Free chapter · Read without an account

14

by Mamuh gummy · AASIYAH

Aasiyah

Mamuhgee

14

Bayan wata biyu Dr Binnah ya sake dawowa qasar tareda iyalansa banda Saed wanda yake karatu sosai,

Baffa bai fada musu ba a binciken da suke da ido da suka saka tako ina a kaf rayuwar BINNAHs yanzu ya saka sika sani dan haka suka samu nutsuwar ruhinsu da kwata kwata baya jikinsu dan kuwa babu kalan baqin ciki da damuwan da basa ciki na rashin Dr Binnah qasar da Haj maryam.

Nutsuwa ce ta shigesu dan haka a ranar basu kwana gidansu ba gidan baffa suka kwana batareda sun nuna masa sunsan BINNAHs na qasar sun dawo ba jiran kira kawai sukeyi daga Dr dayace zai nemesu.

Baffa ma bai taba nuna musu cewan maryam ta dawoba bare Dr Binnah suma suka fuske,

Cikin saa kuwa washe gari da safe katsam sai ga Dr Binnah din da kansa yazo gidan baffan tareda securities dinsa wainda suka sake daga hankalinsu Khamis suka ji duk sun sake shiga tinani da damuwa sedai sunyi farin ciki kuma suna cikinsa sosai wanda yake a bayyane da ganin Dr Binnah dan sunsan zaa hadasu da Haj maryam ne kuma kaman yanda yace zaa maidasu karatu to tabbas jansu zaiyi a jikinsa ya sakasu cikin ahalinsa dan haka bulama da jamilu sam bakinsu yaqi rufuwa khamis ma annashuwa ce a fuskansa sosai.

Da girmamawa sosai da ladabi da nustuwa suka tarbesa suna masa barka da isowa duk da securities sunso hanasu isowa garesa amma ya dakatar dasu yana cewa 'yayansa ne suma"

Wannan kalmar ita ta saka bulama yin farat daya ya ambacesa da "ALH DADDY" yanajin burinsa na farko ya fara cika a take dan kiran Dr Abubakar binnah da Daddy shine zai basa damar amsa sunan 'dan Binnah.

Khamis da jamilu ma washe baki sukai da tsananin farin ciki jamilu ma na cewa Alh Daddyn shima kuma dr din ya amsa da jin dadin daukansa da karbansa da sukai a uban shima kaman yanda ya daukesu yaya kenan.

Suna shiga palon baffa dukansu bayan Alh daddyn suka koma suka tsaya ya zauna suna basa wata irin kulawa mai tsanani kaman shine ya haifosu duniya wanda hakan ya saka Dr din fara jin dadi sosai sbd nasa yayan babban baida lafiyar basa irin wannan tattalin saed kuma yana makaranta bayama tareda su sai time to time dik da akwai wata irin kauna da shaquwa da kulawa da sakewa mai qarfi a tsakaninsa da yayansa dan kaman abokai suke lamarinsu duk da sunzo masa ma a lokacinda ya dan fara manyanta shiyasa  yanzu da tsufa yake fara zuwa su kuma yanxu ne suke zama matasa.

Baffa yayi farin ciki da ganin Dr binnah din cikin girmawa suka gaisa kowa ya fita ya basu guri suna maganganunsu da sakewan datake tsakaninsu har tsawon lokaci kafin suka dawo akan maganar su khamis data kawosa aka kirawosu suka zo suka zauna a gabansu kansu a qasa zuciyoyinsu na cikeda fargaban tinanika da dama da suke fatar abinda suke tsananin son ji zasu ji.

kai tsaye Alh Daddy kaman yanda suka ambacesa daga ranar ya kallesu kafin ya kalli Baffa yafara bayanin yasaka ayi musu komai na qarasa karatunsu a Cyprus inda Saed yake amma kuma ya samu labarin babansu jinya yake sosai dan haka kaman hakan bazai yiyuba sedai su zauna anan su qarasa karatunsu a gaban babansu.

Baffa ma ajiyan zuciya ya sauke yana cewa

"Eh tabbas kam barinsu hannun mahaifinsu bazai taba yiyuwa ba sbd jinya yakeyi hakama bayan jinyar koda lafiyarsa kalau ai bazai yiyuba da ransa ace mijin mahaifiyarsu ya dawo dasu hannunsa dan zasuyi karatu hakan ba lallai ya yiyuba......

Gabaki dayansu a tare suka dago suna sauke idanuwansu akan baffa da kallansa idanuwansu na fara sauyawa da wani irin mugun tashin hankali da jin kalaman kaman zubowan ruwan dutse.

Zufane ya tsinkewa Khamis da bulama a lokaci daya jamilu kuwa jin yayi idanuwansa na cikowa da hawaye kaman ya dora hannu aka ya rusa ihu yaji.

Alh Daddy kuwa cewa yayi

"Eh kuma hakanne Baffa,dole dai hakura zaayi abarsu acan din insha Allah dik taimakon da ake buqata saisu sanar maka zaa gabatar musu dashi insha Allah duka shirye shiryen da aka fara na tafiyarsu Cyprus zaa dakatar."

