Free chapter · Read without an account
BETWEEN TWO HEARTS
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER NINETY TWO:92*
*BETWEEN HEARTS*
*JIDDAAH BARKUM*
———
Motar ta shiga titi a hankali, Zayd ya riƙe sitiyari da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma a kan gearstick, idanunsa a kan hanya, fuskarsa a nutsen ta, kamar babu abin da yake damunsa, ko kuma ba ya son wani ya gane yana damunsa, cikin motar ya yi shiru, sai ƙarar AC da kuma sautin tayoyin da ke shafar titi, hasken fitilun titi na shigowa ta gilashi, suna wucewa ɗaya bayan ɗaya a fuskokinsu, Raihana ta zauna a gefen kujerar, jikinta a matse, hannayenta biyu a kan cinyarta, ta haɗa yatsunta, ta murɗa ɗaya, ta saki, ta sake riƙewa, ta sake murɗawa, ta rasa me ya kamata ta yi da hannuwanta, at this point, gaba ɗaya ta rasa yadda za ta zauna a kujerar nan.
Kamshin turaren da Suhaila ta baza mata yana tashi a jikinta, ya cika motar, har kunya take ji da kamshin kansa, kamar kowanne digo yana sanar da shi cewa ta yi adon ne dominsa, ta ɗan kalli gefe ta ƙasan idonta, ta hango hannunsa a kan sitiyari, agogon hannunsa yana kyalli a hasken titi, nan take ta mayar da idanunta kan hanya kamar wadda wuta ta taɓa, “Ya Allah…” ta faɗa a zuciyarta, motar mai faɗi ce, amma Raihana ta ji kamar wajen ya yi mata ƙanƙanta, sai ta sake ɗan matsawa kusa da window, tana jin sanyin glass ɗin a kafaɗarta, ta ɗan sauke numfashi a hankali, ba ta son ya ji.
Zayd bai ce komai ba, in fact ya yi ma kamar irin bata wajen, irin shi kaɗai ne a motar, alhalin duk wani motsinta a kan idanunsa take yi, sai ya sauke hannunsa daga gearstick, ya taɓa screen ɗin motar, ba tare da ya kalle ta ba, a take sai muryar Sheikh Mishary Rashid Alafasy ta cika motar, a hankali, a tsanake, tana karanta Suratur-Rum, muryar na sauka cikin duhun dare kamar ruwa mai sanyi, Raihana ta ɗan lumshe idanunta, ba ta yi tsammanin haka ba, sai ta ji kamar wani abu a ƙirjinta ya sassauta kaɗan, amma bai tafi gaba ɗaya ba, yatsunta suka sake komawa suna murɗewa, ya ɗan rage ƙarar, kaɗan ne kawai, kamar mutumin da yake son murya ta kasance a cikin motar amma ba ta cika masa kunne ba, hankalinsa kwance, idanunsa a kan titi, kamar ba ya tunanin komai sai hanyar da yake bi, amma Raihana, a cikin nervousness ɗinta, ta ji ayar da take faɗin cewa daga cikin ayoyin Allah ne ya halitta muku matan aure daga kanku, don ku samu natsuwa a wurinsu, kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku, zuciyarta ta buga da ƙarfi, ta sunkuyar da kanta ƙasa, tana jin kunnuwanta suna amsa sound ɗin, ta kasa fahimtar ko ya zaɓi surar da gangan ne, ko kuma kawai haka ta zo, maybe he chose it intentionally, maybe not, ba ta so ta yi tunani sosai, sai ta riƙe yatsunta da ƙarfi, ta rufe idanunta na ɗan lokaci, tana bin muryar da take sauka a hankali, motar ta ci gaba da tafiya, gidaje na wucewa a gefenta, fitulun titi na zuwa suna ƙarewa.
Raihana ta buɗe idanunta a hankali, ta kalli titin da ke gabansu, zuciyarta tana bugawa daidai da tafiyar tayoyin, sai da suka yi nisa sosai, sannan ya ɗan kalle ta ta gefen ido, sai kuma ya maida kansa gaba, ya sauke hannunsa ya rage sautin karatun, har sai da muryar Sheikh ta koma kamar raɗa a cikin motar, “Do you need anything before we get home?” Muryarsa a sanyaye, a kuma nutse, Raihana ta ɗan firgita kaɗan, domin ba ta yi tsammanin zai yi magana ba, ta ɗago idanunta a hankali ta kalle shi, sannan ta girgiza kai a hankali, ba tare da ta ce komai ba, Zayd ya ɗan jinjina kai, bai yi mata wata tambaya ba, ya ci gaba da tuƙinsa, kamar abin da yake jira ke nan, he simply went back to focusing on the road, yayin da sautin karatun ya ci gaba da shawagi a cikin motar, tafiyar minti ashirin ce ta kawo su har gida.
