Free chapter · Read without an account

7&8

by Khadeejarth Sabi'u Yahyah · BA DARAJA

❤️BA DARAJA!!!❤‍🔥
     (True Reality Series)

©® Nainarh KD⁂𝓝𝓴𝓭'𝓼❦♡


Page 7_8

Sallamar Yaya Mari ita ta dakatar da Maman Habib daga ƙoƙarin shiga ɗakin da take yi bayan fitowarta daga kicin ta haɗa wuta da ɗaura ruwa.

Cikin mutunci suka gaisa kasancewar Maman Habib ɗin ta san Yaya Mari sun taɓa haɗu wa sau ɗaya.

“Allah mai iko ashe ta sauka? Ashe shi ya sa na kasa samun sukuni nace bari dai nazo naga Sa'ada da jiki ashe ma har an yi an gama, kai Alhamdulillah sannu da ƙoƙari fa Maman Habib an gode an gode Ubangiji ya saka da alkhairi.”

Cewar Yaya Mari bayan sun gaisa sannan Maman Habib take sanar da ita batun haihuwar.

“Ah bakomai Yaya Mari ai an zama ɗaya yanzu ni zan koma gida na bar yara su kaɗai amma in sha Allah zan sake shigowa.”

Maman Habib ta faɗa lokacin da Yaya Mari ta shiga ciki ta zauna godiya sosai Yaya Mari ta yi ma ta sannan Maman Habib ta sake yiwa Sa'ada sannu da jiki kana ta fice ta bar Yaya Mari na amsa gaisuwar Rabi'u da Abokinsa Malam Lurwanu yayin da take yi ma Sa'ada sannu. Yaya Mari ce ta zauna a gidan ta ci gaba da yin duk wasu abubuwan da ya kamata yayin da a kullum Maman Habib take shigowa sau biyu su gaisa, ta kama ma ta wasu abubuwan da ba'a rasa ba sannan taga mego da jaririyar har zuwa ranar suna da yarinyar ta ci suna Samira.

A iya sanin Sa'ada dai Samira sunan wata tsohuwar budurwar Rabi'u ce da yake bawa Sa'ada labarinta duk da bason ji take ba domin a ganinta tun da ba abin da ya haɗa ta da ita ai baya zo yana bata labari a kanta ba, bayan kuma sun daɗe da rabuwa.

Sai dai ta yi mamakin jin ya sakama ƴar ta sunanta sai dai bata ce da shi komai ba, ta share shi bayan tabi abin da addu'a duk da abin ba wai ya dena damun ranta bane domin Allah ya gani sunan mahaifiyarta da bata raye taso ya saka ma ta kuma abin da ya saka ta daɗa saka rai saboda shi ya yi ma ta alƙawari tun kafin ya aure ta.

HALIMA...

Durƙushe take saman tabarma cikin tsakiyar ɗakinta tana yanka wata zani da aka bata ɗinkin ta kasancewar tun lokacin da suka dawo gidan da kekenta da Yayanta ya siya ma ta ta dawo kuma ba laifi sosai Allah ya sanya albarka domin tana samu sosai da ita.

Gefe guda tana tunanin hali irin na mutane da ya kasance kowa da kalar nasa musamman sarkuwanta wato mahaifiyar mijinta Abbas.

Allah ya gani tana bawa matar girma daidai gwargwado amma bata gani kullum abin da zata ƙirƙiro yau da ban haka ma na gobe da ban duka kuma Haliman tana sane sai dai take kauda kai kurum dan a zauna lafiya.

Ga shima Abbas da ga wurinsa ya kamata ta sama sauƙi amma ina abin dai sai a hankali.

