Free chapter · Read without an account

Page 15&16

by Ammey Laylerh · DUHU na DUKAN duhu

#ROMANCE## #BLACKMONEY #KIDNAPPING *DRUG TRAFFICKING #AGGRAVATED ROBBERY## #AMAZING W*w☞ ☞

______________ #DON

_Wannan itace duniyar da muke rayuwa a cikin ta wacce take kunshe dajin dadi da kuma tsatsanin azaba. Kalilan daga cikin ta sine suke jin dadinta mafi yawan cikin ta kuma sune suke shan hawalarta. KIYAYYA, HASSADA da MUGUNTA sune ababen da suke kara ta'azzara komai a cikin wannan duniyar. Karni bayan karni shekaru naci gaba da shudewa amma babu wani Abu da yake sanjawa, saima kara ta'azzara yake abun tambayar anan shine. Shin wannan duniyar zata taba sanjawa kuwa?.... Sabo da masu karfin ikon cikin sune koda yaushe suke azabtar da talakawan cikinta, burinmu NIGERIAN'MU ta gyara dama duniyar baki daya. To amma ta yaya hakan zata faru???...... Let's go a comments section DON√_

Wannan kayataccen rubutun shine baki daya yayi trending a safiyar yau ta raba.

Inda baki daya ya message din ya dauki hankalun mutane fiye da tunanin mai karatu, domin magana ake ta gyara da gyara kai.duk wata kafa sune dai labaran da suka zama latest irinsu.....

Facebook Tiktok Instagram Telegrams Twitter

Jikin sanyin safiyar yake dan running kadan kadan a cikin kewayen anguwar ta victoria Islan gefensa lioness, said gefen damar sa Vincent ne gefen haggunsa kuma axton ne, daga baya kuma miles ne sai lioness dake a gaba. Kare ne na musamman ba irin sauran karnuka bane ROSER ce ta Haifa mishi. Tana haihuwasa tabar duniya shi kuma Ak ya dauke shi ya kaishi wajen ZAKI aka chakudashi da yayanta ita ta shayar da shi duk ayyukansa irin na zaki yake yi komai tare da lioness yake yi. Suna kaiwa gida ya bude dakinsa ya maida shi bayan ya dan shafa saman kansa tare da zuba masa ruwa a tsakiyar kansa. Tamkar wani mutum ya wani irin girgiza tare da fesar da ruwan dake jikinsa, Ahankali yabar wurin yana nufar compound din gidan. Duk inda ya wulga sai kaga wadan nan samudawan dai suna risina masa tare da gai da shi.

★★★

"Will you shut that your dirty mouth up!, are you stupid Ina magana kana yimin zancen banza da wofi, kodai ka samu tabin hankaline ban sani ko ban sami labari Impossible wannan bamai yiyuwa bane".. Yadda ya hayayyako yana masifar kadai zai sheada maka koma miye aka fada masa a cikin wayar bame dadi bane. " Me gida ka yarda dani na rantse da uban daya haifi ubana Salman baya cikin airport din nan, kasan bazan maka yawa ba fa me gida" Sosae jikin Isa Manu ya dauki wani irin Mazarin bala'i Wanda safiyar yau ne aka sallameshi daga hospital, ta karfin tsiya bawai don ya gama samun sauki ba. "Kai lele karka sa jinina ya tafasa fa, in banda zancen banza taya za'ace an rasa dan mutum sukutum tum a airport. Hauka ma kenan yanfa kaga last call nawa da salman din du du du bai wuce 40 minutes ba" "Na rantse da assamadu me gida bincike iya bincike nayi amma fa maganar gaskiya salman sammm baya cikin airport din nan.....