Sai da suka zo bakin gate ɗin gidan, Zayd ya yi horn sau ɗaya, a hankali, can sai mai gadi ya leƙo daga ƙaramar ƙofar, da ya ga motar Zayd, sai ya koma da sauri ya buɗe babbar ƙofar gabaɗaya, yana ɗaga hannu yana gaishe su, Zayd ya shigo da motar a hankali, ya ƙarasa har wajen parking lot, ya yi parking cikin nutsuwa, sannan ya kashe engine, sautin karatun ya tsaya nan take, shiru ya mamaye motar gaba ɗaya, shirun da ya sa Raihana ta ji bugun zuciyarta fiye da da, kamar ana iya jin sa daga waje, Zayd ya buɗe ƙofar ya sauka, ya rufe ta a bayansa, Raihana kuwa ta ci gaba da zama a kujerar, ta rasa abin da ya kamata ta yi, ta kalli hannayenta, ta kalli ƙofar, ta sake kallon hannayenta, zuciyarta na bugawa ba kakkautawa, “Ya Allah, ka ba ni ƙarfin hali,” ta faɗa a zuciyarta, kafin ta ankara, sai ta ga Zayd ya zagayo ta gefenta, ya buɗe murfin motar, ya tsaya yana kallonta, ƙasa-ƙasa, Raihana ta ji kamar iska ta ƙare mata, ta saukar da idanunta ƙasa da sauri, sannan ta kama lafayyar da ta sauko ƙasa, ta riƙe ta da kyau, ta zuro ƙafafunta a hankali ta sauko, ta ɗan matsa gefe, ya rufe ƙofar, sai ta tsaya a jikin motar, hannayenta a riƙe da lafayyarta, idanunta a ƙasa, ba ta san ina za ta nufa ba, ba ta ma san ina ne part ɗinta a gidan ba, hakan ya sa ta kasa yin wani yunƙuri, kawai ta tsaya a wurin kamar wadda aka dasa, iska mai sanyi na kaɗa mata rufin lafayya, kamshin turaren jikinta na tashi, ita kuwa ko da wasa ba ta kuskura ta ɗaga kai ba.
Zayd ya ƙarasa wajen gateman, suka yi ɗan magana, ya juyo da nufin komawa wajen Raihana, wacce yake tunanin ta yi gaban entrance ɗin tana jiransa, amma ya ɗan tsaya, to his utmost surprise, har yanzu tana nan a tsaye a jikin motar, ba ta motsa ba ko kaɗan, kamar wadda ke jiran umarni, ya sauke idanunsa a kanta, ya tsaya kawai yana kallonta, ganin yadda yake kallonta ne, don fess take kallonsa daga inda take, saboda compound ɗin gidan gabaɗaya shake yake da uban fitilu, kamar me haske ya mamaye ko’ina, kamar ko allura ce ta faɗi za a iya ganinta, sai Raihana ta ji kamar dukkan duniya tana kallonta, ta ɗan haɗiye wani abu mai nauyi a maƙogwaronta, sannan a hankali ta fara takowa zuwa inda yake, hannayenta riƙe da gefen lafayyar da take sanye da ita, kamar ita ce ke ba ta courage, ƙafafunta na ɗaukar mataki ɗaya bayan ɗaya, a nutse, har sai da ta zo daf da shi, sai ya juya ya ci gaba da tafiya, bai ce mata komai ba, ita kuma ta bi bayansa a hankali, tsakaninsu akwai ɗan tazara, tazarar da ta sa ta ji kamar tana bin inuwarsa.
