Free chapter 路 Read without an account
Chapter 7-8
馃拫馃拫馃拫馃拫馃拫馃拫
*TA茦AITACCEN SIRRI*
馃拫馃拫馃拫馃拫馃拫馃拫
Funny馃槀 Love馃挅 and Romantic 馃拫
Mom Islam
_Nace ba, wannan littafin yana 蓷auke da darussa da yawa, ban dariya soyayya mai sanyi da tsayawa arai, gwagwarmaya tare da sadaukarwa馃挮_
Page 7-8
Bakinsa na rawa ya dur茩ushe a gurin cikin tausayin Ammu yace "kiyi ha茩uri Yaya Amina wlhi tallahi ko sauyin fuskar da kikaga nayi Inna ce ta sa ni dan Allah ki koma gidanki anan gidan ba zaki samu ba"
Ammu ta share zafafan hawayen dake ta faman sintiri a saman kumatunta, cikin zafin rai da nadamar zuwanta gidan ta tona asirin cikinta, cikin Muryar kuka tace "wlhi tallahi Inna ki sauya hali kafin mutuwa ta riskeki.." daga fa蓷ar haka ta juya ta fice da sauri, dan bata san taci gaba da kasancewa a cikin gidan tana 茩unsar ba茩inciki.
Da sauri Inna ta janyo mayafi zata fice, yaya Usman yai saurin shan gabanta, cikin fa蓷a da nuna tsantsar tsanar Ammu tace "Usman wlhi tallahi idan baka bani hanya na wuce ba zan sa蓳a maka, "haba Inna kiyi ha茩uri mana dan Allah, wannan 茩iyayyar da kike nunawa Ammu sam bata da amfani, baki da tabbacin mu a wane hali zamu kasance, shin zaki rayu damu ko kuma mu zamu rayu dake Allah shine masani, Yaya Usman ya fa蓷a ransa a 蓳ace.
Inna ta bangajeshi gami da cewa "Allahu Akbar ashe ka fara wa'azi ban sani ba?, ai sai kacemin bakinku 蓷aya da ita, nidai ina 茩ara gaya muku ko bayan raina duk wanda ya taimakawa yarinyar nan wlhi Allah ya isa ban yafe muku ba"
Dukkansu suka bu蓷e baki sbda ada sun 蓷auki abin kamar ba har 茩ar茩ashin zuciyarta take fa蓷a ba, yanzu kam sun tabbatar da gaskiyar zance.
Ammu na komawa gida ta samu Hakeem na zaune a tsakar gida Ahlam na kwance a saman cinyarsa tayi barci, lokacin 茩arfe 12:pm na rana, Ammu tayi sallama ta 茩ara so, Hakeem na ganinta ya fara yun茩urin mi茩ewa tare da 蓷aga Ahlam yana cewa "Ammu an dace kuwa?"
"Hakeem ina aka dace kai duniyar nan da kake gani idan baka dashi ka zamo banza, nidai abinda nakeso dakai ka guji 蓷aukar kayan da ba naka ba, sannan ka tausaya min Hakeem, Ammu ta fa蓷a tana fashewa da kuka, shima kukan yakeyi, ta kar蓳i Ahlam ta shigar da ita 蓷aki, a ranar sam ta kasa ta蓳uka komai jikinta yayi sanyi sosai, ga tunani iri iri da suka addabi zuciyarta, kiran sallahar Azhar da akayi yayi daidai da farkawar Ahlam daga barci. "Yunwa nakeji Ammu.." Ahlam tai maganar cikin shagwa蓳e murya,
Cikin yanayi na damuwa Ammu ta bu蓷e baki zatayi magana kenan...
Gabaki 蓷ayansu hankali a tashe suka mi茩e cak Ammu ta dafe 茩irji, sakamakon kwa蓷a sallama da ake ta yi babu 茩wau茩wautawa, "munshiga uku Ammu" Hakeem ya fa蓷a yana wulli wulli da idanu, kafin Ammu ta yi yun茩urin furta kalma 蓷aya sukaji wasu mutane sun fa蓷o cikin gidan suna cewa "ku shiga kuga gidan" wani mutumi na gefen mai maganar shikuma yana cewa "nifa banason 蓳ata lokaci idan da ace kunbi za蓳ina da gobe gobennan zansa azo a fara gyare-gyaren gidan" a ki蓷ime Ammu tace "Haba dan Allah ya zaku fa蓷o mana gida babu neman izini bare ma kuyi sallama?" Mutumin da ya fara magana daga farko yace "kinga baiwar Allah kiyi ha茩uri mijinki ya riga da ya mutu, sannan kuma yabar basusuka, munan da kike gani taimakonsa muke yi saboda ya samu ya kwanta a kabari cikin salama, "hakane amma tozarci bashi da da蓷i idan muka bar wannan gidan ina zamu?" Ammu tai maganar zuciyarta na 茩una.
"Idan muka gama ciniki zan ware miki ku蓷in da zaki kama haya, amman adalci nayi miki da"
Wanda aka kira ya siyi gidan ya fa蓷a yana wani 蓷age wa Ammu gira.
Sai da suka le茩a ko ina kafin sukayi mata sallama tare da ce mata sun bata nan da kwanaki goma ta tattara kayanta,
Sosai Ammu ta zubar da hawaye, tashi 蓷aya mutuwar Baba ta dawo mata sabuwa fil,
"Ammu dan Allah ina dangin Baba suke naga baki ta蓳a zuwa ba, kuma shima lokacin da yake raye ban ta蓳a ji yace zai je ba"
Hakeem ya watso mata tambayoyin da kunnuwanta suka tsaya da saurarar komai har na tsawon lokaci,
Sai da ta sauke gwauron numfashi kafin tace "Hakeem kenan, ka manta da abinda marigayi babanku ke gaya muku kullum?"
Hakeem yace "Ammu nasan dai yana ce mana mu guji abin hannun mutane sannan mu tsayar da gaskiya"
"Huhmm" Ammu tayi murmishin ya茩e wanda yafi na kuka ciwo kafin tace "mahaifinku Maraya ne, shika蓷ai iyayensa suka haifa, baban mahaifinku ruwa ne ya tafi dashi, bayan an samo gawarsa ciwon zuciya ya kama mahaifiyarsa wanda ya zamo ajalinta har lahira, bayan rasuwarta mahaifinku ya shiga tashin hankali tare da fuskantar tsana daga dangin mamansa da babansa, akan wani dalili".
Sai kuma Ammu ta fashe da kuka,
"Ammu kinyi shiru dalili kuma?"
Hakeem ya tambaye ta sbda ya shiga ru蓷u sosai.
"Kaf ilahirin mutanen 茩auyen sun tsani mahaifiyarsa wai tana da kambun baka, gaskiya wannan 茩arya ne dan kuwa banga wanda ya ta蓳a kamawa ba, dalilin yasa bayan mahaifinku ya girma yakai munzalin aure yayi aureni"
Hakeem zai yi magana Ammu ta dakatar dashi,
Kana tace "nasan zakace mai yasa aka bashi aurena ko?"....!