Free chapter · Read without an account
Page 9&10
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎OCITION.
ꨄ A matukar fusace Babyboo tace. "Da dukkan alamu koma waye wannan kidnappers din yana son raina mana hankali ne kawai..." Ta kai maganar nata tana hucin bacin rai.. "Relax mana ko waye wannan mutumin ma yana son mu yi gaggawa ne a yadda na fahimta. Idan kuma muka yi gaggawa za mu bashi abin da yake so ne kawai don haka" K Mashi din ya fadi yana dan yarfewar nan irin wanda yafi kama dana rashin mafita din nan. "Ga C. V. I din naku nan sunzo babu abinda suka iya sai shirme kuma, amma kuma kafin nan bari mu gabatar da wani babban wasa...." Kai tsaye duk haka sukaji muryan ya sake dakarsu da dawo dasu duniyar mutane. "Ka cewa mutanen dake cikin motar suyo waje, kai kuma sai ka ajje wannan jakar kudin a ciki, ka iya tuki ba?...." Muryan data sake sanjawa ta sake fadi da wani sabon rainin hankalin. "Aha ywwh saboda nasan ka iya kai tsaye ka shiga ciki sai kaja motar..." A daidai lokacin ne K Mashi ya mike cikin motarsa yana taɓa abar dake makale jikin kunnensa da faɗin. “Ku riƙe matsayinku and babu wanda zai yi harbi, haka kuma babu wanda zai matsa sai na bada umarni.” Ya fadi su kuma suna amsawa da yes. Kusan a kidime Aminu Dakata ke jan motar, wanda da dukkan alamu an jima ba'a haɗu ba tabbas, saboda sai dai a jashi tun kan ya hau mulki,don haka ya zama kamar dan koyo. Daya daga cikin jami'an ne ya sanar da cewan “Sir. Ina ganin motsin da ban yarda dashi ba ata ɓangaren arewa.” daidai da lokacin da aka saki wani irin shegen lalataccen murmushin da sautin sane kawai ya fita. "Good!" Babyboo ta furta cikin nutsuwa tana wani dan lumshe ido tare da furta “Yanzu hasalin wasan zai fara ku bar shi ya yi tunanin ya fara fahimtar wasan.”
Daga can cikin ainihin control computer room nasu kuwa AJMAAL ne zaune gaban wata shafaffiyar na'urar dake gabansa ba computer ba. Wanda a cikin kasa da 30 minutes suka dawo dashi bakin aiki bisa dakatarwan da aka masa wacce ta kusa 1 year kenan. Kai tsaye shike bibiyar duk wani shige da ficen jama'ansu. Wani shafo ƙasan kansa yayi yana hurzar da wata iska daga cikin bakinsa, kafin ya taba wani jan launi cikin cikakkiyar murya mai aji da amsa kuwwa ya furta. "Wannan abin mutum ba zai iya yi ba sai dai computer...." wani daga cikin jami'an ne da babu jimawa ya shigo aikin da shi Ajmaal din bai ma san shi ba bai taɓa ganin saba sai yau din ya yace. "Kamar ya kenan yallabai? What are you saying?..." ba tare daya juyowa wame tambayarba YA furta. "Pre-recorder!?" tare da miƙewa tsaye yana furta I minutes, kai tsaye wayarsa fito da ita tare da shiga cikin app na recording nashi kai tsaye tare da saita mutumin yana furta.
"What do you think of the criminal?"
Nan fa wannan jami'in ya ringa zagargaro zagi yana cewa idan har shi zai samu damar ya kama shi da hannunsa da kuwa tabbas sai yayi raga raga da naman jikinsa. Wani irin guntun murmushi Ajmaal ya saki kai tsaye ya shiga cikin abu yana jonawa da wayar nasa, sai ga muryan wannan jami'in ta koma wata kakkausar daya saka shi saurin ja baya yana rike bakinsa. "This isn't a computerized voice, nor is it a pre-recorded voice voice synthesizer...." kai tsaye ya furta yana ci gaba da furta. "It will speak whatever we type. Wannam sak salo ne da kungiyoyin ta'addanci suke amfani dashi wajen juyar da tunanin jami'ai a kansu da raina musu hankalin da zasu yi tunanin ba mutum ɗaya bane...." Wani tafi aka ɗauka duka a control room din, domin ba ƙaramin burgesu yayi ba, wanda kuma dama shi haka yake su biyu ne basu iya gano ko miye dake ɓoye, daga shi sai _RAYYERN KHALID_ daya daga cikin jami'an ne ya daga kansa sama alamar tunani saboda sunan _RAYYERN KHALID_ din kawai daya fado masa. Sosai suka yi missing jami'in da har yau ko za'a hada goma ba zasu taba kaiwa ɗaya kamar sa wajen fikira da hikima da jarumta jajircewa wajen gudanar da aiki irin nasa ba. A hankali kuma yaja idonsa yana lumshe wani abu mai nauyi na danne kirjinsa. Saurin girgiza kansa yayi tare da dafe goshinsa yana barin control room ɗin.
