Free chapter · Read without an account

Chapter 17

by MARYAM STAR · ƊAURIN ZUCI

***

𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
         𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙐𝙈𝘼𝙍 

Chapter 18
  Yayinda ita kuma babbar take da haske me me sirkin jah wannan shi ne kawai banbancinsu bayan na shekaru amma kamar su har ya ɓaci.
      "Daddynsu wai mi ke faruwa da kai ne kake kulle kanka kai kaɗai cikin ɗaki ka fuba wayarka aƙalla na yi maka miss call kusan ashirin amma babu ɗaya daka ɗaga, na dawo gidan na zo ina knocking nanma shiru baka kula ni ba da ace dabarar shigowa ta waccan ƙofar bata faɗo min ba da bazan san kana nan ba."
  Ta faɗi tana nuna hanyar data shigo da hannu, ganin hankalinsa ya koma wajen ƙofar sai ta shammace shi ta fizgi hoton katin tana kallo.
   Amamakance ta buɗe baki tare da faɗin.
     "Zunaina wannan ai Zunainah ce ko Daddynsu?."
   Ta yi tambayar tana me yi mashi nuni da hoton.
    Bin yatsarta manuniya yayi da kallo kafin cike da damuwa ya ce.
    "Yes, ita ce mana." yana kawar da damuwar dake bayyane akan fuskar shi sai kuma kamar wanda ya tuna wani ya yi saurin cewa.
   "And ya jikin Mujaheed ɗin yanzu nike shirin zuwa hospital ɗin kwatsam ina bincike sai nayi tozali da wannan ɗin."
      Lokaci ɗaya ta fashe da kuka me ƙarfi wanda ya soma tsuma zuciyar Daddy a hankali ya janyota jikin shi cikin siggar rarrashi yana ƙoƙarin ɓoye damuwar shi ya ce da ita.
    "Its okay, munyi kuskure kuma mundamu da hakan, mun kuma gane kuskuren mu please kibar shi iya mukaɗai daga ni sai ke bana so kuskuren mu ya sake taɓa wanda suka shafe mu."
   A ɗan fusace  Mommah ya taɗo daga jikin shi fuskarya share-share da hawaye take faɗin.
     "No wannan ba kuskure bane, son kai ne da kuma son duniya, dolene ko muna so ko bama so mu girbi abin da muka shuka, amma miyasa! mi yasa san kanmu zai taɓa zuriyar mu bayan basu san komi ba, mi yasa Afnan da Mujaheed suka kasance masu girbar irin da muka shuga bayan sanda muka yi shukar basu da masaniya, miyasa har yanzu ba zamu fuskanci gaskiya ba muka tsaya muna nuƙu-nuƙu lokaci yayi, lokacin ya zo Alhaji Ahmad."
      Ta faɗa tana goge hawayen da suka ƙi tsaya mata, yayinda Daddy ya sunkuyar da kan shi ƙasa yana kallo wani ɗan ƙaramin mukuli daya faɗo daga cikin kayansa yana tura ranar da mukullin yazo gare shi.
WAIWAYE SHEKARU ASIRIN.

