Free chapter · Read without an account

24. ...a massive jerk!...🖊️

by Noor · RU'UYAA (The dreams we never lived)


Faɗin mamakin dana shiga ɓata lokaci ne... never in my wildest dream nayi tsammanin ganin shi,hawaye na suka tsaya kamar anyi ruwa an ɗauke...share min hawaye na yake da damuwa a fuskar shi '' did I scare you?...''

Ture Hannunshi nayi daga fuskata wannan tambayar ta ƙara fusatani abu a zahiri yake tambaya?

Na tashi tsaye shima ya miƙe yana kallona da alamun tambaya a kyakkyawar fuskar sai naga kamar ya ƙara kyau fiye da lokaci na ƙarshe da muka haɗu...'' me kike yi anan?"

Hararar shi nayi da jajayen idona takaici na kamani...bai ga uniforms ɗin dake jikina bane? '' wasa nake ai ka gani!" nake ji kamar in kwaɗe shi yayi murmushi yana bina da kallon nan nashi da har yau ban san ma'anar shiba...zagaye shi nayi zan wuce ya riƙo hannu na ya rungume ni yana dariya...gwalalo ido nayi ƙirjina na gaba da baya... yace

 '' toh muyi wasan tare!" mamaki ya hanani motsi ko ƙoƙarin ƙwatar kaina..muna tsaye aka turo ƙofa da sauri muka rabu..ko ya rabu dani cikin rashin gaskiya...naji kunya ta lulluɓe ni kumatuna suka ɗau zafi...

Da sauri nabi ta gefen koma waye zan fita..dai dai nan idona ya haɗu dana Farzan daya zuba hannayenshi cikin aljihu...kallon da yayi min yasa na ƙara jin ba daɗi...

Da sauri sauri nake tafiyar banko kallon inda nake sa ƙafafuna ƙwaƙwalwa ta taƙi yin shiru jikina yaƙi yayi sanyi...ji nayi na haɗu da wani abu kamar bango nayi baya baya na faɗi,ƙamshin turaren nan da nake iya tantance mai shi ya daki ƙofar hancina tare da ƙarama zuciya ta gudu...da sauri na ɗago inga ko da gaske shine idonmu ya haɗu na brief second...


Saye yake da baƙar riga,baƙin jeans ya ɗaura trench coat data tsaya daidai guiwar shi hannun shi soke cikin aljihu...gashin kanshi slickly combed, fuskarshi saye da face mask kamar koda yaushe,sai ya cigaba da tafiyar shi kamar ni ban cancanci ya tsaya yaga idan ina lafiya ba


'' wai kai baka iya zama gentle man bane? ka ture ni ko ka taya ni tashi!" nayi maganar ina jifar shi da takalmi na kamar yanda na jefe shi a maina hotels, batareda ya juyo ba ya riƙe takalmin ta baya kamar dama yasan yana zuwa

share shi nayi duk da yanda zuciya ta ke bugu na shiga kakkaɓe kayana, ganin bai tafi ba yasa na miƙe ina kallon shi

Karkatar da kanshi gefe yayi '' I'm sorry..." Deep baritone voice ɗinsa ta sauka a kunne na,mamaki ne ya kusa gamawa dani a tsaye amma sai nayi saurin saita yanayi cike da basarwa na fara faɗin '' ah ai ya wuce kasan ni Abeedahtu ina da karam..''


'' that you didn't fall hard enough to shut that hole on your face!" 

Ya iyar tare da sakin takalmin yana bina da wani irin kallon dayasa naji kamar an watsa min ruwan ƙanƙara, har ina jin zufa tana sauka a bayan wuyana,wai bakina yake kira rame,naso in mayar mashi da magana amma idonshi sun ɗaure min baki har da ƙafa ma,sai kuma yayi ƙasa da idonshi.. nima nayi ƙasa ina kallon abinda yake kallon ashe fitsari na saki

Da sauri nayi zaune ciki kunya na barazanar gamawa da rayuwata..meyasa zanyi fitsari a gaban shi batareda nama sani ba?

girgiza kanshi yayi kafin ya bar hall ɗin,naji haushinsa ya cika zuciya ta '' what a massive jerk!"

