Free chapter · Read without an account

26. ... Maraya ne...🖊️

by Noor · RU'UYAA (The dreams we never lived)





Washegari da sassafe ina kitchen...coffee Leonardo ya miƙo min yace '' ki kai room no 207''

'' Kai bazata yi hausa ba wai?" Nayi maganar da hausa,tsare ni yayi da ido ƙwaƙwalwarsa na aiki a 360..karɓar coffee ɗin nayi ina tunanin yanda zan fara hawa stairs tunda sassafe naga Farzan ya shigo
Parlorn ya nufi elevator da sauri na faɗa ciki tare dashi bayan elevator ta buɗe...saura kaɗan in mashi wanka da coffee ɗin yayi saurin kaucewa

'' baki da nutsuwa!" na zaro ido nace '' ban taɓa jin wannan kalmar ba,akwai a dictionary?"

ya ƙanƙantar da idon shi akai na can yace '' of course you're dumb bazaki San me hakan ke nufi ba!" turo baki nayi fuska a ɓace kafin in bashi amsa elevator ta buɗe yayi gaba yabar ni tsaye a wurin sai dana ga ƙofar zata sake rufewa nayi saurin fita


samun Khalil nayi kwance saman blue carpet dake gaban gadon shi yana excercise...nuna min table yayi na ajiye coffee ɗin anan zan tafi naji yace 

'' zoki dafe min ƙafafuna kada ki bari suyi sama...'' Juyowa nayi idon mu ya haɗu...nake ji kamar in kwarara mashi coffee ɗin dana kawo...'' Uhmm..'' ya nuna min ƙafafun shi yana murmushin gefen baki

Dawowa nayi na dafe mashi ƙafafun yana tashi daga kwance ya zauna sai ya koma..kuma baiyi zufa ba..ɗauke fuska ta nayi gefe dan idan ya ɗago fuskokin mu zasu kasance kusa kusa,hucin shi na sauka a gefen fuska ta...

'' wai har yanzu baka gama ba?" Na tambaya bayan shuɗewar lokaci zuciya tana tafasa


Rashin amsa daga gareshi yasa na juyo daidai ya taso fuskokin mu were inches a part...idon mu ya shige cikin na juna ..bugun zuciya ta ya sauya... lumshe idonshi yayi tare da karkatar da kanshi yana matso da fuskar shi saura kaɗan bakin mu ya haɗu nayi saurin miƙewa

Dariya yayi yana kawarda kanshi gefe '' such a buzz kill...da kin tsaya mana...''

Hanyar fita nayi..wannan Khalil ɗin is a bad influence...'' oh haka fa...baka yi brush ba shine yasa!" 

ina jiyo dariyar shi na riƙa handle ɗin zan fita naji yace '' zoki jira inyi brush sai mu sake gwadawa...''

na buɗe ƙofar na juyo akan kafaɗuna nace '' Too bad..you missed!"

Na fice da sauri, kumatuna suka yi ja..tunowa da haɗuwar mu ta farko yasa murmushi ya wanzu a fuskata


Wurin tagar dake corridor na tafi na tsaya ina kallon tsakar gida,idona ya sauka akan Romo dake zaune saman wani baƙin mashin ƙato irin wanda masu gudun tsere suke hawa...shima yasa baƙaƙen kaya daga sama har ƙasa... hannunshi riƙe da helmet baƙi...ƙila yaji a jikin shi a na kallonshi ya juyo da baƙaƙen idonshi saitin da nake tsaye...duk da nisan da muke dashi sai da zuciya ta ta buga da ƙarfi...kallon shi bai daɗe ba ya ɗauke yasa helmet ɗin ya fice da gudu daga gidan kamar zai tafi lahira...


Zan bar wurin ɗakin ƙofar Seraphina ya buɗe tana ganina fuskarta ta sauya '' ke zonan!'' ƙarasawa nayi gabanta ɗin ta nuna min ɗakinta '' wuce ki gyara min ɗaki...'' tana faɗar haka tayi gaba ta barni tsaye 

'' wuce ki gyara min ɗaki... ba'a gyarawa!" Na kwaikwaye ta amma dai daga ƙarshe banida zaɓi dole na shiga na gyara...