    Zaune yake saman mota ƙafar shi na lilo yayinda takalman shi ke a ƙasa bayan sun fice daga ƙafafuwan shi,  kallon farar fuskar shi me haske irin na zabayyana amma dai nashi hasken bai idasa kai na zabayyana ba, kuma gashin kan shi brown color ne ba baƙi ƙirinba.
     Sake gyara tsayuwa a karona babu adadi Ahmad ya yi domin dai ya gaji da tsayuwar bai san firar tasu zata yi tsayi har haka ba da yace su ƙarasa shagon shi daya kulle saboda zumuɗin ganin abokin na shi.
    "To Alhamdulillahi yanzu dai na yi nasanar kammale dukiyata waje ɗaya na haɗa komi da komi na ware wanda zanci gana da juyawa sauran kuma musamman gwala-gwalaina na killace su waje ɗaya tare da kyautar da su ga yarana Zunaina da Maryam, kuma in sha Allah kai ne mariƙin dukiyarsu saboda kai kaɗai nike da a yanzun bayansu.
     Ya faɗa tare da buɗe tafin hannunsa wani ɗan ƙaramin mukulli amma me tudu sosai ya bayyana a tsakiyar tafin hannun shi.
    Bin key ɗin da kallo Ahmad ya yi yana kallo yanda yayi ma shi kyau sosai hakan ya saka   ya ɗauka tare da jujjuya shi cikin hannun shi kafin daga bisani ya ce.
     "Kai Abdul wallahi kana ɗaure min kai da shige-shigenka ni kaina da aka haifa a cikin garin Katsina bazan iya nuna hanyar da kabi kaje aka ƙera maka wannan key ɗin ba saboda bansan wasu ƙwararru da ke irin wannan ƙirar ba."
   Wata siririyar dariya Abdul ya saki sannan ya ce.
   "Ah to ka zauna nan dai kanka yayi murfi aini tuni na daina biye maka na shiga gari inata ƙara samun haske, inkaji ta yanda aka yi na samu wannan abin dole kayi mamaki wallahi."
     Girgiza kai Ahmad ya yi yana sake danƙar key ɗin cikin tafin hannunsa.
     "Aini ban san yanda aka yi ba ka koyi yawo da shige-shige yanzu ka zama komi da ruwanka indama  bana tunani can nike riskar labarin wai anganka."
    Da fara'a a fuskar Abdul ya ce, "Hummm kaide ka bari wannan key ɗin tare yake da wani ƙaramin box me kyau wallahi a wajen wani mutumi na siye shi lokacin da na shiga kasuwa naji yana bada labarin wai ɓarayi sun takura ma shi har kusan sace box ɗin aka yi kuma gwala-gwalan shi ya adana a ciki Allah yaso shi  yayi ihu mutane suka zo ceto ɓarayin suka gudu, shine ya futo da box ɗin zai siyar, nan take na taya muka yi ciniki na siya yanzu haka da nike baka labari  box ɗin na cikin mota na haɗa komi a ciki du wasu yakardu masu muhimmanci na damƙawa ƴaƴana kuma kaine wanda zaka ada musu a wajenka, kai kaɗai nike da kai kaɗai kuma na yarda da shi a wannan duniyar, Madom ta ce wai inkai ajiya a bank nikam sam ban yarda da wannan tsarin ba yanzudai zo mu je in ajeka gida daga can kuma nima gida na nufa yau a gajiye nike wallahi."
    Ya faɗa tare da dirowa daga kan motar.
    Dogo ne sosai me cikakkiyar ƙira kuma kykakkyawa ne ajin farko a kallon farko zaka tabbatar da hakan.
    Bai bawa Ahmad damar cewa komi ba ya ja hanun shi tare da buɗe front sit ya zaunar da shi sannan ya buɗe mazaunin driver ya zauna tare da tada motar shi ƙirar golf wacce ake yayi a lokacin yabar wajen zuwa unguwar Modoji inda gidajensu shi da Ahmad suke, a ƙofar gidan Ahmad ya tsayar da motar tare da kallon shi ya ce.

   "Kaje ka ɗauko yaranka makaranta yau zamu fita da Mommunsu gashi Maryam ta saka rigima dole harda ita aka tafi islamiyya."
   Waro ido Ahmad yayi tare da faɗin.
    "Kai Abdul tayaya zaka bayar da yarinya irin haka a makaranta ai wallahi malaman ka haɗa da jidali waye bai dan rigimar Maryam ba gaskiya da kayi shawara da ni da babu inda zaku kaita kuma da ace na sani da wuri wallahi da sai na je na ɗaukota da kaina."
  Murmushi Abdul ya yi yana jinjina yanda aboki ɗan uwa kuma aminin shi ke nuna kulawa ga iyalan shi shiyasa yake ganin shi kaɗai ya cancanta data ja ragamar dukiyar daya tarawa ƴaƴan shi wacce yake jin zata wadace su suyi rayuwa ko da baya nan.
     Ɗaukar akwatin yayi tare da fito da shi daga cikin wata jikka ya kalli Ahmad da murmushin da baya rabo daga fuskar shi ya ce.
    "Ko ga dukiyar yaranka nan komi da komi yana a ciki wannan key ɗin shine mukullin akwai wasu golds dana siya amam babu resipt sai an kawo zanje in amsa idan na amsa zan kawo maka, kodayake bara in baka takardar sahidar siyen daman da sunanka na yi amfanin wajen siyen idan ban samu dama ba kaine zaka je ka amso gama takardun nan."
   Ya faɗa yana fito da su daga cikin aljihun shi.