_Kurman Rafi_
A bangaren Nadiya kuwa yunin guda din ranar yau a aiki ta ƙare, Uban wanki ne nata dana Baba sai Gwaggo Talatu. Duk da kasancewar yinin ranar ta yi shi ne cike da ayyuka amma hakan bai sa ta manata da abinda ya faru tsakaninta dasu Shitu ba, kusan zata iya cewa ma gaba daya tunaninta yana kan Shitu din ne da kuma kalaman da ya fada mata kafin ya tafi. A natse ta dago tana kallon sararin samaniya da rana tayi sanyi sosai don har ana goshin magrib ne ma. Sauri sauri gudu ta karasa shanyar kayan da dama sune shanyar ƙarshe, domin kada ta manta yau ma irin jiya bata sayo madaran da zata yi albishir din ta ba, wanda kamo jiya kamo yau da ace tayi da tuni ta kare. Yau dama gwaggo batayi fura ba kasancewar tasan da uban wankin da ita kanta ta tara mata, ga kuma nata gana Baba duk da kasancewar ba wani yawa ke gare su ba, karfe shida dot ta bar gidan sauri sauri gudu gudu don sayo madaran saboda a yau din take son yi gobe akwai makara, kamar kullun bayan ta dawo take tarar da wannan munafukar Aminiyar Gwaggo din mai suna Sabuwa, munafuka ce ta karshen gaske matar nan, don shirya maka wani bom din sai kaji inama ace na gasken ne zai tashi da kai bana Sabuwa ba. A natse ta karaso tana gaida Sabuwan tare dama Gwaggo barka da gida, su dukan su ba wai amsawan dadi ne suka mata ba amma hakan bai hana ta gaida su din ba kamar yadda ta saba tun Dadansu na raye. Wanda tarbiyanta ne hakan, ita kuma gata da kafiya don tasha auna wucewarta ba tare data gaida su din ba tasha shan rankwashi a wurin Gwaggo Talatun. Kai tsaye dakin Baba ta wuce saboda ta shigo masa da awarar data sayo masa a ɗan canjin da suka rage masa, a zaune ta tarar dashi yana ninke kayan wankin da tayi masa, wanda da dukkan alamu gwaggo ce ta watsa masa. Da sallama ta shiga yana amsa mata sallaman cikin mutunci tare da faɗin. "Sannu Nadiya har kin dawo kenan?" da "Eh" ta amsa masa tana kokarin ajje ledan hannunta ba tare data zauna ba. Kai tsaye linkin ta fara amsa ta karasa masa kana ta ciro masa awaran da zafinta tana miƙa mishi, godiya mai tafe da adda'a ya mata da adda'an samun miji na gari, yana cewa taje ta samu ta zauna itama haka nan ta huta. Da to ta amsa masa tana karasa saka masa kayansa a cikin gana masgo. Daidai lokacin da Gwaggo Talatu ke kwala mata kira a jere a jere babu ko dan kakkautawa, a natse ta karasa zuge masa zip din jakar daidai nan Gwaggo ke shigowa dakin a tsawace tana sake surfa mata masifa da bala'in daya saka Baffa cema Gwaggon ta bari Nadiya din ta dan huta. "Ahhh lallai dole wuyarta ya isa yanka mana tun da tana da bai daure mata kugu, in banda haka har ni zan kirata kace na barta ta huta? To shikenan ta zauna ta huta din ko kuma ku nace ku zauna kuci gaba da gulman da kuka saba nawa. "Haba Talatu gulma kuma?...." Babu zata suka jiyo muryan Sabuwa aminiyar Gwaggon tana amshewa da "Yo gulma mana in banda haka na miye cewar ta barta ta huta ɗin?..."
