Free chapter · Read without an account

Page 09

by Ummu~Fadeela · JUYIN LAMARI

*Juyin Lamari*

        By

Ummu Fadeela

Book One

*Arewapen @ummufadeela01*




Page 09







Halima ta hade kai da guiwa tana rera Kuka, duk ta tuna cewa har yanzu Baba baya kulata ko gaisuwarta baya amsawa, duk a dalilin hotunan sai taji zuciyarta ta karye.

"I don't mean to hurt you plsss. Ki dena wannan kukan"

"Yaya Abdul Baba baya mini magana har yanzu, kuma wallahi ba abunda ya faru ba ke nan. Editing na hoton sukayi, kuma na san sharrin Ramlah ne."

Halima ta fada tana sakin kukan da ya fi na farko karfi.

"Is ohk, share hawayenki. I promise you this, duk wanda yake da hannu a wannan aika aikar must pay for it Insha Allahu".

Halima tayi kokarin share hawayenta amma yaki tsayawa.

"Oya share mana, haba amaryar Alhaji Sambo".

Abdul ya fada cikin zolaya yana leka fuskarta.

Ta turo baki gaba tace, "Allah yayaa bana so".

Sai da ya tabbatar ta share hawayenta tas kafin ya barta ta fita daga motar.

Yace, "Idan an tashi ki jirani zan zo in mayar dake gida. I want to discuss something with you." Ta gyada mishi kai, ta wuce.

A hankali take tafiya yana binta da kallo har ta shige cikin makarantar. A duniya akwai abunda zai rusunar da Dubulle ta saka tayi sanyi kalau lokaci daya haka dama?

Abdul yayi wa kansa tambayar yana hasaso ta wata daya kacal baya.


---

Halima taji tamkar ta juya a guje ta fita daga makarantar, amma ta daure tana cigaba da takawa tamkar kafafunta za su fadar da ita sakamakon yadda idanu suka mata caaa.

Idan an kalleta, sai a kama magana kasa-kasa.
Wasu kuma waya suke budewa suga cikin wayar su kalleta. Tun ranar da abun ya faru bata kara shigowa school ba kasancewar rashin lafiyar Umma dake asibiti. Hakan yasa suke kallonta tamkar talabijin.

Ta dinga karfafa kanta ganin bata tankawa kowa ba har ta iso ƙofar lecture hall dinsu.

Tsayuwa tayi tana dafe kirji da sauke numfashi. Dubulle part of her na tsungulinta ta koma ta saukewa masu kallonta kwandon bala'i.

Da sauri ta dago kanta jin wani kamshi mai dadi ya ziyarshi hancinta.

Da bayansa tayi arba lokacin da ya shige cikin hall din ya tura kofa".

Halima ta dafe goshinta tace, "Ya Allah, yau ma nayi missing lectures because of Ya Abdul. duk da ban ga fuskar lakcara din ba. Amma na gane shine. Mtssww taja wani dogon tsaki tuna maganar Mufida.

"I noticed that he is very strict Dubulle. Kuma idan ya riga students shiga class baya barin ko waye ya shigo. Koda mutum daya ne a class din haka zai karantar.'

Jiki a sanyaye ta koma karkashin bishiyar da suke zama ta kai zaune. Incident na ranar ke dawo mata cikin kai daki-daki, a gefe guda kuma damuwar abubuwan dake faruwa a gida, jikin Ummanta, kulata da Baba ya daina yi, ga kuma uwa uba auren da ake son hadata da Alhaji Sambo wanda hakan ke nufin karshen rayuwarta.

"Eh karshen rayuwata mana, rabani da Yaya Abdul tamkar rabani da rayuwata ne" ta fada a bayyane.

Halima tana zaune wajan na tsawon lokaci. Wayarta take dubawa. Ta dago kai jin tsayuwar mutum a kanta.

Kallon sama da kasa Fidoh da Zuby dake tsaye a kanta suke yi mata. Kallo daya zaka yi musu ka san rikakkun yan iskan jami'a ne.

Zuby ta tauna chewing gum ta huro tayi baloon dashi, kafin ta fasa ya bada sautin kasssss a saitin Halima da al'ajabin ganinsu bai bar saman fuskarta ba.

