Free chapter · Read without an account

PAGE 19

by Ibtisam Shakoor · ZAREN ZUMUNCI(The thread of family bond )

…………………ZAREN ZUMUNCI 
              (The thread of family bond)

                     
                              WRITTEN 

                                      BY

                          IBTISAMWRITES ✍️



PAGE 19
 
 
      Haka rayuwar ‘ya’yan ta chigaba da tafiya ,yau dadi ,gobe babu.
 
    
      Duk San da aka ce yau za a hadu ,kowa da kowa, Toh fah sai an yi abin da za a zo ba a ji dadin shi bah.
 
 
    Yaran gaba ki daya Allah ya daura musu wani son girma , ba sa son raini.
 
     
       Bayan wa su shekaru ma su yawa,duk an zama manyan samari da ‘yan mata.
 
    
     Kowa a cikin su ya gama university,and ba kowa ne a cikin Su matan ke son yin aiki ko business bah.
 
    Aleeshbah ba ce kawai ta karanci medicine kuma zata fara internship a hospital.
 
    So kowa ra’ayin shi ya bi ,ya je yin abin da ya ke so.
 
   
     Su ko mazan bayan sun gama aikin na su,dukan su suma Allah ya sa musu son su yi aikin soji.
 
         Nan duk suka tafi,suka yi training na Su ,ga shi yanxu sun zama cikakkun soldiers din da ake ji da su a kasar.
 
         Amma su a cikin su da akwai wadanda su ke da ra’ayin business,bayan aikin soja din.
 
 
     A ciki khalil ,Ayan,Nafisa,Nimra su ne ma su son aiki an office ,so duk an basu aiki a company na gidan.
 
     Aliyu (moddibo) shi kadai ne ma ya karanci architecture saboda yana da son yin Zane tun yana karami.
 
      Yanxu ya zama babban me yin Zane shi ma.
 
  In za a iya yin qiyasi ma a cikin su da suka ta so za a iya cewa duk ya fi su kudi.saboda shi aikin sa ba wai na wasa bane.
 
 
     Sai ya kasance every months end Ana haduwa duka har da mazan in Suna nan, ba su ta fi filin daga bah
a gidan daya daga cikin iyayen na su.
 
    Sun yi wannan tsarin ne tsakanin su,ba sanin iyayen sai dai kawai gani suka ga Ana yi.
 
    Da suka tambaye su sai suka fada musu cewar sun yi hakan ne don su kara dankon zumuncin da ke tsakanin su.
 
      Sannan ko da a cikin su daya na da matsala Toh a nan za a tattauna ta a Samar da mafita.
 
 
    Duk da suna yawan samun sabani da Kanen nasu wajen rashin kuwa da suke musu wata ran , amma ba su kyale su bah sai ma janyo su da suke kuma yi jikin su.
 
 
 
        A cikin haka ne a ka samu wasu a cikin Su da suke crushing akan junan su,both mata da mazan,amma kuma ba Wanda ya fada wa dan uwansa.
 
 
    Kawai dai suna rayuwar su ,suna tunanin in lokaci yayi sai su fada.
 
 
     A cikin su akwai wadanda ba su da ra’ayin aure dangi.ko kadan ba sa so,They believe a yadda suke zumuncin nan na su ,zai iya kawo matsala tsakanin gidajen.
 
 
     A na ta shirye shiryen tarbar mazajen gidan, zai iya kawo su dawo daga aiki da aka tura su .
 
 
  Sun yi like 5 months duka ba sa gida,babu waya,ba sako.Shi ya sa kowa kaga fuskar shi zaka San yana cikin farin ciki.
 
    And a gidan Abba Abbie ma a na ta shirya tarbar da za a ma Aleeshbah,ita ma za ta dawo gida daga India.
 
     Amma kuma babu Wanda ya San da zata dawo , sai mamanta ,ita kadai ta fada wa.
 
    Ko Abbie bai San da dawowar tata ba, shi da a cikin yaran ya fi shakuwa da ita duk da ba a nan ta ta shi tare da su bah.
 
 
    Aleeshbah is someone da in tana wuri, ba a iya ta shi, sai dai a zauna saboda ta iya zama da mutane sannan tana da barkwanci.
 
    Amma in aka tabo ta babu ma Wanda zai ce ta iya wani abu wai shi murmushi.
 
     Sannan ita ma Allah yayi ta ba ta son raini, ko da ka girme ta to kar ka nuna ka raina ta don bata dauka.
 
    
     She believes kowa is equall.In ba ka son a rai na ka kar ka rai na wani ko da na kasa da kai ne.
 
 
      Shi yasa ake yawan samun sabani da ita akan wasu abubuwan.
 
     Tana da tsari akan yadda ta ke tafiyar da rayuwar ta, bata son a shigar mata rayuwa itama bata shiga ta wani bah.
 
    

Ibtisamwrites✍️

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.