Baba na ya lalubo hannunta inda yake jin motsinta ya mata alaman data je, suna tsaye daga bakin ƙofar su kuma suna kare mata zagi ita da Baban, ashe ma sharace zata mata tana sharan jikinta na ɗaukan tsuma na irin zagi da cin mutuncin da suke jifan Baba da kuma Dadanta dashi, gaba ɗaya zuciyarta wani irin tafasa take kamar zata fado daga cikin kirjinta, kiran da aka ma Gwaggo Talatun ne ya katse musu zagin da suke musu. "Ahhh Wasila ƴar albarka yau kuma kece da kira na?" haka Nadiya ta jiyo muryan Gwaggo Talatu cike da alfaharin ita yar ta ai tayi dacen aure, duk da kuwa cewan ba hakan bane, hasalin ubanta itama nata mijin keyi wanda a kusa da kauyen su ita kuma take aure. Daga nan kuma sai taji Gwaggon tif murya tayi kasa, daga ta cikin wayan kuwa cikin kuka Wasilan ke cewa Gwaggon ta temake ta ceceta Haladu zai kasheta da duka da kuma horon yunwa, cikin kasa da murya wacce Nadiya ke jiyowa kasa kasa Gwaggon ke cewa. "Ay shikenan Wasila sai ki baro gidan mijinki ki dawo mu zauna, mu koma abin shune a cikin gari, in banda abinki kusan kullum abinda nake fahimtar dake kenan, kuma ina ranar ma nake ce miki ki dan turomin da kuɗi ko dubu uku ne ko biyu na samu na tsallaka hayi a kashe masa zuciya ta yadda ma sai yanda kika ga damar yi dashi amma kin ki turowa.... " cikin muryan kuka tace."Haba Gwaggo wai ke wacce irin uwa ce ne haka da ina gaya miki matsalata kina min zancen kuɗi? To a ina kike son na samo kuɗin, alhalin kin fi kowa sanin ko nera hamsin wahalar samu take min bare irin wannan kudin har dubu uku? Ni dai wllh yau sai na baro gidan Haladu ba zai kashe ni a banza ba ga yara har biyu ga ciki amma sai yafi kwana uku bai bamu abinci ba, duk da cewan shagon sayayya ne dashi... " aikuwa nan take Gwaggo Talatu ta hau ta da fadan cewa tun da ita banza ce ba sai taci gaba da zama a hakan ba, ita yanzu ko fakar idonsa ai tayi yana barci ta samo dubu ukun koma biyar ta kawo, sosai ta hauta da bala'in cewa gidan tane bata iya kamawa ba, in banda haka ai da ba hakan yake mata ba sanda tana yan mata, kudi da kayan dadi yake sakar mata amma ta tun farko farkon amarcinsu data samu ciki amma yace shi ba yanzu zasu aihu, shikenan ya fara cin ubanta babu kama hannun yaro bayan ya galla sabon aurensa yana wata bakwai da aurenta. Daga nan wayar ta koma daki wanda ya sake sanyaya jikin Nadiya domin ko babu komai duk inda naka yake to kuwa tabbas naka din ne bata sauya zani. Kiran sallan magrib yayi daidai da lokacin data fito daga wanka ta tsugunna ta daura alwala ta shige dakinta. Bayan ta idar da Sallah ta sake fitowa don yin albishir nata. Wajajen Isha'a ta kammala har yankawa ta juye a boket fari bayan ta kaima Gwaggo Talatu wacce ta amshe babu kunya shi kuwa Baba dama baya sha kwata kwata yace zakinsa yayi yawa. Ta jima bacci bai dauketa kasancewar ababuwan da suka sako ta gaba na tunannikan yayyen nata biyu da kusan duk suke cikin matsala, sosai ta raba dare tana raya shi da Sallah da adda'an ubangiji ya kawo musu mafita a cikin gidajen aurensu.