Lafiya qlau dai suke zaune domin baka taɓa jin faɗarsu to fa sai a ɓangaren karɓar kuɗin cefane nan ne a kullum sai an maimaita abu guda domin Abbas duk da yana sane da komai amma ba mai buɗe hannu bane indai a harka ne na bada kuɗin cefane yadda ya kamata wannan kam Halima tana hakuri dashi har gobe gashi yanzu da suka fara tara iyali kullum faɗa masa take amma ya kasa ganewa da yana fakewa da cewar karatun da yake yi ne kuɗaɗen nasa suke tafiya ta can ga kuma gini yanzu kuma ba gini tun da ya gama sun ma tare haka kuma karatun ma ya kammala kuma da yake takardunsa sun yi kyau tuni har ya sama aikin koyarwa a wata makarantar gwamnati na secondary, babban abin da yake rufa ma ta a asiri shi ne wannan sana'a nata na ɗinki badan da shi ba to tabbas batasan yadda zata yi ba shi ya sa a har kullum bata gajiya da godewa Yayanta Ɗan Juma da shi ne ya sai ma ta ke nan.

“Assalamu Alaikum...”

Ta jiyo sallama daga waje. Ta ɗaga murya tana mai amsa wa tare da faɗin a shigo ciki da yake Mama Tsahare ta fi ce dama haka take yi inta bar gidan tun safe to fa sai yamma tana can gidan babban ɗan ta tanayi ma matansa sa ido a acewarsu.

“Maraba lale marhabin wa nake gani kamar mai jego? Wai har an fito ah lallai abin ba wuya yanzu shikenan fa kun yi arba'in kun wuce wurin.”

Halima ta faɗa cikin fara'a lokacin da baƙuwar ta shigo ciki suka gaisa.

Sa'ada ta yi murmushi cikin muryarta da har lokacin Hausa bai gama isarta ba ta furta.

“Wallahi kuwa mun gama wanka ai inda rai da rabo dama abin ba wuya.”
Ta faɗa tana sauke jaririyar ta miƙa wa Halima.
Sake gaisawa suka yi Halima tanayi ma ta barka yayin da Sa'ada ta ci gaba da faɗin.
“Kiyi haƙuri fa ban ma samu nazo nayi miki godiyar ɗawainiya ba tin shekaran jiya da muka yi arba'in ban sama zama ba sai yau gobe ma zan wuce illorin nace bari dai na yaki ce shiririta na shigo na ƙara yi miki godiya.”

Murmushi Halima ta yi tana amsa ma Sa'ada da ba komai ai an zama ɗaya kuma dama amfanin zaman tare ke nan. Sa'ada ta ɗan nisa bayan ɗan shiru da ya ratsa, idanunta naga yankan atamfar da Halima ke yi ta furta.

“Ni kam kina burgeni a duk lokacin da na shigo na tadda kina yanka ko ɗinka kaya, sai naji ina mararin yi sai dai nasan da wuya na iya domin kamar abin zai yi wuya.”

Halima ta murmusa jin yadda Sa'ada ta yi maganar gwiwa a sake yayin da Sa'ada ta ƙara da faɗin.

“Bare ma yanzu da ga ɗawainiyar ƴa ga na miji, ai idan nace zan koya ɗinki ma ai na kira ruwa.”

“Sai dai kuwa idan baki mayar da hankali ba, domin ɗawainiyar yarinya ko ayyukan gida ba zai hanaki ba muddun kin tsara yadda zagi dinga gudanar da al'amurran ki komai zai ke zuwa miki cikin sauƙi.”

Sa'ada ta ɗan yi jim da jin kalaman Halima, riƙe da haɓa ta furta.
“Kuma haka ne ko wata ƙila zan iya gaskiya ina son na koya ɗinki ko dan na gujema zama ba sana'a domin ni kam duk sana'ar da za'a saka jari bata karɓe ni ba muddin zan fara ba'a tafiya ko'ina jarin ke rushewa Yaya Mari tayita faɗa har ta gaji ma ta dena bani jarin.”

“Ai kuwa indai kin mayar da hankali kin koya ɗinki Akwai alkhairi sosai zaki sama na rufin asiri indai Allah ya saka kina da rabo, kuma ki cire wasi-wasi ma a ranki kawai na ba zaki iya ba, kedai ki mayar da hankali muddin da rabonki a ɗinki tabbas zaki sama alkhairi in sha Allah domin ni kam ba abin da zance a ɗinki sai godiya ga Allah.”

