Free chapter · Read without an account
THE SHIFT
Tap the link below ⬇️ to join my WhatsApp group
***
COMMENT SECTION ⬇️
***
⛔️ WARNING!
Duk wanda ya sake taba min ko da harafi ɗaya ne a cikin littafina, ya shirya fuskantar tsautsauran mataki. Wallahi ba zan kyale ba!
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER EIGHTY SEVEN:87*
*THE SHIFT*
*JIDDAAH BARKUM*
——-
Wani irin zazzafan numfashi Zayd ya fitar, wanda ya kusan tarwatsa zuciyar Raihana, idanunsa kuma suna nan ƙyam a kan fuskarta, cikin wata murya ƙasa-ƙasa, mai cike da tsananin iko, ya fara magana, “Kar ki kuskura na sake ganinki gaban kowa da wani sassan jikinki a buɗe, ko da kuwa a cikin gidan nan ne,” ya faɗa a hankali, amma da wani irin matsanancin tsauri a muryarsa, “Idan ba haka ba…” Sai yayi shiru kawai, bai ƙarasa faɗin abin da yake nufi ba, ya barwa zuciyarsa abin da shi kadai ya sani.
Tsoro ne ya gama cika zuciyar Raihana, amma at the same time, wani irin dumi ya ratsa ta, ta ji kamar ya yi gluing ɗinta ne a wajen, ta kasa kwace kanta daga jikinsa, duk da cewa ba wani mugun riƙo ya yi mata ba, a hankali, cikin rawar murya, ta fara ƙoƙarin magana, amma sai ya katse ta, “Shhhh…” Zayd ya sanya yatsansa guda ɗaya a kan lafiyayyun lips ɗinta, ya dakatar da ita daga ci gaba da bayanin da ba zai canza komai a wajensa ba, lumshe idanunsa ya yi kaɗan, yana jin yadda yatsansa da ke kan lips ɗinta ke motsi saboda rawar da bakin yake yi, ga kuma wani azababben kamshin jikinta da ke ƙoƙarin haukata masa ƙwaƙwalwa.
A hankali ta sake trying magana, muryarta na rawa sosai, “Don girman Allah ka barni na tafi kar Ummie ta dawo… wallahi ban san me zan ce mata ba idan na fita, don Allah, zan tafi…” Ta yi shiru, sai ta dan dago kai a hankali tana kallonsa da idanunta cike da roƙo, Zayd kuwa bai amsa ba, kawai ya zuba mata ido, staring at her, idanunsa suka zauna a kan fuskarta na wasu seconds, kamar yana ƙoƙarin karanta duk abin da ke cikin idanunta, Raihana kuwa ta kasa jurewa kallon nasa, sai ta sauke nata idanun ƙasa, tana jin heartbeat ɗinta na ƙara sauri, Zayd ya ɗan yi numfashi a hankali, sai kuma ya ɗan ja baya daga jikinta, ya bata space, domin shi kansa ya san dole ne ya bata hanyar wucewa, dan already, his system had started to change sabida wannan bala’in kamshin nata da ya cika masa hanyar numfashi kamar bai da option ne shi ma sai ya bata hanyar.
Da samun wancan space ɗin, Raihana ba ta tsaya wani tunani ba, ta fice daga ɗakin a hanzarce, kamar wacce aka kora, amma maimakon ta koma falon da suke, direct sai ta nufi ɗakin Suhaila, tana shiga, ta hango hijabin da ta yi sallah da shi a kan sofa, ba tare da ɓata lokaci ba, ta figi hijabin ta ɗora kawai a kanta, ko kaɗan ba ta tsaya wani gyara ko ta kalli yadda yanayinta yake ba, daga nan ta fito da sauri, ta nufi stairs.
A lokacin kam Imran ya riga ya tafi, don haka babu kowa a falon sai Suhaila, wadda ke kwance a kan doguwar kujera tana amsa phone call, yayin da Ummie kuma take tsaye a corridor na kitchen tare da Kubra suna magana, Raihana ta sauke wata doguwar ajiyar zuciya mai tsanani, like she had just escaped a danger zone, ta karaso a hankali ta zauna a gefe guda, tana matse hannayenta da juna saboda yadda heartbeat ɗinta yake ta faman bugawa da sauri, ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, tana ƙoƙarin calming herself down kafin wani ya lura da irin halin da ta shiga.