Fidoh tace, "A haka dai kamar mutum, ashe kura ce lullube da fatar akuya. Me ya hadaki da saurayina har kika samu gut na kwanciya a jikinsa?"

Zuby ta amshe zancen da fadin.

"Bakiga har wani lumshe idanu take yi ba."

Fidoh tace da sauri. "Yo taji kirjin lafiyayyen namiji ba irin wadanda ta saba bibiya a clubs ba."

Suka yi maganar a tare suna kallon Halima.

Zuby ta hade fuska lokaci daya ta zama serious tace.

"Ke yar matsiyata me ya hada kazamin jikinki da nasa. Ko kin dauka shi din irin tarkacen mazan nan ne dake kai ki club cikin dare."

Cewarta tana haskowa Halima hotonta tare da sabon lakcara dinsu dake fuskar wayar.

Tunda suka fara magana dama Halima tayi focusing completely a kan wayarta ta bawa banza ajiyarsu.

Sai dai kalmar diyar matsiyata da Zuby ta ambata yasa ta kasa jurewa, ta mike ta daidaita tsayuwarta da tasu. ta kama kugunta da hannu daya, ta karkata kai gefe ta nuna Zuby da yatsarta tace. "Saka idanunki cikin nawa. Sunana Halima Baraya. Inkiya Dubulle, mai hali dubun da babu na zabe.

Kadan daga cikin tantirancina shine in miki tsirara a wajan nan, kuma babu yadda kika iya dani. Sittin ta Qur'ani idan kin musa kice casss a nan kiga yadda danyen kan Dubulle yake aiki a kan kadangarun bariki irinku."

Ta fada tana juya idanu da tabe baki. Ta dora da fadin. "Ganina a kirjinsa da kuka yi kuma matsayi ne, idan wata a cikinku tana ganin ta kai ta gwada mana mu gani."
Duk iskancin su Zuby kasa cewa komai suka yi suna kallonta. Yadda take tsiwa da karkada jiki tana mar-mar da idanu.

"Shirmen banza da wofi. Da kunsan baku shirya ba kuka tunkari Dubulle" Ta fada tana komawa mazauninta.

"Ke banza, yar iska mai yawon Hotel har kin isa ki daga mana murya, wacece ke." Fidoh tayi karfin halin fada.

Halima ta mike da sauri tace. "Hala bakiji mai kyau ba in maimaita. Sunana Halima Baraya, inkiya Dubulle mai hali dubun da babu na zabe. Ni din kafin Allah ce ba dai mutum ba wallah.

Yawon hotel da clubs kuma iyawa ne. Wasu ko sunje babu mai kallonsu."Ta tabe baki tace tana nuna su da yatsa, "Kamar dai ku din nan, ku riga da kun zama bola. Taxi no garage. Kowa shiga yake sadda yaso ya fita a lokacin da yaso"

A fusace Zuby ta daga hannu da niyyar marinta. Halima tayi saurin cafke hannun ta lankwasa sai da yayi kara, Zuby ta kwala ihu.

"Ki kiyayi taba Dubulle, 'kashi daya gareni, idan na ballaki sai an mika ki Dala orthopaedic.

Zuwa lokacin jama'a sun fara cika wajan. Hayaniya yana tashi. Kawayen su Zuby sun cika wajan suna kokarin dukan Halima.

Itama Halima ta kwance gyalenta ta daure a kunkuminta. Duk wacce ta fada a take Halima ke mayar mata amsa.

Kamar ance ta daga kanta. Ta hangosa yana zuwa toward them, yauma da sunglasses a idanunsa yana taku as giant he is.

Da sauri Halima ta mayar da kanta kasa a take incident na ranar ya dawo mata.

Mufida ta shigo cikin crowd din ta kama Halima da ta juya kan su Fidoh dake auna mata zagi tana ramawa.

"Me haka Halima kike aikatawa, me yasa zaki biye musu ma tun farko"

"Dallah cika ni Malama, sai shegen tsoro. Ni akwai wanda ya isa daga mini hankali ban firgita sa ba. Wannan Halima Baraya ce, bani da tsoro sai dai in bada tsoro"

Halima ta bawa Mufida amsa tana kwace hannunta.

Da kyar aka samu raba fadan da yaso zama tashin hankali a wajan bayan Dean of students sun shiga lamarin.