Halima ta yi maganar tana tattare atamfar da ta yanka ta ɗaure wa  wuri guda tana mai ci gaba da faɗin.

“Ni kuma lokacin da na sama keken yara uku gareni kuma gashi yanzu da nake da yara biyar ba abin da aka fasa.”

Cikin jin dad'i da zak'uwa Sa'ada ta gyara zama tana mai faɗin.

“Ai kuwa Allah ya dawo dani lafiya daga illorin in da rabona zaki koya min kuwa.”

“Ameen tohm. Aw dama kin taɓa faɗa min a Katsina kike ko, ke nan ke haifaffiyar illorin ce?”

“E toh kusan haka sai dai fa mahaifiyata ce 'yar can illorin yayin da mahaifina ya kasance haifaffen Malumfashi, can illorin da zan je yanzu dangin mahaifiya ta ce.”

Jinjina kai Halima ta yi cikin fahimta yayin da firar ta fara yi ma ta dad'i dama ta gaji da zaman shirun da take a lokacin sai kuma Allah ya kawo Sa'adan tun ba lokacin ba ta fahimci Sa'ada bata da hayaniya bare gulma da tsugudidi irin na matan anguwan shi ya sa ta ɗan saki jiki da ita har suke shiga wurin juna da yake sun dawo anguwan da shekara kusan da rabi sannan ita ma Sa'ada suka tare da mijinta, a zahirin gaskiya Halima bata cika sakin jiki da mutanen anguwan ba ne saboda yadda ake yi ma ta wani duba musamman da sarkuwanta ce ta bada ƙofar hakan domin ita ke faɗin ta hana ma ɗanta riƙe mata duk wacce ya auro sai ta koreta su kuma mutane babu bincike kawai sun hau sun zauna, dama kuma haka al'ummar tamu ta wannan ƙarni ta koma, an dena kiwon dabba mutum ake kiwo sai kaga kamar k'iris mutane suke jira wani abu na faruwa da mutum kankace me sun hau sun zauna sannan kuma an sama abin yi. Shi ya sa ma ba da kowacce mata a anguwan Halima take sabgarta ba dan bata k'aunar abin da zai taɓa kima da mutuncinta.

Halima ta ɗan yi jim tana mai jingine bayan ta da jikin kujera tare da ɗan lumshe ido kaɗan tana sauke ajiyar zuciya a hankali, hannunta dafe da k'irjinta, cikin zuciyarta kuwa tana mai karanto addu'o'in neman tsari domin haka kawai sai taji gaban ta ya fad'i, ji take kamar wani abu na shirin faruwa musamman a yau da taji abin da take ji ya ƙaru, wannan yankan da kuma firan da take yi da Sa'ada daurewa kawai take amma kam ita kaɗai tasan abin da take ji.

“Kina lafiya kuwa?”

Sa'ada ta tambaya cikin kulawa ganin yadda lokaci guda yanayin Haliman ya sauya.

“Kodai na cikaki ne da surutu?”

Sa'ada ta sake faɗa tana dafe baki, hakan da ta yi sai ya sa Halima ta ɗan murmusa tare da faɗin.

“Ah wallahi ko ɗaya kawai dai yanayi na ne ya sauya...”

Bata rufe baki ba suka tsinkayi wata murya da duk da yanayin yadda mai muryar ke magana cikin wani irin sauti da kana ji zaka fahimci ba lafiya ba, amma hakan bai hana Halima fahimtar muryar sarkuwanta Mama Tsahare ba cikin 'yan sakanin da muryar ta kai ga ma'ajiyar jinta lokacin kuma ya yi daidai da fad'uwar gaba da ya sake ziyartarta.

“Halima, Halima! Ke Halima kina ina? Ƙari so maza ki duba min yaron nan gaba ɗaya ya tsorani, ki duba fa kiga abin da yake yi, machine ne fa kawai ta kaɗe shi garin saurin da yake yi ya cim mini...”

Mama Tsahare ta saka ma maganarta birki ganin yadda Halima da ta fito ta ƙari sa wurinta a zabure tare da fizgar Habib dake hannunta cikin wani irin yanayi goshinsa na zubar da jini.