A hankali Ummie ta ƙarasa daga corridor ɗin kitchen, Kubra na biye da ita ɗauke da tray ɗin abincin Zayd, da suka ƙaraso falon, Ummie ta tsaya tana kallonsu, Suhaila ta kashe wayarta, sannan ta ɗan kalli Raihana kafin ta ɗaga idanunta ta kalli Ummie, a hankali ta miƙe, Raihana ma ta miƙe, tana wani irin nocking herself together, kamar ba ta son Suhaila ko Ummie su lura da irin yanayin da take ciki, “Let’s go…” Shi ne kawai abin da Ummie ta faɗa, ta yi gaba nan take sai ta juyo, Ummie ta ɗan kalli Kubra, “Ki kai masa abincin ɗakin.” “Okay,” Kubra ta amsa, daga nan tayi gaba, Raihana da Suhaila suka bi bayan Ummie, suka fice daga gidan, 9:00 PM, motar Ummie ta shigo harabar gidan, suka fito suka shiga cikin gidan a hankali, Raihana tana biye da Suhaila, yayin da Ummie ke gaba, gidan ya yi shiru ba wani hayaniya, daga nan sukayi sallama da Ummie kowa ya wuce dakinshi.
Washegari, kayan Raihana suka iso KD, ba tare da wani ɓata lokaci ba, masu aikin furniture da interior setup suka nufi gidan Zayd kai tsaye, akwai carpenters, furniture installers, electricians da interior decorators, kowannensu da aikinsa, kafin ƙarshen ranar, komai ya fara ɗaukar sabon salo, Ummie ba ta bar wani abu a baya ba, daga bed, wardrobes, dressing table, bedside tables, sofas, curtains, carpets, mirrors, kitchen items har zuwa ƙananan abubuwan da Raihana zata bukata komai ta tanadar mata, duk da kayan da Baffa ya riga ya yi mata tun farko, waɗanda har yanzu suna nan lafiya, an ware musu wani ɓangare na daban cikin jerin rooms ɗin da ke part ɗin, aka shirya su da kyau, yayin da sabbin kayan da Ummie ta saya mata aka haɗa su a cikin ɗakunan da suke gefe daban, a hankali, gidan ya fara cika da wani sabon yanayi screaming Amarya vibe everywhere.
Seeyama dai tana part ɗinta ta dinga jin motsi, ta yaye curtains ɗin a hankali, tana kallon compound ɗin, sai dai babu kowa a wajen, sai motoci da aka fake a gefen part ɗin Raihana, ta ɗan daɗe tana kallon wajen, idanunta suna bin wajen da kallo, ta na tsammanin ko za ta ga wani abu maybe ta fahimci me ke faruwa a wajen, amma ba ta ga kowa ba, haka ta gaji da leƙe ta koma ta zauna, ga wata azababbiyar yunwa da ta isheta, cikin takaici ta dafe cikinta, tana jin yadda yunwar take ƙara mata zafi, ita ba iya girki ta yi ba, tun jiya take zubawa kanta junk food, kuma ita dama ba gwanar ciye-ciye bace, tafi gane ta ci abincinta da kyau, ta koshi, amma yau ga abinda rashin iya girki ya ja mata, ta ɗan langwabe kai tana kallon kitchen ɗin da wani takaici.
Ko ma ta iya girkin, a wajenta ba class ɗinta bane, kamar ita taje tayi ta fama da tukunya da yanke-yanke a kitchen? Maid dai ita zata mata komai, kuma ta riga ta yanke shawarar zata kira Mommy ta aiko mata da Rabi kawai ta dawo nan gaba ɗaya, domin ita kaɗai ce cikin maids ɗin gidansu da take iya tolerating halayen Seeyama, don haka, a yanzu da bata da option, sai ta ɗauki wayarta ta yi order ɗin abinci, bayan like forty minutes, aka mata waya, the delivery man is at the door, ta sauke wayar tana tabe baki, sannan ta miƙe, haka ta fito tana wani hararan part ɗin Raihana, kamar irin Raihana din take gani, da ta ƙarasa gate, gateman ɗin na ganinta ya miƙe da sauri, “Good evening—” Amma kafin ya ƙarasa, Seeyama ta zabga masa wata uwar harara, gateman ɗin ya tsaya cak, bai san lokacin da ya koma inda ya taso ba, yana zare ido kawai, Seeyama ta ja wani uban tsaki ta ƙarasa ta buɗe ƙaramar ƙofar gate din da kanta, ta karɓi abincinta, kwali guda mai uban yawa, ta kallesu na ɗan lokaci, sannan ta ɗan gyara hannunta a kan cartons ɗin, gaskiya gwara tayi storing ɗin su a fridge, idan taji yunwa, ta yi warming kawai ta ci, shiyasa ma ta siya varieties da yawa, “At least, I won’t have to worry about food again,” ta faɗa a ranta, tana juya wa cikin part ɗinta da cartons ɗin a hannunta.