Suka ratsa ta tsakiyar compound ɗin, har suka isa bakin part ɗin, Zayd ya zura hannu a aljihu, ya ciro key, ya sa a jikin lock ɗin, ya buɗe entrance ɗin, sannan ya tura ƙofar ya ba ta hanya, Raihana ta tsaya, ba ta shiga ba, idanunta a ƙasa, zuciyarta na bugawa kamar za ta fita daga ƙirjinta, Zayd ya ɗan kalle ta, sannan cikin waccan muryar tasa ya ce, “Are you waiting for an invitation, ko ni ne zan shiga da ke?” Maganar ta ratsa kunnenta, ta ɗaga kai ta kalli gabanta sai ta sake sunkuyar da shi, ba ta ce komai ba, sai kawai ta ɗaga ƙafarta ta ƙetara bakin ƙofar, da addu’a a bakinta, “Bismillah… Allahumma inni as’aluka khayraha wa khayra ma jabaltaha alayh…” ta rera a ranta, tana jin yadda kowace kalma take ba ta ɗan ƙarfi, ta shiga, ta tsaya a cikin falon da hasken ɗakin ya mamaye, ba ta juya ba, tana jin Zayd a bayanta.
Zayd ya tsaya a bakin ƙofar na wasu seconds, idanunsa a kanta, sai ya janyo ƙofar a hankali, ya rufe ta, sannan ya juya, ya nufi hanyar da take zuwa part ɗin Seeyama, takunsa a nutse, a tsaye, babu hanzari ko kadan, yana ɗora hannunsa a kan handle ɗin ƙofar, sai ta buɗe a hankali, alamar ma ba a rufe ta ba, duk da dare ya fara, ba wai ya yi nisa ba, don 20:15 ne kawai, idanunsa suka fara zagaye falon, ba kowa a ciki, sai TV da aka bari a kunne amma an cire sautinsa gabaɗaya, hotuna kawai suke motsi a screen, babu wani ƙazanta a wurin, sai plate ɗin da ta ci abinci kawai yana nan a kan centre table, da kuma bottle ɗin ruwa da na juice da suke nan kusan guda biyar warwatse a falon, pillows ɗin sofa ma a wargaje, ba wani abu bayan haka, ya ɗan girgiza kai a hankali, ya nufi ɗakinta slowly, takunsa a nutse, har ya isa bakin ƙofar ɗakin, ya buɗe, tana nan kwance a kan gadon, rub da ciki, sanye da normal pajamas, riga da wando na cotton, kanta ba dankwali, hannunta a kan wayarta tana ta faman dannawa, jin ƙarar buɗe ƙofar ne ya sa ta juyo, amma da ganin Zayd, sai ta miƙe da sauri, ta ajiye wayar a gefe, kamar wadda ba ta taɓa tsammanin ganinsa ba, “Babe!” ta kira shi, muryarta cike da mamaki da farin ciki a lokaci ɗaya.
Zayd ya zuba mata ido kawai, fuskarsa a yadda take calm, unreadable, babu murmushi, babu wani alamar komai a idanunsa, sai kawai ya tsaya yana kallonta na ƴa seconds, kamar yana ƙoƙarin karanta abin da ke bayan wannan farin cikin nata, ta ƙara matsowa kusa da shi, “Sannu da zuwa, I didn’t know you were coming,” a hankali ya ce, “Why did you leave the door open?” Nan take ta ɗan buɗe baki, tana murza goshinta, “Wallahi I forgot, Mommy ta zo ne, bayan ta tafi, ashe ban rufe ba, I completely forgot,” bai ce komai ba, kawai ya kalli ɗakin nata, idanunsa suka sake zagayawa cikin ɗakin, babu wani laifi a ciki, babu wani abu da za a ce the room is untidy, komai yana cikin order, saboda haka sai ya ɗan sauke numfashi, ya maida kallonsa gare ta, “Is there anything you need?” Da sauri ta gyada kai, kamar wannan ce tambayar da ta daɗe tana jira, ta kama hannunsa, ta riƙe shi da ƙarfi, yatsunta suka matse hannunsa kamar tana tsoron zai sake juyaw ya tafi, “Yes, I need you,” muryarta ta fara karyewa, “Mene ne dalilin da zai sa ka ke avoiding ɗina? Don Allah ni ma ka dinga ba ni lokaci, me na yi maka da zafi haka? Please… is loving you an offence?” Kalamam ƙarshe suka fito cikin wata irin murya mai rauni, hawaye ya fara cika idanunta, kafin ɗaya ya zubo, yana gangarowa a kumatunta a hankali.