Da ƙarfe goma duka yan gidan ne zaune a parlor harda su hajiyoyi,samari da yan matan da suka rage a gidan...

Wasu mutane suka zo daga company'n kaya daban daban suna nunawa yan gidan kowa ya zaɓa...nake ji yan gidan na faɗin kayan designer ne limited edition...

Kowa darjewa yake ya zaɓa...mu masu aiki ba'a barmu mun huta da guje guje zuwa nan da can ba...

yau ma munci Sa'a hankali bai a kanmu da yawa hakan ya rage mana cin mutunci da alamu akwai taron da suke shiryawa ƙarshen mako

Seraphina ta saka wata doguwar riga pink irin ta Disney princesses..ta saki gashinta tayi kyau sosai Hajiya Wareesha sai yaba kyaun yar tata take... sauran yan matan suke binta da kallon kishi...


'' wow you look stunning in that dress phina!" Ayaan ne ya faɗi haka yana ɗaukar doughnut daga plate ɗin da aka ajiye masu '' na gode...'' ta faɗa da murmushi

badiyya tace ''kinfi kama da malnourished akuya a cikin wannan rigar'' 

'' kidai faɗi gaskiya Badiyya, kin san a gidan nan babu kamar Phina...'' juya idonsu sauran sukayi jin maganar Hajiya Wareesha

Hajiya Momma tace''la shakka tunda ita akayi ma wahayin kyau ba...mata duk ƙasusuwa kamar mai fama da kwashiorkor!" Da yawa daga cikin yan matan suka kwashe da dariya

Nima na toshe bakina ina yi ƙasa ƙasa Seraphina kamar zatayi kuka da cin mutuncin data fuskanta...

Sauran ma suka shiga gwada kaya yan mazan na zaɓen wacce tafi kyau...duk Seraphina tafi su samun points...


Sukam ma'aikatan company'n sun zage sai ƙara nuna masu kaya suke...daga nan aka shiga zaɓen sarƙoƙi da awarwaro.. wata sarƙa na gani mai simple design tayi min kyau sosai

Ɗaukar sarƙar seratena ta ajiye... Khalil ne yaxo ya zauna daga gefen da nake tsaye ya gaishe da matan gidan a girmame,kafin ya kalle ni with a smirk on his lips,na ɗauke kaina...such a big flirt he is


yan matan suka zo suka zagaye shida sarƙoƙi suna tambayar shi wane zasu ɗauka...kamar shi mace ne da zai san wanda yafi kyau

'' Uhmm... maybe ku tambaya su aunties...nida ba mace ba...''


'' Mufeedah tace '' ni ina so insa abinda ka zaɓa min ne kawai!"

'' sannu yar iya...'' Mardiyya ta harare ta..abu ya kusan zama rikici sai da Hajiya Hafsah ta tsawatar

Khalil ya shafa ƙeyarshi... sarƙar da nake ta kallo ya ɗauka ya duba...'' I'll take this..'' ya nuna ma staff ɗin har zasu karɓa su ajiye cikin kayan da yan gidan suka zaɓa yace subar shi kawai...

'' Budurwar ka ka siya mawa?" Hajiya Bushrah ta tambaya... nayi mamakin jin yanada budurwa..'' nope... it's for some one else...''

'' Kai Khalil yanzu bayan Eden ɗin da aka sa muku rana kana da budurwa gefe?" 

Sauran yan matan suka tsaya cak...''sa rana...'' suka faɗa a tare...samarin suka kwashe da dariya ganin shocked expressiom ɗin yan matan wasun su kamar zasu yi kuka

'' waih Allah yasa ya Rome baida budurwa what would I have done?" Seraphina ce tayi maganar tana ƙaramar dariya hannunta dafe da ƙirji...



