Free chapter · Read without an account

Page 11

by Ummu~Fadeela · JUYIN LAMARI

*JUYIN LAMARI*

   By


*Ummu Fadeela*


*Arewapen @ummufadeela01*



PAGE 11







Sun dade suna kallon juna kafin tayi saurin sauke idanunta kasa. Da ace zata iya, cewa zata yi. "Kai nake so Yaya Abdul, kai kadai zuciyata ke muradi".

Amma kash, bazata iya ba. Jira take, jiran ranar da zai kalli tsabar idanunta yace. 

"Ina sonki Halima"

Shiyasa ta kagu taji wannan maganar da kullum yake cewa zai sanar da ita.

"Kin yi shiru. Idan babu wadda kike so kinga sai in kyaleki a aura miki mai warin mazan"

A hankali tace, "Babu kowa!"

"Kin tabbata"

Gyada mishi kai tayi tana share hawayen da ya ziraro mata a ido daya. Tun safe take son yin wannan kukan, amma yaki zuwa. Sai gashi yanzu because of Ya Abdul.

Hannunsa ya watsar gefe yana dage kafada yace, "good for you. To kuma meye na kukan?"

"Babu komai" ta fada wani hawayen yana saukowa.

"To share hawayen bana son ganinsu, zamu yi magana da safe, ohk." 

Sai kuma cikin zolaya yace, "gabadaya kin zama raguwa, bana son ganin wannan Halimar. Dubulle nake son gani mai bawa maza tsoro."

Dariya ta danyi kadan ta langabar da kai gefe tace, "Yayaaaa"

Yayi mimicking muryarta yace, "Dubullen Umma"


*LAGOS*

*MALABU HOLDINGS COMPANY*


A cikin babban dakin taron dake cikin company din. Manya manyan board members ne zaune suna meeting.

Board director ya gyara mic dake gabansa yana kallon CEO yace. "Q2 ya zo mana da tarin kalubalen cinikayya tsakaninmu da clients, tsarin shares da kuma importation. Wannan ne dalilin da yasa muka samu asara a wannan quarter din. But akwai wasu tarin nasaror...."

A fusace CEO ya katse shi, cikin fushi yace. "Wane irin nasarori bayan kazamar faduwar da muka yi? Ko dai cire hannun jarin da ake tayi a company din shine nasarori.

To lallai na baku daga yanzu zuwa Q3 idan banga wani canji ba, I will restructure the so called team of yours. Duk zaku bar company din nan, a kawo wadanda suka san abinda suke yi.

Daga haka ya mike, sabon PA dinsa ya tattare tab da system sai wayoyin CEO din ya mara masa baya da sassarfa.

Babban office nashi mai kama da aljannar duniya ya shiga. Ya zauna a kan sofa yana sauke numfashi a jere. 

Sabon PA nashi ya ajiye masa abubuwan daya kwaso daga meeting hall din saman desk nashi. Ya bude fridge ya dauko bottle water da cup ya kawo masa.

Bai bi ta kan cup din ba, ya balle murfin gorar ya kafa kai. Sai da ya shanye tas yayi jifa da goran yace, "Surrounded by fools".

PA ya matso yace, "Iam sorry sir! Amma da kayi hakuri sun gama yi maka bayani may...."

Bai kai karshen maganar ba ya mike a fusace yace. "Who are you, to tell me abun da zan aikata a cikin company dina, I am Alex Malabu. Nine mamallakin wannan company. I said who are you."

Tsabar irin daga muryar da yayi har yan waje suna jinsa. Gabadaya jama'ar ma'aikatan suka rude. Kowa yana tsoron fushin CEO domin guguwar fushinsa zai iya tafiya da aikin duk wanda tsautsayi ya afkawa.

"You are fired"

"Now get out of my office"

Alex ya fada yana nunawa Sabon PA da kwanansa biyu kacal a company din hanyar fita.

Company yayi tsit, babu wanda yayi yunkurin fita bare ya bada hakuri.

Alex ya koma baya-baya ya fada saman sofa yana dafe kansa da yake jin tamkar ba'a jikinsa yake ba. 

Ash colour eyes nasa sun canza zuwa baki. Zufa ya fara gangarowa ta cikin gashin kansa zuwa fuska da wuyansa. Cikin kasa da mintuna goma gabadaya ya fita a hayyacinsa.

Da kyar ya iya lalubo dayar wayarsa dake cikin aljihunsa, ya yi dialling yasa a hands free.

"Son are you with me?" Ta fada jin tana ta magana ba amsa.

"Mamaaaa" ya kira da kyar yana jan sunan. 

"Jesus" Dangana ta fada a rikice tana mikewa daga zaunen da take. Bible dake hannunta tana karantawa ya fadi tare da siririn farin medical glass dinta garin sauri.

Ta rikice lokaci daya. "Boy, kada ka tashi daga inda kake. I am on my way. Don't do anything Boy."