Zayd bai motsa ba, kawai idanunsa suka sauka kan hannun da take riƙe da nasa, sannan suka koma fuskarta, fuskarsa har yanzu babu motsi, amma shiru irin na wanda yake sauraro ne, ba wai wanda bai damu ba, “Ka sani, ba ni na sa kaina ba, I didn’t choose to love you this much, wallahi ba ni da iko a kai is something I can’t control,” ta sauke numfashi mai nauyi, kirjinta na ɗan tashi sama da ƙasa, “Ka gani, ban taɓa zama ni ɗaya ba, I have never been this lonely in my life, amma yau, ga ni, saboda sonka, ina zaune ni ɗaya a nan, ina kallon TV ba sauti, ina cin abinci ni kaɗai, ina jiran ƙofa ta buɗe, ina jiran ka,” muryarta ta ƙara rawa, ta matse hannunsa sosai, “Don Allah ni ma ka daure ka dinga ba ni lokaci, yadda kake ba ta, babe… I’m tired of begging for crumbs of your attention, I’m your wife too!” Kalamam suka rataye a tsakanin su, Zayd ya yi shiru, ya kalle ta sosai, wannan karon ba irin kallon da yake yi mata a baya ba, idanunta har sun canja launi, hawaye na ta zuba ba tare da ta damu da boye su ba, fuskarta a cike take da wani irin ciwo da bai taɓa gani a wurinta ba, Seeyama ba wai tana kuka ne kawai ba, she was desperate, she wanted him, ba wai kawai ta na so ya zauna a gidan ba, tana son ta ji cewa tana da wani wuri a zuciyarsa, tana son ta samu attention ɗin da take ganin Raihana ke samu, tana son ta daina jin kamar ita kaɗai ce a gidan da mijinta yake.
Ta sake kallonsa, kamar tana jiran kalma ɗaya daga bakinsa da za ta tabbatar mata cewa ko ta samu wani matsayi a wurinsa, Zayd ya buɗe baki zai yi magana, amma babu abin da ya fito, ya rufe bakinsa a hankali, for a moment, ya kasa cewa komai, ba don bai da abin cewa ba, amma saboda duk wata kalma da za ta fito daga bakinsa a wannan lokacin tana iya zama kamar alkawari, kuma Zayd ba mutumin da yake bada alkawarin da bai shirya cikawa ba ne, har yanzu hannunta na cikin nasa, ya kalli yadda ta riƙe shi gam-gam, kamar idan ta sake shi, zai sake nisa da ita, kuma duk da yadda zuciyarta take cike da obsession ɗinsa, duk da yadda ta yi shekaru tana son wannan mutumin har soyayyar ta zama kamar wani abu da ba za ta iya sarrafawa ba, a wannan lokacin ta bayyana kamar mace ce kawai da ta gaji da roƙon mijinta ya dube ta.
Zayd ya sake ɗaga idanunsa zuwa fuskarta, ya yi shiru, kuma shi ma, a karo na farko, ya kasa ƙwace hannunsa daga cikin nata, “Ba ka so na ko?” muryarta ta fito da rawa sosai, bakinta na ɗan rawa, “Ba ka so na ba… na sani, na san ba ni da kyau, maybe ban kai macen da za ka so ba, na san cewa ni…” hawaye ya sake zubowa kamar an kunna famfo, ta kasa karasa maganar, sai Zayd ya ɗora yatsansa ɗaya ya dora a kan lips dinsa, “Shhhhhh…” Seeyama ta haɗiye maganarta, tana jan ajiyar zuciya a hankali, calmly ya ɗago hannayensa biyu, ya riƙe fuskarta, manyan fingers ɗinsa suka ɗan sauka a kan kumatunta, yana ɗauke mata hawayen da ke zuba a hankali, zuciyar Seeyama ta fara wani uban bugawa, ji take kamar za ta faso ƙirjinta, ta kasa motsi, ta kasa magana, kawai tana kallonsa ne, idanunta cike da mamaki, kamar ba ta taɓa ganin wannan gefen nasa ba, a hankali Zayd ya zame hannunsa, ya kama hannunta, ya ƙarasa da ita har bakin gadonta, ya kwantar da ita a hankali, sannan ya rufa mata duvet, ya ɗauki wayarta da ke gefenta a kan gadon, ya ajiye ta a kan bedside, daga nan ya sake kallonta da lumshaɗɗun idanunsa, muryarsa ta fito a ƙasa-ƙasa, “Ki yi addu’a and sleep,” Seeyama da ke kallonsa kamar ta ga wani sabon abu, ta kasa amsawa da baki, sai kawai ta yi nodding, tana haɗiye wani uban yawu da ba ta san lokacin da ya taru ba, ba tare da ɓata lokaci ba ta fara addu’a a hankali, Zayd kuwa na tsaye a kanta yana kallonta, bayan ta shafa, ya kashe mata fitilar ɗakin, sannan ya juya ya fice, ya rufo mata ƙofar a hankali.
