Free chapter 路 Read without an account
Chapter 5-6
馃拫馃拫馃拫馃拫馃拫馃拫
*TA茦AITACCEN SIRRI*
馃拫馃拫馃拫馃拫馃拫馃拫
Funny馃槀 Love馃挅 and Romantic 馃拫
Mom Islam
_Nace ba, wannan littafin yana 蓷auke da darussa da yawa, ban dariya soyayya mai sanyi da tsayawa arai, gwagwarmaya tare da sadaukarwa馃挮_
Page 5-6
"Amma me, kana nufin zaka 蓷auki nauyin karatun Ahlam gabaki 蓷aya?"
"Eh idan har kun amince amma fa ina sonta soyayya bata..."
"Kaga dakata malam idan har ba dan Allah zakayi ba mungode bama bu茩ata.
Hakeem yai saurin barin gurin ba tare da ya sake jin abinda mutumin zai ce ba.
Da sassarfa ya 茩arasa gurin Ahlam tare da ru茩o hannunta fuskarsa a tamke yace "Ahlam zan cireki a wannan makarantar insha Allah ko aikin gini ne zan nema saboda ki samu ingantaccen karatu"
Fuskarsa ta kalla taga babu alamar walwala a tare dashi, a shagwa蓳e tace "Yah Hakeem wani abin sukai maka?"
"A'a" yace mata.
Har suka iso gida maganar bawan Allahannan tana ta yi masa yawo a 茩wa茩walwa,
Da sallama suka shiga cikin gidan lokacin Ammu tana zaune a tsakar gida saman tabarma da ledoji a gabanta fuskarta 蓷auke da fara'a, bayan ta amsa sallamarsu tace "auta sun yarda sun barki ko?"
Sunkuyar da kanta 茩asa tayi kafin tace "Ammu nidai yunwa nakeji"
"Ahlam kenan tambayar da nayi miki daban abinda kike nema daban?"
Ammu tai maganar tana kai kallonta ga Hakeem da tunda suka shigo bayan muryarsa da taji yayi sallama bata sake jin maganarsa ba, sbda tasan da haka kawai ne sai yayi magana.
"茒an albarka lafiya kuwa?" Ammu ta tambayeshi tana kunce ledar dake gabanta,
Fuska babu walwala yace "lafiya lau Ammu"
Tunda yace mata lafiya ta rabu dashi sai ta bu蓷e ledar gaba 蓷aya tace "kunga abinda Alhaji Inusa ya kawo mana?"
Ahlam ta le茩o tana murmishi tare da cewa "Ammu wlhi yanada kirki tunda kikaga ya tuna damu, satinsu 蓷aya fa da dawowa amma har sun tuna damu"
Hakeem da sai yanzu yayi magana yace "Ammu ina gaya miki ki rage saurin yarda da mutane kina ganin kamar wasa ko? Idan da ina nan wlhi bazan bari ki kar蓳a ba"
Ammu ta hangame baki tana kallonsa sai kuma tace "sai kuma akayi rashin dace ba ka nan, kuma yanzu zan dafa mana, ka gayamin yaushe rabonka da cin shinkafa da miya a gidan nan?" shiru yayi bai ce komai ba.
Shinkafa ce zata kai mudu uku sai Attaruhu da albasa da tumatur 蓷anye da mangya蓷a harda kifi busashe da maggi, Ahlam dai sai tsalle takeyi, barin gurin yayi saboda shi a ganinsa Ammu taje ta sanar musu da halin da suke ciki, kafin su fara hada hadar 蓷ora abinci sai da Ahlam tasha ragowar garin kwaki kafin Ammu ta gyara tumatur ta zuba a turmi kana ta fara jajjage, 茩arfe 6 Ammu ta kammala komai da komai tare da taimakon Ahlam, tun kafin Ahlam tai sallah ta zuba nata abincin jikinta har rawa yakeyi, sai da taci tayi nak sannan ta mike taje ta 蓷auro alwala ta dawo, lokacin anata kiraye kirayen sallah, ta kabbara sallah kafin ta jingina kanta da bango, sannan ta fara cin abincin.
掳"Babban burina shine in mallaki Ahlam ta ko wacce hanya, saboda itace muradina itace mafarkina tun batakai girman haka ba"
"Haba Alhaji Ibrahim Khalil mai kake fa蓷a haka? Wannan abin da kake yi fa gabaki 蓷aya bai dace dakai ba, yarinya mitsitsiya wacce ko gama wanke mata kashi ba'ayi ba kake wani maganar aurenta?" to idan ma ka aureta ubanme zakaci da ita? ni a ganina Gara ka nemi budurwa mai jini a jika, sanin kanka ne duk inda ka gifta sai 拼an mata sun dinga binka da kallo ga Anam ma 拼ar uwarka?"
Yusuf yai maganar cikin fa蓷a,
Yusuf Muktar babban abokin Alhaji Ibrahim Khalil ne tun na yarinta sannan har yanzu abotarsu tana nan.
