Free chapter · Read without an account

Page 13&14

by Ammey Laylerh · DUHU na DUKAN duhu

*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎OCITION.

ꨄ Likitan da ya gama yi musu bayanin halin da Nadiya ta ke ciki ne ya sake jaddada musu cewar yanzu rayuwarta na ƙarƙashin kulawar ALLAH ne, su kuma abin da ya rage musu shi ne addu'a da kuma bin umarnin likitoci, kafin daga bisani ya kalli Sadiya wacce har lokacin ta kasa cire idanunta daga ƙofar dakin da aka shiga da Nadiya, sannan cikin nutsuwa ya ce mata za ta iya ganinta daga wajen glass ɗin amma kada ta shiga ciki domin tana buƙatar cikakkiyar nutsuwa a wannan lokacin. Kamar wacce aka bata izinin shiga duniya bayan an rufe ta a gabanta haka Sadiya ta ɗago kai, ta kalli likitan fuska cike da alamun tabbatarwa kafin ta bi shi har zuwa wajen glass ɗin, daga bakin glas ta tsaya kai tsaye idanunta na sauka a kan Nadiya suna tsayawa cak kamar an dasa ta a wurin, domin kuwa duk irin yadda ta yi ƙoƙarin shirya kanta tun kafin ta iso wurin amma hakan sai da ya gagareta, ganin ƴar uwarta ce kwance a haka ya sa komai ya sake wargajewa a cikin zuciya da kuma kanta, Nadiya dai? Nadiyan ta ce kwance akan gadon nan, fuskar nan da kullum take cike da ƙarfi walwala da jajircewa amma yau ita ce kwance cikin wannan hali?, da de da numfashin da zata shaka na oxygen ne, jikinta kuma ko ina jone da na'urori, baki daya tana kwance ko ina na jikinta babu inda yake motsi tattare da ita, sake kafe fuskarta da kallo tayi tana sake kallar yadda numfashinta ke tafiya ne wai da taimakon na'urorin da ke kewaye da ita. A hankali Sadiya ta ɗora tafin hannunta akan glass ɗin kamar tana son ta kai gareta, wasu hawaye na fara gangarowa daga idanunta kafin cikin wata irin murya mai daci mai dauke da wani irin raɗaɗi ta ambaci sunan "Nadiya..." a bayyane tare da kife tafin hannunta ɗaya saman fuskarta tana haɗiye wani abu mai nauyi daga kasan kirjinta. kafin ta ɗora da cewa, "Don ALLAH kada ki tafi ki barni..." Kafin taci gaba da kallon ta tana jin kamar duk wani ƙarfin da take da shi a rayuwarta ya tattaru ne a kan gadon da ke gabanta...

Bayan wani ɗan lokaci ne wata nurse daban ta iso gabanta da wasu takardu a hannunta tana kallon Sadiya da babu jimawa ta bar wurin, kallon Sadiyan nurse din ta fara sannan ta kalli Baba dake zaune can baya, kafin ta ce musu akwai wasu magunguna da kayan aikin da ake buƙatar amfani da su yanzu, kuma akwai kudin jinyar da ake bukatar a fara biya domin a ci gaba da kula da ita yadda ya kamata. Sadiya wacce take tunanin abin da kawai zai rage musu shi ne jiran a ce Nadiya ta farfaɗo, sai maganar kuɗin ta saukar mata kamar wani sabon dutsen da aka ɗora mata a kai, ta kalli nurse ɗin cikin rashin fahimta kafin ta ce, "Kudin jinya kuma?" Nurse ɗin ta gyada mata kai tana nuna mata file din da ke hannunta, ta fara bayyana mata abin da ake bukata, Sadiya kuwa da tunda nurse din ta sakar mata da file din ta ɗauka tana rike shi kam a hannunta dake wata irin rawa, idanunta suna sauka kan adadin kudin da aka rubuta, domin itama tayi karatu duk da ba mai zurfi bane, amma duk wani FATA da kuma BURINSU yana ga Nadiya ne, wani irin shiru tayi wanda baki daya wannan shirun da tayi na mamaye wurin din, sake kallon takardar tayi tana jin kamar watakila idan ta ƙara kallonta sau biyu adadin zai canza ne, sai dai amma sammm bai canza ɗin ba. Don haka ta ɗago kai tana kallon nurse ɗin, "Amma..." ta fara magana kafin muryarta ta tsaya, ta sake haɗiye wani abu mai nauyi tana cewa, "Mu ba mu da wannan kuɗin yanzu likita." Nurse ɗin ta ɗan yi shiru sannan ta ce musu su yi ƙoƙarin nemo shi saboda akwai wasu abubuwan da asibitin ba zai iya ci gaba da bayarwa ba dole sai idan sun biya kuɗin.

