Free chapter · Read without an account

Chapter 22

by MARYAM STAR · ƊAURIN ZUCI

***

𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
         𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍

JAJIRTATTU WRITES ASSOCIATION💪

Chapter 22
Saminaka bai yi shawara da kowa ba ya ɗauki ƙanin shi Muhammad ya kaiwa matar shi akan ta raine shi, wannan ya dasa wata ƙauna haɗi da girmamawa me tsanani tsakanin Muhammad da yayan shi Saminaka.

   Koda ya girma ya kammala karatu nan take Saminaka ya shefa shi a gurbin da ya bar ma shi na kasuwanci, shiyasa koda ya hau mulki harkokin kasuwan cinsa basu tsaya ba, saboda zaƙaƙurin ɗan shi da kuma tsayayyen ƙanen shi sam basa bawa koda ƙanƙanuwar matsala damar kusantar su.

Komi ya soma ne daga lokacin da saminaka ya cika shekara biyu da hawa karagar mulki, lokacinda Makafa da ƙwaro suka fito suna nuna ma shi asalin kalarsu tare da buƙatar su kai tsaye, ba kaɗan ba ya jijjiga da jin manufar su, akuma lokacinne ya soma gane kan wasu abubuwan da suka faru a baya tun kafin hawan shi mulki, dama haka ake yi musu? wananne dalilin dama? kenan su ne suke assasa komi da saka hannu da goyon bayansu.?
    Ya jefawa kan shi tambayar yana kallon dattijuwar fuskar Ƙwaro, da babu kunya bare tsoron Allah ya zage yana rantaɓo jawabin karairayi da zalunci.
    Girgiza kan shi ya soma yi cike da takaici sannan ya ce.
   "Ku kuka zo har inda nike kuka nuna min dacewar in fito a harkar siyasa, duda a ƙasan zuciyata bana da ra'ayin hakan amma kuma na amince saboda hujjojin da kuka kafa min da kuma roƙon da kukai min wanda ya saka na gaga musa muku, mi yasa yanzu kuma zaku zo kai tsaye ku tunkare da wannan batun, dama kenan abin da ke faruwa da saka hannayenku, kenan kune kuke assasa komi shirinku ne, son zukatanku ne tsarin ku ne kuke aiwatarwa ko???.
    Ya jefa musu tambayar yana jin wani ɗaci na dabaibaye zuciyar shi.
    Wani makirin murmushi Ƙwaro ya yi sannan ya ce.
   "Kamar yanda kake tunani, kamar yanda ka zata  harma da abin da tunaninka bai taɓa baka ba tunaninka bai taɓa zuwa akaiba duka mune, shirun mu ne tsarin mu ne muke aiwatarwa mukuma sa a aiwatar kota ƙarfin tsiya ko cikin salama saboda tsira da rayuwa."
     A wannan zaman sai da makafa da ƙwaro suka idasa warware notikan kan Saminak.
    Yayinda al'umar gari kuma suke cike da alfaharin wannan zamab domin kuwa an tsara shi ne da sunan tattaunawa akan yanda za'a magance matsalar ta'adanci da rashin tsaro, suna murna akan wannan tattaunawa...
    Yayin da a ciki kuma tashin hankali da kiɗima tsoro haɗi da firgice suka cike duniyar Saminaka.
    