Lokaci guda kuma ƙwaƙwalwata ta fara aiki,nan ne gidan su?kuma ni yar aikin suce? ina Allah Allah kada in haɗu da wani na miƙe na fara tafiya duk ƙyanƙyami ya kamani,kamar wata mai yoyon fitsari? abun ya fito salin alin batareda na sani ba

Sashen muna koma na wuce baye na wanke jiki har lokacin na kasa dena jin nauyin abinda ya faru

ina tsaka da canja kaya Hansa'u ta shigo tana min kallo a ɗaɗɗage '' ke!''

Ban tanka ba taja tsuki '' Fauziyya tace bata so ta ganki a dining!" tana botsare botsare ta juya ta fita daga ɗakin.. lumshe idona nayi da ace akwai yanda zan tserewa zuwa wurin ai da tuni na dena...

Alwala nayi bayan Mama Asabe ta fito nayi sallah ina zaune har sallar Isha'i...koda na second ne,naso inyi yanda Fauziyya ta faɗa ɗin sai dai albashina ba'a hannunta yake ba...jiki ba ƙwari na fita daga ɗakin


Kamar kullum zaune suke suna hirar samarin gidan... precisely Khalil da Romo..wai wayafi kyau a cikinsu? Wasu na faɗar Romo wasu na faɗin Khalil

Wuce sunayi zan fita naji an riƙo hannu na Fauziyya ce '' bana ce kada inga ƙafarki a wurin nan ba?" Juyowa sukayi suna kallon mu na fisge hannu na

 '' ki gafarce ni ranki shi daɗe,it must have slipped my mind!...''

Zagaye ta nayi na fita daga sashen...ina jiyo muryoyinsu wai nayi fiffike ina tashi sama da nisa...

Kitchen na shiga,a maimakon in tafi dining,sai na tsaya a nan ina taya masu wanke wanke...na ɗauka na tsira sai da aka bani wani juice da aka haɗa da fruits wai in Kay dining....naji ina zufa amma babu damar musu yasa na karɓa...


'' ya makaranta Ibraheem?" Alhaji Kabeer yayi tambayar yana kallon Khalil da yayi ƙasa da kanshi da girmamawa

'' Alhmadulillah kawu...karatu da godiya...'' ya amsa yana zuba wani abinci a plate ɗin shi...yace '' naga hajjo ko kulani batayi ba...ina fatan ba'a shiga tsakanin muba?" Sai lokacin tsohuwar tayi murmushi da basarwa tace '' wazai shiga tsakanin mu kuma?'' ya ɗage kafaɗa...aka cigaba da hira cikin nishaɗi... Seraphina idonta buɗe tana jira taga inda zata ga Roman...

'' Ya I.B ina Ya Rome?" Yan matan suka kalli sashen Khalil expectantly, daga sanda ta kira sunan shi light atmosphere ɗin ta ɓace fuskar Alhaji Hussein tayi duhu yaja dogon numfashi batareda yace komai ba...

'' Ɗan iskan yaron ina zai zo ya gaishe da mutane? Baya girma ba...''

'' aunty don't curse him!" Seraphina ta faɗa tana turo baki...juya idonta Hajiya Momma tayi... sauran matan gidan basu ce komai ba haka ma hajjo


samarin suma sunyi shiru...no one talks about Roman...

'' come on...daga dawowa Sai faɗa .. just chill..." Khalil ya faɗa yana tura cokalin abinci cikin bakinshi hakan yaba su dariya...aka dawo yanayin murna da farin ciki...

Shigowa Dining ɗin nayi ɗauke da farantin juice a hannu na...'' bani ɗaya nan!" Khalil ya ɗaga hannun shi kamar yaron dake tambaya a aji murmushin nan manne da fuskarshi... naji kamar in juya idona amma na cije na ajiye mashi ɗaya a gabanshi '' Thanks kitten...'' yanzu kam kasa haƙura nayi Saida na juya ido...


