Free chapter · Read without an account

10

by Mamuh gummy · AASIYAH

Aasiyah

Mamuhgee

10

Haihuwan SAED ya saka Haj maryam Binnah sake zama kaman head ta familyn a mata sbd yanzu Mijinta Dr Abubakar shine shugaban familyn sbd Alh binnah tsufa ya fara masa yawa ga ciwo sun fara shigowa dan haka ma aka daukesa aka tafi dashi Cyprus acan yake jinya.

Saed nada wata tara Allah ya karbi ran Alh binnah yabar duniya dan haka sai suka sake samun rauni bayan shi anty khadija ma SAED nada shekaru biyu ta ta rasu.

Dawowa Nigeria sukai kwata kwata da zama sbd dole Dr ya tattaro komai dan cigaba da kula da BINNAH's da tarin dukiyar da suke da ita wadda take sake wani irin habbaka.

Haj maryam ta maida hankalinta sosai gurin bawa yayanta biyu rak tarbiya wato Aliyu da SAED duk da aliyu ya girma amma haka yake biyewa SAED kaman yaro suyita wasa sbd yanayin hankalinsa da ba daidaiba,

Hankalinsu a kwance yake suna rayuwarsu ta jin dadi da wayewa babu ruwansu da komai da kowa sai tsananin so da kaunar junansu.

Baffa ma hankalinsa kwance yake sedai shima ciwon tsufa sun kasa barinsa dan haka yake yau ciwo gobe lafiya ahaka dai aketa yawon qasashe dashi gurin neman lafiya hardai aka hakura aka dawo dashi gida sbd ya samu sauki tsufan ne kawai ya hana lafiyar zama.

Shekaru su qara tafiya SAED ya girma ya zama saurayi tareda dan uwansa da suke tsananin son juna wanda shi kansa Aliyu din baya tina cewa ba Amminsu ce ta haifesaba,

Wani irin gata da tsananin so da kaunar iyaye SAED da Aliyu suka tashi cikinsa sedai SAED komawa yayi shine kaman babba sbd yanda Aliyun yake ga karatunsa baya gudu sam sbd babu wani abu dayake ganewa gameda karatun.

Ana cikin haka itama Haj Maryam nata karatun data fara tintini ya kammala dan haka yanxu tanada iliminta na boko sosai data samu dan haka rayuwa ta sake mata dadi sai yanda takeso.

SAED na kammala junior level dinsa na secondary school iyayensa suka maidasa Cyprus karatu shi kadai sai mai kula dashi mutum daya wanda tin anan gida sun saba daman shine mai kulawa dashi.

Bayan tafiyar SAED kewa ta kama Aliyu wanda Amminsu bata iya barinsa tafiya kowace qasa idan bada itaba sbd tsaro da kiyayewa duk da ya zama saurayi babba hankalinta baya kwanciya yaje koina.

Anan yaci gaba da nasa karatun ana kulawa dashi sosai dan shima kansa baya iya tafiya kowace qasa ko tafiyar kwana ba tareda Amminba dan haka shine dan Ammi Saed kuma dan Dr Daddy kaman yanda suke fada.

*******

Iyalan Malam Ashiru kuwa rayuwa suma ta dauki wani juyin da mai dadi ba tsawon shekaru babu haske babu sanyi babu farin ciki ko kadan a rayuwarsu sai matsaloli da rikice rikice,

A farko bayan fitar maryam rayuwarsu rayuwa mai dadi da jin dadi suka fara shimfidawa dan kuwa dadi suka ringa ci dasha da siya sbd samu ya bude masa harma dasu gyaran gida yana fadan duk maryam din ta kashe masa gida da wanki.

Yaran sunyi kewan mahaifiyarsu gabaki dayansu sosai kuma sunso zuwa gareta kwarai musamman jamilu dayake qarami amma sai Baban ya dauke hankalinsu da juyar musu dashi ta hanyar ringa siya musu kayan jin dadi sosai yana hanasu bata kowace matsayi da mahimmanci a zuciya da rayuwarsu dan haka sai suma suka shagala suka kama babansu da shine yake basu wannan jin dadin.

Karatun boko babansu yafi maida hankali akai sosai suyi duk da suna na addinin amma saima sunga dama suke zuwa amma boko sbd sun saka buri da kulafucin sai sunyi kudi kota yaya sai suka maida masa hankali sosai baji ba gani.