A wannan lokacin ne Sadiya ta kalli Baba, wani irin kallon da shi ma ya fahimci abinda ke faruwa ko da yake bai iya ganin takardar ba, ya ɗaga kansa a hankali yana cewa, "Nawa ne kuɗin?" Sadiya ta yi shiru. "Sadiya..." ya sake kiran sunanta a hankali. Ta matsa kusa da shi tana tana rasa yadda ma za tayi, kafin a hankali ta kama hannunsa tana cewa, "Baba..." sai kuma muryarta ta karye sanin shi din ma ba shi ne dashi, amma duk da haka cikin karfin hali tace, "Kuɗin sun yi yawa ne! Suna da yawa." Baba ya yi shiru na ƴan daƙiƙu kafin ya ce, "Nawa ne kuwa?" A hankali ta gaya masa adadin, shi ma sai ya yi shiru kamar wanda aka ɗauke masa numfashi, domin duk abin da yake da shi a rayuwarsa bai kai wannan adadin ba in dai ba gidansa da yake ciki zai daga ya sayar ko gonarsa kwalli daya jak ba, kuma abin da ya fi masa ciwo shi ne sanin cewar sau da tari a yawancin wasu lokuta Nadiyan ce take taimaka musu da abin da take samu, wani lokacin ma tana rage nata bukatun ne domin ta samu ta tallafa masa ko ta tallafa wa Sadiya, yau kuwa gata dai ita ce kwance a wurin nan, ita ce ake nema mata kuɗin da su kansu basu san daga ina za su samo shi ba. "Za mu nemo su, IN SHA ALLAHU duk inda suke zamu samo." Baba ya furta kamar yana ƙarfafa kansa da kalmar fiye da yadda yake ƙarfafama Sadiya ne, amma tuni muryan nasa tana ɗauke ne da rauni. Sadiya kam wani sunkuyar da kanta tayi, hawaye suka sake zubo mata. "Daga ina Baba?" Ta furta cikin muryan kuka, "Daga ina za mu samo su? Nadiya ce ma kullum idan ta samu wani abu take kokarin taga ta taimaka mana, yanzu kuma gashi ita ce take can kwance, mu kuma muna nan muna neman ta inda zamu samo kuɗin jinyarta..." Ta kasa ƙarasa maganar tana rufe fuskarta da hannayenta tana sakin wani irin kuka mai daci da kona zuciya.

Ba su daɗe suna cikin wannan halin ba sai nurse ɗin ta sake dawowa tana sanar da su cewar ya kamata su yi gaggawar shirya kuɗin saboda wasu daga cikin abubuwan da aka fara yi wa Nadiyan ana buƙatar a biya su, kuma ba za su iya ci gaba da ƙara wasu ababuwa ko magunguna ba dole sai an fara biyan kuɗin jinyar. Sadiya ta ɗago kai da sauri, "Amma likita ya ce za a kula da ita." Nurse ɗin ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ce, "Za a kula da ita, amma Hajiya akwai tsarin asibitin kuma akwai abubuwan da dole a biya ɗin." Kalaman da kai tsaye suka yi ma Sadiya nauyi fiye da yadda ko hasashe zasu iya gindayowa, domin yanzu ba wai tsoron rasa Nadiya kawai suke yi ba, sun shiga tsoron cewa ko da ALLAH ya raya musu ita, su kasa yin abin da ake bukata domin a ci gaba da ceto rayuwarta.

