Free chapter · Read without an account

PAGE 20

by Ibtisam Shakoor · ZAREN ZUMUNCI(The thread of family bond )

…………………ZAREN ZUMUNCI 
              (The thread of family bond)

                     
                              WRITTEN 

                                      BY

                          IBTISAMWRITES ✍️



PAGE 20
 
Rana ba ta karya, ranar da mayan bakin gidan za su dawo ta yi. In da, dukan su a gidan kakanin su za su sauka.
 
   An musu tarba mai kyau, an shirya musu abinci kala kala, da kayan Sha.
 
   Duk surukan gidan sun zo amma banda Ammi, saboda ta ce ita yau tana da uzuri.
 
    “Ya’yan nata In sun dawo, sun huta sa zo su gaisa. Ita ta na ta shirin tarbar yarta da ta dade ba sa tare da ita.”
 
    Ta yi mata shiri na musamman, an gyara mata dakin da ta ta zauna, an saka mata duk abubuwan da ta ke da ra’ayi.
 
    An tsara mata dakin nata dai dai da tsarinta.
 
     Dukkan su sun sauko daga cikin jirgin, sanye da kaya su na Soldiers, with glasses on their faces. Su na tafiya cikin nutsuwa a jere.
 
 
     Sun karaso cikin mota da aka turo driver ya dauke su, drivers din sun musu barka da zuwa sannan suka karbi luggage din su, don saka wa a boot.
 
Sun shiga cikin motoci, suka dauki hanyar zuwa gida.
 
    A bangaren Aleeshbah ma jirgin su ya sauka , Ammi da driver ne su ka tafi dauko ta,which ita Aleeshbah ba ya kawo cewar Ammi zata zo daukan ta bah.
 
      Ta San yau ‘yan uwan nata za su dawo so bata kawo wannan akan ta bah.
 
 
       Daman kuma ita she prefer it like that, a dauko ta bah tare da kowa ya ganta bah, ta fi son in ta dawo ,ta huta sosai kafin ace ma zata hadu da mutane.
 
     Ta tsara in ta dawo ,gida zata huce ta ga Ammi din ta da kuma Abbie din  ta .in ya so kowa ma sai daga baya sa hadu . Ba matsala ba ne.
 
 
      And kawai sai ganin Ammi ta yi ta fito daga cikin motar,she was so happy to have finally meet her mom .
 
 
     A duk shekarun da aka yi , ba su taba Haduwa face to face bah ,sai dai su yi waya.
 
    Aleeshbah boarding school ta yi so lokacin da su Ammi ta ke zuwa india ziyara, lokacin Aleeshbah bata nan ta na school.
 
      And Aleeshbah, ta sa wa kanta in ba su hadu da family din ta na Nigeria bah a zahiri, babu me ganin ta ko a hoto.
 
 
       That is why Ammi na ganin ‘Yar tata a zahiri,ta rungume ta tana mai Jin dadin ganin ta.
 
 
        Haka dai suka hakura da rungume rungumen juna suka shiga mota don tafiya gida.
 
      A motar ma dai ba su hakura bah ,Aleeshbah kanta ta daura akan cinyar Ammi,suna ‘Yar hirar su ta ‘ya da uwa.
 
 
    Haka suka koma gida ,Ammi ta ce “beta ko abinci za a zuba miki ki fara ci kafin kiyi wanka?”
  
     Ta girgiza kai ta ce “no Ammi I ‘m not hungry “wankan kawai zan yi.
 
 
      Ammi ta bude idanuwanta ta ce ,” ya zaki ce ba Kya Jin yunwa bayan yanxu kika dawo? Ma za - Ma za je ki yi wanka ki zo nan da kai na zan Baki abinci a baki”.
 
 
 
 Ibtisamwrites ✍️

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.