A hakan Allah ya taimakesu ya basu kwakwalwa suna samun ilimin sosai shiyasa Baba bayajin qyashin kashe musu duka dan abinda yake samu sbd yayi mugun mugun saka musu burin suyi kudin gaske ya samu rayuwar dayake tsananin buri.

Maryam batafi wata tara ba dgaa fita rayuwarsu Baba Ashirun yayo auren wata bazawara Aisha.

Amarci da jin dadi aka bude sedai tafiya na fara nisa aka fara samun matsala akan 'yayansa dan bai hadasu da kowa da komaiba bai kuma yadda a takura su ba dan haka tafara shan baqar wahalarsu dan duk sun sake zama marasa amfani da rashin jin qai da dan tausayawa,

Babu wanda take amfanuwa dashi a cikinsu daga karshe ma kaman baiwa tazama a tsakanin Baban da yaran taxo ta samu ciki wahala ta saka ya zube ta kuma samun wani ya zube take tubure ta haukace musu itama ta zama mara tausayin ba sauki ta dena yiwa kowa nasiha da amfani a gidan.

Kasuwanci ta fara na cikin gida tana tallafawa kanta daga nan ta sake samun yanci da karfin ji da kowa a gidan daman itama batada sauki kwantar da kai tayi sbd a zauna lafiya,

Halayenta da babu sauki ko kadan data fidda ya saka suka fara dan shakkarta a gidan dan kuwa masifarta da balainta ya wuce tinaninsu,

Qarin abinda ya sakasu shakkarta shine rashi da yayiwa babansu daurin minti ta sama data qasa komai baya samu yanxu baya maganin sisi kullum cikin kame kame yake da buga bugar da babu haske a cikinta.

Suma yaran yanxu kowa nema yake yanda zai samu duk sun fara zaucewa radadin mugun talauci na neman kar su gashi yanzu kowa ta kansa yake nafsi nafsi,

Baba Aisha ce kadai me yan kudi a gidan kuma ko tsintsiya bata iya siya a gidan wadda wani zai qaru da ita dan haka da yunwa suka fara fuskantar mugun illar talauci da haukarsa gashi basada dangana ko kadan dan basu samu wannan karatun ba tin yara.

Shi kansa ubansu yanzu zarewa yake neman yayi duk ya 'bata a gurin tinanin yanda ko haram ce zata shigo hannunsu dan kuwa a hakan da suke daga shi har yayan babu abinda bazasu iyaba akan su samu.

Shekaru sun tafi yanzu ahalin baba Ashiru yaqin neman survival suke dan kuwa sun gama bushewa da gama cikakkiyar zarewa da kuncewa akan baqin talaucin da baida sauki ko kadan,

Zuciyoyinsu kudi da arziki suke nema kota wane hali,

Babu kauna ko misqala zarratin bare tausayi da jin qai tsakaninsu da Baba Aisha wadda ta zamar musu karfen kafa dan kuwa shi kansa Baban rabuwa yakeson yi da ita amma ya kasa kuma tanada kudi sosai dan kasuwancinta sosai yake tafiya ta zama batada lokacin komai da kowa saina kasuwancin nata,

Babu abinda suke kauna sama da fitar Baba Aisha a rayuwarsu ko a mace ko a raye ko a nakashe sudai kawai ta bar rayuwarsu amma dukiyarta ta zauna a hannunsu dan bazasu taba barinta ta tafi batareda sun mallake dukiyar da aka tara a gabansu ba kuma karkashinsu.

Baba Aisha sanin muguwar karfin zuciya da taurin zuciya tareda kaifin hali irin nasu ya sanyata sake tsayuwa dan kuwa tasan bazasu taba barin dukiyartaba hakama tsakaninta da Baba Ashiru yanxu sunan aure ne kawai a baki babu sauran kowace alaqar aure ko girmamawa.

Baba Ashirun shi kansa babu abinda ya tsana tsanar gaske irin ganin Baba Aisha a gidansa dan haka shi da 'yayansa suka sakota gaba.

Ranar da aka wayi gari da wata muguwar zafin rana kuma a ranar Baba Aisha take aikin wainar shinkafar da aka kawo mata kwangila ta tiya kusan goma sha biyar da fankasau na tiya kusan biyar shima dan haka aiki takeyi sosai tareda yaranta dake zuwa tayata aiki irin wannan su biyu.

