Free chapter · Read without an account

024

by Kansa'u Bello · MEERAH

*MEERAH*

     *024*


    Sai da ya gama shan ƙamshinsa sannan ya ɗago ya kalle ni yace.

   "Baki gaji da riƙon kayan bane hala?." Ya yi maganar yana zube min duka idanunsa a saman fuskata, hawayen da suka ciko min ido na daure na mayar da su da ƙyar sannan na ajiye kayan na juya da nufin tafiya ya dakatar da ni.

   Ji nake tamkar na masa dukan tsiya ko zan huce takaicin da ya shaƙa min, amma sai dai babu damar hakan. Dole na matsa kusa da shi na ajiye farantin a saman table ɗin dake gabansa.

  Ina ajiye wa na miƙe da niyyar tafiya a karo na biyu ya kuma dakatar dani ta hanyar bani umarnin zuba masa, tsuguna wa na yi na fara zuba masa kira ya shigo cikin wayata. Ni da shi a tare muka sauke ido a kan wayar da na ajiye saman table ɗin lokacin da nake ƙoƙarin zuba masa Coffee ɗin.

   Sunan Nawaz da nayi saving da alamar heart ya ɗauki hankalin Ajmal har sai da ya dakata da abinda yake yi ya tsayar da idonsa a kan wayar. Hannu na saka na latse wayar haskenta ya ɗauke sannan na kammala zuba masa na miƙe na fice a ɗakin cikin sauri.

****** Da wani irin kallo Ajmal ya bi bayanta, sunan da ya gani yana kiran nata na masa kai-kawo a cikin zuciyarsa. 

   Ji ya yi kan nasa na ƙara yi masa nauyi don haka ya ɗauki Coffee ɗin da ta zuba masa ya yi masa zuƙa ɗaya ya miƙe ya shige bedroom ba tare da ya ɗauke ko laptop ɗin tasa ba.

   Yana shiga bathroom ya nufa ya sakar ma kansa shower, ya jima ruwa na sauka a kansa sannan ya kashe ya ɗauki rigar wanka ya ɗaura ya fito. 

   Da ƙyar ya iya ɗaukar Paracetamol ya sha sannan ya haye gadonsa ya kwanta yana jin yanda zazzaɓi ke saukar masa. 

   Idanunsa ya lumshe yana jin zuciyarsa a ƙuntace, ga wani irin nauyi da kansa ya masa, bai san lokacin da wani wahalallen bacci ya ɗauke shi ba.


*Meerah....*

   Sai da na tabbatar na gama fice wa daga ɓangaren baki ɗaya sannan na dakata ina sauke ajiyar zuciya, don irin kallon da naga yana bina da shi lokacin da kiran Nawaz ya shigo min sai da ya kayar min da gaba.

  "Mutum sai baƙin halin tsiya." Na furta a hankali sannan na juya na nufi ɓangaren mu. Ban samu kowa a Palour ba don haka na saye sama, sai da na zauna a saman gado na sannan na kira Nawaz.

   Haƙuri na bashi a kan rashin amsa kiransa da ban yi ba, na sanar masa ina yin aiki ne.

   "Kar ki damu, dama na kira ne naji su Yaya sun sauka lafiya." Nawaz ya faɗa cikin sanyin murya.

   "Lafiya lau Alhamdulillah." Na bashi amsa. Hira muka ɗan taɓa ina tambayar sa su Umma da su Raihana, da kuma jikin Abba, amsa min ya yi da cewa.

   "Umma dasu Raihana suna lafiya, Abba kuma jiki sai godiyar Allah." Addu'ar samun sauƙi na masa ya amsa kafin ya min sallama a kan zai wuce filin Ball ne. 

  Addu'a na yi masa nima na ajiye wayar na sauka ƙasa don na san zuwa yanzu Momy suna Kitchen suna aikin abincin dare ita da Bintu.

   Koda naje ɗin kuwa na same su har sun kusa kammala wa, don haka na shiga taimaka musu da abinda ya rage har muka kammala, kafin kowa ya shige ɗakinsa saboda an kusa kiran sallar magrib.


 *Ajmal....*

   Tunda ya kwanta bacci ya ɗauke shi bai farka ba har sai da Sultan ya dawo daga hirarsa, ya shigo bedroom ɗin nasa ya same sa kwance yana bacci. Mamaki ya yi sosai domin kuwa ya tabbatar cewa ba lafiya ba, don Ajmal ɗin baya bacci a irin wannan lokacin.

   Zama ya yi a bakin gadon ya shiga kiran sunansa, a hankali ya buɗe idanunsa da suka yi masa nauyi sosai ya sauke su a kan Sultan ɗin da ya zuba masa ido.

   "Lafiya kuwa Man, neke damunka ne?." Sultan ya tambaye shi cike da kulawa. 

