Free chapter · Read without an account
THE TWO WIVES
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER NINETY FIVE:95*
*THE TWO WIVES*
*JIDDAAH BARKUM*
———
Hajiya Balaraba ta kalleta, “Ohh… ita ce sister ɗin naki?” Bintu ta yi shiru, jikinta ya gama la’asar da ganin reaction ɗin Mommy ɗinta, sai kawai ta gyada kai, Hajiya Balaraba ta amsa kai tsaye, “Ehh, tana da kishiya, kuma ita Raihanan ce ayy,” ta ɗan tsaya, sannan ta kalleta, “Ku bakusan wa ta aura ba kenan?” Bintu ta haɗiye yawu, “Munsani… amma ban san shi ne mijin Anty Seeyama ba,” Hajiya Balaraba ta jinjina kai a hankali, “Toh… shi ne,” Bintu dai ta yi muƙus, ta kasa cewa komai, sai kawai ta zauna tana kallon Mommy ɗinta, zuciyarta na ƙara ɗaukar wani irin yanayi da ita kanta ba ta san dalili ba.
Haka Seeyama ta ƙarasa laƙe-laƙen ta, daga ƙarshe ta fito daga ɗakin, ko kallon gadon da ta tashi a kai ma ba ta yi ba, bare ta gyara, kai tsaye ta fito falon, inda Zayd ke zaune yana jiranta, ta fito tana cika tana ɓatsewa, ta durƙusa ta kwashe used bottles ɗin da suke wajen, ta je bin ta yi discarding ɗin su, sannan ta dawo ta kwashe pillows ɗin ta watsa kan sofa, daga ƙarshe ta ɗauki plate ɗin da ya kwana a wajen, ta nufi kitchen, Zayd na kallonta, bai ce mata kala ba, ita ma haka, bata yi wani yunƙurin wahalar da kanta ba, kamar yadda take faɗa, ita ba yar wahala ba ce, ta buɗe fridge ɗin kawai, ta ɗauko potato porridge ɗin da ta yi ordering jiya ta ajiye, ta ƙarasa wajen warming ɗin, sai da ta yi kacha-kacha da wajen, kamar a lokacin ne take dafa abincin, ba wai dumamawa zatayi ba, ba wani arrangement, nothing, kawai ta ɗauki plate ta jibga abincin a kai, ta ɗora wani spoon a gefen plate ɗin, duk abincin ya baci a kan plate ɗin, ba ta yi tunanin ta kintsa shi ba ko kaɗan, a matsayinta na matar da take serving mijinta, especially as a newlywed woman, ta ɗauko plate ɗin ta nufi falon, fuskar nan a bala’in haɗe, ta je ta dungura plate ɗin a kan stool ɗin gefen kujerar Zayd, sannan ta juya, ta nufi kitchen ɗin, tana shirin ta haɗo nata.
Zayd ya kalli abincin, sannan ya ɗaga idanunsa ya kalli Seeyama wadda ta kusa shiga kitchen, “Hey, excuse me,” ya faɗa da wata murya da kawai za ka ji ka san yana ƙoƙarin controlling himself daga anger ɗin da ke tasowa a hankali, Seeyama ta juyo, amma ba ta ƙaraso ba, kawai ta tsaya a wajen, “Waye kika ajiyewa wannan abun?” ya tambayeta, Seeyama ta ɗan turo baki, kamar tambayar ma ba ta da wani muhimmanci, “Naka ne mana, ba ka ce na haɗa breakfast ba?” Zayd ya lumshe idanunsa, ya ɗan yi shiru, yana ƙoƙarin ganin fushin da ke tasowa a cikinsa bai rinjaye shi ba, a hankali ya buɗe idanunsa, ya kalleta, “Okay…” Ya yi ɗan pause, “Ina nata abincin?” Seeyama ta ɗaga gira, ta kalleshi cikin wani irin kallon da ya yi kama da wanda aka zo daidai inda take so, cike da confidence ta ce, “Wa ke nan?” Zayd ya yi shiru na ɗan lokaci, ya kalleta kawai, kamar har yanzu yana ƙoƙarin tabbatar da cewa da gaske ita ce take magana da shi haka, daga ƙarshe ya ce a hankali, “Nace miki ki haɗa breakfast for everyone, ko?” Ta jinjina kai da confidence, “Ehh, kuma abinda na yi kenan, tunda ni da kai ne a gidan,” Zayd ya sake jin ransa na baci, amma ya daure, ya sauke numfashi a hankali, sannan ya ce, “Ki je ki zuba mata nata, ki kawo min,” Seeyama ta sake kankance idanunta, “Kanata cewa na zuba maka nata?” Ta ɗan yi tsaki, “Wai wace ita? Wannan shafaffiyar da man da ba za ka iya faɗin sunanta ba?”
