Free chapter · Read without an account

12

by Mamuh gummy · AASIYAH

Aasiyah

Mamuhgee

12

Labarin daya fara tayar da tsigar jikinsu suka fara ji daga bakin Babansu gameda su waye asalin BINNAHs wainda babu mai irin tarin arzikinsu a wannan qarnin hakama a taqaice 'dan mahaifiyarsu Haj maryam Binnah shine asalin magaji daya tak da BINNAHs suke dashi sbd dayan 'dan a gurinsu take a gurin labarinsa ya shude babusa alissafin da zaa bayar ma.

Shiru sukai dukkaninsu tareda dauke wuta kansu na daukan wani irin zafin da kowannensu yana buqatan lokaci shi daya dazai digesting abinda sukaji dan haka daya bayan daya batareda sunce komaiba kowa ya shige suka kwanta tareda mantawa da Baban a gurin sai tsakar dare ya ringa kiran bulama wanda ya kasa bacci ya kuma kasa motsawa sedai jamilu yaxo ya daukesa ya maidasa dakin shima bawai dan yana cikin cikakken tinaninsa ba gabaki daya sunyi nisa a tinanin dayake da karfin gaske.

Kaf gidan tin daga kan baban har su babu wanda idanuwansa suka ko rufe bare rintsawa yanda suka ga rana haka suka ga daren zuciyar kowa da wani irin tinanin dayake daya dana dan uwansa dan kuwa tabbas lokacin haduwa da mahaifiyarsu yayi haduwan da babu rabuwa sai kuma yanda hali ya bayar.

Gari na wayewa dukkaninsu a nitse suka shirya suka sake zaunawa da babansu akan komawansu ga Haj maryam dan samun abin nema masa lafiyar da zasu tabbatarda sun dawo da ita rayuwarsa.

Wani sanyin da rabonda zuciyarsa da rayuwarsa ta samu irinsa harya manta yaji dan kuwa a yanda yakejin wata irin wutar dake cin jinin yayansa yasan lokacin cikar burinsu ne yayi koda zasu rasa ransu ne kuwa.

A karan farko da suka taba dora kafafunsu a hanyar xuwa gidan kakansu kenan tin bayan shekaru masu dan yawa na rabuwar iyayensu,

Basu ji komai na shakka,fargaba,nauyi kunya ko damuwa ba saima wani nutsuwa da kwanciyan hankalin da suka samu suka tinkari gidan Baffa.

Gidan ya jima da sauyuwa dan haka ma qyar suka gane gidan amma baya nan ya jima da barin nan din,

Sunyi tinanin hakan daman dan sunsan bazai taba yiyuwaba zamansa anan yana matsayin mahaifin haj maryam binnah.

Da bincike mai nutsuwa da tsanani suka gane inda ya koma dan haka washe gari suka isa garesa dan shine hanyar da dole zasubi dan komawa rayuwar mahaifiyarsu.

Sunbi ta hanyarsa ne ba don suna kewarsa ba ko buqatansa a rayuwarsu shima sai don saboda sun san cewa Baffa shi ne mafi kusa da ita kuma wanda zai iya hada uwa da yayanta.

Baffa yana zaune a harabar gidansa cikin lafiyayyar rumfar hutawansa datake tsare da wasu lafiyayyun kayan laushi da kujerun zama masu kyau da tsari yana kishingide ya tsufa sosai duk da akwai jin dadi sosai amma tsufan dai ya riga yaxo,

Mai gadin gidan bai barsu sun shigoba saida yazo ya sanar dan haka shiru baffan yayi yana tinanin su waye din su khamis saida ya jima yana nazari kafin ya tina da sune sbd kaman yanda suka yafesu suma tini suka gogesu a rayuwarsu..

Mamaki ne mai karfin gaske ya rufe tsohon ya sake shiga nazarin zuwansu garesa yana juya sunayensu a zuciyarsa dayaji tana kasa samun sukuni ko kadan tukuna yace a bari su shigo.

A jere suka shigo dukkaninsu kusan sunyi tsawo daya sum zama manyan samari masu karfin gaske,

Basui kama da yaran da ya sani ba acan baya sbd hatta kamanninsu sun sauya sosai amma kai tsaye yana kallansu ya tabbatarda jinin Ashiru ne sbd kamannin sun nuna sosai.

