Free chapter · Read without an account

PAGE 12

by Ibtisam Shakoor · ZAREN ZUMUNCI(The thread of family bond )

……………….
                      ZAREN ZUMUNCI
              (The thread of family bond)

                         WRITTEN 


                               BY


                  IBTISAMWRITES ✍️



PAGE 12
    
Haka ta je daki ta fada wa inne cewar za ta fita shopping,inne ta kalleta ta ce kin San zaki fita amma baki sanar da ni bah sai yanxu da kika gama shirya wa?
 
    Bayan dai Inne ta gama fadan me yasa bata fada ba tun dazu, sai ta ce ta je amma kar ta dade.
 
Fauziyya ta tafi da sauri. Ta rungume ta ta ce,
 
“Thank you, Inne. I love you.”
Ta fice da sauri.
 
 Inne kawai ta yi murmushin abin da ’yarta tayi ta ci gaba da abin da take yi.
 
  Fauziyya na karasawa, su ma su Ibrahim na karasawa, amma ba su hadu ba sai da suka shiga ciki.
Fauziyya ta zagaya wajen perfumes.
 
  Ta hango wanda Inne ke using, ta saka hannu za ta dauka, sai shi ma Ibrahim ya saka.
 
   Anan duka suka dago ido suna kallon juna.kowa yana ganin ya riga dan uwansa,sai kowa yayi kokarin shi ne zai dauki perfume din nan.
 
Haka dai, da kyar, ganin kamar ya ga hawaye a idonta, sai ya ce ya bar mata, kar ta yi kuka.
    
     Budar bakin Fauziyya sai ta ce ita fah ba wani hawaye da ya gani a idon ta ,kawai dai yasan cewar shi ne ba shi da gaskiya shi ya sa ya ce ta dauka .sai ta dauki perfume din tayi tafiyar ta without saying anything again.
 
Haka dai har suka gama shopping ba Wanda ya kuma cewa dan uwansa kaka .sai dai kawai su ka rin ga satar kallon junan su.
 
Haka dai suka fita bayan sun gama shopping din ba ta kuma hadu da iklima din bah ta fito ta na me kiran ta a waya,ta tambaye ta Ina ta je ne ,ta zo na su hadu bah.
 Iklima ta daga wayar tana me cewa ta tsallaka shan ice cream ne tun da ita ta gama nata shopping kuma ita Fauziyya din bata karaso bah.
 
  Shi kuma Ibrahim, ganin za su tafi, kuma bata kula da shi ba sai ya yi magana ya ce “bari na tsokani mai kokarin yin kukan nan”.Da Dan karfi inda Fauziyya ta jiyo me yace.
 
         Sai ta juyo but still ba ta ce komai ba shi kuma ganin bata yi magana bah sai yayi ta kokarin sai ta kula shi har dai ya samu  ya karbi number dinta.
 
   Bayan ta koma gida wajen Isha, sai ta ga bakuwar number ta kirawo ta, wajen three missed calls.
Sai ta ce bari ta kira.
 
    She has forgotten cewar fa ta yi exchanging number da wani, sai bayan da ta kira ta tuna.
 
 A bangaren Ibrahim kuma ganin ya kirawo bata yi picking ba sai ya ce maybe bata kusa da wayar ne ,amma kuma ya kasa hakuri,every second sai ya duba wayar ya gani ya kira ko bata kira bah, a haka sai ga kiran Fauziyya nan ya shigo phone na shi ,by mistake hannu shi ya daga amma yana realizing cewar hannu sa ya Danna dauka sai yayi sauri ya kashe, in his defense shi ne zai kirawo ta ba ita bah .
  
  Sai Ibrahim ya kuma kiranta da wayarsa.
Sun dan yi hira,sai suka yi sallama suka kashe wayar,yana me cewa sai na kiran ta su gaisa time to time.Daga nan kusan duk two days haka yake kiranta.
 
 
   A haka har suka ci wata guda da haduwa ,har shakuwa ta shiga tsakaninsu. Daga nan kuma sai suka fara soyayya.”
 
    Sai kawai ta tsinci kanta da murmushi, duk wannan bacin ran da take ciki.
Meanwhile, a can bangaren Alh. Lawal, shi ma Abdulahad ya samu babansa ya fada masa cewa ba ya son ya auri Fauziyya.
 
   Da babansa ya tambaye shi dalili, sai ya ce kawai shi ne bai shirya auren yanzu ba, shi yasa.
Alh. Lawal yayi shiru yana kallonsa.
Sai ya ce,
“Ya shi, ka tafi. Za mu yi magana da Alh. Aliyun.”
 
 Bayan fitowar Alh. Aliyu daga meeting din da suka yi na company dinsa, sai ga kiran Alh. Lawal ya shigo cikin wayarsa.
Ya daga, suka gaisa, sannan ya ce in babu damuwa yana so yau su hadu, amma a gida.
Sai Alh. Aliyu ya ce babu matsala, sai sun hadu.
Haka suka hadu.
Alh. Lawal ke fada masa yadda suka yi da Abdulahad dazu.
Sai Daddy Aliyu yayi tambaya ya ce,
“Ko dai dama ba a tambayi ra’ayin yaran nan ba ne kafin a fara maganar auren?”
Alh. Lawal ya ce,
“A’a, ko daya. An tuntube su. Sai daisu ma din suna tsoron fadar ra’ayinsu, kar ace ba a karba ba, shi yasa suka yi shiru. Amma yanzu da suka ga da gaske ne fa, ai ga shi sun fito fili suna fada.”
 
 
 
Ibtisamwrites✍️

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.