Daga wannan rana ya soma fuskanyar barazana tare da ƙalubale, kuma daga sanda ya gane gaskiga bai yarda ya sake koda minti ɗaya ba tare da du wani abu daya danganci su Makafa, du wata dukiya da yasan tasu ce ko kuma hawan shi mulki ya sameta ya tattara ya aje domin kuwa yana ji kamar yana tare da wuta ne tana ƙone jikin shi, bai tsorata sanda ya tsanantawa kan shi bincike akan su Makafa domin kuwa da kansu suka sanar da shi suɗin ko su waye.
        Daga kuma ranar ne ya soma fuskantar barazana daga rayuwar shi, komi ya cakuɗe ma shi ya rasa ta ina zai fara, abu ɗaya ke ba shi salama idan ya tuna da baya tare da su bayan mulkin da ke kan shi babu wani nauyi ko wani abu da zai alaƙanta shi da su, ya soma ƙirƙirar wasu hanyoyi da dabarun da yake ganin zasu sake nesanta alaƙar mulkin shi da su amma kuma abu yaci tura, a kuma lokacin ne kan shi ya soma ƙullewa  tamau du wanda zai tunkara sai ya gane da hannunsa a ciki, cikin ƙanƙanin lokaci ya soma gane shi ɗin kamar kiyashi ne a tsakiyar giwaye, tako ina bai da sukuni bare walwala, ga shi yanzu su Makafa sun taso shi gaba.

****
Tunanin shi ya katse ne sanda ya ji an turo ƙofar ɗakin an shigi da sallama.
     Lumshe jiƙaƙun idanuwansa ya yi lokacin daya shaƙi ƙamshin turaren Uncle tare sa wani ƙamshin na daban wanda ya ke kyautata zaton na ɗaya daga cikin ƙwararun Doctors ɗin da Junaid ke gayyatowa gidan dan duba lafiyar sa ne.
     Buɗe idanuwan shi da suka ƙanƙance ya yi yana  kallon Doctor ɗin daya zage yana da aikin duba shi, zuba musu idanuwa kawai ya yi domin shi yasan ko ciwon shi bana asibiti bane kawaide ana ciwo daban magani daban.
     Haka Doctor ɗin ya bawa Uncle umarnin juya shi yana ta aikin tattaɓa jijiyoyin jikin shi domin tantance lafiyarsu.
    Kamar dai dauran Doctors ɗin shima du jimawar da yayi yana gwaje-gwaje da taɓe-taɓe bai gano komi ba dangane da ciwo, hakan kuma ba ƙaramin ɗaure kan shi yayi ba, daya kalli Uncle akan su tattauna sai ya ja shi suka fice can waje suka tattauna ɗin, babu jimawa sai gasu sun dawo Dr. Shareef yayi ma shi allurar barci domin ya samu hutun tunanu da yawan damuwa ya kwashe kayan aikin shi yayi gaba.
     Lumashe ido kawai Saminaka yayi yana jin yanda azaba ke ziyartarsa adu lokacin da za'a bashi allura ko wani magani me saka barci, sam baya iya yin barci hasalima surutai yake ji a jikin kan shi, gashi ba koda wane lokaci yake son yin magana ba saboda wahalar da yake sha wajen yin manar ba kaɗan bace ji yake kamar ana zara ran shi an ciccira naman jikin shi....
     Yanzu ma shiru ya yi zafafan hawaye na sintiri a gefe da gefen fuskar shi yana jin da ace yana da dama daya dafe kan shi da tsananin ƙarfi wataƙila ya samu sassauci daga azabar da yake ji.


******
Maryam ce zaune tana aikin dama kunun da zata bawa kaka, lokacin rana ta ganjare sosai domin kuwa gab ake da fara kiran sallar azahar, tun da shabiyu ta gabato ta ke jin wannan hatsabibin barcin da ke zuwae mata bagatattan wasu lokatan na ƙoƙarin fizgarta, da ƙyar ta idasa dama kunun ta ɗauki kofin ta nuɗi ɗan ƙaramin ɗakin da yake ciki, a gaggauce ta aje kofin tare da duƙawa ta kwanta tana karanto addu'ar barci dukuwa da yanda barci ya nemi yafi ƙarfinta hakan bai hanata cika alƙawarin data ɗaukarwa kakanta ba na kasance me riƙo da ibada ko awanne hali.
     Sai da taɗanyi nisa a barcin nata sannan Aljani Kaizul ya bayyana bayan ya ɓatar da siffar Kaka ya saki tattausan murmushi yana jin tsananin alfahi da tarbiyar da yayi mata, da jelar shi yayi amfani wajen safa kanta yana ragw hasken shi gudun kar ya tashe ta, aiko sai ya tsinto sautinta cikin barci tana faɗin.  "Laaailaha illah anta subahanaka innikuntu minazzalumin."
    Wani murmushin ya sake yi tare da lulluɓe ta da yanar kariyar ta yanda babu abin da ya isa ya kusance bare har ya cutar da ita face ikkon Rabil izzati sannan ya ɓace ta cikin hasken shi.