Abin da ya fara girgiza Baffa shi ne yadda kallonsu ya kasance mai cikeda wani irin kaifi,

Ba kallon yara ne da suka zo neman mahaifiya ba akwai wani abu a idanunsu,wani buri,wani yunƙuri,wata ƙishirwa.

Baffa ya daɗe yana kallonsu kafin ya bude baki a natse da kwanciyan hankali ya amsa gaisuwansu da suka zauna suna yi masa a tsananin nustuwa.

"Me kuka zo yi?"

Khamis ne ya ɗan sunkuyar da kansa yana kokarin bawa baffan girma da bayyanarda nutsuwansa dan kuwa duk abinda suke suna kwantar da kai daidai yanda zasu samu a cikin sauki da qwarewa a juyar da tinani akansu.

Dauke kallansa daga kansu baffa yayi yana dan sallamar lawal dayake tareda shi wato mai kulawa dashi sosai daga gurin dan bayason ma a yasan su din su waye tukuna.

Jamilu ne ya bude baki muryansa a kamale ya gaida Baffan yana dorawa da yaya jikinsa sbd tsufa ya nuna kaman lafiyar yanxu ba isashiya bace.

Amsawa yayi a taqaice yana dan sake kallansu kafin ya kuma cewa

"Ya rayuwa? Ya mahaifinku?

An zama manyan matasa yanzu aiki kukeyi ko?

To Allah ya taimaka ya qara rufa asiri"

Babu wanda yace amin a cikinsu sai khamis dayace

"Bama aikin dai tukuna,muna fatar farawa sbd karatun ma bamu qarasa kammalawa ba munata kokarin dai"

Shiru suka dan yi gurin babu wanda yace komai kowa da tinanin dayake ransa banda Baffa dayake jinsu babu alaqar komai bayan ta zamansu baqi.

Bulama dayafi iya bakinsa fiyeda kowa a cikinsu shine ya dan muskuta yana bude baki da karfin haali yace

"Baffa shekaru sun tafi rayuwa ta ganar damu kuskurenmu akan mahaifiyarmu da aka rabamu da ita duk da laifin namu na ƙuruciya ne a lokacin dan munyi kewanta munso zuwa gareta Baba ya hanamu hakan kuma bai taba barinmu hakanba,

Baffa dan ayanzu kam mun gane babban kuskurenmu ma daya hanamu yin gaba a rayuwa shine rashin bin uwa dan haka munzo neman gafara da yafiyarta ko Allah zai bamu hasken rayuwa"

Jamilu fashewa yayi da kuka mai taba zuciya yana sunkuyar da kai qasa da cewa

"Baffa dan Allah ka hadamu da Mahaifiyarmu mu nema yafiyarta mu gyara gobenmu"

Khamis na ganin hakan ya sunkuyar da kansa shima yana tsiyayo hawaye yana ambatar sunan Baffan da tsananin damuwa.

Bulama me bakin magana shine ya ringa fadan halinda suke ciki kawai yafiyarta suke nema ba komaiba tace ta yafe musu shine abinda kadai ya kawosu suke nema.

Baffa shiru yayi kawai yana jinsu duk da yaji dadin kalamansu da suke maimaitawa da kuma yanda suka san cewa uwa uwa ce dan yasan Maryam tabbas bazata taba ciresu daga zuciyarta ba har abada dan haka zaiso ta yafe musu amma bayajin nutsuwan dawowansu rayuwarta sam kawai dai ta yafe musun amma kowa yayi rayuwarsa a duniyarsa daban.

Bude baki yayi bai musu nasiha ko nuna karban tubansu ba dan harga Allah ya yafesu daga rayuwar maryam bazai taba son kuma su dawo ba,

"Allah ya yafe mana gabaki daya ya kuma sake ganar damu ya tsare gaba"

Bayan hakan bai kuma cewa komaiba sai sukai shiru suna jiran ya qara da wata kalmar suka zuba masa idanuwansu da suke shirye da komai.