Tinda aka tashi gidan da aikin babu wanda ya kalleta bare aikinta suka ringa ficewa daya bayan daya basu dawo ba sai yamma lis lokacin babu kowa gidan masu aikin sun tafi daga ita Baba aisha din sai Baba Ashiru wanda yana zaune akazo aka karba aikin aka buga lissafin kudinta dubu dari harda sitttin da wani abu aka bata.

Suna ficewa ya bude baki yace

"Baba Aisha kizo kibar gidan nan tinda sanaar babbaka wuta kika kama bazaki kashe mana gida da hayaqi da kaurin wuta ba babu yanda zaayi ciwon asthma ya kama mutum sbd hayaqi ba ko kwandala bazaki iya bawa mutum ko aroba yaje asibiti bare siyan magani,

Gida dai nawa ne,indai aikin wuta kika kama to baa gidan nan ba sedai ki aje daga yanzu indai kinason zaman gidan nan"

Wani mugun kallo tai masa tana jin takaici da baqin cikin saninsa a rayuwarta tace

"Allah dai ya wanke maka zuciya daga tsatsan baqin ciki da hassada Baba Ashiru sbd dai wannan maganar taka shine qarara,

Aiki dai kama aje kalamanka a gefe bazan dena ba sbd sanaata ce ta ciyar da kaina da sitirta kaina wanda Allah ya dora maka ka kasa,

Zuciyarka data yayanka duk tsatsa nauyi haka zaku hakura kuna kallan arxiki a gurin mutanen da Allah yaso ya bawa.....

Baqin cikin kalamanta akan 'yayansa ya sanyasa jin wani zazzafan bacin rai da baqin ciki ya dauki butar kusa dashi ta karfe me nauyi ya jefa mata a fuska cikin saa kuwa ya sameta a goshi take jini ya feso ta kurma ihu da karfi tana dafe goshin jikinta na daukan rawa.

Ganin jini na gangarowa kan fuskanta ya sanyata jin wata hauka taxo mata da tashin hankali da rufewan zuciya ta dauki butar itama tayi kansa ta buga masa a tsakiyar kai da karfi yana zaune aikuwa take shima jinin ya balle yana gangarowa.

Miqewa tsaye yayi cikeda zuciya da zafin baqin cikin shekaru yayi kanta ya rufeta da bugu da butar yana buga mata koina.

Duk inda ya buga mata ballewa jini keyi sbd nauyi ne da butar da wata irin tsatsa tako ina.

Cikin azaba ta kasa hakura itama ta dauko tandar karfen da suka gama gasa waina yanzu yanzu da zafinta sosai ta buga masa a kai take jini ya kuma balle masa ya riqe tandar ya fizge ya jefar ya kara rufeta da mugun duka mai muni.

Kwacewa tayi ta miqe da sauri jikinta na rawa jini tako ina ta nufi babban kwanon suyar da suka gama soya fankasau yana kan wuta har lokacin sbd bazasu iya saukewa ba sedai suka janye wutar suka barsa da gwarwashi idan ya mutu zai huce a cike yake da mangyada mai tsananin zafin gaske bata tsaya wata wata ba ta dauki gatuwar tasa ta debo mangyadan tayo kansa ta zuba masa a kafafuwansa gabaki daya take ya zube a gurin ransa na neman fita.

A daidai wannan lokacin su khamis suka shigo gidan gabaki dayansu kuma sai akan idonsu

Da wani irin mummunan tashin hankali sukayo kan Baban wanda take fatar kafafunsa tin daga gwiwa ta fara sabulewa har qasa cikin rashin kyan gani.

Babu wata wata kai tsaye khamis da bulama suka shaqota a tare khamis yayi mata wata muguwar kwashewa ta kife kasa da karfi tana kokarin fasa ihun neman agaji dan balain datake gani a idanuwansu sedai kafin ta bude bakinta suka daga babban kaskon man suka juye mata gabaki daya a take ta soye kaman kazar hausa batateda ko shurawa tayi ba.

#MAMUH

#BEST STORY

#BEST LOVE

#PERFECT REVENGE

#BINNAHS

***

***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.