Da fitarsa, Seeyama ta dafe ƙirjinta da sauri, she couldn't believe what had just happened, “Wayyo Allah na…” abin da ta ce kenan, ta miƙe tsaye, ta fara kai da kawowa a cikin ɗakin, gaba ɗaya ta rasa me ya kamata ta yi, she was speechless at this moment, “What could this be?” ta tambayi kanta, ta tsaya, ta sake dafe ƙirjinta, sannan ta sauke wani dogon numfashi, daga ƙarshe dai ta haƙura ta koma ta kwanta, sai faman blushing take yi, ranta fes, kamar an wanke mata zuciya da ruwan madara.
Raihana ta tsaya a tsakiyar falon, idanunta na bin komai a hankali, ta kalli yadda aka tsara komai cikin tsari, kowanne abu yana a inda ya kamata ya kasance, babu wani abu da ke a rikice, everything was screaming luxury, tun daga kayan falon, zuwa curtains ɗin, carpets, lighting, har ma da yadda aka jera furniture ɗin, kamar wani show-room ne da ake kula da shi kullum, wani irin kamshi mai daɗi ya cika falon, kamshin da ya sa ta ja numfashi a hankali, sannan ta sake sakin shi, zuciyarta na ɗan samun sassauci, amma ba gaba ɗaya ba, ta sake waige-waige, part din ya yi mata girma sosai, kuma yanzu da take tsaye ita kaɗai a cikin falon, sai ta fara jin wani irin rashin sanin abin da ya kamata ta yi, ta kalli wata hanya, sannan ta kalli wata, hanyoyi daban-daban ne suka raba falon, amma ko ɗaya ba ta san inda take kaiwa ba, “Yanzu ina zan bi?” ta tambayi kanta a hankali, cikin raɗa, “Ya Allah, I don't even know where my room is…” ba ta san inda ɗakinta yake ba, balle ta san inda bedroom ɗin Zayd yake, ko kuma sauran sassan gidan, saboda haka, ta nufi ɗaya daga cikin sofas ɗin da ke falon, sai kawai ta nemi waje ta zauna a hankali, ta haɗe hannayenta a kan cinyarta, ta sauke idanunta ƙasa, can sai ta ɗago, ta sake kallon ƙofar da Zayd ya fita ta cikinta, zuciyarta ta ɗan buga, kamar tana jiran ta ga ta buɗe, amma ƙofar ta ci gaba da kasancewa a rufe, shiru, babu motsi, sai ƙarar agogon bango da ke tafiya a hankali, tik, tik, tik, ita kuwa ta ci gaba da zama a nan, hannayenta a haɗe, tana jiran abin da zai faru next.
Daga ɗakin Seeyama, kai tsaye part ɗin Raihana ya dawo, tana jin ƙarar buɗe ƙofar, amma ta ƙi waigawa, kawai ta ci gaba da zamanta kamar ba ta ji komai ba, Zayd ya rufe ƙofar a hankali, sannan ya fara takowa cikin falon, staring at her, yana mamakin me take yi a nan, ba ya nemi dakinta ba, Raihana na jin idanunsa a kanta, amma ta dake, ta ƙi kallonsa, ta zauna kamar wadda komai yake lafiya, idanunta a ƙasa, hannayenta a haɗe a cinyarta, Zayd kuwa ya ɗauke kai, kamar bai san tana wurin ba, ya yi gaba da niyyar wucewa ta gefenta, Raihana ta kalle shi ta ƙarshen ido, ta san idan ta biye masa, tsaf zai banzatar da lamarinta, sai dai idan ta kwana a wurin, saboda haka, kafin ya yi nisa, sai ta miƙe da sauri, tana ɗan haɗe rai, “Ina ne ɗakina toh?” Cak ya tsaya, sai kuma ya juyo a hankali, ya kalle ta daga sama har ƙasa, kamar yana ƙoƙarin fahimtar dalilin da ya sa take tambayar abin da ya kamata ta sani tun farko, ya ɗan ɗage gira ɗaya, calmly yace, “Kin zauna ne kina jiran na nuna miki?” Raihana ta murguda baki, duk da har yanzu ba kallonsa take ba, idanunta na ƙasa, “Toh ka nuna min ne?” ta tambaya, muryarta a ƙasa amma da ɗan kaushi a ciki, “You just opened the door for me and walked away, ba ka ce min komai ba, ka tafi wani wuri ka bar ni a zaune.”