'' meyasa kika kira sunan shi...'' Arman ne ya faɗi haka '' saboda shima mutum ne ...'' ta juya idonta

Khalil kam tunda aka faɗi maganar sa ranar shi yanayin shi ya sauya, muna haɗa ido yayi ƙasa da nashi.. weird 

Farzan ne ya iso wurin hannun shi riƙe da kofin tangaran yana shan shayi a ciki ya zauna gefen Khalil yana kallon bajakolin kayan dake wurin da murna rubuce a fuskarshi da kowa bai kasa lura ba


'' did you hit a jackpot?" Khalil ya ɗage gira..kurɓar coffee ɗin shi yayi da murmushin mugunta yace

 '' abinda yafi jackpot na samu...akwai wani abu dake cimin tuwo a ƙwarya.. yau nayi maganin ab...'' kafin ya gama magana,babbar ƙofar shigowa parlorn ta buɗe dukan mu muka mayarda kan mu...muga waye zai shigo

Ƙamshin shi ya fara isowa kafin shida kanshi ya ɓullo...Romo ne...he was disheveled...gashinshi ya ɓaci ga ƙananan tabo a gefen baki da kuncin shi...ya yagalgalu

Kamar wanda aka ƙwato daga bakin zaki...wurin yayi tsit kamar an ɗauke ruwa..kowa yabi shi da kallo.. tafiya yake kamar yanda ya saba.. fuskarshi kamar hadari, sanda ya wuce ta gefena sai da gabana ya faɗi... Farzan ya furzar da shayin dake bakin shi yana kallon Roman hakan ya dawo da kowa daga suman zaunen da sukayi 

Take fuskar Farzan ta canja daga murna zuwa fushi...Romo bai shiga elevator ba ta stairs yake bi

'' ya akayi ka dawo?" Yayi tambayar hannayenshi dunƙule daga gefenshi..mun sha mamaki musamman ni dama bai kamata ya dawo bane?

'' oh... disappointed to see me?'' kofin shayin shi Farzan ya wurga ma Romo... Na gwalalo ido kowa ya rufe bakin shi

amma kofin bai cimma Romo ba ya tsaya few steps ƙasan shi...shayin yayi staining wasu daga cikin dresses ɗin da kuma farin tiles ɗin

Farzan kamar zai kama da wuta... coldly Romo yace ''Lord!you're such an embarrassment to the male gender a new born baby would have done better!" 

sai ya juyo yana kallon Farzan dake tafasa fuskarshi tayi ja,ember eyes ɗinsa kamar ƙyanƙyashen garwashi 

flatly Roman yace '' idan kaji zafi,akwai bango a kusa bang your head on it! har abada bazaka taɓa matakin dana taka ba.. never!" 

Ya juya yana tafiya kamar babu abinda ya dame shi a duniyar nan...nabi bayan shi da kallo wani irin abu na sauka a zuciya ta game dashi...

Lokaci guda bayan tafiyar shi muka dawo da kallon mu akan Farzan '' Dude...abinda kayi kenan? You targeted Rome so kake ka kashe shi?" 

A fusace Farzan yace '' nayi baƙin cikin rashin mutuwar shi!" Babu wanda ya ga sanda ta tashi sai dai gani muka yi ta share Farzan da mari...'' ɗan uwanka kake ƙoƙarin kashewa Farzan? I brought you up better than this.. '' sosai ɓacin rai ya bayyana a fuskar Hajiya Hafsah 

Hannu ya cusa cikin gashin shi ya faɗa da ƙarfi '' SHIBA ƊAN UWANA BANE!!" daga haka yabar wurin..da sauri Khalil yabi bayan Romo riƙe da sarƙarshi...Hajiya Hafsah tayi tsaye a wurin kamar an ɗasa ta..

'' kada Kiyi fushi Hajiya...lamarin yara sai a hankali!" Hajiya Ruƙayyah ta tausasa

'' kuma gashi Roman ɗin ya dawo gida lafiya lau kiyi haƙuri!" Hajiya Wareesha ta ƙara


'' dama shegen yaron da taurin rai...mai zai same shi? Mtchewww! dama ace ya karya koda yan ƙasusuwa ne!" Hajiya Momma ta faɗi hakan


Seraphina idonta suka ciko da hawaye ta haye sama da gudu tana kuka... Mukhtar yake murmushin ɓoye

'' gaskiya Farzan ya ƙetare iyaka wannan lokaci...'' inji Jawaad

'' ko? Nasan da cewa dukan mu Bama son Roman amma duk da haka shi jinin mune...idan Hajjo ko kawu mansir suka san cewa Farzan ya yi ƙoƙarin raunata Roman,zai fuskanci hukunci mai tsanani!" Inji Ayaan

