Free chapter · Read without an account

PAGE 11

by Ibtisam Shakoor · ZAREN ZUMUNCI(The thread of family bond )

***


https://www.arewapen.com/book?id=6ab8fc22c237adaad549e3a2


***


………………….
                  ZAREN ZUMUNCI
             (The thread of family bond)
   
                        WRITTEN 

                               BY

                   IBTISAMWRITES ✍️

    
PAGE 11
     Ana ta shirye shirye a ko wane bangare saboda ba sa son ace an zo wani abu be yi bah ko be isa bah.
 
  Biki yana ta karatowa, kowa na ta shiri.Amma ban da Fauziyya.
 
   Ita tana nan tana tayin nata tunanin na cewa, ta yaya hakan zai faru ace wai ta auri wani ba Ibrahim dinta ba?
“Impossible!”
Haka tayi ta zagaye dakin nata.
Can dai ta mike ta ce,
“Bari ta je wajen Daddy. Komai zai faru, daga nan sai dai ya faru.”
Haka nan ta tashi ta je parlour din Daddy.

   Allah ya so ta same shi yana shirin fita. Sai ga shi ta shigo, shi kuma ganin irin yadda ’yar tasa ta shigo a rikice ne yasa ya tsaya yana tambayar ta lafiya.
Sai kawai ta fashe da kuka tana cewa,
“Daddy, ni bana son na aure shi. Bana son auren.”
Daddy ya ce,
“Shi wa kenan?”
Sai ta ce,
“Abdulahad.”
Shiru ne ya biyo bayan ’yan seconds.

   Sai ya ce ta bari. In yaso, idan ya dawo za su yi maganar. Ta kwanta da hankalinta.
Alh. Aliyu was deeply in thought.
Yana cewa,

  “Me yake faruwa ne a gidana? Kowa ba ya son wanda aka zaba masa.”

   Ya ce idan ya dawo zai yi magana da su duka before ya kuma kira Alh. Lawal. Gwara ya yi magana da su, ya ji ko akwai mai wani korafi.

    Bayan barin Fauziyya daga wurin Daddy dinta, tana komawa dakinta sai ta fada cikin tunani na yadda suka fara haduwa da Ibrahim har suka fada soyayya.
 

    “Wata rana ne tana zaune sai friend dinta Iklima ta kirawo ta a waya ta ce,
‘Fauzy, kina gida ne?’
Sai ta ce mata,
‘Eh, ina gida.’
Ta ce,
   
   ‘Kin manta da yau muka yi za mu je shopping? Gani ni na karasa amma ban gan ki ba. Kai haba Fauziyya, ya zaki min haka ma? Maza-maza please ki taho yanzu.’


Sak Fauziyya tayi don gaba ki daya ta manta da maganar fitar ta su.


Sai kawai Fauziyya ta ce mata ta manta amma yanxu nan za ta taho bari da fada wa inne tukunna.

Fauziyya cikin sauri ta shirya ta je ta fada wa Inne cewa za ta tafi shopping.

 



Ibtisamwrites ✍️

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.