Tun kiran farko da Mama Tsahare ta kwalawa Halima daga ita har Sa'ada suka miƙe a tare suka nufa ƙofa har Sa'ada ta kusan kada 'yarta Samira a lokacin kuwa da suka ji zuban zancen da Mama Tsahare wacce da alama a firgice take take yi sai Sa'ada ta yi sak tsaye ƙofar ɗakin Halima lokacin da idanunta suka kai ga Habib da ke hannun Mama Tsahare.

Halima ma da idanunta suka yi mugun ganin halin da ɗan ta ke ciki bata san lokacin da ta kaiga Mama Tsahare ba kawai taga Habib ɗan ne kwance saman cinyarta tana tattaɓa fuskarsa tare da kai bakin zanen jikinta tana goge jinin da ya ɓata goshinsa ya zubo har saman fuskarsa.

Hankali tashe ta ɗago idanunta da suka rine lokaci guda ta watsa su a kan Mama Tsahare dake tsaye tana zare ido cikin jiran tsammani.

Ja da baya Mama Tsahare ta yi tana kwalalo ido hannu dafe a k'irji ta furta.

“Naga Annabi idan nayi hali na gari. Halima karki faɗa min ɗan nan mutuwa ya yi, wayyo ni Tsahare.”

Wani mak'ok'on takaici ne ko bak'in ciki da cikinsu Halima ta kasa banbance wa, shi ne ya zo ya tokare ma ta a mak'oshi, ta sadda kanta tana duban yaron ta Habib, hannayenta mak'ale cikin nasa, yayin da yaron yake wani irin k'ak'afe wa yana son bud'e baki amma ya kasa, da gani sunan mahaifiyarsa yake son ya kira, cikin ikon Allah muryar nasa ta fito a shak'e daidai da lokacin da hawaye sirara suka gangaro daga idonsa na dama ya furta.
“Mama...”
Maganar da ta kasance ta k'arshe tsakaninsu haka kuma komai ya tsaya cak tare da bugun zuciyarta na wasu dak'ik'u kafin ta ci gaba da bugawa cikin sauri-sauri daidai lokacin kuma siririn hawaye ya fito daga idonta ya d'iga saman fuskar yaron da lokaci guda wani haske da haiba ya cika fuskar nashi idanunsa kafe akan mahaifiyarsa da ta koma tamkar statue.

Mama Tsahare ta fasa k'ara tana zubewa saman gwiwowinta gaban Halima kamar mai neman gafara saura k'iris yayayyen yaron Halima mai suna Aliyu ya suɓuto daga bayanta Sa'ada ta yi hanzarin ƙari sawa ta kwance yaron da ya farka ya fara kuka.

Jingina ta yi da garu idanunta akan yaronta da ya rasu a hannunta hannayensu sark'e da na juna, tun hawayenta da ya d'iga saman fuskarsa bata k'ara fitar da hawaye ba a wannan lokaci za'a iya cewa kusan zaucewa Halima ta yi sai dai ba uhum bare uhm uhm kukan ma sai na zuci idanunta kafe kan d'an ta can k'asar zuciyarta da take jin tamkar zata fashe kuwa babu abin da take furta wa sai kalmar;

“Inna lillahi wa-inna ilayhi raji'oon³, allahumma- jurnee fee museebatee wakhluf lee khayran minha, Hasbiyallhu wani'imal wakil...”

Su ne kawai abin da take fad'i tana nanata wa cikin wani irin kara ya.

Ta ja ajiyar zuciya lokacin da Sa'ada ta dafa ta cikin alhini tana furta kalaman ban hak'uri da k'arfafa gwiwa a gare ta.

“Kiyi hak'uri Halima Ubangijinmu da ya fimu k'aunar Habib ya amshi abin sa, sai mu bisa da addu'a, Allah ya yi masa rahama, ki daure kinji Allah ya baki hak'urin juriya.”