Halima ta zauna tana sauke numfashi. Mufida dai tana tsaye a gefenta ta kasa yin magana.

"Allah yana gani tsoron bala'in ki nake yi Dubulle. Yanzu kika iya cacan baki da wadannan gidiga-gidigan matan?."

A harzuke Halima ta dago har lokacin tana sauke numfashi tace, "Dallah can banza kawai. Kiyi ta tsoro a mayar da ke bola. Yanzu haka ji nake kamar in sume dan takaicin raba fadan nan da akayi."

Mufidah ta tabe baki tace, "Ke dai ba yarinya bace. A ajin karshe kike fa a jami'a ya kamata ki san kin girma."

"A'a ni ce na haifi Kano karshen girma ke nan, kinga Mufidah rabani da jarabar ki inji da damuwata"

Halima ta bata amsa dai-dai isowar class rep nasu wajan. Ya kalli Halima yace.

"Hajiya Halima manyan kasa, kin san ke kadai ce kika rage a team namu baki je wajan supervisor dinmu for your project consultation ba ko?.

Na san kinga sanarwa a group an canza mu daga hannun Dr Bashir zuwa wannan sabon lakacara din, so is better ki hanzarta zuwa ki gabatar da kan ki. kinga bamu da lokaci, and mutumin dan girman kai ne. Kiyi addu'a kafin ki shiga wallahi."

Dan murmushi tayi tace, "class rep nayi busy kwana biyu Mahaifiya ta babu lafiya. Ko ta kan wayar bana bi shiyasa, amma yanzu zan je"

Cikin zolaya yace, "ai ke GURU ce shiyasa bakya duba waya, mu kam ai ko yaushe muna makale da ita.

Bayan tafiyar class rep, Halima ta juya ta kalli Mufidah dake tsaye bisa kafafunta har lokacin tace, "so ta tabbata ke nan mutumin can shine supervisor dinmu?.

"Tambayeni" cewar Mufidah tana barin wajan.

Halima ta kwashe akalla minti biyar tana tsaye bakin ƙofar office din da aka tabbatar mata nasa ne ta kasa yin knocking. Daga karshe tayi gathering courage ta buga sau biyu.

Sai bayan kamar minti uku, har ta cire ran za a amsa, daga ciki taji deep voice nasa ya amsa da.

"Yes, come in"

Ta tura ƙofar ta shiga da sallama. Daga bakin ƙofar ta tsaya gefe kadan jin kamar bai amsa sallamar ba.

Halima tayi kasa da kanta. Tace

"Good evening Sir!"

Nan ma shiru bata ji alamar an amsa ba. Don haka taja bakinta bata kara yin magana ba.

Wayarsa dake gaban table yayi kara, ta dan saci kallon bangaren da yake.

'Dr. Tareeq Olamide'

Shine sunan da ta fara arba dashi jikin wani shape da akayiwa ado da golden rubutu.

"Ashe ma arne ne, shiyasa baya amsa sallama"

Halima ta fada ciki ciki tana kara satan kallonsa.

Yana zaune kan kujerar office din dake dan juyawa kadan-kadan. Yayi focusing a kan kyakkyawar tablet dake gabanshi, an kirasa ne ta video call.

"Hey, dude. I just saw your misscalls. Wassup?" Na cikin wayar yayi magana.

Dr Tareeq ya lumshe idanunsa ya bude a lokaci daya yana dan sosa eyebrow nashi. Ya amsa da fadin.

"Rocking"

Na cikin wayar yace, "woww, chill bruh"

Dr Tareeq ya bude idanu yace, "wani irin chill, kai kasan yadda nake karbar gashi kuwa? Kano weather is too bad at all. Kamar ana gasa ni tsabar zafi."

"Oh sorry, sai yaushe zaka dawo, har yanzu contract din bai kare ba?"

Dr Tareeq ya kara juyawa yace, "Yeahh, I think in the next 5months".

"Ohk enjoy your time, I have a meeting to attend in the next 10minutes bye"

Dr Tareeq ma ya daga mishi hannu kafin ya katse call din.

Ko bangaren da Halima take tsaye har kafafunta sun fara rawa bai duba ba, bare ya san da wanzuwarta a wajan.

Ya mike ya shige toilet dake manne da office din.

