Free chapter · Read without an account
THE NEW ROUTINE
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER NINETY THREE:93*
*THE NEW ROUTINE*
*JIDDAAH BARKUM*
———
Kawai ya zuba mata idanunsa masu cike da wani irin calmness din nasa, yana kallonta a nutse na wasu daƙiƙa kaɗan, idanunsa suna yawo a fuskarta kamar yana karanta abin da take tunani, kafin daga ƙarshe ya amsa mata, cikin wannan irin muryar da ba ta da hayaniya amma take da command a cikinta, “Duk ɗakunan gidan naki ne… kawai kar na ga kafarki a ɗakina,” Raihana ta ɗan ɗaga gira, ta buɗe baki kaɗan kamar za ta ƙara magana, amma kafin ta samu damar cewa komai, Zayd ya riga ya juya, ba tare da ya jira ta ce komai ba, ya ci gaba da tafiya a hankali zuwa hanyar part ɗinsa, takunsa na fitar da wani irin class, body language ɗinsa gaba ɗaya cike yake da confidence da wannan calmness ɗin da yake sa mutum ya ji kamar komai yana ƙarƙashin control ɗinsa.
Raihana kuwa ta tsaya tana kallonsa, idanunta suka bi bayansa har na ɗan lokaci, sannan ta fara zuba masa wata uwar harara ƙasa-ƙasa, ta tura baki, kamar wadda aka faɗa wa magana da ta ɗan bata mata rai, a hankali, can ƙasa, ta fara magana ita kaɗai, “Toh dama me zai kawo ni ɗakinka?!” Ko da yake ta faɗa a hankali ne, Zayd, wanda ke da wani irin sharp hearing, rasss! ya ji ta, amma bai ko ɗan juyo ba, not even a glance, ya cigaba da tafiyarsa kamar bai ji komai ba, hannunsa ɗaya a aljihu, takunsa steady, har sai da ya bace gaba ɗaya daga idanunta, tana ganin ya bace gaba daya, sai Raihana ta saki wani dogon numfashi, kamar yanzu ne aka sake mata numfashi da ta dade tana riƙewa, ta sake taɓe baki, daga nan ta juya, ta fara motsawa a hankali, ta bi wani direction daban da wanda shi ya bi, idanunta suna yawo cikin falon yayin da take ƙoƙarin gane inda nata ɗakin yake.
Amma part ɗin ya yi mata girma sosai, gabaɗaya gidan yana da wani irin luxury da ya sa take jin kamar tana cikin wani five-star private residence, kowanne corridor yana kama da zai kai ta wani sabon sashe, ta tsaya a wani wuri, ta kalli dama, ta kalli hagu, sai ta sake kallon gabanta, “Ya Allah…” Ta furta cikin raɗa, ta ɗan dafe lafayyarta, “Yanzu kuma ina zan fara nema?” Ta ci gaba da tafiya, tana neman inda nata ɗakin yake a cikin wannan uban part mai azabar girma, zuciyarta kuwa har yanzu tana ɗan bugawa saboda tsoron ta, Allah tsoronta kar ta je ta afka dakin da ya shiga, ta ci gaba da tafiya a hankali, tana bin wata hanyar da ta ɗauka kamar ita ce za ta kai ta nata part ɗin, ta yi tafiya na ɗan lokaci, har ta iso wani corridor da yake da ƙofofi guda uku kacal, ta kalli ƙofar farko, ta kalli ta biyu, sai ta kalli ta uku, “Maybe this one…” Ta furta a hankali, sai ta buɗe ƙofar farko.
Da ta shiga, sai ta tsaya cak, idanunta suka sauka kan wasu set-set na kayan lefe da aka shirya cikin tsari, kusan set uku, an ajiye su a wani gefe na ɗakin, sai kuma wasu daga cikin kayan amfaninta da ta gane nan take, a nan ne ta daina ƙoƙarin buɗe sauran ƙofofin, ba ta son sake yin wani wrong turn, ta shiga gaba ɗaya, ta rufe ƙofar bayanta, sannan ta kai hannunta ta kulle ta da key, sai ta tsaya na ɗan seconds, ta jingina bayanta da ƙofar, ta sauke wani dogon numfashi, “Finally…” Ta furta cikin raɗa, kamar wadda ta gama wani dogon journey, daga nan ta juya ta fara kallon ɗakin, room ɗin yana da kyau sosai, amma ba irin luxury ɗin da zai sa mutum ya ji kamar yana cikin showroom ba, komai yana da simple, neat and classy, babban bed ɗin yana tsaye a tsakiyar ɗakin, an shimfiɗa shi da soft neutral bedding, curtains masu laushi suna rufe windows ɗin, yayin da warm lights ɗin da ke cikin ɗakin suke ba wajen wani irin calm and cozy feeling, a gefe akwai elegant dressing mirror, sai wardrobe mai faɗi, sannan wata ƙaramar sofa da aka ajiye a wani gefe.
