Free chapter · Read without an account
Chapter 21
by MARYAM STAR · ƊAURIN ZUCI
***
𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍
Chapter 21
Da kallon tausayi Samunaka ya bi bayan Junaid wasu irin zafaffan hawayen na zuraro ma shi, a zuciyar shi yake faɗin.
'Yah Allah kaika ɗora mana jarabawar da take wahalar da rayukanmu da rayukanmu Allah ka saka mana akan cutarwar da ake mana Allah ka isar mana ni da zuriyata da kulluhin musulmai Allah ka sakawa bayinka da ake cutar da su ba tare da haƙƙi ba ka kawo sauƙi a al'amurran ƙasata Nigeria ALLAH ka bamu shuwagabanni masu tausayi da jin ƙai ALLAH ka hankaɗa asirai macuta masu yaudarar mu ka toni asirin munafukai masu hannu a cikin wannan cutarwar da ake mana.'
Ya yi addu'ar a zuciyarsa idon shi na shararar zafafan hawaye.
Maida dubansa ya yi sama a zahiri kallo p.o.p ya ke amma a baɗini tunanin ranar da rayuwar shi ta sauya ya ke.
FLASH BACK
Zaune ya ke a fararen kujerun da aka kafe a ƙayataccen garden ɗin, a gaban shi takardun jarida ne barbaje yana dubawa, cikakkiyar fuskarsa me cike da kamala sanye da farin medical glass.
A babban get ɗin shiga SAMUNAKA mansion suka tsayarda motocin su don bincike, bayan an gama tabbatar da basa tare da du wani abu me cutarwa aka basu damar shiga ciki ta hanyar wage musu duka get ɗin suka kutsa da motocinsu cikin harabar gidan.
K.B shi ne mai kula da shige da ficen baƙi na musamman da ke ziyartar Alhaji Abubakar saminaka, yanzun ma tsaye ya ke cikin shigar shi ta baƙaƙen suit amma bai saka ta saman ba sai ya ratayata a kafaɗa, ya ɗaure ƙugunshi tamau da belt ga fuskar shi sanye da gilashi.
Da gara'a ya ƙarasa wajen motocinsu tare da yin welcoming nasu cike da ƙwarewa a aikin shi, bayan sun gama gaisawa ya yi musu jagora zuwa cikin garden ɗin.
"Sannunku da zuwa." Alhaji Saminaka ya tare su da fara'a yana tashi tsaye cike da girmamawa.
Fuskokinsu cike da fara'a suka miƙa ma shi hannuwa sukai musabiha cike da mutum, kafin suka zazzauna.
Janyo ɗaya daga cikin news paper ɗin da ke aje kan study table ɗin yana dubawa.
"Kai lamarin ƙasar nan sai du'a'i kawai lamurra kullum daɗa hautsinewa suna cakuɗewa suke gaba ɗaya ƙasar nan ta lalace wallahi." Makafa ya faɗi fuskar shi na nuna zallar damuwa.
Girgiza kai kawai Saminaka ya yi cike da jimami ya ce.
"Ai lamarin ƙasar nan sai du'a'i kawai matsala an rasa gane kanta bare ƙasanta, gaku nan dai kullum cikin fafutika kuke amma kuma jiya i yau ni nama rasa gane kan wannan lamari."
Nan Ƙwaro ya saka baki shima suka taru suna tattaunawa akan abin lamarin, kasancewar shi babba a cikinsu kuma ya daɗe ana damawa da shi a harka siyayya.
Ƙara gyara nutsuwarsa ya yi cike da kamala ya ce. "A taƙaice dai muje kan abin da ya kawo mu.
Wato Alhaji Abubakar Allah da ikon sa ya zaɓeka a kan ka wakilci jama'ar ƙasar nan da suke buƙatar tallafinka, mun jima muna tantance waɗanda suka dace da su jagoranci al'umma sai kawai sunanka ya faɗo, a taƙaice ba tare da kwana-kwana ba muna so ka tifo takarar kujerar shugaban ƙasa a wannan zaɓen domin kai ne mafi cancanta da zaka yi abin da ya dace."
Baki buɗe Saminaka ke kallon Farin dattijon da ke gaban shi, du yanda ya so buɗar baki yayi wata magana dake nuni da rashin amincewa cikin ikon Allah abu ya gagara domin lokaci ɗaya yaji kamar an ɗaure harshen shi ya gagara faɗin asalin abin da ke zuciyar shi.
Haka Ƙwaro da Makafa suka zauna suka cigaba da yiwa Saminaka bayani tare da kawo ma shi hujjojin da suka gamsar da shi, saide kuma a can ƙasan zuciyar shi yana jin kamar bai amince ba, amma a baki sai ya furta ya amince ya karɓi tayin su da hannu bibiyu.