Haka ta koma kitchen ɗin, ta ɗebi wanda za ta ci tayi reserving sauran a freezer, sannan ta ɗauko bottled water kawai, daga nan ta dawo falon, ta janyo remote ɗin tana tabe baki, “Bari na yi kallo, na rage zaman nan, mutum kamar maye an barshi shi kaɗai.” Tayi powering TV ɗin, sannan ta janyo abincinta kusa da ita, ta zauna tana ci tana kallo, lokaci-lokaci tana ɗan sauke idanuwanta kan screen ɗin tana bin abin da ake nunawa, bayan ɗan lokaci, ta gama cin abincin gaba ɗaya, ta ture plate din gefe, ta ɗauki bottled water ɗin ta sha kaɗan, sannan ta janyo wayarta, ta shiga contacts ɗinta, Mommy, ta danna call, wayar ta fara ringing a hannunta, yayin da ta jingina da kujerar ta miƙe ƙafafuwanta tana jiran a ɗaga.
A Arman Mansion ma, Anty Sadiya yau da wuri ta zo, ba tare da ɓata lokaci ba, aka fara gyaran jiki, babu wani abu da ta manta ba ta yi wa Raihana ba, har da su tsumi, su tantabara, da duk wasu abubuwan da suka dace da gyaran jiki na amarya, Raihana kuwa duk lokacin da aka bata wani abu na ci ko sha kawai ci take, amma ba don ranta ya so ba, tana cin ne saboda Anty Sadiya ta dage mata da kuma tsayuwar Ummie a wajen, da aka gama, aka zauna aka zana mata jan ƙunshi da black henna a hannayenta da ƙafa, tsarinsa ya yi wani irin masifar kyau, saboda hasken fatarta, jan ƙunshin da black henna ɗin suka fito sosai, har Raihana da kanta ta dinga kallon hannayenta tana admiring ɗin su.
Gaskiya ma ba zata iya tuna when last ta yi henna haka ba sai idan Maryam ta takura mata ne sai tayi a fingers kawai, ta juyar da hannunta ɗaya, ta sake kallon ɗayan, “Yayi kyau sosai,” ta faɗa a hankali, murmushi kaɗan ya bayyana a fuskarta, Anty Sadiya tayi dariya, “Kin dai yi masa kyau,” Raihana kawai tayi murmushi, daga nan aka zauna aka yarfa mata uban kitso, abinda ya ɗauki kusan good two hours ana yi, Raihana ta zauna patiently har aka gama, da aka nuna mata kitson a mudubi kuwa, “Ya Allah…” Kamar ba hannu ne ya yi ba, kitson ya zauna mata da wani irin kyau, ya ƙara fito da shape ɗin fuskarta da delicate features ɗinta.
Suhaila kuwa ta kasa daina yaba mata, “Anty Rayy!” Ta matso kusa da ita tana kallon gashin, “Wallahi this is so beautiful!” Ta juya ta kalli wani gefen, “Look at this! Wallahi dama a kie mayen gashi ne.” Raihana ta yi dariya kaɗan, tana jin kunya saboda yawan yabon da ake mata, Suhaila kuwa bata gajiya, “Wallahi, you look so pretty.” Raihana ta sauke idanunta tana murmushi, Ummie da ta shigo lokacin da aka gama, ta tsaya kawai, idanunta suka sauka kan Raihana, ta kasa cewa komai na ɗan lokaci, kawai ta zuba mata ido, a zuciyarta kuma kalma ɗaya ce take maimaituwa, “Fatabarakallahu Ahsanal Khaliqeen…” Ta sake kallonta, sannan ta ɗan jinjina kai cikin gamsuwa, “Allah ya kiyaye ki daga idon mutane,” ta faɗa a hankali, Raihana ta ɗan sunkuyar da kanta, Suhaila tayi karafff ta amsa, “Ameen Yaa Allah.” Ummie ta sake kallonta na ɗan lokaci, da alama yau ma gyaran jiki bai yi mata komai ba sai ƙara fito da irin kyawun da Allah Ya riga Ya bata.