Raihana ta sake kallon ko’ina, sai ta sauke idanunta, ta fara ƙoƙarin kwance lafayyar da ke jikinta, a hankali ta cire ta, ta nade ta neatly, sannan ta ajiye ta gefe, daga nan ta cire sarkarta da ƴan kunnen da ke kunnenta, ta ajiye su a kan dressing table, sai ta ɗan shafa wuyanta da hannunta, ta sauke ajiyar zuciya, “Let me just freshen up,” ta furta cikin ƙaramin murya, sannan ta nufi bathroom, ta shiga, ta rufe ƙofar, bayan ɗan lokaci, ta fara yin warm bath sosai, ruwan ɗumi ya sauka a jikinta, yana taimaka mata ta saki wannan tension ɗin da ta kwashe yini tana ji, ta tsaya ƙarƙashin ruwan na ɗan lokaci, idanunta a rufe, kafin ta sauke numfashi a hankali, for the first time since ta shigo gidan… zuciyarta ta fara samun nutsuwa, bayan ta gama, ta yi alwala, sannan ta fito cikin ɗakin tana ɗaure da towel, ta ƙarasa wajen wardrobe, ta buɗe shi, sai kawai ta tsaya, idanunta suka buɗe kaɗan.
A cikin wardrobe ɗin akwai kayanta, ba wai kaɗan ba, komai da komai, wasu kayan gida, wasu dogayen gowns, hijabs ɗinta, wasu kayan da ta san su, har da wasu da bata ma san a yaushe ta same su ba, Raihana ta ɗan taɓa ɗaya daga cikin kayan, daga ƙarshe ta zaɓi wata simple, free-size gown mai kyau, ta saka, ta ɗora hijab ɗinta a kanta, ta gyara shi cikin sauƙi, sannan ta nufi gaban dressing mirror, ta kalli kanta na ƴan seconds, fuskarta ta yi calming sosai bayan wankan, duk wani trace na gajiyar ranar ya ɗan ragu, ta ɗauko turare, ta fesa kaɗan a jikinta, “Just a little…” Sai ta ajiye turaren, daga nan ta dawo wajen sofa, inda ta hango wata prayer mat da aka ajiye a kai, ta ɗauke ta a hankali, ta shimfiɗa ta a ƙasa, sai ta tsaya na ɗan lokaci, ta gyara hijab ɗinta, ta kalli agogo, lokaci sallar Isha’i har ya ja dan kusan tara saura yanzun, ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta tsaya kan sallayar, a hankali ta fara sallar Isha’i, zuciyarta tana neman wannan irin peace ɗin da ba ta samu ba tun lokacin da ta shigo wannan sabon gidan, a wannan lokacin babu wani tension, ita kaɗai ce da Ubangijinta, sai nutsuwa ta fara sauka a zuciyarta a hankali.
Haka daren ya kasance, daban ga kowanne daga cikin mutanen uku, Seeyama kuwa, tunanin yadda Zayd ya canja mata a yau ya bar ta speechless, har yanzu tana ƙoƙarin fahimtar abin da ya faru, da kuma dalilin da ya sa mutumin da ta saba gani cikin wani irin hali ya nuna mata wani sabon side ɗinsa, Raihana kuwa, tunaninta ya koma kan sabon wurin da ta tsinci kanta a ciki, sabon gida, sabuwar rayuwa, da kuma yadda za tayi coping da wannan ɗan rainin hankalin, sarkin baƙaƙen maganganu… Shi kuwa Mr Armaan… babu wanda zai iya gane meye ma abun da yake tunani, ya kwanta cikin nutsuwarsa, kamar yadda ya saba, amma abin da ke yawo a zuciyarsa… Allah kaɗai Ya sani, haka daren ya kasance, kowanne da irin tunanin da ya kwanta da shi a zuciyarsa, sai mu ce Allah Ya tashe mu lafiya ❤️ ZAYSEERA 💕
Washegari ya tashi da asuba bayan yayi nafilolin sa da addu’o’i, ya fito daga ɗakinsa sanye yake da black jallabiyya wacce ta fito da well-structured body dinsa, kuma ta sake bayyana yadda fatarsa ke da haske, tafe yake a hankali cikin corridors ɗin gidan, bai san ina zai nufa ba, don bai san a ina ne ɗakin da ta sauka ba, amma ya san tunda ta ga ya bi wannan part ɗin, toh definitely zai yi wuya ta kasance a wannan din, sabida haka sai ya bi ɗayan hanyar, ya yi ɗa knocking a first door ɗin dake sashin da Raihana take.