A can ƙauyen nasu kuwa duk inda ka wulga magana ɗaya ce kawai ke tashi, maganar Nadiya da abin da ya faru da ita ake, wasu matayen aure ne wasu yan mata ne sa'anninta wasu kuwa ma sun zarta ta, ba maza ba mata duk inda ka wuce gutsiri tsomar abin da ya faru kawai suke mayarwa, wasu kuma suna ta jefa maganganu suna cewa komai ya faru ne saboda Shitu da kuma rikicin da ya jawo musu, wasu suna cewa Nadiya ce ta jawo wa kanta matsala saboda yadda take kin sauraron mutane, su kuma mutanen dama da guntun haushin ta a ransu na tsaurin ran da take jin tana shi, wasu kuma suna tausaya mata ne suna cewa ai yarinya ce kawai da rayuwa ta riga ta ɗora mata nauyin da ya fi ƙarfinta. A can gidansu kuwa Gwaggo Talatu da har zuwa wannan lokacin suna zaune da Sabuwa ne suna cigaba da tattauna abin da ya faru ɗin, domin ta fita bayan lafawar komai har zuwa inda abun ya faru ta dakko bokitinta suka dawo, suma basu bar maganar da suke yi tun farko ba, sai ma ci gaba da mayar da yadda lamarin ya faru da yadda Fulanin suka zo da yadda mutanen ƙauyen suka watse suke, harda karin gishiri da magi suke musamman ma ba Sabuwa da tafi yanko ta kamar wacce a gaban tane komai ya faru, ita kuma Gwaggo Talatu tana amsawa cikin wata irin zuciya mai cike da haushin Nadiya, tana cewa tun farko yarinyar ce dama ta cika taurin kai, kullum ana nuna mata ga yadda za tayi amma ba'a isa ba sai ta yi nata, yanzu ga shi nan abinda ta jawo wa kanta. A cikin wannan zancen ne ma Gwaggo Talatu ta furta wata magana mai tsananin muni tana cewa, "Ni wllh Allah yasa ma ta mutu, ko ma hutu da fitina, yarinya karama sai shegen gizago, ina cin ubanta amma wllh bana iyawa saboda shegen kwarjinin da take dashi." Sabuwa ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ce, "Kai ƙawata dadina dake fa baki da dama." Gwaggo ta wani ɗage kafada tana cewa, "Toh me zan ce daya wuce wannan? Yarinyar nan tun tana ƙarama take azabar dani wllh" Daidai lokacin da suke cikin wannan gulmar ne Baba Gaje ta fado gidan kamar wacce aka jeho haka ta shigo ta tsaya a bakin ƙofar tana kallonsu na ƴan daƙiƙu ɗaya bayan ɗaya. domin kalmar ƙarshen da ta ji daga bakin Gwaggo Talatu ta isa ta kunna mata wata sabuwar wutar ne cikin zuciyarta.

"Ke Talatu!"

Ta furta a tsawace wanda ya saka Gwaggo Talatu juyowa da sauri tana kallonta. Kafin Baba Gaje ta shiga nunata da yatsa tana mai furta. "Wllh wannan bakar zuciyar taki babu inda zata kai ki ta baro, kuma da kikema yarinyar nan fatan mutuwa, kin manta cewa ita ce ƴar da kike ma fatan mutuwar ita ke tallafe da rayuwarku? Tun uwar ta na raye kike uzzira mata, kina manta duk da taurin kan nata kina mata duk abinda kika ga dama, wanda nake da tabbacin cewa albarkacin sunan Matar Mahaifinta da kike amsawa kawai kike ci, in banda haka ko ni da kai na da tuni na jima da raba Nadiya dake ko dan wannan gantalallen tallar da kike ɗora mata, banda uban aikin da kike jibga mata daga inda akace gari ya gama wayewa shikenan kiyamar Nadiya ta tsaya, har sai zuwa wani daren baccin take samun salama, amma duk baki duba hakan ba kike mata fatar mutuwa yarinyar dake can tsakanin rai da mutuwa ke kina nan kina fatan mutuwarta?" Gwaggo Talatu ta yunkuro da niyar magana amma Baba Gaje bata bata damar hakan ba, ta ci gaba da cewa, "Da ƴarki ce ta shiga irin wannan matsalar da tuni kin riga kin bi ta asibiti kin zauna a kanta,amma dake Nadiya ba ke kika haife ta ba, sai ki kayi zamanki kina mata ma fatan mutuwar ta? IN SHA ALLAHU sai kinga irin daukakar da ALLAH zai yima Nadiya da idonki, domin ni ba zan miki fatan ki mutu ba, sai kinga yadda ikon ALLAH yake tun da na jima da fahimtar cewa ke jahila ce, ko a cikin jahilan ma ke lamba daya ce..." Daga haka ta juya tana barin gidan.

