Free chapter · Read without an account

THE FIRST TIER

by Maryam · THE THRONE OF THORNS

‎From the moment  suka tsoma ƙafar su cikin gurin wata heavy aura ta buge su.Tun daga reception ɗin suka fara gane cewa sabuwar duniya suka shigo.
‎
‎Jere su aka kuma yi kafin aka fara kwance su,da kwance musu abun idonsa.
‎
‎
‎Sai maimaita musu dokoki akeyi sannan aka kuma chage su in and out.
‎
‎
‎Gurin ya rabu gida uku da first tier, second tier sai third tier.Third tier shine the most dangerous place gaba ɗaya a gurin wanda ko waiters are not allowed to even go near it .
‎
‎
‎
‎Shiga sukayi cikin FIRST TIERbayan an duba tambarin dake jikin kayan su an gane staffs ne.
‎
‎Wani irin hayaƙi ne ya bugo hancin su na shisha.Ga mata da maza ana ta rawa.Yawanci ƴan side ɗin ƴan mata da samari ne.Wutar gurin sai canja colors takeyi.Faɗar irin dukiyar da aka narka a gurin nan ɓata lokaci ne.
‎
‎
‎Duk wani ko wasu manya-manyan models,ƴan Film,manyan mawaƙa da duk wasu shegu da ke jin su wasu ne zaka sane su a gurin.Dan kaf gurin babu ƙaramin dan iska Dan ba wanda zaka gani a first tier bai taɓa kisa ba.
‎
‎Direct ɓangaren abinci aka kaisu inda Maleeka ita giya zata dinga rabawa.Aikin su suka fara ko ɗago kai basa yi saboda tsoro.
‎
‎
‎Wani mutum ne zai kai wajen 40 yrs ko sama da haka, cikin waenda suka taho tare dasu Atti ne ya ke ƙoƙarin ɗora wata peppered soup akan center table ɗin wasu ƴan mata da suka zagaye wajen su biyar . Sai tafarfasa take a kan hot plate .Matan da suke zaune kamar wasu gangsters duk sarƙar kasa a ƙafar su da huda a harshen su sun saka mai wata mitsitsiyar barima, sai shan shisha suke da cocaine duk sunyi tatil.
‎
‎
‎Garin ya gyara wata suite case dake kan gurin gaba ɗaya hot soup ɗin ta ɓaro akan ƙafar sa,gaba ɗaya glass ɗin ya tawatwatse a gurin,nan da nan fatar ƙafar tashi ta kwashe,amma saboda firgita da yayi ko lura da zafin bai yi.
‎
‎Ɗurƙusa sawa yayi a gurin a razane ya na cewa "ma'am am very sorry" gaba ɗaya ya rasa mai zai ce ma sai maimaita abu ɗaya yake duk ya rikice.
‎
‎Jikin sa ne ya ɗau mazari kamar an jona mai socket sakamakon ganin wata a cikin su ta ɗago jajayen idon ta da suka nuna alamun bata hayyacin ta. 
‎
‎Nufo inda yake tayi tana zama a kujerar gurin tana mai alamar ya matso.Tabbas da ace a lokacin za'a duba jinin sa to ba ƙaramin hawa yayi ba, zuciyar sai bugun tara tara take.
‎
‎
‎Haka yabi ta cikin glass ɗin ya taka ya ƙarasa ya durƙusa a gaban ta.Fuskar sa sai ɗigar da zufa take duk da sanyin da gurin ya ɗauka na manya manyan AC dake zagaye a tier ɗin.
‎
‎Watsa mai firgitattun idanuwanya tayi,tana jawo rigar sa.Hannun ta tasa ta riqo gabar sa da yatsun ta guda biyu wanda suke ɗauke da wasu mugayen nails a jiki, tasa edge ɗin farcen nata tana zagaye bakinsa da shi kafin ta buɗe bakin cikin wata low dangerous voice tace "ya akayi ka ɓarar ehmm",bakin sai rawa yake ya kasa magana .
‎
‎Atti ce da tazo wucewa ta tsaya tana kallon abinda ke faruwa, cikin takaicin abinda yarinyar ke mai,dan tasan tabbas ya haife ta,ko bai haife ta baya girme ta sosai.
‎
‎Damƙar wuyan sa tayi cikin shammata tana buɗe bakin sa ta ɗauki ƙwalbar wata giya mai ƙarfin gaske tana kwankwada mai sai cije baki take.Bata tsaya ba sai da ta ga ya fita hayyacin da sai tari yake yana shiɗewa.
‎
‎Kallonsa tayi tana nuna mai ƙasa inda soup ɗin ya ɓare tana cewa "lashe ",zare ido Atti tayi tana nufar gurin,riqo hannunta akayi ta baya  tana juyowa taga ashe wannan yarinyar ce wacce suke zauna tare guri ɗaya.Yarinyar ce ta girgiza mata kai alamar kar taje,fasa zuwa tayi suka tsaya suna cigaba da kallon ya zata kaya.
‎
‎
‎
‎Tsugunnawa yayi ya fara lashe wa hawaye na ɗiga a idonsa,sai da ya lashe komai gaba ɗaya harshen sa yayi farfashe ya ƙoƙƙone.
‎
‎Ɗagowa yayi fuskarsa duk hawaye yace na gama muryarsa na rawa,nuna mai glass ɗin tayi da ido alamar wannan fah, hannu yasa ya fara tattarewa,sai daya kai wata zabgegiyar kwalba tukun tasa takalmin kafar ta irin manyan boot ɗin nan na ƴan ball tana murje hannun,rintse idonsa yayi saboda wata irin azaba da ya keji.
‎
‎
‎Kafin ta mai alama da ido ya cigaba,hannun sa na hagu ya sa ya cigaba har lokacin bata ɗauke kafar ta akan ɗaya hannun ba,jini sai bin gurin yake saboda kwalbar ta shige har ta hudo ta baya.
‎
‎Sai da ya gama tattare gurin ta ɗaga mai hannun amma ina tuni hannun ya tashi a aiki ya rabe biyu.Da hannu ta nuna mai hot plate ɗin alamar ya tafi da shi,durƙusawa yayi zai dauka kawai tasa hannu ta danne fuskar sa a kai.Wannan karan kam abin ya fi ƙarfin sa sai da ya saki wani uban ihu,amma bata bari ba sai da ta ga ba ya numfashi,wani irin ihu matan dake gurin suka ɗauka da kirari kafin ita kuma ta tashi tana wani bubbuɗawa,ta shige wani ɗaki.
‎
‎
‎Atti kam gaba ɗaya jikin ta sai rawa yake,yarinyar da take kusa da ita mai suna Ramlah kuwa sai kuka take.Kallon gurin Atti tayi yacce mutane ke behaving normally kamar ba ɗan Adam aka gama kashewa cikin tsantsar wulaƙanci da ƙas-ƙanci
‎
‎Ɗaya daga cikin masu tsaron gurin ne ya zo ya saɓe shi a kafa ɗa,gaba ɗaya naman fuskarsa ya zagwanye da aka ɗago shi, ba'a iya ganin komai sai ƙashin fuskar.......Wani ne yazo ya gansu a tsaye  gurin yace,are done with the FIRST TIER......
‎
‎
‎Saurin goge hawaye ta ramlah tayi tana giɗa kai kamar ƙadangaruwa..end of chapter 15........... written by Muraimaa Naabba ✍️✍️.....
‎
‎
‎

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.