Raihana kuwa tana zaune akan prayer mat, ta idar da Wutri kenan, sai ta ɗan kalli ƙofar, gabanta na faɗuwa, ta yi shiru, a hankali ta sake jin knocking ɗin, sai ta mike ta ƙaraso wajen a ɗan tsorace, “Waye?” Muryarsa ta fito a ɗan dusashe, sabida baccin da ya tashi da kuma dadewa bai ce komai ba, “As-Salah,” kawai ya ce, daga nan ya juya ya wuce, without waiting for her response, Raihana ta ɗan juya ido, “Hmm…” Ta tabe baki, tana kallon ƙofar kamar wadda aka bar mata wani puzzle da safe, sannan ta koma kan sallayarta, kai tsaye bangaren Seeyama ya nufa, ya isa ya buɗe ƙofar nata, aikuwa tana nan, ta yi rashe-rashe akan gado tana baccinta peacefully, like a little baby, irin kamar yanzu ne ma daren ya fara, Zayd kawai ya tsaya yana kallonta, idanunsa suka tsaya a kanta na wasu seconds, fuskarsa kuwa babu wani expression mai yawa, kafin a hankali ya saka hannunsa ya ɗan bubbuga gefen pillow ɗin da take, Seeyama ta juya kawai zuwa ɗayan side ɗin, ba tare da ma ta buɗe ido ta ga waye ba, Zayd ya ɗan lumshe idanunsa ya sake budewa a kanta, ya sake sunkuyowa ya ƙara bubbugawa da ƙarfi, yana kiran sunanta, “Seeyamaah…” “Wake up,” brain ɗinta na jin muryarsa, sai ta ɗan buɗe ido, ta ɗaga kai kaɗan, ta ganshi tsaye a kanta, “Babe…” Ta kira shi cikin muryar bacci, tana mutsuka idanunta, “Tashi kiyi sallah,” ya faɗa a nutse, sai ta ɗan turo baki, tana sake maida kanta kan pillow, “Zanyi da safe fa… yanzu nan baccin ya ɗauke ni, please,” Zayd ya ɗan haɗe rai, “Stand up, Seeyama,” Seeyama ta turo baki tana tashi zaune, “Babe, da safe da yanzu duk ɗaya ne, ka barni nayi bacci, please,” ta faɗa tana kallonsa da sleepy eyes, Zayd ya tsaya yana kallonta na seconds kaɗan, “Seeyama…” Kawai ya kira sunanta cikin wannan calm voice ɗin nasa, amma akwai warning a ciki, sai ta san babu room for negotiation, ta yi shiru, Zayd ya sa hannu ya janye duvet ɗin da ta sake rufe kanta da shi, “You are wasting my time, get up,” Seeyama ta kalle shi, ta sake turo baki, “Okayyy…” A hankali ta mike, ta shige toilet ɗin tana jan ƙafafunta kamar wadda aka tilasta mata barin mafi kyawun bacci a duniya.
Zayd kuwa ya ƙi tafiya, domin ya san tsaff yana fita zata dawo ta koma ta kwanta, sabida haka ya tsaya a wajen, hannunsa ɗaya a aljihu, yana jiran ta, bayan ɗan lokaci ta fito daure da alwala, tana turo baki, sai da ta yi baja-baja da kayan wardrobe ɗinta, Zayd yana tsaye yana kallonta kawai, expression ɗinsa getting more serious by the second, Seeyama ta ci gaba da searching, har sai da ta samo hijab da ƙyar, ta ɗaga shi tana kallonsa, hijab ɗin ko cinyarta bai kai ba, Zayd ya kalle ta, ya kalli hijab ɗin, sannan ya sake kallonta, ya girgiza kai a hankali, “Cire wannan,” Seeyama ta ɗan daure fuska, “Babe…” “Nemo abaya ki saka,” ya faɗa calmly, kamar magana ce da ba ta buƙatar argument, Seeyama ta sake kallon hijab ɗin, “But babe, this one is okay…” Zayd ya ɗan ɗaga gira, hijab ɗin gashi nan ko tsintsiyar hannunta bai rufe ba, bai ce komai ba, just one look, Seeyama ta fahimta, ta yi shiru, ta ajiye hijab ɗin, ta fara neman abayar, ganin kamar bata son daukowa sai Zayd ya juya, ya ɗauko ɗaya daga cikin abayar ya miƙa mata, Seeyama ta karɓa tana ɗan turo baki, ta saka abayar, sannan ta ɗora hijab ɗin, tana kabbara sallah, Zayd ya fice daga ɗakin, yana fita kuwa ya kalli time a wayar sa dake hannunsa, ya kusa missing sallah.