Ganin wata kalmar suke jira daga bakinsa ya sanyasa dan gyara zama hankali kwance batareda bada tabbaci ba yace

"Maryam bata qasar yanzu haka tana Cyprus dan haka ba maganar yanzu yanzu bace ku tafi insha Allah zan sanar da ita komai idan ta dawo zakuji komai"

Shiru sukai sbd jin wai batama rayuwa a qasar,

Jamilu sake fasa kuka yayi yana cewa

"Baffa wlh bazan iya komawa koina na iya rayuwaba yanzu batareda sanin mahaifiyata ta yafemun ba,

Jin nakeyi kaman rayuwata bazata kai ba,

Baffa ka mana rai dan Allah kada mu shiga masifar da batada magani,nidai bazan iya tafiya koina ba"

Jin hakan Bulama ya kalli jamilun da sauri ta qasan ido sbd dai shima wlh bazai iya komawaba yana ganin wannan aljannar duniyar da Baffa yake ciki shi kadai yana rayuwa dan haka shima kukan ya fasa yana fin jamilu jero kalamai masu taba zuciya da bayyanarda tsantsar nadamarsu.

Baffa kallansu ya tsaya yana yi kafin ya dauke idanuwansa daga kansu yana jin zuciyarsa kwata kwata babu natsuwa.

Duk wata tari da girman nadamarsu sun nunawa baffa da kuka da komai tareda labarai masu taba zuciya dan haka ya sassauto dole ya sallamesu tareda basu kudi mai yawa amma sam suka qi karba sbd ba wannan kudin suke so ba koda zai kwashe komai nasa ya basu basa so komawa rayuwar maryam sukeso dan amsa sunan 'yayan Haj maryam binnah da duniya zata sani.

Tafiya sukai suna fitowa a hanyarsu ta isa gida jamilu ya tsaya chemist din anguwansu yaci bashin paracetamol na dari biyu sbd kansa dake ciwon kukan daya ringa yi da girmansa.

Suna shigowa gida khamis bokita ya dauka ya zuba ruwa ya fada wanka yana jin ko zai siyar da qoda da huhu da hantarsa dan ya koma rayuwar Maryam binnah saiyayi dan kuwa saiya amsa sunan Khamis Binnah matiqar Mrayam din na amsa sunan BINNAHs.

Bulama kuwa zaunawa yayi idanuwansa duk sun kumbura sbd kukan da shima ya sha a gaban baffa yafara bawa Baba labarin duniyar da Baffa kadaima yake ciki.

Washe gari haka suka sake komawa gidan baffa da yamma suka qara bayyanarda tubansu har dare suna gidan aka kawo abinci mai lafiya da tsari suka ci suka koshi sai guraren 9 suka koma gida.

Suna dawowa kowa shigewa yayi dan da qafa suka dawo kuma ko yauma basu karba kudin baffan ba sbd ko a zalama da karfin kafircinsu sunada akida ta tsayawa akan raayin abinda sukai niya da buri akansa.

Washe gari ma haka suka kuma komawa gidan baffa wanda zuwa lokacin ya fara yadda da tubansu da sauyawansu dan idan suka zo zaunawa sukeyi suyi shiru cikin tinani gwanin tausayi.

A cikin kwanaki kadan suka maida gidab Baffa gurin zuwansu kullum can suke wuni suna masa hidimar kulawa dashi dan sun kwacewa lawal kulawa da baffan yanzu sosai suke nuna masa kulawa da kauna da tattali kaman zasu basa rayukansu.

Abincin safe rana dana dare mai kyau da lafiya suke ci su koshi su dawo gida su kwanta hankalinsu kwance dawowan Haj maryam kawai suke jira.

Babansu ahankali ahankali yafara ganin sauyin rayuwa sbd kwata kwata babu me lokacin tsayawa kulawa dashi kullum suna can kuma idan sun dawo dare yayi dan abinda suke masa bame yawa bane a kwanta ga yunwa na neman shigarsa sbd duk yanda sukaso kawo masa abincin ba daman fitowa dashi dan haka sedai su basa hakuri ko su ciyo masa bashin wani abin yaci ya kwanta ya koma so daya kenan yakeci a wuni.

Tin bayajin komai yana sake alfahari dasu akan yanda suka tsayu tsayin dakan komawa rayuwan maryam kota halin yaya harya fara jin damuwan nasa halin dayake cikin dan ya dena samun kulawa kwata kwata sai abinda hali ya bayar kuma a yanda idanuwansu da zuciyarsu ta riga ta bushe akan wannan burin nasu sabo babu abinda zai hanasu cimmasa.