Washe gari duk da rashin ishashshen barcin da bata samu jiya a daren jiya da wuri ba amma hakan bai hana mata tashi da wuri ba. Tsakanin makarantar nasu da gidansu da ƴar tafiya sosai kuma sa'arta daya yauma Gwaggo batayi koko ba, don indai har tayi sai ta gama sayar mata kana take tafiya makarantar da take tsallaken garinsu, dake tana sakandire ne ajin ƙarshe, kuma exam fita ma suke saka ran farawa nan da 2 weeks. Duk wannan uban nisan amma haka kullum a ƙafa take zuwa ta kuma dawo, idan kaga ta hau mashin sai dai idan Baba ya ɗan bata tun da ba laifi sa'a nar nasa na gara masa, barin ma yanzu da ake cikin damuna. Tun ƙarfe ɗaya yau aka taso su maimakon ƙarfe biyun da ake taso su kasancewar shirye shiryen jarabawan fita suke, a tafiya a machine taje don haka yanzu a kafa ta biyo ayarin masu tafiyan kafa din, duk da cewan taci kasuwan albishir din ta, amma kuma idan tayi da duba hidindumun cikin gidansu duk da kuwa cewan Baba na bakin kokarinsa itama tana tallafawa sosai, don haka komai nata yake a gindaya a lissafe cikin tsari. A ƙofar gida ta tarar da Baban yana tuka tufkarsa da su Baba Malami makwafcinsa suna zaune suna firansu. Gaida su tayi har kasa tana cewa "Sannu da aiki Baba."
"Yawwa Nadiya, har an dawo kenan!?"
"Eh Baba." ta bashi amsa tana kokarin wucewa bayan yace. "Toh Madallah, sannu da dawowa ubangiji ya bada abinda ake nema." da amin ta amsa masa murmushin da akan jima ba'a gani ba daga gareta kawace a kyakkyawar fuskanta tana shige wa cikin gidan. Gwaggo Talatu bata gidan da alamu tayi wani wurin kenan, don haka tayi shigewanta daki don taga alaman yau ma bata furar, wanda kusan dama hakan take, in bata ga dama ba sai ta shafe kwana da kwanaki bata yi, sai taji ta fara shiga halin hau ila'in rashin kudi kana take zaburowa tayi. Kwanciyarta tayi bayan tayi Sallah don hutasshewa ma gajiya, ɗan fara baccin nata kenan sama sama taji hayaniyar shigowan Gwaggon ita da sabuwa din dai suna shewa da dukkan alamu wani sabon sharrin suka je suka kullo. Labulen dakin aka ɗaga taga Gwaggo Talatu ce, yau babu faɗin ba hayaniyar data saba mata kawai cewa tayi da ita. "Ya kamata a dora girkin rana lokaci yana tafiya har karfe biyu na shirin kawo kai" Da toh ta amsa mata tana miƙewa, ta chanja kayanta zuwa karamar riga da fallen zani ta saka hula a kanta ta fito zuwa tsakar gidan. Ashe alale za'a yi shi ne ko surfa waken ba'a yi , kanta ta girgiza kawai ta zuba waken a turfin da yayi zurfi sosai saboda karamar tabaryan da ake saka ma, da dukkan karfin da ALALH ya halasta mata take dukan waken, don haka cikin lokaci kankani ta gama surfa waken, kasancewarta mai kazar kazar komai da rai ra karfinta take yi, sam bata da ganda tun bata karasa haka ba take ayyuka masu nauyi. Ɗebe waken tayi a baho ta nufi gaban kwallar gwaggo daya da randa. Tas ta wanke waken ta zauna ta tsince tana jin fira da shewarsu suna daga daki, gaban biahiyarsu ta nufa ta zauna ta soma gyara waken tana tsince hancin da rigarsa. Kiran karfe biyu daidai da lokacin data gama tsince waken tas ta nufi gidan Inna Duduwa mai markade, wacce kaf kauyen nasu ita kadai ce mai Inji dan kyarkyari, da danta Mubarak ya sayo mata a birne dake neman kudi yake fita a garin Bauchi, wanda shi ma sai daya nuna kamar yana son ta amma kuma yanayinta na rashin bama abu muhimmanci ya saka shi kamar janyewa shima, baya da haka ga uban gayya Shitu wanda da yaji labarin kana son Nadiya yake yanka maka kashedi, idan kakiji kuma ai baka ki gani ba, sai ya barka maka shedar da dole zaka janye. Fita tayi ba tare data nemi da Gwaggo din ta bata kudin markaden