  Kansa dake sara masa ya dafe yana lumshe ido har sai da ya lafa masa sannan ya iya bawa Sultan amsa da cewa.

   "Ciwon kai ne kawai kuma na sha magani, ban ma san bacci ya ɗauke ni ba."

   "Sorry Bro, Allah ya sauwaƙa, yanzu ka tashi kayi alwala mu wuce Masjid time ya kusa." Sultan ya faɗa yana miƙewa don zuwa ya ɗauro alwala.

   "Okay." Kawai Ajmal ya faɗa a taƙaice yana ƙara dafe kansa. Fita Sultan ya yi ya nufi nasa bedroom ɗin da tunanin abinda ke damun ɗan'uwan nasa.

  **** Bayan fitar Sultan ya ɗan jima a zaune kafin ya iya miƙe wa ya nufi bayi, wanka ya ƙara yi don ya samu jikinsa ya sake kafin ya ɗaura alwala ya fito. Jallabiya kawai ya iya saka wa saboda lokaci da ya kusa ƙure wa, don ana gab da tayar da sallah. 

   Yana fitowa ya samu Sultan na jiransa, don haka wuce wa kawai suka yi. Basu dawo gida ba sai da aka yi sallar isha'i, don bayan idar da sallar magrib kwanciya Ajmal ya yi yana sauraren karatun Alkur'ani da aka saka.

    har sai da lokacin isha'i ya yi aka gabatar da sallah sannan suka wuce gida tare da ƙannen su gaba ɗaya.

   Kai tsaye ɓangaren Momy suka nufa don cin abincin dare kamar yanda suka saba, lokacin da suka shiga sun samu babu kowa a Palon duk sun shige sallah, sai ƙatuwar tv plasma dake kunne an saka karatun Alkur'ani a tashar sunnah tv.

   Zama suka yi Sultan ya ɗauki remote ya sauya channel zuwa na wasanni don akwai wasan da yake son kallo.

  Gaba ɗaya hankalin samarin ya koma kan wasan da ake bugawa tsakanin Real madrid da Manchester united, yayinda kowa ke buri da fatan team ɗinsa ne zai yi nasara.

   Duk wannan abin dake faruwa Ajmal na kwance saman doguwar kujera, idanunsa a lumshe ya yi nisa a cikin tunani. Ga ciwon kan da ya takura masa, don zuwa yanzu har da zazzaɓi ne ya saukar masa.

   Duk ihun da su Aryan ke yi kasancewar sune kan gaba a wasan bai saka ya buɗe ido ya kalle su ba, Sultan da hankalinsa ke rabe a kan sa ne ya matso kusa da shi yana cewa.

  "Man ko dai na kira Doctor yazo ya duba ka ne?." Ya ƙare maganar dai-dai lokacin da Momy ke ƙarasowa inda suke.

   "A'a Son ciwon kan ne bai sauka ba har yanzu kuma baka yi magana an kira maka Doctor ba?." Ta ƙare maganar tana kallon Ajmal da kulawa sosai.

   "Wallahi kuwa Momy, nima a haka na dawo na same sa a kwance. Nace na kira masa Doctor yace baya buƙata, gashi kuma da alama ciwon kan ya takura masa sosai." Sultan ya bawa Momy amsa muryarsa ɗauke da damuwa.

   Kallon Momy Ajmal ya yi cike da girmamawa, da soyayyar uwa da yake mata yace.

   "Kar hankalinki ya tashi Momy, ciwon kai ne kawai kuma da sauƙi ma." 

   "Ina fa kawai a ciwon kai Ajmal, bari dai a kira Doctor yazo ya duba ka." Ta ƙare maganar tana mayar da kallonta ga Sultan tace.

   "Sultan kira min Doctor yazo ya duba min shi." 

   "Okay Momy." Sultan ya faɗa yana ɗaukar wayarsa ya shiga neman lambar Family Doctor ɗinsu.

    Hankalin su Jawad duk kansu ya dawo suna tambayar abinda ya samu Yayan nasu, haɗi da jera masa sannu cike da damuwar ciwon nasa.

  Amsa musu ya yi a hankali yana mayar da idonsa ya lumshe, yana jin wani irin nauyi a zuciyarsa. 

  Sultan kuwa kiran Doctor ya yi ya sanar masa cewar ana buƙatar ganinsa sannan ya ajiye wayar, ya mayar da hankalinsa ga a ɗaya kan Ajmal ɗin.

   "Wai ina Meerah ne?." Sultan ya yi wa Momy tambayar da ta saka Ajmal kasa kunne don jin amsar da Momy zata bayar, don tunda suka shigo yake zuba idon ganin ta inda zata fito.

   "Wannan ai ta auri zaman ɗaki, kwata kwata yanzu bata son fito wa ta zauna a cikin mutane,  yini take yi a ɗaki tana faman danna waya." Momy ta bawa Sultan amsa. Amsar da ta yi tsaye a zuciyar Ajmal ta saka shi tunani mai zurfi da ƙoƙarin fassara abinda hakan ke nufi.