Jikin baffa suke sake shiga sosai cikin kwantar da kai da tsantsar biyayya da nutsuwa har tsawon lokaci hakama nasu daina bibiyar sanin BINNAH's ba da jin asalin waye su.

A duk lokacinda suka sake samun sabon bayani akan su waye BINNAHs hankalinsu sake tashi yake sosai suna neman rasa hakuri da nustuwansu amma suka kanne suna biye da baffa sau da kafa.

Jikin Baba Ashiru yafara rikicewa sosai dan kuwa kafafu sun caccabe sun narke wasu ruwa sukeyi andena zuwa asibiti wankewa ga rashin abinci da kulawa sai yafara zarewa koyaushe cikin fada da sambatu yake gashi su yaran sunata kara kokarin fara samar da hanyar kudin kaisa neman lafiya.

Labari ne yakaiwa Dr Binnah dawowan yayan maryam dinsa rayuwar baffanta sbd suna neman gafararta dan gyara lahira da duniyarsu kuma baffa yaqi hadasu da ita dan haka da kansa ya kira baffan sukai magana sosai ya bada daman a kawosu BINNAHs mansion dan sadar da maryam da yayanta wainda har cikin ransa yaji yana kaunarsu da tsananin tausayinsu sbd bincike ya saka akai akansu yasan komai ko karatunsu duka ya dakata.

Baffa baiso hakan ba amma sbd yanda Dr din ya masa bayanin ba komai bane insha Allah shiriyar da ake musu fata ce tazo,

Lokacinda Dr Binnah din ya dawo qasar da kansa ya fara zuwa gidan Baffa a ranar ne su Khamis suka fara ganinsa a zahiri dan haka gabaki dayansu jininsu wata irin dahuwa yafara akan tsananin farin ciki da ganin kofar arzikinsu a gabansu da kansa dan haka dukkanin biyayya da nustuwarsu tattarota sukai suka kwantar da kai tareda nuna masa nadamarsu sosai mai kashe jiki da kukan daya taba zuciyarsa sosai dan haka take ya yanke shawarar tafiya dasu ga maryam din a washe gari.

Jin hakan ya saka duniyarsu tsayawa cak da tsantsan farin cikinsa basu taba samun irinsaba a rayuwarsu kaf dan haka koda suka koma gida babu wanda ya rintsa a cikinsu daqyar sukaga safiya ta waye.

Da safen haka suka dan yiwa baban abinda zasu masa wanda shima jamilu ne yayi khamis tini ya fita yana waje yana nazarinda baya buqatan kowa da komai a kusa dashi,

Bulama kuwa gugar kafarsa ya taqarqare yanayi sbd sanin rayuwarsa zata sauyane daga yanzu.

Baba Ashiru bai iya cewa komaiba banda binsu da ido shidai kawai koma mene aje a samo dukiya azo aji dashi.

Karfe goman safe wata mahaukaciyar Mercedes-Benz tazo har anguwan ta daukesu tin anan khamis yake sake jin kirjinsa na nauyi.

Duniyar da aka kaisu datake dauke da sunan BINNAHs Mansion itace matakin farko data saka burinsu na baya rushewa a take wani burin na doruwa sbd sanyi ma jikinsu da jininsu tareda idanuwansu sukai take kowannensu yaji baida kuzari ko kadan hawayen gaske da suka fito daga zuciyoyinsu na irin abinda suka gani suka fara ciko idanuwansu Take bulama ya fasa wani irin kuka jikinsa na daukan rawar gaske yana toshe bakinsa kada kukan ya fito dan kuwa kansa bugawa yake neman yi.

Khamis ma jikinsa rawa yafara sosai idanuwansa na yin jajir ya kafe idanuwansa tareda tsayar dasu cak akan makeken hoton Haj maryam dake tareda 'Danta SAED da dayan 'dan nata Aliyu,

Jamilu ma kukan yafara yana sharbe majina yana neman zarewa sbd baimasan tinanin yi ba.

##MAMUH

#CRAZIEST BETRAYAL

#PERFECT REVENGE

#STRUGGLE FOR POWER

#BINNAHS

#SECOND KILL

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.