Free chapter · Read without an account
MATAR GIDA PAGE 73
by Maimuna Bala · MATAR GIDA
MATAR GIDA BOOK 2
SHUUKRAN/022
YOTA ASSOCIATION
P73
Unaisa ta mayar da dubanta ga Anty Aisha kafin ta yi magana cikin muryar kuka ta ce ''baya sona Anty baya kaunata ko kallon fuskata baya son yi,na yi rashin lafiya na kwanta asibiti ko sau ɗaya bai zo ya duba ni ba a gaskiya Anty bazan iya ba'' ta kare magana cikin kuka ganin yadda take kuka yasa Anty Aisha tashi daga inda take ta je ta rungume ta shiga rarrashinta,saida ta yi mai isarta kafin daga bisani ta yi shiru ita dai Mama ƙasa magana ta yi sai kallonsu take zuciyarta cike da tunanuka iri daban daban,jiki babu kwari Unaisa ta yunƙura tare da fita daga ɗakin buta ta dauko ta wanke fuskarta daga haka ta koma ɗaki,bayan komawarta ɗaki waje ta samu ta zauna,bayan wasu ƴan mintina ta kwanta tana mayar da numfashi,Mama da Anty Aisha duk suka kalleta,numfasawa Mama ta yi kafin ta mayar da dubanta ga Unaisa ta ce ''yaya zaman ki da kishiyarki?" Unaisa bata ce komai sai Anty Aisha ta ari bakin Unaisa ta ce ''ina ganin babu matsala tsakanin su dan gaskiya matar tana da hankali'' Mama ta yi murmushi kawai alamar rashin gamsuwa da maganar Anty Aisha,ta ce ''haka dai ki ka ce'' Unaisa na daga kwance ta ce ''gaskiya ta faɗa maki Mama,Maman Sudais ba ta da matsalah'' shiru Mama ta yi kafin ta numfasa ta ce ''shikenan tun da haka ku ka ce amma abinda nake so ku fahimta shine kishiya dai kishiya ce'' Unaisa ta ce ''haka ne Mama'' gyara zama Mama ta yi kafin ta mayar da dubanta ga Unaisa fuskarta babu alamar wasa ta ce ''Unaisa'' Unaisa na daga kwance ta amsa Mama ta daura da ''kamar yadda Aisha ta faɗa maki kashe aure ba mafita bace abinda zan faɗa maki shine ki dage da addu'a ki daure kina tashi duk dare ki kai kukan ki ga Allah,ni ban san gidan Mallam ba ban san gidan boka ba,Allah da ma'aiki mahaifiyata ta nuna min komai girman damuwa Allah nake kaiwa kukana saboda haka abinda zan faɗa maki shine ki dage da addu'a Allah ya zaɓa maki abinda ya fi alkairi insha Allah za ki ga canji,sannan ki dage wajen yiwa cikin jikin ki addu'a Allah ya ba ki ƴaƴa masu albarka rayayyu shiryayyu ya kuma sauke ki lafiya,sannan ki roƙi Allah in da sauran zama tsakanin ku Allah ya karkato da hankalinsa gareki in kuma babu sauran Ubangiji ya haɗa kowa da rabonsa'' shiru Mama ta yi na wasu ƴan mintina kafin ta mayar da dubanta ga Unaisa ta ce ''ina son ki sani ko wanne namiji da yanayinsa ba iya maza ba har mu mata dukkanin da irin halittar da Allah ya yi mana wani yana da saurin sauka in ya yi fushi wani kuma yana daukan lokaci kafin ya sauko,saboda haka shawarar da zan ba ki shin ne ki ƙara dage wajen yiwa mijinki biyayya da sauke hakkinsa a kanki,sannan ki ƙara hakuri duk wacce kika gani gidan miji hakuri take saboda haka ki yi hakuri ki kuma ƙara hakuri,tsafta da ibadah da ki ka ce kina yi to ki ƙara kan wanda ki ke da,ki ƙara mayar da hankali wajen koyan girki'' shiru Mama ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta ce ''laifi na ne ki yi hakuri ki yafe min Unaisa'' Mama ta kare magana muryarta na rawa,da wani irin sauri Unaisa ta yunƙura ta tashi daga kwanciyar da take ta ƙaraso inda Mama ke zaune ta rusuna ta ce ''a'a Mama ba haka bane ƙaddara ce ba ki yi min laifin komai ba Mama'' murmushin takaici Mama ta yi ta ce ''da na ba ki irin tarbiyyar da na bawa Aisha baza ki shiga wata kungiya ba,za ki zauna gidan mijin ki lafiya kamar yadda Aisha ta zauna da