   Sunan da yaga an kira ta da shi ɗazu, da irin yanda tayi saurin kashe wayar ya dawo masa a rai. 

  'Me hakan ke nufi? Meye alaƙar ta da yaron da ya yi ƙoƙarin dakatar da wata alaƙa ƙulluwa a tsakanin su?.' tambayoyin da suka shiga yi masa kai-kawo a cikin zuciyarsa kenan.

   'Soyayya mana, kai baka ga ta saka alamar heart a gaban sunansa ba. Yanzu haka ma da shi take waya shi yasa bata sauko ba.' wata zuciyar tasa ta bashi amsar da ta ƙara hassala shi.

   Yana cikin wannan saƙe saƙen ya ji ƙaran saukowar ta daga sama, hakan ya saka  shi buɗe idanunsa kaɗan ya sauke a kanta yana  binta da kallon da babu wanda zai gane yana yi.

  Haka kawai zuciyarsa ke raya masa cewar waya ta gama yi da yaron can, wani irin ɓacin rai yaji yana taso masa na raunin wayon da aka masa. Wato yaron nan bai ji gargaɗin da ya masa ba, har sai da ya san yanda ya yi ya shiga rayuwarta bayan barin sa ƙasar?.

  "To wai ma yaushe hakan ta faru ne?." Ya yi wa kansa tambayar da bashi da amsar ta. Tunanin da ya yi nisa a ciki ya sahar bai san lokacin da ta ƙara so wurin ba. Sai saukar muryarta yaji tana gaishe sa haɗi da yi masa sannu, don Momy ta sanar mata baya da lafiya.

  Amsa mata ya yi a dake kamar yanda ya saba, dai-dai lokacin kuma aka dannan doorbell Ya Aryan yaje ya buɗe. Doctor ne ya ƙara so don haka aka nuna masa wurin zama. Gaishe da Momy ya yi cike da girmamawa ta amsa da kulawa.

  Sultan ya bashi hannu suka yi musabiha, haka ma su Fadeel. Bayan sun gama gaisawa Momy ta yi masa bayanin wanda bashi da lafiyar. Ajmal ya kalla wanda har yanzu idanunsa suke a lumshe yace.

  "Sannu yallaɓai Ajmal, yaya jiki?."

  "Alhamdulillah." Ya bashi amsa, tambayoyi ya yi masa ya amsa masa sannan ya auna zafin jikinsa da gwada BP ɗinsa. Sai da  ya kammala sannan ya kalli Momy yace.

  "Jininsa ya haura, hakan ya haifar masa da ciwon kai da zazzaɓin, yanzu zan saka masa drip da allurai ne sai a rubuta masa magani. 

   "Okay Sultan ko zaka kai sa ɗakinsa ne?." Momy ta faɗa tana kallon Sultan ɗin fuskarta ɗauke da damuwar jin halin da Ajmal ɗin ke ciki.

  "Nan ma za'a iya saka masa, ai drip ɗin ɗaya ne kawai za'a saka." Cewar Doctor. Filo Sultan ya saka masa ya kwanta da kyau sannan aka saka masa drip ɗin da ya haɗa allurai ya zuba a ciki. Magani ya rubuta ya bawa Sultan sannan ya musu sallama ya tafi.

   Duk zagaye sa suka yi suna ta faman yi masa sannu cike da damuwa, sai da yace suje suci abincin su sannan suka tashi suka nufi table ɗin. Sultan kuwa kasa tashi tayi ya zauna kusa da shi yana jera masa sannu.


*Nawaz....*

    Zaune yake a saman tabarmar da aka shimfiɗa a cikin baranda yana cin abincin darensa da Basma ta kawo masa. Tattaunawa suke yi da Umma a kan maganar jinyar Abba.

   Sai da ya kammala cin abincin ya sha ruwa ya yi hamdala sannan ya kalli Umma yace.

   "Umma dama akwai wasu kuɗi da aka turo min na wata waƙa da aka biya ni, dama ina ta tunanin yanda za'a yi a samu kuɗin da za'a kai Abba asibiti ayi masa gashin fi goben. Kin ga yanzu sai ayi amfani da shi muga abinda  Allah zai yi kuma." Ya ƙare maganar yana ciro kuɗi a aljihunsa ya ajiye a gabanta.

   "Masha Allah, Allah ya maka albarka ya ƙara maka buɗi na alkairi." Cewar Umma cike da farin cikin samun mafitar da aka yi, ɗin dama tunanin inda za'a samu kuɗin nan take yi.

  Nawaz na ƙoƙarin yin magana kiran ya shigo cikin wayarsa, don haka ya dakata da maganar ya kal kallonsa ga wayar.......

  Barkanmu da dare.

   *Oum Fatima*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.