Sam aibanta yarinyar da Yusuf yayi abin beyi masa da蓷i ba, duk da yasan shi蓷in ba yaro bane a 茩alla zekai shekaru 40yrsyrs bai ta蓳a sha'awar aure ba sai yanzu da yayi ido hu蓷u da Ahlam,
Rai a 蓳ace ya mi茩e tare da shafa kwantaccen sajen fuskarsa da yasha gyara kafin ya kalli Yusuf yace "zanci gaba da 蓷awainiyar dakon son yarinyar har lokacin da zata san menene so"
Yusuf yayi murmushi kafin shima ya mi茩e yana ha蓷e hannayensa guri guda kana yace "am very sorry Ibrahim Khalil, gaskiya ina mugun tausaya maka saboda wannan yarinyar da kake magana a kanta batasan menene so ba, batasan ya ake kula da miji ba, musamman ma kai da kake bu茩atar kulawa fiye da tunanin ka, bazakasan kayi babban kuskure ba har sai ranar da kuka kasance a matsayin ma'aurata. Sosai maganar da Yusuf yayi masa ta sake tunzura ransa, sbda shi mutum ne mai tsananin taurin kai akan abinda zuciyarsa takeso.
馃挗馃挗
Farkon labari
Ranar Laraba rana ce da ilahirin mutanen garin Ma茩arfi ke farin cikin kasancewa da fito da kayayyakin siyarwa su kawo kasuwa, kasuwar cike take da 蓷umbin al'umma mata da maza, Baba Ali ya kasance 蓷aya daga cikin mutanen dake bada babbar gudunmawa tare da shawarwari gurin kawo ci gaban kasuwar, sannan yana siyar da hatsi kama daga gero masara dawa dauro da shinkafa, a wannan sana'ar yake rufawa kansa asiri har yayi gida madai-daici wanda yake zaune da matarsa da yaransa biyu, Hakeem da Ahlam Hakeem yanada shekaru goma sha biyar Allah yayiwa baba Ali rasuwa, ita kuma Ahlam tanada shekara biyu a duniya, sosai mutuwar Baba Ali ta bawa mutane mamaki duk da cewar ba'a mamaki da ikon Allah, kasancewar yayi mutuwar da kowane bawa ya gani sai ya tsorata, mutawace da kaf fa蓷in duniya babu mahalu茩in da zai so ta riskeshi, kafin mutuwarsa yayi ta barin abin almara mutum ne mai barkwanci kowa nasa ne, ya kasance abin hannunsa bai rufe masa ido ba, baya shakkar taimakawa koma waye yake neman taimako, aka wayi gari an wurgar da gawarsa a 茩ofar gidansa a gindin bishiyar kuka an 茩wa茩ule masa idanuwa da harshe, sosai mutanen yankin nasu suka tsorata, Hakeem yayi kuka sosai gunin ban tausayi, Ammu kam har suma take yi, tsabar al'ajabi da firgici. a kwana a tashi har Baba Ali yayi kwana arba'in da rasuwa ba'a samu labarin wanda suka aikata muguntar cire idanu da harshe ba, abinda zai bawa mai karatu mamaki tashi 蓷aya wasu mutane daban suka dinga zuwa wai suna bin Baba Ali bashin ku蓷a蓷e, hakan yasa duk wani abin da ya mallaka ya 茩are a biyan bashi, daga 茩arshe dai aka fara maganar 蓷aga gida a siyar, Ammu ta dakatar tace zata nemi 拼an uwanta akan su taimaka mata, koda taje gurin danginta ta sanar musu da halin da suke ciki, kasancewar mahaifiyarta bata raye bata cika samun goyon bayan wasu abubuwan ba, sbda mamanta ita ka蓷ai ta haifa tun tana 茩arama take kar蓳ar zalunci da tsangwama daga gurin 拼an uwanta wanda suke uba 蓷aya.
Ranar da sukayi mata al茩awarin yana cika ta dawo da 茩arin gwaiwarta,
Da sallama ta shigo gidan fuskarta wasai ta 茩araso gurin 拼an uwan nata dake zaune a gindin bishiyar ce蓷iya, suna ganinta suka hau yatsina fuska da kawar da kai, abin mamaki harda yaya Usman dake rarrashinta, wanda ya kasance kaf cikinsu yafisu sau茩in kai, Inna Wasila ta wani gallawa Ammu harara tare da cewa "banyi tunanin baki da hankali da tunani ba sai yau, mijinnaki da ya riga ya mutu abinda ya bari dama a shari'ance shi za'a biya masa bashi, dan haka ki koma gida ki gayawa mai rabon gadon ya kirawo mai siyan gidan naku, ai nasan idan aka siyar baza'a rasa ragowar ku蓷in da za'a kama haya ba, Ammu ta fashe da kuka, yaya Usman ya taso cike da nuna kulawa duk da taga sauyin fuska a tare dashi, ya kamo hannunta,
Kada ka sake ka sake koda taku 蓷aya daga nan inda kake, idan ko kayi bada yawuna ba"
Inna wasila tai maganar cikin bada umarni..!
Domin neman 茩arin bayani
***