A compound suka haɗu da gateman, “Morning, sir,” gateman ya gaida shi, Zayd ya ɗan gyada masa kai kawai, “Morning,” daga nan suka wuce zuwa masallaci, Zayd yana tafiya steady kamar yadda ya saba, babu wani rush a body language ɗinsa duk da cewa ya san lokaci yana tafiya, shi dai Zayd Armaan… even in the middle of fajr rush, still had that same calm, controlled aura, sai wajen 6:30am, after sunrise, Zayd ya shigo gidan, kai tsaye part ɗin Raihana ya nufa, ya daɗe kishingide a nan falon, cikin nutsuwa har ya kunna news ɗin safe a BBC, muryar mai gabatar da labarin tana amsakuwa a hankali, shi kuwa yana saurare ne casually, babu wani expression a fuskarsa, daga ƙarshe ya ɗan lumshe idanunsa.
Raihana kuwa bayan ta idar da sallah, ta koma kan gadonta tayi kwanciyarta, don bata san abinda zata yi ba, kuma ma ko tanada abun yi ɗin, still tana da buƙatar ta ɗan huta, domin jiyan ma ba wai wani baccin kirki ta samu ba, kasancewarta a sabon waje, bakon gida, da duk irin abubuwan da suka faru, bata dade da kwanciya ba bacci ya yi gaba da ita, sai wajen 8:30 ta farka, ta buɗe idanunta a hankali, ta ɗan kalli ceiling ɗin ɗakin kamar tana trying to remember where exactly she was, sai kuma ta tuna, ta sake lumshe ido na seconds kaɗan kafin ta tashi zaune, ta gyara kan gadon data kwana, ta gyara pillows ɗin, sannan kai tsaye ta faɗa bathroom, bayan ta gama wanka, ta fito ta tsaya a gaban wardrobe, idanunta na yawo kan kayan, ta ɗan tsaya tana kallon su, kamar wadda take wondering what to wear, daga ƙarshe ta ɗauko wata atamfa coffee brown mai kyau, dinkin riga da skirt, ta saka ta, bata yi wani abu da sunan kwalliya ba, illa kawai turare sai lip balm, ta ɗauko dankwalin zata ɗaura, sai kuma ta jefa shi kan gadon, ta koma wardrobe ɗin ta ɗauko wani ƙaramin veil cream ta yafa, ta gyara shi yadda ya zauna a kanta, daga nan ta koma kan sofa ta zauna, ta janyo wayarta, ta kalli screen ɗin na ɗan lokaci, tana so ta kira Umma, amma safiya ce, bata so ta firgita ta, ko ta sa ta fara tunanin wani abu ne ya faru har ta kira da sassafe, ta girgiza kai a hankali, sai ta canja akalar wayar zuwa ga Khausar.
Bayan sun gaisa, Khausar ta gama tsokanar ta da cewa, “Sai yau kika tuna damu kenan, Amarya? Kinyi luffff a gidanki, WhatsApp ɗin ma ba ko yaushe ake samunki ba!” Raihana ta ɗan yi murmushi, “Kin dai ji dashi…” Khausar tayi dariya, “Dama haka zaki ce mana, ni ma dake school ta ɗauke min hankali ne, ban bi ta kanki ba, kin san final year student ba zamaaaa!” Ta ƙarasa tana dariya, Raihana dai taji duk, ta manta da tsokanar Khausar gaba ɗaya, brain ɗinta ya tafi kan maganar school, da yanzu fa itama graduation zata yi ko? Nan take sai wani irin tunani ya shigo mata, ta ɗan cije lips ɗinta, idanunta suka sauka ƙasa, sai ta ji wani uban malolon baƙin ciki ya cika mata zuciya, a zuciyarta kuwa, ta ƙuduri aniyar sai ta tambayeshi, zata koma school, domin gaskiya bazata bar wahalarta for years ya zama in vain ba, “Zan koma…” Ta furta a zuciyarta da determination, har suka yi sallama da Khausar, bata ji mood ɗinta ya dawo dai-dai ba, ta ajiye wayar a gefenta, ta ɗan zauna shiru, daga nan kuma sai cikinta ya fara tambayarta shima, ta ɗan dafe cikinta, “Hmm…” Ta tuna da rabonta da abinci tun da rana a Armaan Mansion, ta kalli ƙofar ɗakin, sai a fara tunanin, “Yanzu fa… maybe yana falon,” nan take ta tabe baki, “Ina ruwana toh dashi ma?” Ta faɗa a hankali, tana ɗan ɗaga gira, “Na biye masa kila sai na mutu da yunwa,” ta ƙara faɗa, sannan ta girgiza kai kamar tana arguing da kanta, “Whatever,” daga haka ta mike, ta ɗauki wayarta, ta duba screen ɗin once more, sannan ta fice daga ɗakin zuwa neman ina kitchen ma yake a gidan.