mijinta lafiya,sama da shekaru sha bakwai ko sau ɗaya Aisha bata taɓa kawo ƙarar mijinta ba har ya koma ga Allah shima kuma haka bai taɓa kaiwa kowa ƙarar Aisha ba,tabbas laifi na ne Unaisa,son da nake maki ya rufe min ido yasa na ƙasa sauke nauyin da Allah ya daura min matsayin mahaifiyarki'' Mama ta faɗa tare da goge hawaye da gefen zani,Unaisa da Aisha suka yi shiru ko wacce da tunanin da take jiki babu kwari Mama ta yunƙura tare miƙewa tsaye ta fita daga ɗakin bayan fitar Mama Anty Aisha ta mayar da dubanta ga Unaisa ta ce ''kin ji abinda Mama ta faɗa maki dan Allah ki dauri ki yi amfani da shawarar da muka ba ki kuma zamu taya ki da addu'a'' a hankali Unaisa ta gyaɗa kai alamar to,karfe uku da wasu mintina Ɗalhatu ya dawo ya dauki Unaisa har cikin gidan ya shiga ya gaida Mama ya ajiye mata rafar ɗari biyar guda ɗaya Mama ta kalle kuɗin shiru sai kuma ta yi masa godiya,a hanyarsu ta komawa gida babu wanda ya yiwa wani magana ko kaɗan Unaisa bata son ganinsa a yadda ta shiryawa kanta bata so koma gidan sa ba yau kawai zata koma ne saboda Mama,bayan tafiyar Unaisa Anty Aisha da Mama suka ƙara tattauna kan batun zamantakewar Unaisa da Ɗalha ganin yadda Mama ta shiga damuwa sosai Anty Aisha ta danna nata damuwar ta shiga kwantarwa Mama da hankali inda ta cewa Mama duk bayan sati biyu zata riƙa tafiya gidan Unaisa tana dubata ko saboda ciki dake jikinta bai dace a barta ta yawaita tunani ba,sosai Mama ta ji dadin abin da Aisha ta faɗa tabbas Unaisa tana bukatar kulawa sosai,karfe takwas da wasu mintina na daren wannan ranar Mama ta kira ƙaninta Baffah Abdullahi wanda suke ciki ɗaya dake da zama garin Gombe Mama ce babba sai Baffah Abdullahi sai Babah Rabi,Baffah Abdullahi shine abokin shawarar Mama har da Babah Rabi mace ce amma Mama tafi samun kusanci da Baffah Abdullahi bayan sun gaisa ne Mama ta faɗa masa halin da Unaisa ke ciki gidan mijinta,Baffah ya ce shawarar da Mama ta bawa Unaisa shawara ce mai kyau sannan shima zai taya Unaisa addu'a,sosai Mama ta je dadi jin abinda Baffah Abdullahi ya faɗa daga haka suka yi sallama
Unaisa ce zaune cikin ɗakin fitarta kenan daga wanka,zaune take gaban madubi saman kujera tana shafe jikinta da body lotion Amirah ta shigo ɗakin bakinta dauke da sallama,amsa sallamar Unaisa ta yi tare da gyara zaman bathrope dake jikinta fuskar Amirah dauke da murmushi ta samu waje ta zauna,a hankali Unaisa ta yunƙura tare da miƙewa tsaye kanta babu ɗan kwali dogon sumarta ya sauko har tsakiyar bayanta zama ta yi bakin bed tana mayar da dubanta ga Amirah tare da faɗin ''barka da dare Maman Sudais'' Amirah ta faɗaɗa murmushi ta ce ''yauwa barkan ki dai Amarya ya ƙarfin jikin?" murmushi kawai Unaisa ta yi ba tare da ta ce komai ba,yan danne danne Amirah ta yi cikin wayarta ta fidda wasu hutona biyu ta miƙawa Unaisa ta na faɗin ''anko ɗin Nailah less 50k na uni,atamfa 25k na kamu'' sosai less da atamfar sun yiwa Unaisa kyau murya can ƙasa ta ce ''masha Allah sun yi kyau sosai yaushi za a yi bikin?" Amirah ta bata amsa ta ce ''next month ending (karshen wata me kamawa)'' gyara zama Unaisa ta yi fuskarta dauke da murmushi ta ce ''allah ya kaimu Ubangiji ya basu zaman lafiya'' Amirah ta amsa da ameen ta ce ''tashi za ki mu je mu faɗa masa ya bumu kuɗin tun yanzu mu bada ɗinki da wuri kar lokaci ya ƙore'' ta ƙare magana tana kallon Unaisa ɗan jimm Unaisa ta yi tana tunani can ta ce ''ina ganin ki je kawai ba sai na tafi ba'' baki buɗe Amirah ke kallon Unaisa can