Free chapter · Read without an account
3️⃣1️⃣
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Under team yota's amazing pen
Page3️⃣1️⃣
Tun ta fito yake Binta da kallo dan ji yake kamar yafi shekara be ganta ba, yayi kewar ta sosai baya son ya ce zeje gidan anty dan be san wani excuse din ze bata ba in yaje, but da bata zo yau ba ko gobe se ya shirya yaje
Be da tabbacin ma zai ganta tunda ba zaman parlour suke ba sedai in gaida shi zasu zo yi, Amman wannan ganin ai ba gani bane
Shi gani yayi ta canja mai kamar wata mara lafiya, to ko meke damunta ya wa kanshi tambayar yana jin kamar yaje ya ji meke damun nata
Da kyar ta iya janye idonta daga nashi wanda shi Bama shi da alamar yin hakan,
Cikin rashin kuzari ta gaida su, Ahmad ma na tsokanarta kawai murmushi tayi mai tayi gaba a binda bata su saba yi ba idan suka haɗu
Kitchen ta nufa inda su batul suke, wanda jin shigowar su ya Umar sukayi saurin komawa
Bata ce musu komai ba ta duba nisan girkin nasu taga Bama wani nisa sukayi ba sundai kawai haɗa duk abinda za'a buƙata Amman Yanzu ma suka sa ruwan tuwo
"Idan kun gama gyaran alayyahun ku tafi zan ƙarasa"
"Kai Adda wallahi shiyasa nike son ki thank you" batul tayi maganar tana blowing mata air kisses
"Gamsahamnida (thank you) adda in miki ta ƴan ƙasar da kike so Korea"
Murmushi tayi ta ɗan girgiza kai tace
"Wallahi Allah dai ya shirya min ku, tsabar laziness"
Tukunya ta dauko ta fara ƙoƙarin preparing miyan
Suna gamawa suka ajje mata kan carbinet suka fita
Ba ita ta fito ba sai da ta tabbatar ta kammala komai saboda Bama tason fitowa su ƙara haduwa
Kamar ko tasani, tun yana jiran yaga fitowar ta suna ɗan jefa hira da su Ammi amman shiru kake ji, sai leƙen hanyar kitchen yake yi a fakaice, amman ba alamun ma tana da niyyar fitowa
Sallar la'asar da ake kira yasa su fita masallaci shi da Ahmad, itama jin kiran sallah yasa ta san sun dai fita by now
Abincin ta ɗiba aplate ta leƙa parlourn bata hango ƴan parlourn Amman tana iya jin muryoyin su, bata ji na Ya Ahmad ba bare shi gogan dan haka tayi saurin fitowa ta shige ɗakin ta
Duk abinda suke daga ita har ya Umar din akan idon amma, murmushi tayi tana tunanin wannan wani kalan soyayya ce
Tana shiga ta ajje plate ɗin kan gado tayi hanyar toilet, kafin ta shiga tace dasu batul
"na gama nasa a warmers, ku dauko ku kai dining ki fadawa su amma kuyi serving nasu"
Da to suka amsa ta suka tashi dan suje suyi abinda ta saka su
Alwala tayi ta fito tayi sallah, bayan ta idar ne tana zaune kan dadduman Ammi ta shigo ta same ta a haka tace
"Kin gama girkin ne habibty"
"Eh Ammi na gama nace masu Khadijah ma suje su faɗa muku"
"Okay to ke ba zaki fito ki ci bane"
"A'a na ɗiba" ta nuna mata plate ɗin da ke kan gadon
"Yanzu dan rashin mutunci ki rasa inda zaki ijje plate sai kan gado, duk gurin ɗakin nan be miki ba sai kan gado"
"Yanzu zan ɗauke"
"A'a karma ki ɗauke ki barshi"
Tayi magana tana ƙoƙarin barin ɗakin
"Ammi" Anisa ta kira sunan nata amman takasa cewa komai banda haka
Juyowa tayi ta kalle ta jin ta kira sunan ta amma bata sake cewa komai ba
"Meya faru"
"Daman abu nike son faɗa miki Amma sai anjima"
Ajiyar zuciya ta sauke tace"to Allah ya kaimu"
Bayan fitar Ammi ne ta fara saƙe saƙen yanda zata ma faɗa mata dan ta lura kamar tana son haɗin, tunda ɗazu tana iya jiyo hirar su a parlourn suna ta maida zancen yanda sukayi da Abba
Har amma na cewa abarta maybe kunya take ji shiyasa takasa magana tace abata time
Parlourn ta leƙa taga basa nan, tasan bazai wuce suna dining suna lunch ba
Komawa tayi ta janyo wayar ta ta fara kallon Film ɗinta, kallon take Amman hankalinta gaba ɗaya baya kai, har amma ta shigo bata sani ba
"Anisa meya faru ne"
A ɗan razane ta juyo ta kalla inda ammah ke tsaye dan bata ji sanda ta shigo ba
"Eh lafiya klau Ammah"
"Anya lafiya kuwa dan tun kika zo baki mun kama da wadda take klau ba, meke damun ki"
Jitayi zuciyar ta ta karye, wani kuka ne ya taho mata tace
"Amma danAllah kar ayi haɗin nan dan bana son ya Faruq ko kaɗan"
______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺
***