"Eh hakan shine ko acan ma gaban babansu da zasuyi karatun kayi kokari Allah zai saka maka da khairan insha Allah"

Maida kallansu sukai akan su khamis din dake zufa suna danne abinda ya tokare kirjinsu da maqoshinsu dan numfashin Khamis har wata daukewa yakeyi jamilu kuwa saida hawayensa suka sauko ya share batareda anganiba bulama bude baki yayi zaiyi magana Baffa ya katsesa sbd yasan me zai fada shikuma bazai bari a rabosu da gidan ubansu ba gwara su zauna acan.

Hanasu magana baffa yayi ya sakasu godiya wa Alh Daddy din harya tafi suna zaune babu wanda ya motsa.

Koda suka bar palon suka koma dakin khamis suka zauna shiru jamilu ne kadai yaketa matsar hawayen baqin cikin dayake neman kashesa sauran ko magana da kukan babu me iya yi idanuwansu sunyi jajir khamis sai ajiyan zuciya yake yanajin babu yanda zai yadda ya rasa damar nan da Alh Daddy yayi niya koda zai rasa ransa.

Bulama kuwa maimaita kalman "su koma gidan ubansu kawai zaa taimaka musu acan" yakeyi yana jin bazai taba karban wannan hukuncin ba da Baffa yasha gabansu ya yanke musu.

Basu kwana a gidan ba da daddare suka koma gidansu babu wanda yace komai har lokacin shiru shiru sukai sedai idanuwansu jajir suka wuni babu rahama da sauki ko kadan a cikinsu sai zallan baqin ciki da wani zafi.

Babansu tinda suka dawo babu wanda yabi ta kansa yana kallansu ya hango tsantsar baqin ciki da damuwa a tattare dasu wadda ta saka yaji zuciyarsa ta fara samun rashin nutsuwa dan haka yayi shiru baice musu komaiba shima yasha jinin jikinsa sbd bai taba ganin yaninsu irin hakanba da ko basu furta komaiba yanajin ba daidaiba.

Haka suka kwana shiru ba bayanin komai aka kuma yini suka kwana shiru,

Baba Ashiru jin yayi gabaki daya jikinsa ya mutu ya kuma kasa tambayarsu komai har aka kwana biyu baqin cikinsu bai gusheba sai qaruwa yake zurfafan gaske.

Acan Kuwa an aiko lawal da mota yaxo ya karbi takardunsu ya tafi wanda hakan dai ya tabbatarda anan din gaban babansu gidan ubansu cikin mataccen gida da ukubar talauci zasuyi karatu ana jefo musu taimako daga BINNAHs kaman almjirai zasuyi rayuwa karshe su gama karatun a samar musu wani dan gurin aikin da zaa ringa basu albashinda dashi rayuwarsu zata dogara dashi zasu gina zuriarsu cikin lissafi da wahala batareda sun shiga ahalin BINNAHs ba sun amsa sunan,sunyi rayuwar da suke buri,sun juya duniyarsu a hannunsu,sun riqe power din da suke tsananin buri da mafarki.

Sati uku ya wuce walwala da annushuwa tareda komai ya tsaya musu kansu ya dauki zafi zuciya ta rasa sukuni,

Shi kansa baba Ashiru halinda suke ciki shi yake ciki ruhinsa da zuciyarsa gabaki daya sun rasa sukuni ga ciwo ga azaba yanaji yana gani gasu da 'yan kudade amma rasa walwalan nema masa lafiya bare basa kulawa dan haka yake cikin qunci da dacin zuciya mai tsanani shima gashi a yanxu dayake ganin sun saka rai da dorawa akan burinsu babu abinda zaiyi ko fada musu su tina da matsayinsa da yanayinsa su dawo da cikakkiyar kulawansu akansa.

Yau haka kowa ya gama abinda yakeyi ya kwanta gidan da duniyarma tayi tsit sbd daren dayayi nisa.

Jamilu yau satinsa biyu tinda akai zaman da aka yanke shawaran rusa rayuwarsu bai iya rintsawa ba wanda kusan dukansu babu wanda ya taba bacci daga ranar kwana suke tinani da baqin ciki.

Karfe uku daidai jamilun ya bude idanuwansa daga kwancen dayake ya kalli duhun dakin da babu abinda kake gani na haske bayan dan hasken farin watan daya ratso dakin ta window ya juya ahankali ya kalli Inda bulama yake kwance yaga idanuwansa rufe bacci yake ya maida kallansa akan Khamis wanda shima idanuwan nasa a rufe suke sai ya tashi zaune cikin nutsuwa ya saka hannu gefen mataccen pilonsa ya dauki wayarsa ya rage mata haske sosai ya miqe tsaye ya fice dakin.

Yana ficewa Khamis da idanuwansa bude kuma yana jinsa ya bude idanuwansa tareda kallan kofar dakin da jamilun ya bari a bude ya tashi zaune tareda miqewa yabi bayansa cikin sanda.