ta ce ''a'a ba za mu yi haka da ke ba tashi za ki yi muje ki karɓi naki na ƙarɓi nawa har ƙudin ɗinki fa zan tambaya kuma bani da gyale da zai shiga da zanin kin ga kuwa ina buƙatar sabbin gyalulluka'' ta ƙare magana tare da miƙewa tsaye tana nufar hanyar fita daga ɗakin,da ido Unaisa ta bita har ta kai kofar ɗakin Unaisa ta ce ''dan Allah Maman Sudais'' ki tambaya har da nawa sanyi nake ji ba zan iya fita ba'' Amirah ta buɗe baki da niyyar magana sai kuma ta fasa ta ce ''to babu damuwa Allah yasa ya bada da yawa'' Unaisa ta yi murmushi ta ce ''ameen'' Ɗalha na zaune ɗaki hannusa riƙe da waya sanye yake cikin riga da wando nigth wear Amirah ce ta shigo bakinta dauke da sallama a hankali ya ɗago ya kalleta tare da amsa sallamar fuskar Amirah dauke da murmushi ta je ta zauna daf da shi cikin kwantar da murya ta ce ''barka da hutawa Abban Sudais''ta faɗa tana wani shigewa jikinsa hankalin Ɗalha na kan waya ya ce ''yauwa barkan ki ya aka yi?" shiru ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta ce ''bikin Nailah ya ƙarato'' sai kuma ta yi shiru dan jin abinda zai ce amma sai ta ga ya yi shiru bai ce komai ba ganin bai da niyyar magana Amirah ta ce ''an fitar da anko Husnah ta tura min,ya yi kyau sosai'' ta faɗa tare da miƙo masa wayarta kamar ba zai ƙaraɓa sai kuma ya ƙarɓi wayar ya zubawa hutun less da atamfar ido bayan wasu sakanni ya ce ''ok sun yi kyau'' ya faɗa tare da miƙa mata wayar ƙarɓar wayar ta yi ta ce ''Allah yasa baza mu takura ka ba'' shiru ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta kwantar da murya ta ce ''75k kowacce zata buƙata kuɗin ankon'' ɗan jimm ta yi kafin ta daura da ''muna bukatar sabbin gyalulluka da takalma sai kuɗin ɗinki'' daga haka ta ja bakinta ta yi shiru bai tanka ba ya cigaba da abinda yake a waya sama da mintina biyar bai ce komai ba Amirah ta taɓe baki tare da miƙewa tsaye Ɗalha ya ce ''nawa ne gaba ɗaya kuɗin,komai da komai'' sai da ta saita nitsuwarta kafin ta ce ''kowacce zata buƙace 250k'' babu shiri Ɗalha ya ɗago tare da zuba mata idanunsa saurin kawar da kai ta yi bata yarda ta kallesa ba sai jin muryar sa ta yi ya ce ''me za ku yi da 250k?" Kai tsaye Amirah ta ce ''kuɗin ɗinki da takalma sai gyalulluka kuma da zamu yi liƙi za fa a yi kamu'' taɓe baki kawai Ɗalha ya yi kamar bazai ce komai ba sai kuma ya ce ''mata kun iya ba kanku wahala ankon dole ne baku da kayan da za ku sa ne? dole sai kun yi anko?" ita dai Amirah bata ce komai ba,hasalima wani waje daban take kallo kamar ba da ita yake magana ba,tana ji yana magana shi kaɗai amma taƙi tanka sa tana shirin magana ta ji ya ce ''ina shinkafa da salak ku ke ci wajen uni sai gulmar mazajenku bayan kun gama ku dauki selfie shikenan fa,shine zaku sa less ɗin 50k?" sosai ya ba Amirah dariya amma ta daure bata yi dariyar ba,ta haɗe fuska shi kuwa ya kafeta da ido yana jiran jin abinda zata faɗa,sun dauki sama da mintina uku haka can Amirah ta ji ya yi magana a ɗakile kamar wanda aka wa dole ya ce ''shikenan zan tura'' sai sannan ta yi murmushi kafin ta shiga jero masa godiya bai kula ta ba ya cigaba da danna wayarsa,washe gari misalin ƙarfe tara Unaisa na tsaye kitchen tana haɗa breakfast ta ji shigar saƙo wayarta,wayarta dake daure kan kitchen island ta dauko ta duba ta ga saƙon kuɗi ne 250k daga Ɗalha ba tare da ɓata lokaci ba ta kira layin Ɗalha wayar har ta ƙasa bai ɗaga ba nan ta sake kira amma bai ɗaga ba hakan yasa ta ajiye wayar ta cigaba da abinda ta ke
SHUUKRAN