'' na sani yarinyar nan mayyace! Daga zuwan ya Khalil harta yi bewitching ɗin shi!" Mufeedah ce tayi maganar tana huci kamar zata kama da wuta...yan aiki suka sadda kansu wasu suna dariya


'' na shiga uku...me nayi Kum...''

'' rufe ma mutane baki munafuka!" Heedayah da itama da alamu taji haushin murmushin da Khalil yayi min 


Khalil yake kallon su batareda ya fahimci inda lamari ya dosa ba...

'' duh she's so ug..''

'' SHUT UP!!" Farzan ya daka masu tsawar data sa suka firgita..nima da kaina sai da naji yan hanji na sun kaɗa

'' bar yara suyi magana, yarinyar nan tunda tazo sai saɓani ake samu a gidan nan!" Hajiya Bushrah da alamu ban mata ba ko kaɗan


'' come-on aunty kada ki faɗa min kema kin yarda da superstitions...''

'' babu maganar superstitions anan Farzan,kalli kai da kanka baka cika magana ba amma saboda wannan yarinyar kayi sentence mai tsawo. mai zamu kira wannan fisabilillahi?" 

Sauran suka gyaɗa kansu cike da goyon bayan abinda ta faɗa '' kuma fa yarinyar nan mahaukaciya ce...'' Hajiya Momma ta shiga faɗin abinda nayi mata harda ƙara gishiri da mai da yaji.. Seraphina ma ta faɗi nata labarin..sukayi min baƙin painti

'' da gaske kitten ɗin tayi haka?" Khalil ya tambaya da mamaki yana kallona...ɗauke idona nayi nake ji kamar kamar....


'' ƙarya za'a yimaka Ibrahim?" ya girgiza kanshi...Hajjo batace komai ba...sai saurare da take...babu wani abu dazai bada damar sanin abinda take tunani...


A hankali nake jin ƙamshin turaren shi tun daga nesa..sai nake ji yana ƙara kusantowa..kowa yayi tsit aka zuba ma hanyar shigowa Dining ɗin ido... Romo ne ya ɓullo hannun shi riƙe da plate nacin abinci...sakin baki nayi da naga babu face mask a fuskar shi...kamar irin mazan da nake karantawa a novel babu abinda yafi ɗaukar idona a kyakkyawar fuskar tashi sai hancin shi da yake dogo ƙofar hancin ƙarami nake tunanin taya yake numfashi?

Gashin girar shi a cike..fuskarshi fara sosai kamar baida jini...laɓɓanshi jajaye marasa kauri...saye yake da dogon wandon roba da large black t shirt da za'a iya fitar da guda biyu a ciki gashinsa pinned with a butterfly hair clip

Fuskarsa ba expression,bayan shi akwai wata mai aiki riƙe da wani plate daban a hannunta...jayewa kaɗan ɗin da yayi ya bani damar ganin ko wacece '' DIYAAM!!" Na kira da mamaki...

Leƙo kanta tayi daga bayan shi taga waye ya kirata..da gaske ita ɗince...

Wuce ni Yayi ya zauna a kan kujerar dake gefen Khalil... Diyaam ta ajiye plate ɗin dake hannunta ta tsaya gefe na...amma bata yimin magana ba...sai leƙa fuskar ta nake dan in tabbatar idan ita ɗin ce...

Tsit wurin ya ɗauka, shikam ogan kamar baisan tension ɗin daya sauke a dining ba ya shiga cin abincin daya kawo wanda bai yi kama dana yan Nigeria ba ...


Fuskar Seraphina tayi ja blushing take? 

'' toh mara kunya...mai idanu a tsakiyar kai, gaisuwar ma ba zamu samu ba kenan?" Hajiya Momma ce tayi maganar da takaici a muryar ta

'' tsawon rai zaki samu idan an gaishe ji ɗin?!" He answered with a chilled voice Batareda ya ɗago daga kwanon shi ba,wurin ya sake yin shiru kamar anyi ruwa an ɗauke, Hajiya Momma zata sake magana seraphina ta riga


'' Aunty ki...''