Zayd ya yi shiru, kawai ya kalleta, kallon da ya cika da mamakin irin uban rainin da ta masa cikin dare ɗaya, ya kasa fahimtar yadda ta iya juya simple instruction ɗinsa zuwa irin wannan gardamar, ya buɗe baki zai yi magana, amma kafin ya ce komai, Seeyama ta riga ta juya, “Tunda baka da abin faɗa, shikenan…” Ta faɗa tana gunguni a ƙarƙashin numfashinta, sannan ta shige kitchen ɗin, ta bar Zayd a zaune a wajen, shi kuwa ya ci gaba da kallon bayanta na wasu seconds, fuskarsa ta kasance calm, amma wannan karon, haƙurinsa ya fara samun testing sosai, kawai sai ya miƙe, ya ɗauki plate ɗin da ta ajiye da abincin, ya nufi ƙofar fita, ya fice daga part ɗin completely.
Seeyama ta leka ta gefen ƙofa, da ta ga ya ɗauki abincin ya fice, ai kuwa sai ta fito da sauri ta bi bayansa, amma kafin ta ƙaraso, ya riga ya bace, cikin sassarfa ta ƙarasa bakin ƙofar part ɗin Raihana, shi kuwa, da ya shiga, sai ya tarar da Raihana wadda yunwa ta kusa ta halaka, kwance a kan doguwar sofa, idanunta a lumshe suke, hannunta ɗaya a kan cikinta, wayarta na gefenta tana haske, amma da yake a silent take, babu wani sound, Zayd ya tsaya kanta yana kallonta, fuskarta tayi fayauu, kitson da akayi mata ya yi kanana kamar ba da hannu aka yi shi ba, ɗa veil ɗin dake kanta ya sauka kan hannun kujerar, fuskarta ta yi haske, ga nan pink lips ɗinta ɗan mitsili, kamar yana motsi ne a duk numfashin da ta sauke, ya tsaya yana kallonta na wasu seconds, kafin ya yi wani yunƙuri, BAM! Seeyama ta banko ƙofar ta shigo.
Ta tsaya cak, tana kallonsa, a tsaye a kan Raihana da plate din a hannunsa, sannan idanunta suka sauka kan Raihana wadda ke bacci a nutse, Raihana data ji kamar inuwar mutum a kanta, a hankali ta buɗe idanunta, sai ta ga mutum a tsaye a gabanta, ta ɗan ɗaga kanta, Seeyama ta ƙaraso, tana kallon Zayd da plate ɗin da yake riƙe da shi, sannan ta juya ta fara kallon Raihana wadda ta riga ta tashi zaune, itama nan ta fara kallon ikon Allah, Seeyama ta fara kare wa Raihana kallo from head to toe, zuciyarta kuwa… ba wani azababben bugu kawai take yi ba, wani bala’in kishi ne ya taso a cikinta wanda ita kanta ba ta san tana yi ba, ashe duk da ba kishi take ba… yanzu ne kishin na gaske, gasken ya taso, har ta ji kamar huhunta ba zai iya ba ta iskar da take buƙata ba, ta taɓa ganin Raihana a lokacin da aka watsa hotunansu da Zayd, ta san yarinyar ta haɗu, amma ba ta san haka take a zahiri ba, Raihana ma ta bi ta da kallo daga inda take zaune, ta haɗe rai, ta na kare mata kallo daga sama har ƙasa, sannan ta tabe baki, duk da ba ta taɓa ganinta ba, kallo ɗaya ya isa ta gane ta, ta yi wani ɗan ƙwafa a ranta, sannan cikin sanyin murya ta ce, “Ya za ki shigo min ɗaki ba sallama ba, ba neman izini? Ko ba ki san nan ɗin ɗakin matar aure ba ne?” Ta ɗan karkatar da kanta, “Idan da kinyi mummunan ganin da zai makantar da ke fa?” Ta sa hannu ta sosa wuya, kanta a karkace, tana kallon Seeyama directly in the eyes, “Next time, try to ask for permission before barging into someone’s private space.”