      Tun daya tunkari wajen yake jin akwai babban lamarin da ya auku sai ya ƙara hanzari akan wanda yake yi hakan ya bashi damar bayyana cikin abin da bai fi sakanni huɗu ba.
    Karewa sababbin halittun da Mafaka ya ƙara zubawa don tsaron yayi, nan take ya hura iskar ɓadda sau ta yanda Aljani indai hatsabibi ne bai isa ya gane komi zai faru a wajen ba balle kuma su iya yin wani abu.
    Haka ya dinga fatali gami da lalata du wani abu da zai nuna shi a madubin tsafi ko wani abu na daban.
     Da hannunsa yayi amfani bayan ya koma siffa irinta  mutane ya kunce ɗaurin da aka yiwa Muhammad tare da  fesa ma shi wasu ruwa domin ya dawo hayyacinsa, sai de kasancewar tsafin da makafa  ya yi ma shi me ƙarfi ne yasaka ya kasa koda motsa saima yunƙurin aman daya soma yi a galabaice.
     Kaizul ne ya taimaka ma shi har ya samu ya amayar da tsafin daya shiga cikin shi dan kuwa har ya soma bin jinin shi nan take ya haifar ma shi da fita daga hayyaci, ba tare da ɗaukar  lokaci ba Kaizul ya cire duka tsafin da aka yiwa Muhammad ɗin, ya taimaka ma shi ya jinginar da shi tare da yin amfani da ƙarfinsa ya tafasa ruwa masu zafi cikin abin da bai wuce sakanni biyu ba ya haɗawa Muhammad ɗin cooffie ya kawo ma shi, duda zafin da gare shi hakan bai hana Muhammad yi mashi sha ɗaya ba, tun da ya kafe kofin bai yarda ya dire ba sai da ya shanye tas sannan ya dire gumi na tsatstsafo ma shi.
    A firkice ya rarrafa dan har lokacin yana jin ciwo a ƙafar shi ya nufi wajen Zunaina dake kwance kamar gawa, a ɗimauce ya kalli kyakkyawar fuskar mutane da Kaizul ke amfani da ita ya soma roƙansa . "Dan Allah ka taimaka ka tashi ta bata numfashi wallahi tsafi ya saka ya hankaɗe ta daga jikina."
 Muhammad yayi maganar yana jijjigata wasu ruwa masu zafi na ciccikowa a idanuwansa yana jin tsanar Makafa na sake lunkuwa a cikin zuciyar shi.
    "A'a Muhammad ni bana take dokar Ubangiji ba zan iya taimaka mata ba saboda iyakokin addini da bana son tsallakewa amma kai zaka iya taimaka mata idan kana so."
     Da hanzari Muhammad ya katsi numfashinsa ta hanyar faɗin. "Dan Allah ta ina zai taimaka mata please."
   Ƙanƙance kyawawan dara-daran idanuwasa Kaizul ya yi yana hango yanayin bugun da ɗaurarriyar zuciyar muhammad ke yi yasan ba kaɗan ba yana jin ciwo saboda ko yaya ya motsa ta da ƙarfi ko fargaba sai yaji ciwo saboda ɗaurin da aka yi mata bana wasa bane amma sam Muhammad ɗin baya damuwa.
    "Malam ka faɗa hanyar da zanbi in ceto rayuwar matata ka tsaya kana kallona me gani har hanji kawai😡." Muhammad ya faɗa a mugun hasale saboda ganin yanda Kaizul ɗin keta ja masa rai shi kuma ba jakaɗan ba ya ruɗe da yanayin da Zunaina ke ciki.
    "Taya ka gane ina gani har hanji, kenan akwai abin da kake ƙoƙari ɓoyewa kuma kake tsoron bayyanarsa a zuciyarka ka, humm karka damu ka bayyana kawai kanka tsaye babu wata damuwa ai hakan zai taimaka sosai."