ba, kasancewar tasan dama ba bata zata yi ba. Sai dai fitanta kenan babu nisa taga ana cin uban gudu tu shan kwanarta ta farko, wanda ya saka gabanta faɗuwa da mugun ƙarfi, dakewa tayi taci gaba da tafiya amma kuma gudun na sake karuwa ana ihu ana cewa kowa ya nemi maboya Shitu ne yaje ya sake jangwalo musu fadan fulani, gashi can har sun kwantar da wajen mutan uku an nemi kuma shi Shitun an rasa. Ras haka gabanta yay wata irin Mummunan faduwan daya saka boket din hannunta kusan faɗuwa. Gashi gaba ɗaya kuma sai idanun wasu daga cikin mutanen dake gudun ya dawo kanta suna zubo mata na mujiya, wanda ya sakata dan fara komawa da baya da baya tana jan ƙafa. Daidai da isowar wasu kungiyar matasan daban wacce fulanin ke a bayansu, saukar nasu idanuwan a kan Nadiya da dama wasun su da yawa yawansu ke jin haushinta yadda take kin kulasu suka shiga nunama fulanin nan Nadiya, suna cewa dasu wannan itace kadarar da indai suka taɓa ta kamar sun taɓa Shitu ne, wani irin sake Mummunar bugawa gaban Nadiya yayi cike da wani tashin hankali, kokarin gudun itama take amma fulanin da suke ganganko guda suka zagayeta suna mata ƙawanya. Wani yawun da babu shi take kokarin ganin ta hadiye, sai dai babu shi babu labarinsa, bada dawo daga cikin duniyar da take ciki ba ta tsoro taji saukar wani abu a gefen kirjinta, wanda ya sakata sakin boket din wani gigitaccen zafi na game jikinta, bata kuma dawowa daga wannan duniyarba ta sake jin saukar wani abu mai kama da guduma a tsakiyar gadon bayanta. An sake dagawa za'a doka mata kenan taji saukan wata muryan da bata san taba tana dakatar dasu, ita kuma daidai lokacin take yanke jiki ta zube kasa. Idanunta suko ciko da wani abu da bata san ko miye ba, ranta ya shiga kokarin fita daga jikinta, idanunta suka fara kokarin lumshe wa, ta tuna da maganar Baba ta daren jiya.
"Kiyi hakuri komai lokacine Nadiya, karki yarda zuciyarki ta rinjayeki akan wani abu dake cikin duniyar, karki taba yarda imaninki ya gushe daga gare ki saboda ganin ke kina nan cikin kunci yayinda wasu mutanen ke can suna daga cikin wani yanki na jin daɗin rayuwar dake cikin duniyar, yayin da wasu ke bangare guda suna kuka suna kwankwaɗar ɗaci da mikin dake cikinta!. A rayuwar nan zaki yi ta ganin abubuwa suna tafiya saɓanin tunanin ki, saboda ALLAH ne yake tsara komai ya tafi yanda ya so a lokacin da ya so. Zaki ga ya wadata mai saɓa masa ya hana mai yi masa biyayya, wannan duka na daga cikin jarrabobinsa ne, ta yadda zaki ga ya sauƙaƙa ma azzalumai ya ƙuntata ma wanda aka zalunta, wannan talala ne mai kamar sake yake musu, Saboda haka kada kiyi tunanin bai san halin da kike ciki ba ko ya manta da ke ne, idan kika ƙosa a wannan jarabawar zaki iya faɗuwa kasa warwas saboda rashin haƙuri, shine sai kiga mutum ya fara a wahala ya ƙare a cikinta, shi yasa kullum nake cikin tunasar dake. Domin rayuwar ba gasa ba ce ko wasan tseren da kowa zai kai ga nasara a lokaci guda. Wasu suna samun abin da suke nema ne cikin sauƙi yayin da wasu kuma sai bayan dogon lokaci. Don haka, kada ki bari nasarar wani ta sa ki ji kamar kin fadi ko ke marar nasara ce, abin da ya dace kici gaba da yi shi ne ki mai da hankali kan al'amuran ki , ki ci gaba da ƙoƙari, ki yi haƙuri, domin jinkiri ba yana nufin ba zaka samu wani abu daga cikin rayuwa bane... "
Ahankali idanunta suka kara sa lumshewa ji da ganinta na ɗauke wa daidai lokacin da tunanin ke barranta daga cikin duniyarta, numfashinta na barin gangar jikinta....
BY AMMEY LAYLERH ✍🏻
***
༺𝙂𝙐𝘿𝙐𝙉 𝘿𝘼 𝘽𝘼𝘽𝙐 𝙏𝙎𝙄𝙍𝘼༺
Kᴡᴀɴᴄɪʏᴀ ᴛᴀ ғɪsʜɪ
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️