Zayd ya yi difff, daga inda yake tsaye, plate ɗin abinci a hannunsa, yana kallon Raihana kamar bai taɓa ganinta ba, Seeyama ta buɗe baki, amma ta kasa magana, sai ta dubi Zayd, “Babe, you saw that, right? Look at what you’ve brought upon me!” Ta nuna Raihana da hannu, “Wata yar iska da ko a matsayin maid ɗina ba zan ɗauke ta ba, ta tsaya tana faɗa min magana a gabanka!” Ta ƙara cike da haushi, “Toh ba dole ba na zuba mata abinci, ka ɗauko zaka kawo mata, ita uban waye ya hana ta dafa nata?” Ta ɗan yi tsaki, “Ko kuma ni kaɗai da ka tsana ka saka dole sai na yi girki, ita sai dai ka nemo mata kenan abinda za ta ci?” Zayd ya daka mata tsawa, “Seeyama!” Seeyama ta zabura, amma ba ta matsa ba, kawai ta tsaya tana kallonsa da wani irin kallo, Raihana kuwa ta yi shiru, ta miƙe a hankali, ta ɗauki wayarta, ta yi niyyar wucewa ta gefe, amma Seeyama ta wani janyo ta baya, Raihana ta sa hannu ta kabe hannun Seeyama daga jikinta nan take, tana watsa mata wani shegen kallo, kamar tana cewa baki da hankali amma koh? Sannan cikin wata murya mai cike da gargadi ta ce, “Kar ki ƙara kuskuren sake taɓa ni,” ta ɗan kalleta kai tsaye, “Ba ni da lokacin shirmenki,” daga nan ba ta sake kallon kowa a cikinsu ba, ta wuce abinta.
Zayd ya kalli Seeyama bayan bacewar Raihana gabaɗaya, ya rasa haƙurin shi, “Ki na da hankali? Waye ya ba ki izinin shigowa nan?” Ta matsa baya saboda ganin irin mugun kallon da yake watsa mata, ta fara magana cikin ɗan rawar murya, “Toh ba abinci na kawo maka ba, ka ɗauka zaka ba wa matar so, ai dole na bi ka, tunda ni ka hana a kawo min mai taimaka min na gama wahalar haɗa abun, ka ɗauko ka kawo mata, ita ɗin kuturwa ce ne sannan—” “Shut your fucking mouth right there!” Ya daka mata tsawa, Seeyama ta sake ja baya, tana zaro ido, Zayd ya ajiye abincin a stool ɗin wajen, sannan ya juya ya ci gaba da magana cikin ɓacin ran da yake dannewa tun ɗazu, “Ki na da hankali? Kinsan abinda kike faɗa? Idan kin ba ni abinci na kawo mata, does that warrant you following me here and talking to me like this?” Haka Seeyama ta haɗe rai, ta watsa masa wani kallo, sannan cikin ɗan rawar murya ta fara magana, “Toh kai ka yi adalci ne da zaka ɗauko abincina ka kawo mata bayan kai na ba wa—” Zayd ya ɗaga hannunsa, ya katse ta, ranshi ya gama ɓaci, shi ba gwanin doguwar magana ba ne, kuma wallahi wannan abin har ya saka masa ciwon kai, yana so ya yi mata magana, amma ya ma rasa perfect words da zai yi amfani da su wajen bayyana mata irin rashin hankalin da take yi, Seeyama ta fara kamar za ta yi kuka, “Ai kana sane amma—” Cikin tsawa ya katse ta, “Seeyama, you must be very stupid, fita ki ba ni waje!” Wallahi kawai a ƙofar ɗakin ta gan ta, ba ta taɓa jin muryar Zayd ta ɗaga haka ba.
