Free chapter · Read without an account
Page 3
CHINA - GUANGZHOU
A cikin babbar masana'antar kera motocin alfarma ta "MUHAMMAD ELITE AUTOMOBILES GROUP - CHINA BRANCH", wata masana'anta da ta shahara a duniya wajen kera manyan motoci irin su Rolls Royce Phantom da Maybach da aka yi customizing dinsu ga sarakuna da manyan attajirai na kasashen Larabawa. Masana'antar tana da ma'aikata sama da dubu goma, kuma tana fitar da motoci zuwa kasashe 40 na duniya.
A bene na 88 na katafaren ginin masana'antar, wanda aka yi shi da gilashi mai sheki, yana kallon dukkan birnin Guangzhou, wani ofis ne. aljanna nan duniya. Katon ofis ne wanda tsawonsa ya kai kusan gidan kwana uku, an lullube kasan shi da carpet mai taushi launin toka-toka daga kamfanin *Royal Persian*. A tsakiya akwai wata katon tebur mai sheki da aka yi da itacen Black Ebony daga dajin Africa, farashin teburin kadai ya kai dala dubu hamsin.
Daga bayan teburin, taga mai fadin mita 10 ta bude tana nuna hasken rana da ke fadowa kan birnin. Labulen tagan an yi su ne da siliki mai tsada daga Italiya.
Tsaye a jikin tagan, wani mutum ne.
*HAMMAMUHAMMAD GADDAFI GWARAM.*
Sanye yake cikin Bakar Suit mai tsada na kamfanin "Ermenegildo Zegna - Italian Bespoke", wanda farashinsa ya kai dala dubu goma sha biyar. Rigan ciki kuwa fari ce tas, mai kyalli, ta Tom Ford. Madaurin wuya kuma -baki ne na Hermès, an daure shi da kwarewa. Takalman kafarsa kuwa na kamfanin Berluti - Alessandro Patina Leather Oxfords ne, bakake masu sheki, farashin su dala dubu uku. A hannun hagunsa kuwa akwai agogo mai tsadar gaske, agogon Patek Philippe Grandmaster Chime, agogon da duniya baki daya babu guda 7, farashinsa ya kai dala miliyan biyu da dubu dari biyu. Agogo ne da ke dauke da lu'u-lu'u 20 a gefe.
Gaba daya hannayen shi na cikin aljihun wandon suit din shi, yana kallon window, kunnensa makale da Bluetooth na *AirPods Pro Max* baki. Yayi nisa a duniyar tunani. Tun daga bayansa zaka san Allah yayi kyakkyawar halitta.
Mutum ne mai kirji mai fadi, wanda ko da suit din a jikinsa, ka kan ga tsokar kirjinshi ya cika wajen. Wuyansa a miqe yake, ga wani irin kyakkyawan wuya da Allah ya bashi. Fuskarsa... Ya Allah! Fuskarsa wani irin kyau ne da idan mace ta ganshi sai ta manta da sunanta.
Fatar jikinsa ba ta da haske sosai, chocolate color ne, launin da mata ke mutuwa akai., jikinsa a tsare yake. Cikinsa kuwa a shafe yake, kuma daga cikin rigar zaka ga wani 6-pack da ya fito ya cika riga, yana sheki saboda yana yawan zuwa gym.
Gashin kansa, sai saye ne da gyaran fuska wanda ya sake kawata fuskan shi, Yana da dogon hanci mai kyau, gira kuwa cikakke ne kamar an gyara ta da pen. Idanunsa wani abin kallo ne. Manyan idanu ne, farare tas kamar madara, sai dai akwai wani lokaci idan ya shiga damuwa su kan koma ja-jajir, kamar wuta.
Lips dinsa na sama suna da duhu kadan, na kasa kuma sunyi ruwan hoda, masu taushi da sheki pink.
Gefen teburin, wayarsa iPhone 18 Pro Max - Titanium Black Edition ta ke ta ruri, cikin wani irin sauti mai dadi na ringtone na Larabci. Amma saboda nisan da yayi a duniyar tunani, bai ji ba. Sai gab da zata yanke ne ya dawo daga duniyar tunanin, ya juya da sauri ya dauki wayar.
