage na ɗaukar da aka samu.
Sannan lauyan da ke kare su Nazzy ya kasa zuwa da wasu hujjojin da za su ƙaryata shaidun lauyan mai ƙara, dole ya buƙaci a ba shi lokaci domin ya sake shirya wa.
Alƙali ya amince an ɗaga shari'ar sati mai zuwa.
Sai dai cikin ɗanyen kan Nazzy wanda ya gaji da tsare shin da aka yi, ya fara masifa yana zazzaga rashin kunya.
Duk yanda Mahaifinsa ya so kwaɓarsa abin ya gagara, sai da ya daɓawa cikinsa wuƙa ta hanyar amsa laifin da ake zargin su cike da gadara, da ganin cewa ya fi ƙarfin ɗauri.
Ai kuwa lauyan masu ƙara bai ɓata lokaci ba ya yi amfani da hakan ya saka alƙali ya yanke hukunci nan take, sai dai hukuncin ya zo da sauƙi don lauyan su Nazzy ya tabbatar wa da Kotu cewar su Nazzy ɗin suna ƙasa da shekara 18 ne. Wannan shi ne ya kawo sassaucin hukuncin da suka samu.
Da wannan kotu ta tashi ran su Ya Sultan fes, yayin da ran Hon. Ado Aaji Doguwa da iyalansa yake a matuƙar ƙuntace. Hakan kuma ba ƙaramar gaba ya sake haifar wa ba a tsakanin iyalansu, domin Ado Doguwa na ganin da gangan Hon. Abbas ya jefa masa yaro gidan horon yara ƙanana.
Wannan kenan.
(Ina so in yi ɗan tsokaci a kan yadda shari'ar nan ta gudana, na san za a iya ganin kurakurai sosai a kan yadda na saka shari'ar a taƙaice ba tare da faɗaɗa bincike ba.
Bana son tsawaita abin ne saboda kai tsaye ba a kan hakan na gina labarina ba.
Kawai dai wannan rikicin ya shigo ne a matsayin background tension a cikin labarin ba ainihin jigon labarin ba.)
*Bayan wata ɗaya....*
Abubuwa da dama sun faru a wata ɗaya da ya shuɗe, ciki har da tafiyar su Yaya Ajmal London. Sannan da dawowar su Yaya Maheer da suka samu hutu.
A ɓangare na nima Alhamdulillah na sake naci gaba da rayuwata yanda na saba, na manta da abin da ya faru domin kuwa har mun koma School ni da Zeezee mun ci gaba da baza iya yi da ƴanmatanci.
A ɓangaren alaƙa ta da Nawaz kuwa tun lokacin da Momy ta saka Ya Sultan ya ba ta Number ɗin sa ta kira shi ta ce tana son zuwa har gida ta yi masa godiya a kan taimakon da ya yi min. Yaso hana ta ya ce ta bari ba sai tazo ba, shi duk abin da ya yi don Allah ya yi amma ta ƙi amincewa da hakan.
Saboda Sultan ya ba ta labarin irin ƙoƙarin da Nawaz ɗin ya yi, da irin dattakon da ya nuna na ƙin amsar kuɗin da suka ba shi. Hakan ya sa ta tambayi Dady ya ba ta izinin zuwa, sannan ya ba ta kuɗi masu yawa ya ce ta ba su.
Godiya ta yi masa sannan ta kira Nawaz ɗin da kanta ya turo mata da adireshin gidan su, saka ni tayi na shirya driver ya ɗauke mu muka tafi. Babban shopping mall ta saka muka fara zuwa ta yi sayayyar kayan amfani masu yawa sannan muka wuce gidan nasu.
Lokacin da muka isa ƙofar gidan Nawaz ta kira ya fito ya yi mana iso cikin gidan.......
Barkanmu da dare.
*Oum Fatima*
***