Bulama na jinsu dukansu shima dan haka ya miqe ya isa bakin kofar dakin ya labe yana jiran jin abinda ya fidda su da fatan abinda yake tinanine da tsananin so zai kasance dan kuwa nasa shirin ne kila zasu cika masa.

Jamilu dakin Baba ya nufa kai tsaye tareda tura kofar dakin wadda ta bada sauti kadan ya shige.

Baba dake bacci duka kwanakin rabi da rabi jin sautin karar bude kofar a kunnensa ya saka idanuwansa budewa yana cewa

"Waye ne?"

Jamilun bai amsaba ya iso gaban baban wanda ya saka baban yunkurawa da karfi yana kokarin tasowa zaune ya bude baki yace

"Khamis ne?

Bulame kaine??

Jamilu ne??

Cikin wani irin taushi jamilun yace

"Nine Baba,nine nazo ka taimaka ka bari mu samu abinda muke so kaji?"

Wani zufane ya fesowa baban ya bude idanuwansa sosai cikin duhun yana neman inda zaiga dan hasken kallan fuskan jamilun yace

"Me kake nufi jamilu?

Ni ai nafi kowa son ku cika burinku ku rayu cikin daula"

"Yawwa baba ka bamu daman hakan,ka tafiyarka ka huta da wannan ciwon naka,

Ka bamu rayuwarka dakace zaka iya badawa dan mu samu jin dadi....

Ture jamilun Baban yayi da karfi yana cewa

"Bakada hankali,shaye shaye ka fara ko??

Tasowa jamilun yayi yana cewa

"Baba ka cika alkawarinka kawai na bamu rayuwarka sbd bazamu taba samun abinda mukeso ba saimun zama marayu,

Idan kana nan bazasu karbemu ba,

Idan kana nan Mahaifiyarmu bazata shirya damu ba baffanta ma bazai bari ba baba"

Hannuwansa ya saka ya janye pilon baban yana dagawa sama zai danna masa baban ya saka hannuwansa biyu da karfi yana turesa tareda bude bakinsa da karfi ya kwala kiran "khamis"

Khamis daya shigo dakin cikin sanda tin shigowan Jamilu yana jinsa ya sake lafewa yana dauke numfashi sbd kadama a jisa.

Sake kiran khamis din yayi wanda hakan ya saka bulama isowa dakin cikin sanda shima yana lafewa a bango.

Baban na kuma bude baki khamis ya tako da sauri cikin duhun ya lalabosa

Baban na kuma jin wani ata kansa yana lalabar fuskansa ga jamilu na shafo kafafunsa dan neman kansa yasan wani a cikinsu ma ya shigo dakin kenan take jikinsa ya dauki rawa ya bude baki yace

"Waye,khamis kaine ko bulam....? bai qarasa ba khamis din ya rufe masa baki da sauri da kuma karfi yana bude baki yacewa jamilu

"Ashe bakada hankali zaka bari yana magana sosai haka a cikin dare zaa iya jinsa"

Jamilu na jin hakan ya sake riqe pilon hannunsa da karfi yana yowa ta inda yaji khamis kenan gurin kan Baban.

Yana zuwa danna pilon yayi da karfin gaske amma baa kan fuskan baban ba sbd baa gani kuma dai jikinsa rawa yakeyi yanajin zuciyarsa kaman bazata iyaba shakka da fargaba na shigarsa saida sukaji shiru baya fizge fizge khamis yace

"Meye haka kakeyi ne wai??

Ka nutsu fa kada ka lalata abinda yinsa ya zama dole tinda ba ja da baya yasan komai”

Sake daga pilon yayi yana cewa bana ganin komai.

Da karfin gaske baba Ashiru ya saka hannuwansa duka biyu ya sake ture jamilu wanda yayi baya ya fadi da karfi sai akan bulama dake jikik bango lafe kaman kadangare ya shanye numfashi yana jiran su gama.

Da mamakin gaske jamilu ya tabasa da hannuwansa yana cewa

"Bulama"

Shiru bulaman yayi har saida jamilun yace

"Khamis ga wani anan ko waye kaman mu fara dashi sbd yaji komaiba"

Da sauri khamis daya hada gumi yace

"Waye?waye a gurin?

Jamilu riqesa kada ka sakesa bari na dauko wani abu"

Ture jamilu bulama yayi yana cewa da sauri

"Kada ka saki bakinsa kana saki ihun jamaa zaiyi"

Sunajin bulamane suka sake ajiyan zuciya take jamilu ya kuma daga pillow din bulama ya kunna hasken fitilar wayarsa haske ya bayyana fes a dakin idanuwan Baba Ashiru jajir suka bude akansu ya kallesu jikinsa na rawa wasu zafafan hawaye masu tsananin daci da baqin cikin dabai taba dandanawa a duniyaba dayafi zafi da radadin talauci dama na ciwon soyuwar mangyadan dake jikinsa suka ciko idanuwansa kafin su sauko su gangaro pilo ya rufe fuskansa.

#MAMUH

#AASIYAH

***

***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.