'' Toh magulmata saura inji wani ya faɗi abinda ya faru..'' Hajiya Zeenatu ta kacace su da faɗa .. Hajiya Hafsah ta fara barin wurin cike da kunya kafin samarin suka zare jiki ɗaya bayan ɗaya

Suma ma'aikatan company'n sallamar su akayi..ya rage mu yan aiki muka shiga gyara wurin da aka ɓata


Tsofaffin yan aikin suna hira tsakaninsu bada gangan ba na samu kaina da saurare

'' da ace Yallaɓai Roman ne yayi ma yallaɓai Farzan ko wani daga cikin yan gidan haka,da sai inda ƙarfin hajiyoyin nan ya ƙare wurin ganin an hukunta shi!" Lateefa ta faɗa murya ƙasa

Hajar tace '' ai matan gidan nan munafukai ne, maraicin uwa a gida irin haka masifa ne abi a sakoka gaba yallaɓai Roman yana ban tausayi wallahi!" 

'' Toh ba yana da uba ba?" karima tayi tambayar


Suka ja tsaki kusan lokaci guda '' uban ai hoto ne kawai! shida babu duk ɗaya ne! " 

Ban iyarda sauraren maganganun suba na bar wurin tausayin Romo na kamani...tafiya nake banma san inda zani ba ko ɗakin shi ban sani ba da sai na shiga...ina wannan tunanin na kawo wurin wata corner a ƙarshen corridor naga wata ƙofa baƙa nan ma babu number sai XXXX uku 

Ina tsaka da tunanin ko nan ne ɗakin shi naga Khalil ya fito daga ciki...ɓoyewa nayi sai da naga tafiyar shi daga wurin da sauri na isa bakin ƙofar na ƙwanƙwasa babu amsa daga ciki
 Tura ƙofar nayi na shiga, parlor na ci karo dashi wanda painting ciki da kuma furnitures ɗin ruwan toka ne ƙamshin shi ya cika wurin..a ciki ɗakuna uku ne...ban san wane ne ɗakin shiba

Na tsakiyar na nufa naji ƙofar gam..sai na koma na gefen dama ina tura ƙofar ta buɗe

Leƙa kaina nayi na hange shi kwance saman gado yana kallon ceiling da alamu bacci yake duba da yanda ƙirjin shi ke sama da ƙasa...

Na shiga yanayi tsakanin in ƙarasa ciki ko in koma...daga ƙarshe na shiga ..ina tafiya a hankali har na iso bakin makeken gadon shi daya kasance baƙi kamar sauran abubuwan dake ɗakin duk da kuwa labule a sauke yake hakan ya ƙarama ɗakin duhu..wai shi komai nashi baƙi 

Wurin kanshi na tsaya ina leƙa kyakkyawar fuskarshi... zuciya tana tsananin bugu da ƙarfi...saye yake da baƙar riga data ƙara ma fatarshi haske gashin shi ya tarwatse saman pillow'n..hannu na miƙa zan gyara mashi blanket saboda akwai sanyi sosai

Buɗe idonshi yayi kamar zombie,na firgita..ya damƙo hannuna ya jawoni na faɗo gefenshi ya mulmula kaina...kamar sojan dake kwance a tanti amma yana lure kada a shammace shi da hari... zuciya ta takawo maƙoshi...idona suka fito kamar zasu faɗi ya sakar min nauyin shi ...yake kallona kamar zai yanka ni da idonshi.. fuskar shiba annuri

'' what're you doing here?" Muryarshi bata ɓoye fushin da yake ƙoƙarin dannewa ba

'' Uhmm......dubawa nake idan kana numfashi...na ɗauka ka mutu...'' that was an awful lie... fuskar shi ta ƙara duhu,hucinsa yake sauka a fuskata da mugun zafi,ya tsare ni da shegun idonshi kamar yana karantar abinda ke wakana a zuciya ta.. gashi na kasa numfashi saboda yanda yabi ya haye ni kamar nima gadon shine...shi ɗan abunda ban ce ba...



***

RU'UYAA…📖



₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta ***

Autumn writes 📖🖋️









Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.