    Wani shiru ne ya gifta a tsakaninsu lokacin da Ahmad ya buɗe box ɗin yayi tozali da sinƙin gold manyan kusan guda koma a jefe, a saman su kuma sarƙoƙi ne danƙara-danƙaran sarƙoƙi zobba da yan hannaye ne ga kuma takardun ko wane a linke an aje a ciki.
    Ahmad zai yi ƙarya idan yace hankalin shi bai tsananin tashi ba, domin kuwa har wata zufa ce ke tsatstsafo mashi a ɗimauce ya ce da Abdull.
    "Abdul mi yasa ka zaɓe ni wajen kula da dukiyarka baka tunanin wata rana tunani ya sauya baka tunanin zan iya yi maka butulci idan na gudu da dukiyarfa."
   "Bana tunanin duka abin da ka lissafo cancantarka ta saka na zaɓe ka karka manta kai kaɗai nike da shi bayan Allah da iyalaina."
****
Karka manta kai kaɗai nike da shi bagan ALLAH da iyalaina."
    Daddy ya maimaita kalaman da Abdul ya faɗa a wancan lokacin yana rintse idanuwansa da tsananin ƙarfi zafafan hawayen danasani haɗi da tashin hankali na silalowa daga idanuwansa, ido a rufe ya zauna jagwab a ƙasa tare da lalubar key ɗin ya damƙeshi a saitin zuciyar shi dake dokawa da tsananin ƙarfi.
    Bawai ya manta da du abubuwan sa suka faru bane a baya, amma ya kasa tuna ta yanda aka yi tunanin shi da zuciyar shi suka sauya ya kasa tuna ta ya da aka yi ya karya yarda da amincin da Abdul yayi mashi ya zaɓe shi wajen kulawa da rayuwar ƴarsa da dukiyarsa.

Mommah tun lokacin da ta fuskanci Alhaji Ahmad yayi nisa a tunani sam baya jin abin da take faɗi ya saka ta yasar da hoton da ke hannunta ta fice zuciyarya a cunkushe ta sauka down stairs ta fice compound inda driver ke jiranta ta shiga bayan ya buɗe mata tana share hawayen da suka ƙi tsayawa a idanuwanta, ahaka Yahaya Driver yaja motar suka fice daga gidan, jifa jifa yake kallon yanda Mommah ke share hawaye haka kawai ya kasa haƙuri ya ce da ita.
    "Hajiya kiyi haƙuri idan na yi miki katsalandan, haƙiƙa na lura kina cikin damuwa kuma nasan hakan bazai rasa nasaba da rashin lafiyar Alhaji ƙarami ba a halin yanzu addu'arki kawai yake da buƙata sabaza ita ce zata zama tsari a gare shi kuma zai samu sassauci ne ta sanadiyar hakan domin ALLAH na karmar addu'ar iyaye akan ƴaƴayensu kuka ba mafita mabe saima ƙara ma shi damuwa da zai yi domin kuwa kowa yasan yanda Alhaji ƙarami yake da biyayya da tausayin iyayi ba zai taɓa samun nutsuwa ba ida yana ganin damuwa atare da ke ki daure kici gaba da addu'a muma zamu tayaku in sha Allah domin Mujahidu ɗane na halak.".....✍🏻

KUCI GABA DA BIYO NI  DOMIN JIN YANDA ZATA KAYA A CIKIN WANNAN ZAZZAFAN LABARIN

MARYAM STAR CE ...✍🏻

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.