Ta buɗe ƙofar da sauri, amma a daidai lokacin Suhaila ma ta turo kai cikin ɗakin, nan ta tsaya, tana kallon Suhaila a wulakance, ita kuma Suhaila fuskarta ɗauke da murmushinta, Seeyama ta kalli Suhaila, wacce ke ɗauke da basket na food warmers, abinci ne Ummie ta ce a kawo wa Raihana, ta san baƙuwa ce a gidan, kafin ta sake a gidan, ta ɗora nata, ta dauke kallonta daga basket din, ta dawo dashi a kan fuskar Suhaila, sannan ta ja wani uban tsaki, “Bundle of hypocrite,” ta faɗa a hankali, kafin ta tabe baki ta wuce ta na bangaje Suhaila, murmushin Suhaila ya ɗauke nan take, ta bi bayan Seeyama wacce ta wuce fuuuu, kamar zata tashi sama, Suhaila ta tabe baki, sannan ta shigo ciki, Zayd na tsaye a inda ya tsaya, duk da kasancewarsa mutum ne da ba zaka iya karanta yanayinsa nan take ba, amma idan ka kalle shi a wannan lokacin, zaka san ya kai maƙura wajen ɓacin rai, Suhaila ta shigo ta ajiye basket ɗin, sannan ta kalleshi, a sanyaye ta kirashi, “Akhie..” A hankali ya ɗaga idanunsa ya kalleta shi ma, amma bai ce komai ba, ta ɗan tsaya na wasu seconds kafin ta ƙaraso wajensa, “What happened?” Zayd ya ɗan lumshe idanunsa, “Nothing,” “Bari na mata magana,” daga nan ya juya ya wuce, ya nufi hanyar da za ta sadashi da ɗakin Raihana, Suhaila ta bi bayansa da kallo, har ya ɓace daga gabanta, a sanyaye ta koma kan sofa ta zauna, sai kuma ta tuna da Sameer da suka zo tare, tun farko ita kaɗai za ta zo, amma da Sameer ya ce nan zai zo, Zayd ya aike shi ya siyo kayan abinci, sai tace su taho tare, sai da suka biya suka yi siyayyar, sannan suka karaso gidan, sai ta tashi ta fita ta masa magana kan ya shigo da kayan, haka kuwa aka yi, ya jibge su tsaff a store ɗin.
Raihana na kwance rub da ciki a kan gadon, ranta a masifar dagule, ba wai iya ganin Seeyama ne ya rikita ta ba, wato shi har da zuwa wajenta ya ci abinci, ita kuma ya barta da yunwa, sannan at last ya ɗauko wai gantalallen ragowar dankali ya kawo mata, bata san sanda hawaye ya zubo mata ba, kuma she’s sure ta san ba wai a kan wannan ne take kukan ba, amma kuma still, bata san ainihin dalilin hawayen ba, a hankali Zayd ya tura ƙofar, ya tsaya na wasu seconds yana kallonta, taji an taɓa ƙofar, amma ta ƙi juyawa, sai kawai ta sa hannu ɗaya tana share hawayen da suka zubo mata, dama luckily, ta juya wa ƙofar baya ne, a hankali ya ƙaraso wajen gadon, ya tsaya a gabanta yana kallonta, ita kuma da ta fahimci ya zo, ta maza ta runtse idanunta, kamar mai bacci, ya san idanunta biyu ne a rufe, ya ga lokacin da hannunta ya motsa ya kai fuskarta, tana share hawaye, saboda haka kawai sai ya yi tsaye yana kallonta, calmly yace, “Stand up, ki je ki yi breakfast,” Raihana ta ji wani malolon baƙin ciki ya tokare mata maƙogwaro, ashe ya san ba ta yi breakfast ɗin ba ma kenan? Har zata cigaba da pretending tana bacci, amma ganin ya raina mata wayo, wai ta je ta yi breakfast da wannan gantalallen abincin da ko arzikin murfi babu, sai ta buɗe idanunta, ta tashi a hankali, ta janyo veil din dake kan pillow ta rufe kanta, sannan ta mike tana son ta bar wajen ma ta kyale shi, amma da ta zo za ta gifta shi, sai ya sa hannu ya riƙo damtsen hannunta, ya dawo da ita gabansa, ya tsaya yana kallonta, ita kuma ta ƙi yarda ta kalleshi, ta fara saka hannunta ɗayan, tana ƙoƙarin janye hannunta daga riƙon da yake mata, amma ta yi tayi ya ƙi sakinta, a hankali ta ɗago kanta ta kalleshi, sai kuma ta janye idanunta da sauri, ganin irin kallon da yake mata kamar wanda bai taɓa ganin ta ba sai yau, zuciyarta na bala’in bugawa, amma ta dake, muryarta ta fito a hankali, sai ta fara magana a tsintsinke, “Ka cika ni… ni bana cin abincin Azumi nake.”