Free chapter 路 Read without an account

30

by Anisa Muhammad Yahaya 路 NUFIN ALLAH


馃挄 NUFIN ALLAH 馃挄 
By
Anisa Muhammad yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA

Under team yota's amazing pen

Page 3锔忊儯0锔忊儯


Anty na zaune a parlour taga fitowar Anisa da kamar wani abu na damun ta 

Kallon ta take tana tunanin to me yake damunta dan tun jiya ta lura da haka batayi magana bane saboda tayi tunanin ita da 拼anuwan nata ne

Wajen da anty take ta 茩araso ta zauna 茩asan 茩afarta tana gaida ita tace

"Anty daman gida Nike son inje nayi mantuwa inna dauko sai ko gobe ne in dawo in ban dawo yau ba"

"Me kika manta haka,  to ki fa蓷a wa su batul inda yake su ba driver ya kawo Miki ba sai kin sha wahalar komawa ba"

"A'a basu san inda na ijje ba a can cikin kaya ne, kona fa蓷a musu baza su gane ba ni ka蓷ai nasan inda na ijje"

"shikenan to ki shirya sai in ma Malam ya'u magana ya kai ki"

"To anty Nagode"  harta tashi zatayi gaba anty tace

"Wai Anisa me ke damun ki tun jiya na lura bakida kuzari, ko ke da 拼anuwan naki ne?"

"A'a babu komai anty banda lafiya ne fa kawai"

"Bakida lapiya shine kawai?, Amman agaishe ki memakon kiyi magana, daman mutum in bashida lapiya Zama yake haka"

"A'a anty bafa wani rashin lafiya bane mura ne ke damuna shine ya 蓷an saukar mun da zazza蓳i Amman na sha magani fah"

"To Allah kyauta kidai ringa kulawa"

"In Sha Allah" ta juya ta tafi a ranta tana tunanin gwara ta je ta sanar da ammi kafin Abba ya nemi jin ra'ayin ta gobe dan shekaran jiya bayan sun gama maganar nan koda ta kwanta kan sallaya kasa baccin tayi

Ba ta son Abba ya nemi jin ta bakin ta kuma tasan zuwa gobe ko jibi daya fa蓷a dole ya neme ta gwara ma ta tafi ta koma gurin ammin ta

Tun suka tunkaro gate din gidan taji damuwar datake ciki na yayewa a hankali tun ma bata yi ido hudu da ammin ta ba

Sauka tayi ta shiga cikin gidan da 蓷an sassarfa 

Zaune ta same su ita da Amma da mommy suna hira sai dariya suke, su batul na ta gurin dining suna gyaran alayyahu 

Dan jiya anty ta kira mommy ta sanar da ita, itama take fa蓷awa Ammi da Amma, shine amma takasa hakuri ta zo yau suna hirar zancen cike da nishadi 

Kara sowa tayi ta gaida su suka amsa mommy na cewa

"A'a naganki ke ka蓷ai ina sauran 拼anuwan naki"

"Ba tare muke ba ni ka蓷ai na dawo" ta fa蓷a kanta a sunkuye dan ji tayi haka kawai yau tana jin nauyin Mommy 

"Saboda maisa" Ammi ta tambaya tana kallon ta dan taga tayi mata kamada wata mara lafiya 

Duk dan tsabar daurawa kai

"Mantuwa nayi, abu zan 蓷auka"

"Bakida lapiya ne?"Amma ta tambaya tana kallon ta 

"A'a lafiya ta klau mura nakeyi"

"Oh to Allah sauwa茩e, Amman kin dai sha magani koh??"
"Eh nasha"

Su Khadijah ne itama suka gaida ta ta amsa tana cewa

"Yanzu ku duk girman kitchen ku rasa ina za kuyi gyaran alayyahu sai anan, ai kun kyauta"

Murmushi kawai sukayi basu ce komai ba itama tayi hanyar 蓷akinta ta shiga

Su su amma ma basu lura dasu a gurin ba sai yanzu

Ita fa tayi tunanin Ammi kawai zata samu batayi tunanin ma Ganin su mommy ba , Amman Bara ta jira zuwa su tafi sai ta mata maganar 

Fitowa tayi Bayan ta canja kaya zuwa Normal kayanta na gida, wani material ne mara nauyi ta dakko ta saka dan a rayuwar ta ita idan ba fita zatayi ba ba son saka atampa take ba

Dawowar su kenan daga Company 蓷in baba na shinkafa wanda anan Ahmad ke aiki bayan wannan ma yanada nashi business din 

Ya raka Ahmad ya Duba wasu files ne da yarasa inda ya ijje su

Sallama sukayi suka shigo parlourn suka gaida su amma 

"Babana Anga files 蓷in?"
Fa蓷in ammi tana kallon Ahmad 

"Eh ammi ashe acan na barshi bansani ba"

"Mashallah Allah ya taimaka" fadin mommy tana musu sannu

Fitowar ta kenan suka ha蓷a ido dashi, jitayi zuciyar ta tayi wani mummunar buga wa, baya ta蓷an yi ka蓷an tana zare wannan manyan idon nata tana 蓷an dafe 茩irji kamar wadda ta ga Wani abun mutuwa





______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 馃尯

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.