Halima ta wani turo baki gaba tana kunkuni tace Arne kawai.

Ta juya a hankali ta fita daga office din.

Dr Tareeq ya fito after some minutes, bai ga yarinyar ba. Dage kafada yayi ya ci gaba da aiyukansa.

Halima ta sauko daga saman offices din, a inda ta bar Mufidah nan ta sameta cikin kuncin rai tace.

"Ke Mufidah yau anyi mini karshen wulakanci a duniya. Wai ni Dubulle mutumin nan zai bari tsaye cikin ofishinsa yaki amsa sallamata da gaisuwata?

"Karshe fa shigewa yayi cikin bayi ya barni bushe a wajan"

Cewar Halima tana nuna kanta. Fuskarta ya gaza boye bakin cikin dake cikin zuciyarta"

Mufidah ta sheke da dariya har tana rike cikinta, ta dago ta kalli Halima tace.

"Ko dai baki fada masa wace ke ba, baki sanar dashi Halima Baraya ce a gabansa ba".

Ta kuma fashewa da dariya.

Halima ta daure fuska tamau, tace. "Mufidah bana son kuturun walakanci. Ya ina sanar dake busashshen cin mutuncin da aka yi mini, kuma ki buge da dariya."

Sanin halinta yasa Mufidah tsagaitawa daga dariyar tace.

"Amma kema Dubulle inace nan na sanar dake halin malamin nan, sannan ko cikakken minti ashirin ba'a yi ba da class rep ya kara miki tuni a kan halinsa. Kinga jurewa zaki yi tunda ke kike nema a wajansa"

Halima taja tsaki tace, "Idan na koma gobe ya kara walakanta ni bazan jure ba. Ke kin sanni."

Mufidah ta kalleta da kyau kafin tace. "Idan kika yi masa rashin kunyar taki da kika saba, kinsan makomar sakamakon lokacin karatun ki da kika bata a jami'a"

"Me kike nufi ke nan" ta watsowa Mufidah tambayar.

"Ah'ah ina nufin babu project, babu certificate mana Halima Baraya. Ni kinga zo mu wuce dare yanayi ga driver yazo".

"Wallahi Mufida da in shiga motar ku gwara na daskare a wajan nan. Na gwammaci in taka sayyada ta daga nan har gida tunda ba mutuwa zan ba".

Mufida tace. "Ke dai kika san abunda kika taka. Ai ina ganinki dazu ma Ya Abdul ne ya ajiyeki"

"To ko shima gorin zaki yi mini" cewar Halima a fusace.

"Ah'ah wace ni. Na isa ince gyambon dan sarki yana doyi. Kawai dai in tuna miki ne Yaya Abdul dan Abba ne. Probably Abba ne ya saya masa motar kamar yadda ya sayi wannan."

A guje Mufidah ta bar wajan ganin Halima tayo kanta.

Wasa-wasa, sai da Halima ta kwashe awa daya a harabar makarantar tana jiran Ya Abdul amma shiru bai zo ba.

A karo na barkatai, ta dago wayarta dake nuna karfe shida na yamma ta kuma kiransa, not reachable.

Kusan babu kowa a harabar wajan kawai ta mike ta fara tafiya tana jin zuciyarta ba dadi. A bayyane tace.

"Ka san ba zuwa zakayi ba, ka sani nayi ta zaman jiranka kamar marar abun yi. Idan ba don ina son jin abinda zaka fada mini ba zan tsaya ne."

Tana tafiya batafi taku uku ba taji an yiwa mota key a parking space. Da sauri ta juya dan ta dade zaune a wajan bata ga wani ya zo wurin ba.

Hakan na nufin koma wayene ya dade zaune a cikin motar.

Halima ba ta san tsoro ba, amma jin yadda motar ke binta a hankali a baya, sai taji wani abu ya darsu a ranta. Ga duhun magariba ya shiga. Gashi wajan kafa ya dauke.

Kamar yadda take tafiya a hankali haka motar ke bin bayanta slowly. Ta dan tsaya kadan dan ganin motar ko zata wuce. Motar ma sai ta tsaya.

Ta fara tafiya da sauri. Sai motar ma ta kara sauri.

Duba arewapen kuyi following ummufadeela01 domin karanta har zuwa page 11.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.