A daya bangaren, cikin muryar damuwa, Salim ya yi sallama.
"Assalamu Alaikum, Hamma Muhammad barka da warhaka..."
Shiru. Kusan minti biyar babu amsa. Wayar na kunnen Salim, sai dai shiru kake ji, kamar ta yanke.
Salim ya ciro wayar ya duba, yana tunanin wayar ta yanke, amma sai ya ga har yanzu tana aiki. Ya sake kaiwa kunnensa.
"Hamma? Hamma kana jina?"
Sai can, cikin wata irin murya mai sanyi da nauyi, kamar murya daga karkashin kasa, wacce ke dauke da wani irin iko da zai iya girgiza zuciya, Hamma Muhammad yace:
"Barka dai na gaban goshin tsohuwa..."
Ya karasa maganar cikin muryan shi mai cike da izza,
Salim kuwa sai da ya saki wani irin murmushi mai sauti, duk da damuwar da yake ciki, yana mamakin halin Hamman nashi. Yace, "Hamma ai kai ne mafi soyuwa a wajen Hajiya Kaka, duk cikin family nan babu wanda ta fi so kamar kai."
Hamma Muhammad bai amsa ba. Shiru yayi na wani lokaci, kafin yace, "Ya kake? Ina fatan mutanen gidan kowa yana lafiya?"
Cikin sanyin murya Salim yace, "Lafiya lau Hamma Muhammad."
Sai Hamma Muhammad ya sake yin shiru,, mai nauyi. Sai ya sake cewa, "Me yake faruwa Salim? Ko jikin Baba ne ya tashi?"
Salim ya dan yi shiru, ya hadiye wani abu a makogwaronsa, yace, "Aa Hamma kawai dai..."
Cikin kosawa da gajiyawa, Hamma Muhammad yace, "Kawai me...? Kayi magana mana, Salim!"
Salim ya ja wani irin numfashi mai nauyi, yace, "Hamma Jazzeelah ne..."
Da jin sunan nan JAZZEELAH, wani irin dokawa kirjin Hamma Muhammad yayi. Dukan mai karfi gaske har sai da ya kai hannu ya dafa baki daya desk din da ke gabansa, yana kokarin kar ya fadi. Idanunsa da suke farare tas sun fara canzawa a hankali suna komawa jajir.
Cikin kokawa da numfashi, duk da a zahiri mutum ba zai iya fahimtar halin da yake ciki ba saboda ya boye shi da kwarewa, yace, "Me ya same ta?"
Cikin jan numfashi da wani irin rauni da kuka, Salim yace, "Hamma Aunty Jazzeelah... c..i..ki gare ta..."
Wani irin sake dokawa kirjinshi yayi, fiye da tunanin mai sauraro. Zuciyarsa ta buga da karfi kamar zata fito ta fasa kirji. Yace, "Ban ji me kace min ba, ko zaka sake fada idan ba damuwa..."
A wancan bangaren, Salim zuciyarsa ta karye. Wani irin kuka mai zafi ya zo masa, hawaye masu zafi suka zubo masa a fuska. Yace da karfi, "Hamma Muhammad! Aunty Jazzeelah ciki gare ta! Kuma ta kasa fadin ko na waye! Hamma Aunty Jazzeelah na cikin wani hali! Dan Allah ka dawo gida!"
Sauke wayar kawai Hamma Muhammad yayi daga kunnensa. Bai kashe ba, wayar na hannunsa.
Kafafuwansa sun kasa daukar sa.
Wani irin sarawa kansa yayi, yana jin kwakwalwarsa na juyawa. Ya rike kansa da tsananin karfi, yana sake wani irin kara, kara wanda Salim ya jiyo ta waya kamar zata fasa masa kunne, kara na ciwo da takaici da haushi da suka hade wuri daya.
A daya bangaren, wani irin faduwa kirjin Salim yayi, yana kiran, "Hamma! Dan Allah ka dawo! Ka da ka bari ciwonka ya tashi! Hamma!"
Amma Hamma Muhammad baya jin komai.