Ai jin kalaman da suke fitowa daga bakin Sa'ada sai kukan Mama Tsahare ya k'ara sauti ta shiga sambatu kamar wacce ta zare.

Sa'ada ta kai hannu tare da rufe idanun Habib tana mai karanta addu'ar da ma'aiki (S.A.W) ya umarce mu a lokacin rufe idon mamaci.

“Allahummagh-fir li-fulanin (Habib) - warfa' darajatahu fil-mahdiyyeen, wakhlufhu fee 'akibihi fil-ghabireen, waghfir lana walahu ya rabbal-'alameen wafsah lahu fee kabrih, wanawwir lahu feeh.”

Sannan ta duba Mama Tsahare ta cikin rashin jin dad'i ta furta.

“Haba Mama Tsahare kin manta Ubangiji ya tanadi azaba ga masu kuka da kururuwa ga mamaci addu'a ya kamata kiyi garesa ba hayagaga ba, ki duba Halima da take Mahaifiyarsa bata yi abin da kike yi ba.”

Mama Tsahare taja ajiyar zuciya tana fyace majina ta ke fad'in.

“Barni 'yar nan baki san me nake yima kuka ba shikenan nayi sila na kuma yi ajalin d'an Abbas sai da Halima ta nuna min batason fitar da zan yi da yaran nan musamman shi Habib har ce min ta yi yau d'in ya tashi baya jin dad'i sosai, amma saboda na nuna ma ta na isa da jikokina sai na tattara gaba d'aya yaran har da d'an yaye na yi tafiya ta gashi na zama sila Habib yaron kirki ba ruwansa ya rasa ransa kaico kaiconi Tsahare san zuciya bai yi ba.”

Ta k'are maganar tana girgiza kai cikin yanayi na jimami da nadama.


Sa'ada ta girgiza kai kurum.

“Dama can Allah ya nufa wannan ne hanyar tafiyarsa ki daure kawai ki bisa da addu'a.”

Ta fad'a tana mai da hankalinta ga sauran yaran da suka yi jugum har da masu kuka ganin halin da mahaifiyarsu ta shiga ga kakarsu tana kuka shi kam Ali sai jijjiga hannun Habib yake yana fad'in ya tashi cikin gwaraci domin a duk lokacin da yake rigimarsa Habib ne zai yi ta lallashi har sai ya yi shiru ko bacci.

Da kyar Sa'ada ta samu Mama Tsahare ta yi shiru da abin da take yi suka taimaka wa Halima ta shiga d'aki, zuwa lokacin kuma makwabta da hayagagar Mama Tsahare ta isa garesu sun fara cika gidan, ana haka kuma sai ga Abbas ya dawo gidan ya tarar da mummunan labari.


Months Later!


Duk da k'ok'arin danne wa da kuma mik'a lamurran ta ga Allah da Halima ta yi amma cikin 'yan watannin da suka biyo bayan rasuwar babban d'an ta Habib sai da Depression yaso kamata domin bayan rasuwar mahaifiyarta to fa rasuwar d'an ne abu na biyu da ya gigita ta musamman ganin yadda Abbas ya nuna kamar ma mutuwar bata dame shi ba domin ba'a yi kwanaki goma da rasuwar ba aka saka ranar aurensa nan da makwanni biyar masu k'aratowa duk da yaso b'oyema Halima sai dai tuni labari ya je ma ta wannan shi ya k'ara rura wutar halin da take ciki har cutar damuwa taso kamata domin badan k'arfin addu'a ba da kuma gudun mawar da Sa'ada ta bayar na kwantar ma ta da hankali da abubuwan da suka dace da tuni wani zancen a ke. 

Tun bayan rasuwar wata magana bata sake had'ata da Mama Tsahare ba, ba kuma dan ta k'ullace ta ba, sai dan matsayinta na uwa da kuma tunanin da ya kasa barin kanta ya sa take ganin kamar Mama Tsahare ce silar rasuwar d'an ta musamman da abin ya had'e ma ta da abubuwan da Mama Tsahare ta yi ma ta a baya, shi ya sa ta kasa yi ma ta uzuri duk da ta kula tun bayan rasuwar ba k'aramin sanyi jikin Mama Tsahare ya yi ba, duk wasu abubuwa na cuzgunawa da take yi ma ta ta dena, sai dai a ganin Halima duk tanayi ne out of guilty na abin da ya faru silarta kuma bayan wani lokaci zata d'aura daga inda ta tsaya shi ya sa sam ta kasa yi ma ta uzuri.