Bayan Hajiya Hauwa ta ɗauki wayar Seeyama, babu wani gaisuwa, babu “Hello Mommy, ya kike?” ko wani abu, Seeyama kai tsaye ta fara da korafi, “Mommy, ni dai gaskiya ki aikomin da Rabi kafin baƙinciki, yunwa da kadaici su kashe ni, haka zan cigaba da zama a gidan nan kamar ina gidan yari, ya hana kowa shigowa, kuma ni ya hanani fita!” Muryarta cike take da complaints, tana wani turo baki kamar ita ce aka yi wa babban zalunci, “Abinda kika sa na yi ma na gyara gida, na je na bashi hakuri, ko kallona bai yi ba, ya fice ya barni a gantale! Wallahi ni Mommy, ba zan iya abinda kika ce ba.” Ta ɗan ja numfashi, sannan ta ƙara da sauri, “Sannan dan ya maida ni mayunwaciya, ya aiko wannan munafikin Sameer ɗin da uban kayan abinci kamar ce masa aka yi a yunwace nake!”
Hajiya Hauwa ta yi shiru tana sauraron ta, ta jingina da kujerarta, tana ɗan murza goshinta a hankali, Seeyama kuwa tana can gefe tana ci gaba da tabe baki, “Mommy…” Hajiya Hauwa ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce cikin nutsuwa, “Matsalar ta dake, baki da hakuri, Seeyama.” Seeyama ta yi shiru na ɗan second, tana kallon screen ɗin wayar da fuskar da ta nuna cewa she wasn’t impressed, Hajiya Hauwa ta ci gaba, “Ta yaya za ki ci ribar zaman duniya? Komai a hankali ake farawa, zatonki daga kin gama gyaran gidan sai Zayd ya zauna ya fara, ‘Seeyama, thank you, I love you, I can’t do without you?’” Ta ɗan yi tsaki, “Common sense, please, ki nutsu ki bishi a hankali.” Seeyama ta wani tabe baki, ta ɗaga gira tana kallon ceiling, “Hmm.”
Sai ta ƙara da cewa, “Gashi yanzu naga alamun shegiyar matsiyaciyar yarinyar can zata dawo nan, dan na ji ana ta motsi a part ɗin…” Ta yi shiru na ɗan second, “Ko ma ta dawo wa ya sani, kinga kuwa rashin mutunci a wajenshi sai abinda zai yi gaba, tunda har matar so—” Seeyama ba ta ƙarasa maganar ba sai Hajiya Hauwa ta zabura tana katse ta sannan ta gyara zamanta, “Kina nufin ta na gidan yanzu ta dawo?” Seeyama ta tabe baki, “Ni ina na sani? Kawai motsi na ji, ba wai ganinsu na yi ba.” Hajiya Hauwa ta yi shiru na ɗan lokaci, sai ta ce, “Toh, duk abinda kika gani ki sanar da ni, gobe zan zo, sai na kawo miki Rabin da kaina.” Seeyama ta ɗan yi murmushi a karon farko, “Toh shikenan, Mommy, sai gobe.” “Okay.” Daga nan suka katse wayar, Seeyama ta sauke wayar daga kunnenta, ta ɗan jingina da kujera, “Finally…” Ta ɗauki remote ɗin tana komawa kallon TV, kamar dai duk matsalar da ta gama yi wa Mommy Hauwa kuka a kai yanzu ba ta dame ta ba, amma a zuciyarta, magana ɗaya ce ta fi makale mata, Raihana tana dawowa ko ma ta dawo, ta ɗan tabe baki, “Hmm… let her come.”