Free chapter · Read without an account

CHAPTER 12.

by HAERMEEBRAERH✍️✨ · ZAWARA.

ZAWARA.








NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ 











PAGE 12.











Samir ya haɗu da Munirah ne a wani babban taron da manyan mata ƴan kasuwa suka gudanar a Transcorp Hilton Hall dake cikin garin Abuja a No 1 Aguiyi Ironsi street,Maitama. A wannan ranar kowacce ƴar kasuwa ta je da ɗanta ko ƴarta wanda sune za su zamo magajin dukiyar iyayen nasu domin saka hannu a wasu takardu. A kaf cikin yaran masu hannu da shunin da Samir ya gani a wajen Munirah ce yarinyar da tafi tafiya da hankalinsa da nutuwarsa. Ba tare da ɓata lokaci ba ya isa wajenta ya gabatar da kansa. Duk da cewa a tsakanin mahaifiyarsa da mahaifiyarta akwai competition hakan bai hana yaran ɗaura kyakkyawar alaƙa a wajen ba. 

Munirah na daga cikin irin wayayyun yaran Abujar nan da suke rayuwa cike da ƴanci babu takura. Hakan ne ya bata damar sakin jiki suka fara soyayya mai zafi ita da Samir. Munirah ta sadaukar wa da Samir abubuwa masu muhimmanci a rayuwarta wanda a baya take ganin babu namiji ko macen da ta isa ta sakar wa sirrinta ballantana har ta mallaka musu. A cikin abinda Muni ta mallaka wa Samir har da gangar jikinta da zuciyarta. Duk abinda mahafiyarta ta ce mata ta yi,indai Samir ya nuna rashin amincewarsa ko da a fuska ne to Munirah ta bar wannan abun kenan bari na har abada. Maganar samari kuwa dama tinda ya nuna mata baya son sharing ta ajiye kowa a gefe,tinda dama ita bata yin irin soyayyar nan ta zamani da ake yi ai ta zinace-zinace da sunan soyayya.

A duk ranar da Samir ya je garin Abuja kwana suke yi suna aikata duk abinda zuciyarsu ta raya musu daidai ne. Zuwa club da hotels ya zame musu tamkar ibada. Akan Samir Munirah ta sha yin dambe da faɗa da ƴan mata kala-kala,wani lokacin ma har da shi kansa uban gayyar take zage wa su daku. Idan suka yi faɗa kaca-kaca ba sa iya yin sati ɗaya ko su haura sati biyu basu nemi juna ba. Samir na iya keta hazo ya bi Munirah duk ƙasar da ta je saboda ta guje masa. Idan kuma shi ne ya yi fushin sai ta tattaro komatsenta ta dawo Kano da zama ta yi ta aikin ban haƙuri har sai ta shawo kan abunta.

Shaƙuwarsu ce ta jawo haɗin kai a tsakanin iyayensu mata. Domin kuwa daga Samir ɗin har Munirah iyayensu maza sun rasu. Ganin irin soyayya da shaƙuwar dake tsakaninsu sai iyayen nasu suka shirya musu lavish engagement party. Ko da Samir ya zo venue ɗin da iyayensa suka sanar da su ya fahimci mai suke ƙullawa sai ya hau watsi da kujeru da tables yana masifa tare da cin mutuncin tarbiyya da ɗabi'un Munirah. Cikin fushi da ɓacin rai Samir ya kalli mahaifiyar Munirah da ta riga ta tsorata da abubuwan da Samir ya dinga aikatawa a wajen ya ce.

"Ƴarki ce ta faɗa miki ni Samir Yusha'u Gwamnati zan auri mace kamarta? To in auri Muni in ce na auri wa? Please ku dena wannan drama ɗin because i cannot marry public toilet na kai ta gidana da sunan matar da za ta zamo uwar yarana."

Da jin haka sai mutanen wajen suka cika da mamaki tare da yin ƙus-ƙus suna tattaunawa akan kalaman da Samir ya yi amfani da su wajen bayyana wacece Munirah a idonsa. Munirah wadda bata jima da isa wajen taron ba sai ta ƙame a wajen cike da jin kunya,muzanci tare da tsantsar damuwa da karyewar zuciya. Hawaye ne ke yi mata tsananin gudu a kuncinta tana jin wani irin zafi da ƙunci a cikin ranta. A hankali ta juya za ta tafi saboda bata da sauran ta cewa. Muryar Hajjah Barirah ce ta karaɗe wajen tare da ƙarar saukar zazzafan marin da ta sauke wa Samir a saman kyakkyawar fuskarsa. Cak Munirah ta tsaya tare da juyawa ta kalli yanda ran Hajjah Barirah ya yi matuƙar ɓaci ta na nuna Samir ta ce masa.

"Tinda kake abubuwanka ban taɓa shiga sabgar shirmen ka ba sai yau Samir. Yanzu kai baka ji kunya ba da za ka kira yarinyar da kuke making love a koda yaushe da public toilet? Idan ita public toilet ce to kai menene tinda tare da kai take yin duk abinda kake ƙin ta dominsa. Idan baka son wannan engagement ɗin akwai hanyoyi da dama da za ka faɗi hakan you don't have to be so mean and stupid."