Daga wannan ranar Saminaka ya zama ɗaya daga cikin ƴan takarar da aka tsayar kuma aka tantance aka yarje musu da su yi compaing, kusan komi na hidima da wahalhalun siyasa ba shi yayi ba yana zaune a gida ake aiwatar da komi, su Makafa sukai uwa sukai makarɓiya wajen ganin sun tabbatar da shi akan mulki.
Babban abin da ya bawa Saminaka mamaki bai wuce yanda yaketa samun karɓuwa ba domin kuwa tun gabanin isowar lokacin zaɓe aka soma yanke hukunci shine zai ci zaɓe a wannan shekarar.
Gaba ɗaya ƙasa ta shaida kuma ta aminta da shi a matsayin wanda zai mulki mutanen ƙasarsa.
Koda lokacin zaɓe ya gabato bai wani sha wahala ba domin anrigada an zaɓe shi, sai de har zuwa lokacin bai ji yana da ra'ayin mulki ba acan ƙasan zuciyar shi sai de kuma kamar an ɗaure shi a dole sai ya yi mulki don haka sai kawai ya duƙufa neman zaɓin Allah tare da addu'ar fatan alkairi akan ya zama adalin shugaba ga jama'ar ƙasar shi.
Daga ƙarshe dai ya ci zame an zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa, wanda hakan ya sauya wasu al'amurra nashi da dama wani abu kamar dutse me tsananin nauyi ya haye kan shi, ya daina tunani akan rayuwar shi da iyalin shi ya daina tunani akan ɗumbin dukiyar shi, lissafin shi gaba ɗaya ya sauka daga kan shi da iyalan shi ya koma akan ta yanda zai mulki al'umar ƙasar shi cikin aminci....
Daga ranar da aka rantsar da shi bai sake sakin jiki ya yi barci me nauyi ba gaba daya nutsuwa da kwanciyar hankali suka ƙaurace ma shi, a maimakon ya ƙara haske da ƙiba sai ya soma ramewa duda dai shi ɗin ba fari bane can sosai kawai dai hutu da naira ne da ya taso a cikinsu suka saka shi yin haske, yanzu ko da ya hau karagar murki sai ya soma duhu wannan hasken na shi ya soma disashewa saboda damuwa da tunani....
Kamar yanda ya hana kan shi sukuni wajen laluben yanda zai tafiyar da mulkin shi, mulkin da zai iya rantsuwa akan yazo ma shi kamar almara ne domin kuwa yafi yi ma shi kama da mafarki, tofa kwalliya ta biya kuɗin sabulu domin kuwa jama'ar gari sai sam barka ko'ina sai yabon tsari da hangen nesan da yake da shi ta fanin mulki ake, hankulan jama'a suka kwanta musamman da suka tabbatar da yanzu suna cikin aminci kowa zaka gani fuskar shi da annuri da walwala, musaman ta fanni tsaro da lafiya da aka ƙarfafa sannan aka maida tallafin man fetir fa aka cire nan da nan rayuwa ta yi sauƙi komi ya wuce aka manta da wahalar da aka sha kafin hawan shi mulki.
Gaba ɗaya ragamar kasuwancin Saminaka ya tattara ya bawa na hannun damarsa tare da kuma babban ɗan shi Junaid wanda ba a Nigeria yake da zama ba yana can Dubai sai de yana ƙoƙari matuƙa wajen ganin ya tafiyar da komi daidai ba tare da ya taso ƙafar shi cikin ƙasar ba.
A gefe kuma ga Muhammad Saminaka wanda ya kasance ƙani ɗaya tilo da Saminaka ke da shi kuma shi ya raine shi a cikin gidan shi tare da ƴaƴan shi kasancewar mahaifiyarsu ta rasu wajen haihuwar shi, kuma dama su huɗu ta haifa a duniya bayan Abubakar Saminaka sai ƙannensa guda biyu twins wanda namijin ya rasu yaaae macen daga nan bata sake haihuwa ba sai bayan shekaru ashirin da biyar ta samu ciki ta haifi Muhammad wand a wajen haihuwar shi tasa matuƙar wahala kasancewar girma ya zo mata a lokacin daga ƙarshe dai ta rasu ta barshi yana jinjiri...✍🏻
KUCI GABA DA BIYO NI DAN JIN YANDA ZATA KAYA
Na gode muku da jumurin karatu nicw taku har ƙullum.
#Maryamstar
#daurinzuci
#hausanovel