   Ya faɗi haske na fita daga bakinsa.
    Iyakar ƙuluwa Muhammad ya ƙulu ji yake kamar ya kama Kaizul da duka ganin yana raina masa hankali.
    "Malam idan zaka taimaka min ka taimaka min bana biƙatar wasu surutanka can kaji da gane-gane da saka idonka na banza da  kasan babu kyau a addini."
    Dariyar da ta fito da wani haske me tartsatsi Kaizul yayi cike jinjina hasala da taurin kan Muhammad wanda yasan gado yayi a wajen Makafa ya ce.
   "To tunda gane-ganen babu kyau bari inbari kawai dama bana son keta iyakata shiga hurumin mata da miji dama ai bai dace ba sam."
   Ya faɗa yana miƙewa hasken shi na bayyana ya soma yin sama kamar zai tashi ko kuma ya ɓace, hakan ya saka Muhammad saurin cewa cikin ɗaga sautin "Kaizul pleassssssssssse ." yana jin idanuwansa na ƙoƙarin kawo ruwa.
    Dariyar data jijjiga ginin Kaizul yayi ba tare da ya sauko ba yayi wasu ƴan dabarbaru ya tataro tsafin da Makafa ya turawa Zunaina ya tara shi cikin hunhunta ta hanyar fitar numfashi, amma saboda yana son ƙure ƙaryar Muhammad sai yace.
    "Ka janyo numfashinta da bakinka kar ka daina har ta fitar da du wani tsafi data shaƙa sannan ka kwantar da ita a jikinka ka bata kariya in sha Allahu zata dawo normal.
     Ya faɗa hankalin shi na tafiya gida wajen Maryam dan yasan du irin nauyin barcin da zai saka mata lokacin tada sallah na yi zata farka dan bata wasa da sallah ko kaɗan musamman ma dake yin azahar ɗinta tun ƙarfe ɗaya da ƴan mintuna, katangar kariga yayi musu yanda ya tabbatar zasu samu kaɗaicewa da junansu su biyu ba tare da wani tsafi ko halittun da ke zagaye da su sun kula da abin da ke wakana a wajen ba, yana tafiya akan gajimare yana murmushi tare da hasko ƙurewae taurin kai da zurfin cikin Muhammad a yau. 
    Da komawar shi gida ko mintuna biyu bai rufa ba Maryam ta farka tana azkar, da hanzari ta miƙe tsaye ko gama buɗewa lumsasun idanuwanta basu yi ba ta nufi wajen randar ruwa ta cika babbar  butarsu wacce ta gama ragwaɓewa ta nufi zagayayyen wajen da suka geɓe domin zagawa ta ɗan watsa ruwa sabida ta ji ƙafin jikinta sannan ta fito tayi alwala a gaggauce, farar ƙar ɗin doguwar rigar abaya wacce daga gani taɗan kwana biyu ta ɗauka ya saka sannan ta ɗauki hijjabinta da prayer mate ta fice waje domin tada sallah, da wannan damar Kaizul ya yi amfani wajen bin iska ya ɓace zuwa masallacin madina domin acan yake gabatar da kamsu salawat .....✍🏻

Tofa wata sabuwa inji ƴan caca, wannan kuma Maryam ɗin daga ina, to kodai alhana ce itama???

Hhhhh dole inyi dariyar Muhammad wallahi wato har na fara shinshino wani abu dangane da Zunaina akan shi, todai maji ma gani ku ci gaba da biyo ni sannu a hankali dan jin yanda zata kaya a cikin wannan zazzafan labari me ɗaukar hankali nice taku har kullum meson ganin farincikin ku.

MARYAM STAR.... ✍🏻

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.