Tun bayan rasuwar ma bata k'ara taka keke da sunan ɗinki ba, domin har yanzu da bikin Abbas ya rage saura sati guda kuma still bai fito ya sanar da ita maganar auren nasa ba bata gama dawowa daidanta ba, Sa'ada ta tafi illorin a gurguje ta yi sati uku ta dawo duk saboda halin da Haliman ke ciki kuma tun da ta dawo batayi ma ta maganar koyon ɗinkin ba ta bari ne sai Haliman ta samu natsuwa sannan ta sanar da ita cewa har keken ɗinkin 'yan uwanta sun siya ma ta.


**

Taji shigowarsa d'akin sai dai bata d'aga ido ta dubesa ba bare ta kula shi ciki-ciki ta amsa sallamar da ya yi wannan d'in ma saboda ya zame ma ta dole ne.

Abbas ya zauna daga gefen gadon yana kallon ta cikin sanyin jikin da bai nuna ba ya d'an yi gyaran murya tare da umartarta da ta tashi zasu yi magana.

Ya kuma yin still kamar mai nazarin abin da zai sanar da ita Halima ta d'auke kanta daga duban k'aramar akwatin da ya shigo da ita ya aje tsakiyar d'akin ba tare da dubeshi ba ta furta.

“Idan ba abin da zaka fad'a dan Allah ina buk'atar na kwanta.”

Abbas ya d'ago yanayi ma ta duba kamar na mamaki ita kuma ta kauda da kanta sai kuma ya basar tare da tattaro natsuwarsa ya fara zuba zancen da ya saka Halima d'ago idanunta ta fara yi masa wani duba, bata katse shi ba har sai da ya kai aya.

“Abbas! Ka faɗa min matsayin da ka ɗaukeni a cikin gidanka, mata ko kuma wani tarkace? Wannan wulaƙancin duk miye sila, gaba ɗaya ka canza kamar ba kai ba, kullum sai fito da wasu muggan halaye kake da ban sanka da su ba, gaba ɗaya ka mayar dani wata mara daraja a idanunka idan laifi nayi maka ka sanar dani ba wai ka dinga azabtar dani ba...”

Halima ta ƙare maganar cikin ƙunar rai da na zuci tabbas ta gaji, idan ta ce ta gaji kuwa tana nufin eh ta gaji da halayen Abbas gaba ɗaya. 

Miƙe wa tsaye Abbas ya yi yana yi ma ta wani irin duba da bashi da fassara kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya furta.

“Yanzu Halima saboda nace miki zan ƙara Aure shi ne kike nema kiyi min sharri?’’

Ƙurr ta yi ma sa da ido kamar mai neman wani abu a jikinsa sai kuma ta yi wata dariya da bata da alaƙa da farin ciki tana girgiza kai.

 Tabbas yau ta yarda da kalmar nan ta namiji ƙanin aljali.

“Abbas ke nan. Lallai wato sharri ma nake ma ka ko? Da fari Yaro na ya rasu ka nuna halin ko'in kula, ban damu ba na kawar da kai, ama a je wannan a gefe ka faɗa min Abbas duk irin k'ara auren da kakeyi shin tsakanin ka da Allah ka tab'a siyamin daidai da yadi ka bani a matsayin kayan fad'ar kishiya? shi ne sai yanzu zakazo da wannan kayan tsiyan kana wani fad'a min nawa ne kuma aure zaka k'ara! Ka manta saboda kai duniya take zagina akan wacce bata barin kishiyoyi bayan kuma ba halina bane amma babu mai fahimta ta, ka saka duniya tana mini kallon wacce bana barin duk matan da ka aura, kuma mai bin bokaye....”