Cike da jin nauyin mahaifiyar Munirah wadda ranta yake a matuƙar ɓace Hajjah Barirah ta yi folding hannayenta waje ɗaya ta ce.

"Don Allah ki yi haƙuri akan abinda ya faru. Da na san haka yaron nan zai yi da ban amince aka haɗa musu wannan taron bazatar ba."

Kai kawai Hajiyah Nusrah ta kaɗa ta taka zuwa wajen ƴarta Munirah ta kama hannunta ta kalli Samir ta nuna mata shi ta ce.

"Kin ga irin mijin da kike yi wa makahon so ko? Kin kuma ga kallon da yake yi miki duk da cewar he was your first. Kamar yanda na sha gaya miki ne Muni,duk yanda mace ta kai da ji da kyau da taƙamar mulki ko dukiya;matsawar za ta sakar wa namiji jikinta to wannan darajar tata za ta yi ƙasa ta wulaƙanta tare da ƙasƙanta a idonsa."

Murmushin takaici Hajiyah Nusrah ta yi sannan ta ci gaba da cewa.

"Bana manta ranar da kika dawo gida kika bayyana min abinda ya faru a tsakaninki da Munir,idan za ki iya tuna wa i was so furious saboda kin sakar masa ƙima da darajarki ta ƴa mace,amma ke,ke ɗin murmushi kike yi fuskar ki na bayyana irin farinciki da nishaɗin da kike ciki. Daga ƙarshe kika ce min Mom da ni da Samir mun zamo ƙaddarar junanmu,duk inda ya je ya dawo wajena zai tsaya,haka zalika nima duk inda na je na dawo wajensa zan koma. We are stock with each other,we can't do without each other Mom,I love him so very much. A wannan ranar na tabbatar da na rasa ƴata. Dan haka ni ba zan yi mamaki ba dan Samir ya yi mana wannan irin cin mutunci a yau,dama ɗan kuka shine yake jawo wa uwarsa jifa."

Hajiyah Nusrah na gama maganarta ta ja hannun Munirah suka bar hall ɗin ranta a matuƙar ɓace. Tun daga wannan ranar ta saka wa Munirah dokoki tare da manyan takunkumi duk dan ta rabu da Samir. Sai dai ko sati biyu ba a cika ba Munirah da Samir suka sake ɗinke wa kamar babu abinda ya faru na ɓacin rai a tsakaninsu. Ganin haka sai Hajjah Barirah da Hajiyah Nusrah suka saddaƙar tabbas babu mai raba tsakanin Samir da Munirah sai mahaliccinsu. 

Lokacin da Hajjah Barirah ta fara gajiya da shige da fice tare da rashin hutun jiki da ruhi game da kasuwancinsu sai ta nemi Samir akan ya mayar da hankali akan kasuwancin ya ajiye maganar kula da asibitinsa tunda yana da ƙwararrun likitoci a cikinsa. Samir sai ya amince da muradin Hajjah,sai dai a duk sanda ya shigo Kano yana leƙa asibitin nasa har ma ya duba marasa lafiya. 

Ana haka Samir ya yi wa wata yarinya ciki iyayenta suka zo har gidan Hajjah Barirah suka ci mata mutunci sannan suka yi alƙawarin za su dawo mata da ɗa ko ƴar da aka haifa idan lokaci ya yi. Tun daga wannan ranar Hajjah ta fara matsa wa Samir akan ya nemi matar aure ko ta aura masa Munirah ko yana so ko baya so. Da jin haka sai Samir ya sake bin jikin yarinyar da ya yi wa ciki ya dinga yi mata wayo yana sake keɓe wa da ita yana bata kuɗi. Daga ƙarshe ya samu nasarar saka mata wata ƙwayar zubar da ciki mai ƙarfi a abun sha,tana komawa gida daga hotel ɗin da suka saba haɗuwa ta yi ɓari. Wannan shine silar rabuwarsa da yarinyar.

Duk da cewar sun rabu sai da Munirah ta sa aka nemo mata gidansu yarinyar ta yi hayar marasa jin unguwar ta basu kuɗi mai yawa suka banka wa gidan su yarinyar wuta. 

Lokacin da gobarar ta tashi mutanen gidan duk basa nan sun yi tafiya,dan haka sai aka dinga raɗe-raɗin cewa wataƙila sun manta sun kunna gas ne ko kuma sun bar abinda idan wutar lantarki ta jima zai ƙone ya ƙona waje. A ɓangaren Munirah kuwa zuciyarta ce ta yi mata daɗi saboda ta ɗauki fansar kwana mata da saurayi da yarinyar ta yi. Munirah na yi wa Samir wani irin mahaukacin so ne da take jin za ta iya yin kisan kai akansa ko kuma ita ɗin ta kashe kanta. Munirah ta yi alƙawarin babu wata ƴa mace da ta isa ta auri Samir ko ta yi tarayya da shi matsawar tana raye a duniya. Idan kuma mace ta kuskura ta yi gangancin raɓar Samir da sunan aure ko soyayya tabbas ita ce za ta zamo ajalinta..........

*Ƙaƙa-ƙara-ƙaƙa! Ga Munirah ƴar hau,ga Nansy Ƙaya my fiful. Da alama dikansu sun ci kai.*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.