'' ke dalla rufemin baki! Shashar yarinya kina nan kina kare shi bayan shi bai masan dake ba!'' juya idonta Seraphina tayi,itako Hajiya Momma kamar zata kama da wuta 

Kowa a dining ɗin suka zuba ma Romo ido nikam nayi mamakin abinda ta faɗa..kuma batare da Khalil suka zoba? Meyasa kowa yake murna da Khalil amma ba Romo ba?da yake dai a gabana ya saki rashin kunya bari in kama kaina


Da baƙin cikin halin ɗan nashi Alhaji Hussein yace '' Ibrahim ina fatan kana mayarda hankali a karatu baka biyewa mutanen banza kamar wasu ?" Daga ji kasan da wanda yake amma wanda ake maganar dan shi,bai motsa ba


'' Kawu Rom baya bin mutanen banza,sannan shine yayi graduating a saman yan ajin su...''

Ɗauke kanshi Alhaji Hussein yayi Farzan yace '' da gaske?cuz he seems as dumb as fuck!!" Muryar shi ɗauke da gubar data kasa ɓoyuwa

Cikin son daidaita yanayi Khalil yace '' come on,kada kabashi kunya a gaban budurwar shi mana!" 

'' wacece budurwar tashi?" Seraphina ce tayi tambayar idonta waje,sai kowa ya dawo da kallonshi akan Romo that was unbothered..

Farzan ma ya dakata da abincin da zai kai baki yana jiran amsar Khalil...nikam so nake in bar wurin nan ƙafafuna har sun fara ciwo..ina tsaka da tunanin uzurin da zan bada in bar wurin naji Khalil yace '' gata tsaye a bayana..." Ya nuna ni...lokaci guda kowa ya sauke idonshi akaina....


Shock rubuce a fuskokinsu...nima dai shock ɗin na shiga sai rarrabar ido nake...

Mukhtar da Farzan ban san wanda yafi Zama shocked cikinsu ba...

''No way!!"

''Impossible''

'' wannan mummunar yarinyar ce budurwar ya Rom?''

Muryoyin suka faɗa a lokaci ɗaya... Seraphina,Huriyya... Jameelah da Khadeejah ne suka faɗi a dukan su sun tashi tsaye daga wurin zaman su


Khalil yayi ƙasa da kanshi yana murmushi

'' Ya Rome,da gaske wannan itace budurwarka?" Khadeejah tayi tambayar cautiously cike da tsoron amsar da zata biyo baya ..kowa ma amsar shi yake jira har dani 

'' Ask Google!" Batareda ya ɗago daga abincin shiba garmahon muryarshi ta amsa kuwwa a kunne na a karo na biyu,ƙafafuna kamar zasu zubar dani 

Damƙe tiren dake hannu na nayi..cikina ya ɗaure..zufar da ba'a gani ta wanke goshina mutumin nan zai sani a matsala dama can ba wani sona mutan gidan suke ba yanzu kuma wannan...

Miƙewa yayi babu wani sauran bayani ya nemi fita daga wurin

Alhaji Hussein da tunda yayi magana Roman bai ce ko ehm ba ya paka abincin shi gefe ya kalli ɗan nashi dake barin wurin ya miƙe '' Romano!"


Kamar Romo bazai tsaya ba can kuma sai ya tsaya batareda ya juyo ba ... Alhaji Hussein kamar zai yi aman wuta ya nuna shi yace '' kai bazaka zama ɗa na gari ba? A matsayina na ubanka ba zaka girmama niba? Kaje wata ƙasa ka dawo bazaka iya gaishe niba... I'm your father!'' wurin yayi tsit kamar babu mai rai a wurin, mu masu aiki kan mu a ƙasa sai rarrabar ido muke

'' My father....'' ya furta slowly kamar abun na bashi mamaki,sai ya juyo ta kafaɗarshi 

'' didn't see you there...PADRE!''... Voice cold as ice, idonshi da tsananin duhu ya cigaba da tafiyar shi




***

RU'UYAA…📖



₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta ***

Autumn writes 📖🖋️


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.