“To ai ba ƙarya ake miki ba!”

Suka tsinkayi murya daga ƙofa ana mai furta wannan kalma cikin wata kakkausar murya da ta sanya su saurin juyawa duk da Halima ta ɗauki muryar kuma ba tayi mamakin jin fitowar wannan kalma daga bakin ta ba.

Mama Tsahare (Mahaifiyar Abbas) dake tsaye ta ƙari so ciki tana bin Halima da wani mugun kallo da bashi da fassara.

Halima ta yi murmushi na takaici tana yi ma sarkuwan nata wani duba.

“Mama ke nan daga ke har Abbas da sauran mutane ba zan nema yardar ku ba, domin na dogara da Allah kuma yardar sa nake nema domin shi ya san menene a zuciyata, kuje kuyi duk tunanin da zaku iya akaina ban damu ba. Hmmm koda yake dama can ba k'auna ta kike ba shi ya sa kika yi abin da kika yi kika cusa min bak'in cikin rasa d'ana yanzu kuma d'an ki zai k'ara aure kin goya masa baya, kema uwa ce kuma kamar yadda kika rabani d'ana hmmm ba zan ce Allah ya miki abin da kika min ba saboda...”

Bata rufe baki ba wani haske ya yi tau a idanunta sakamakon marin da Abbas ya yi ma ta, zuciyar Halima tazo wuya tana jin takai k'ololuwa na b'acin rai, ta dubesa ganin an daketa ana nema a hanata kuka a ganinta ai ba laifi ta yi ba dan ta amayarma Mama Tsahare abin da ke cikinta duk da bak'in cikin da takaici ne ya zama sila.

“Koda wasa ba zan lamunci ki furta kalaman raini ga mahaifiyata ba kuma ina tsaye ina duban ki, Halima wai kin zare ne mutuwar d'a sai kace akanki aka fara duk kin canza hali kina neman d'aurama mahaifiyata alhakin a kanta sai kace ba musulma ba, shin baki yarda da k'addara ba ne?”

Abbas ke kalaman cikin huci. Halima ita ma da ta gama kaiwa iya wuya bata san lokacin da ta bud'e baki ba cikin b'acin rai ta furta kalaman da suka bada gagarumar gudummawar da ta yi silar kwancer k'ulli mai daraja kuma hakan ya zama mafarin duk wasu k'ok'ofi na k'addarar aurensu.

“Ai ba k'arya nayi ma ita uwar taka ba, domin bata cancanci zama uwa ba, tabbas mata dai irin wannan mai fad'in k'arya akan matan 'ya'yanta dan ta burge mutane ai bata cancanci ta zama uwa ba, kuma na fad'a ita ce ta zama sila na mutuwar d'ana Habib ba dan haka ba wata k'ila Habib d'ina yana nan a raye.”

B'acin rai da ya sa ta yi kalaman tare da zugar gangar shed'an basu bari taga munin abin da ta yi ba, haka shima Abbas b'acin ransa da ya k'aru ya saka shi yanke hukuncin da sai da ya furta kalaman sannan danasani ya biyo baya.

“Ban auri macen da zata yi wannan kalamai ga mahaifiyata ba kuma na ci gaba da zama da ita saboda haka Halima ki tattara tsiyarki kije na sake ki!”

Furta kalmar sakin ya yi daidai da bugawar zuciyar kowannensu yayin da Mama Tsahare ta dafe baki cikin wani irin yanayi da bashi da alak'a da farin ciki, a hankali kuma sanyi ya ziyarci ilahirin jikinta a karo na farko taji ta yi danasanin duka halayenta domin a saboda hakan gashi ta zama sila na rabuwar aure ga 'ya'ya tsakani, kuma halinta ya zubar da darajarta a idon Halima, ta sani ba ta a kan daidai kuma Abbas ya san hakan amma ya zab'i da ya goyi bayanta ya rabu da uwan 'ya'yansa duk da cikin b'acin rai ne kuma ita ma Haliman b'acin rai ne ya sa ta furta kalaman da ta yi har suka zama silar igiyar aurenta d'aya...


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.