Medical glass din ta dauka, ta zura wasu silifas masu laushi na falo. Sanye take da bujen siket da ya wuce guiwarta kadan. Sai riga mai gajeren hannu da ya bayyana lafta laftan damtsenta. Farace sol gajeruwa sosai. Kanta sanye da hula da yafi kama da hular bacci.

"Driver! Ta kwala kiran lokacinda ta fito compound a birkice. Securities dake cike ta kowanne angle na gidan kowa ya maida attention dinsa kanta. Da gudu driver da wasu securities din suka iso.

"Oya, muje company yanzu, and I don't want convoy. Private fita zamu yi" Dangana ta fada. Driver ya yace. "Yes maa"

Suna tafiya amma Dangana gani take kamar bazasu kai bai.

Jama'a suna ta hada-hada lokacin da suka shigo. Lifter suka shiga zuwa 5th floor inda office nashi yake. Floor din shiru sai karar na'urori ke tashi. kowa ya makale a office nasa.

Mrs Hannah secretary din Alex ta tashi da hanzari, jikinta yana tsuma ta yi kasa da kai tace.

"Wellcome Maa"

Dangana ta daga hannunta ta sharara mata mari cikin fusata tace, "Baki da amfani a nan Hannah, kina nan har Boy ya shiga cikin wannan halin baki kirani ba."

"Sorry Maa" 

Ta fada tana dafe da kuncinta 

"Sorry for your self, don kujerarki tana rawa a ma'aikatar nan."

Zuge glass da ya raba office nashi dana secretary din tayi. Ta hangosa kwance saman sofa sai juyi yake. Ta durkusa gabansa cikin damuwa tace.

"Oh no. Boy me ya same ka."

"Mother! help me mother!"
Ya furta ciki ciki. Ya mike zaune kadan ya dora kansa saman shoulder dinta. A hankali take shafa kansa tace.

"Zaka iya tashi muje zuwa asibiti"

Ya kwabe fuska yana girgiza kansa, idanunsa a tamke.

Da kyar ta iya taimaka masa ya mike. Kasancewar yana da tsawo sosai, da kadan ta wuce waist nashi.

"Mother! I can't walk."

Ya kuma fada. Zaro ido tayi lokacin da ya koma ya zauna yana dafe kansa. Tace. "Jesus, Boy bari ka gwada tashi da kadan-kadan muje zuwa kasa."

Lumshe ido yayi bai ce komai ba. Ta kuma fadin ohk bari in kira Priest Father yazo ya same mu a nan" 

Wayarta ta danna tayi maganar minti daya ta kashe wayar. Gefen da kan Alex yake ta zauna hadi da dora kansa a kan cinyarta tana shafa kyakkyawan sumanshi gently. 

Bude kofar office din akayi. Wani mutum mai kimanin shekaru 60 ya shigo da wasu biye dashi. Hannunsa daya rike da Bible daya kuma rike da Sanda mai kyau yana dogarawa. A kallo daya zaka fahimci babban limamin coci ne daga yanayin suturar jikinsa.

Dangana ta mike da sauri ta zube a gabansa, idanunta a rufe tace. "Welcome Father"

Ya jinjina kansa yace " How is Alex?"

Ta kara yin kasa da kai tace, "Alex yana fama Father. Ayi masa addu'a.

Ya karaso gaban kujerar da yake kwance ya bude tsakiyar Bible dake hannunsa ya rufe idanunsa. Duk sauran ma rufe idanu suka yi harda Dangana ya fara jero addu'a.

"A cikin sunan Uba, da d'a, da ruhu mai tsarki" duk suka hada baki wajan fadin, "Emen"

“Ya Ubangiji Mai Iko Dukka, muna roƙonka ka dubi bawanka Alex cikin rahama. Ka sauƙaƙa masa wannan ciwo da yake damunsa, ka ba shi lafiya da ƙarfi. Ka ba likitoci hikima su gano abin da ke damunsa, su kuma samu hanyar da za ta taimaka masa.

Ya Ubangiji, ka ba Alex kwanciyar hankali, ka cire masa tsoro da damuwa, ka kasance tare da shi a wannan lokaci na wahala. Ka kiyaye shi, ka kuma cika zuciyarsa da bege da imani.

Muna roƙon wannan ta wurin Almasihu Ubangijinmu.

"Emen" suka kuma amsawa.

Priest ya dubi Dangana yace, "kada kusa damuwa a rai. Zai warke nan bada dadewa ba.

Bayan tafiyarsu Dangana tayi tagumi tana kallon yadda ya samu bacci.

Karar da wayarta tayi ya dawar da ita daga tunanin da ta keyi. Ta amsa wayar ta ajiye kan hannun kujeran tana kallon Alex dake bacci.

"Dangana yaya jikin Abba."
"Da sauki, yanzu priest father ya fita. Ya zo ya masa addu'a".

