Free chapter · Read without an account

Page 1

by Mrs Classy Write · RABO DA KADDARA

⚜️ *RABO DA KADDARA* ⚜️
_Marubuciya: MRS CLASSY WRITE_
_Page 1_

Wani irin karan mari ne yake tashi a cikin falon, har sai da kunnuwan kowa suka yi ruri.

Duk falon ya dauki wani irin shiru mai ban tsoro. Shiru da zaka ji bugun zuciyar kowa. Sai karar AC kadai ne yake tashi a hankali, tare da shekarar kukkan da take kokarin boye wa a tsakiyar makoshinta.

Fatima ta dafe kuncinta da hannunta daya. Idanunta sun ciko da hawaye, amma ta ki barin su su zubo. A gabanta, Baba ne a tsaye. Fuskar sa ta hade, idanunsa sun yi ja-jawur kamar saboda tsananin bacin rai ya cinye zuciyarsa.

"Dan ubanki!" Ya sake daka mata wata tsawar. Muryarsa na rawa. "Nace miki cikin uban waye a jikinki yanzu Fatima? Da abin da kike so ki saka min kenan ko tukuicin da zaki bani kenan?"

Kalmomin nasa kamar wukake ne a zuciyar Fatima. Jikinta na rawa.

Ta kasa magana. Harshenta ya makale. Wani irin tari mai tsanani ne ya taso mata daga kirji, tana kokarin tari amma hawaye ne ke fitowa maimakon sauti.

A gefe, Salim ne ya mike cikin sauri. Amma tsoro ya bayyana a fuskarsa. Ya nufi Baba, ya kama hannunsa.

"Baba, dan Allah kayi hakuri. Dan Allah. Idan kun bi ta a hankali zata yi magana. Dan Allah Baba..."

Baba bai kalle shi ba. Ya ture hannun Salim din.

A can tsakiyar gefen falo, a kan kujera mai laushi, Mommy ce zaune. Tana kallon kasa, hannunta na wasa da zane. Ita ma ta kasa magana.

Amma Abidah... Abidah da take zaune a kasa kusa da Mommy, ita ce ta kasa jurewa.

Cikin wani irin sauri, ta mike. Kuka ne ya kwace mata, kuka mai cin zuciya, kuka na tausayi da takaici. Ta nufi Fatima, ta rungume ta da karfi a jikinta. Ta damke ta kamar zata kare ta daga duniyar da ke son ta cinye ta.

"Fatima..." Ta fashe da kuka. "Kada ki yi shiru, dan Allah ki yi magana. Me ke faruwa dake? Waye yayi miki haka?"

Fatima ta jingina kanta a kafadar Abidah. A wannan lokacin ne duk hawayen da ta boye suka sauko. Ta fashe da wani irin kuka, kukan da ya girgiza falon. Kuka ne na mace daya tilo da ta rasa mafaka. Kuka ne na tsoro, na kunya, da nadama.

Kanta a kasa tace, "Bansan cikin nan na waye ba..."

Kowa a falon ya tsaya cak. Saboda jin abinda ta fada.

Baba ya ja da baya kamar an harbe shi. Mommy ta dafe kirji.

Yaya Bilal! Ya kasa jurewa,

Wanda tun dazu yake hade rai a kofar falo, ya shigo cikin falon da wani irin gudu. Idanunsa sunyi jajir, jijiyoyin wuyansa sun tashi saboda bacin rai.

"Me kika ce? Baki san na waye ba?!" Ya daka mata tsawa, muryarsa na rawa. "Kin zama karuwa kenan a cikin gidanmu? Kin bata mana suna? To yau sai jikin ki ya gaya miki!"

Kafin kowa ya ankara, hannunsa ya nufi wandon da yake jikinsa. Ya cire belt din fata mai kauri da yake daure da shi.

"Bilal! Kada ka aikata!" Salim ya yi ihu yana kokarin kamashi, amma Bilal ya tureshi da karfi har ya fadi a kan kujera.

Ya daga belt din sama.

"Yau sai kin mutu ko kin fadi gaskiya!"

_SHAAAW!_

Karan farko ya sauka a bayanta. Fatima ta yi wani irin kara mai tsanani, ta fadi a kasa. Jikinta na rawa.

"Bilal dan Allah!" Abidah ta fashe da kuka tana janta a jiki, tana kokarin kare ta. "Zaka kashe ta mana!"

Amma Bilal baya ji. Bacin rai ya rufe masa kunnuwa. Ya sake daga belt din.

_SHAAAW! SHAAAW!_

Ya shiga dukanta babu tausayi. Duk inda ya sauka, Fatima na karkarwa a kasa. Ba ta iya magana, sai hawaye da kuka mai cin zuciya. Jikinta ya yi laushi.

A lokacin ne wani ihu ya fito daga kusurwar falo. Kara ce ta tsufa, amma mai karfi da zafi.

"Bilall! Ka kasheta zakayi saboda baka da asara!"

Hajja Kaka tace!

Tsohuwa mai ran karfe, wadda tun dazu take zaune tana kallon abin da ke faruwa tana shiru, ta mike da wani karfi da ba a zata ba. Fuskarta cike da hawaye. Ta nufi Bilal da sauri, ta ture shi da duk karfinta har belt din ya fado daga hannunsa.

"Shege! Mara tausayi! Ita ce kake duka kamar dabba? Kana dukan ta sai kace ka samu kato? 'Ya mace ce fa! Ba namiji ba!"

Ta fashe da kuka, kuka mai tsanani, ta fadi kasa kusa da Fatima. Ta rungume Fatima da karfi a jikinta, tana shafa kanta.

"Kiyi hakuri yarinyar kirki, haka RABO DA KADDARA ya zo... Fatima ta... ki tashi dan Allah... kada ki mutu ki bar ni..."

A jikin Hajja Kaka, idanun Fatima suka lumshe. Numfashinta ya yi sama. Ta _suma._

"Fatima ta suma!" Abidah ta yi ihu.

Duk gidan ya rude. Salim ya ruga ya debo ruwa. Mommy na kuka, Baba ya dafe kansa ya zauna a kasa.

Hajja Kaka na rungume da Fatima da ta sume a jikinta, tana kuka tana cewa, "Rabo da Kaddara... Ya Allah kawo mana mafita a cikin wannan kaddara..."

---

Masu bukatar a musu tallah zaku iya tuntubana ta wannan number 👉*** MRS CLASSY WRITE nagode🙏

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.