"Stop your dirty mouth Lel... Chak ya tsaya ba tare daya kai ƙarshen Eee ɗin ba sakamon rumgumeshin da yaji anyi ta baya, kafin ya tsinci murya ɗa mafi ƙololuwar soyuwa a gareshi yana furta. " Nayi Surprise Daddy" Wani irin guntun numfashi Isa Manu ya fesar tare da juyo da Salman zuwa gabansa, sai kuma yaɗan shiga bubbuga gadon bayansa tare da furta. "Daddy's boy kafa tsoratar dani sosai irin sosae ɗin nan fa nake nufi" "So sorry daddy" Salman ya furta tare irin kama gefin kunnen sa guda. Wani ƙayataccen murmushi Isa Manu ya saki tare da nufar stairs da yaron nashi Yana faɗin "kai dai muje sama akwai abubuwan yi da yawa a gabanmu" nan suka nufi saman abinda. Har ɓangaren sa ya kaishi saida ya tabbatar Salman ɗin ya shige bethroom kana yabar ɗakin yana furta. "Karka ɗauki dogon laƙaci daddy's boy ka sameni cikin office ɗin cikin gida just 40 minutes kawai na baka" Ficewa yayi a sashen ta wata ɓarauniyar hanya. 45 minutes ago Sai gashi ya fito sanye cikin ƙananun kaya na shan iska, office ɗin daddy'nsa dake cikin gidan ya nufa direct. Yana tafe yana latsa faskekiyar wayar dake rike a hannunsa. Kai tsaye ya tura office ɗin mahaifin nashi ba tare dako neman izini ba, da sauri Isa Manu daya lula wata duniyar ta daban ya ɗago kansa tare da duban her yaron nashi abin alfaharinsa, ganin yadda daddy'n ke kallon sane ya sanya shi ƙarasowa cikin office ɗin yana zama kan kujerar dake facing da mahaifin nashi. Wasu files ya janyo tare da turasu zuwa gaban Salman. Files ɗin ya shiga dubuwa sosae kafin ya ɗago kansa yana dubar mahaifin nasa tare da ɗan fada fuska yana wani irin yamutsata. "Daddy?" Ya faɗa cikin wata kasalalliyar muryan dake nuni da taɓarar nan irin ta ƴaƴan hutu. "Yes daddy's boy duka abin da kagani a jikin files ɗin haka nake son komi ya tafi a yadda na tsara" "Amma daddy meye amfanin haɗa alaƙana da ita yarinyar da ka sako batun neman neman aurenta?" Wani dogon numfashi Isa Manu yaja tare da tattaro hankalin sa baki ɗaya zuwa ga Salman ɗin. "Ita kuwa take da amfani daddy's boy, idan har hasashena ya bani daidai yarinyar tana da wani ɓoyayyan abu kodai tana akwai abinda ta riga ta sani kame da wani abu!" Ya sauƙe numfashi kafin yaci gaba da faɗin. "Tunda har akayi kidnapping nata Ni meyasa basu haɗa dani ba, neman aurenta da zaka shiga shine zai janyo hankalin koma waye zuwa gare mu. Kuma yarinyar zata kasance a ƙarƙashin ikon mune hakan shine first kafin mu tafi plan B"

"Amma daddy.... "Amma me? Daddy's boy" Isa manu'n yay saurin tarar numfashin Salman ɗin. Hakan ya sanya shi yin shiru ba tare daya sake yunkurin furta ko wacce kalma ba. "Hakan shine best solutions namu boy kana a tada hankulan jama'a. Ka sanya su Bom fire su tada zanga-zanga game da kwamushen su governor da kuma minister da Akayi ta haka ne kaɗai zamu cimma burin mu. Ya zaman mun jefi tsuntsu ɗaya da dutse biyu kenan Ni dasu Boshosho zamuji da sauran". "Wow Wow hoooooo wuuuu woohoo hooo good idea daddy ina alfahari dakai.... Salman ya fadi yana ihu tamkar wani ɗan daba.

Mu haɗe a next fage my gold fan's...... ~ BY AMMEY LAYLERH ✍️~ *🦅 MIKIYA 🦅* _Mai hangen nesa 👀_ *~We want an end to oppression💪~* *** ____________________ *NA MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~ ✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.