A fusace yace, "Dangana ki dauki dana ki kai mini shi asibiti yanzun nan. Bana son shirme. Ya yaro yana cikin wani hali ki kira ayi ta masa ihu a kansa da sunan addu'a. Yanzun nan ba sai anjima ba, ku wuce hospital dashi. Ke kin san matsalarsa ba tun yanzu ba."

A fusace itama tace. "Hold on Alaji. Yaronka ko yarona? Ina da Ikon yin duk yadda naso da Alex, because he is my Son".

"To shikenan. Ki kara minti biyar da Abba baki wuce dashi asibiti ba. Zaki ga yadda zanyi dake."

Tsaki taja lokacin da ya kashe wayar. 

Kasancewar ta san baya magana biyu. Tasa security suka yi clearing company compound din gabadaya mutanen dake waje aka shigar dasu cikin, gudun kada su daukeshi hoto. Kafin securities uku suka kama Alex dake bacci aka sauko dashi zuwa mota. Mother ta shiga baya, driver da security daya suka shiga gaba suka wuce asibiti.

A emergency aka karbeshi likitoci suka rufu a kansa.



*KANO"

Gadan-gadan su Innani suka dauki zancan auren Halima da Alhaji Sambo da a ka sanya rana wata daya, kamar yadda Alhajin ya roka saboda Umrah da zai tafi.

An kawo lefe daidai gwargwado. Halima bata dauki zancen auren gaskiya bane, sai da aka kawo lefe. Tayiwa Umma da Baba alkawarin wannan auren, Duk da zuciyarta tana ga Yaya Abdul. Mutumin da har yau bai taba furta mata kalmar so ba.

"Anya zan iya cika wannan alkawarin?"

Ta yiwa kanta tambayar. Duk ta rame sai karewa take yi a tsaye. Ga harkar makaranta dake kara daukar zafi, saukin ma ta samu Dr Tareeq ya dan kulata har sun fara project din. Amma yana da azabar iya yi. Domin duk cikin team din ita kadai yake bawa corrections.

Yau ma kamar kullum ina zaune a makaranta, saboda corrections daya bani jiya. 

Tun around karfe 4 na shigo, amma har yanzu da agogon wayata ta nuna karfe 4:50 bai shigo makarantar ba. Don haka na zauna a karkashin bishiya ina dakon zuwansa.

A karo na hudu na daga idanu. Muka yi ido hudu da daya daga cikin wasu matasa su uku dake zaune nesa dani kadan. Da sauri ya dauke kansa yana pressing wayarsa.

Tunda suka zauna a wajan jikina yaki aminta dasu. Nayi kasa da kaina ina kara duba agogon dake makale a hannuna. 

Karfe biyar ciff, na mike tsaye da nufin komawa gida kawai. 

A lokacin na hangosa ya fito daga senate building yana tahowa toward us. Dan dakatawa nayi kadan ina sauke ajiyar zuciya. Hangoshi da na kuma yi ya tsaya da wani student ya sanya ni karasawa garesu nima.

"Good evening Sir!"

Ga mamaki na bai amsa ni ba ya ci gaba da attending wa wadda suke magana. Kamar anyi masa dole ya kalleni bayan tafiyar mutumin yace da turancinsa kamar baturen London.


"Hadza, right?"

Na girgiza kai ina mamakin yadda kullum sai ya tambaya sunana, ko na sanar dashi kuma ba zai fasa kirana Hadiza ba gobe.

"No sir, I am Halima"

Gyada kai yayi yace, "any probs?"

Na dago idanu da wuri na wani kallesa, lallai gayen nan, ni zai tambaya ko akwai wani damuwa bayan wahalan da yake bani a kan project dina.

"No sir, na gyara corrections da ka bani ne na dawar as you said yesterday"

"Oh yeah, I just forgot " ya fada yana karbar takardun da na mika masa. Ya dora da fadin.

“I’ll review it tonight. Meet me at my office tomorrow at 11 a.m.”

Daga haka ya wuce. Na raka keyarsa da kallo ina jinjina girman kai irin na wannan bawan.

Time da na juya wayam naga babu wadancan samari uku dake zaune a gefena dazu.

Na cigaba da tafiya ina gwada layin Yaya Abdul ko yana kusa yazo ya dauke ni. Amma layin not reachable. Har na kusa fitowa main get ban samu abun hawa ba. 

Kasancewar wajan shiru, karfe shida ta kusa ga yanayin sararin samaniya dake tara gajimare alamar hadari na gaf da haduwa ya sani kara saurin tafiyata.

Kamar almara kamar mafarki naji karan cin taya a gabana. Kofofin baka wuluk din motar suka bude a tare. Matasa uku suka fito. Kafin inyi wani yunkuri, daya a cikinsu ya jefa wata fara tas din hankici a fuskata.










































Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.