*DSS HEADQUARTERS ABUJA*

Cike sosai babban dakin yake da duk wani jami'i na DSS da suka fito daga sassa daban daban, wasu daga cikinsu manyan jami'ai ne, wasu kuma suna zaune ne a gefe suna sauraron bayanan da ake gabatarwa, amma abu ɗaya ne ya haɗa dukkan fuskokin da ke cikin dakin a wannan lokacin; nauyin sunan da aka ambata a tsakiyar taron kawai neman zarar da kan wasu yake, daga tsakiyar screen na teburin taron an saka hoton wani mutum na shekarun baya, hoton jami'in da ya taɓa zama ɗaya daga cikin mutanen da hukumar ta fi dogaro da su wajen wasu daga cikin ayyuka masu hatsari, mutumin da sunansa ya taɓa zama kamar wata alamar tsoratarwa a cikin DSS, wanda idan aka ambaci aikin sa a cikin case kan kaɗa ƴaƴan hanjin abokan gaba. Ba kowa bane wannan tsohon Jami'in nasu fa ce *RAYYERN KHALID* Wani daga cikin Jami'an dake zaune a gefe guda ne ya sauke kansa yana kallon hoton na ɗan lokaci kafin cikin wata murya mai nauyi ya furta "Da gaske shi ne?" Wani da ke kusa da shi ya amsa masa da, "Vice President ya tabbatar da hakan." Na uku ya girgiza kai a hankali yana cewa, "Amma ba ance ya mutu ba? Why kuma yanzun ace an gan shi a raye." Wani tsohon jami'in dake bayan su ya yi shiru kafin ya ce, "An ce ya mutu ne... amma ba mu sami ganin gawarsa ba." Kalmar data saka wasu suka kalli juna kenan, domin kowa dake wannan dakin ya san Rayyern Khalid ba irin jami'in da za a manta da sunansa ba ne cikin sauƙi, saboda sun san irin ayyukan da ya gudanar, sun san yadda yake iya shiga inda wasu ke tsoron shiga, kowa ya kasancene yana tsoron mutuwa yayin da shi da kansa yake fuskantar Mutuwar. Sun san yadda yake iya karantar mutum kafin shi mutumin ya kai ga furta abin da ke bakinsa, kuma mafi yawansu sun san cewa idan aka ce akwai mutum ɗaya da zai iya juya aikin da aka tsara masa zuwa wani salo na daban to shi ne, RAYYERN ne domin RAYYERN yana ɗaya daga cikin matakin farkon da suke rike da kungiyar DSS... General Director da tun da aka zaune bai ce komai bane yana daga zaune a saman teburin yana kallon dukkan su cikin wani irin nazartan kalaman kowannensu kafin ya ce, "Abin da muke tattaunawa a yau ba wai kawai gano wanda ya sace Sameer bane." Ya ɗan tsaya ya fesar da numfashi kafin ya ɗora da fadin, "Muna magana ne akan mutum mafi hatsarin da wasa dashi kamar wasa da wuta. Domin kuma shi ne mutum na farkon wajen sanin makamar iya cimma mutum da yaki, mutumin da ya san tsarin wannan hukuma fiye da yadda yawancin mutanen da ke zaune a wannan dakin suka sani." Baki daya wani irin shiru ne ya mamaye dakin. K Mashi ne ya amshe zancen tare da gyara zamansa yana cewa, "Kwarai kuwa Sir, domin kuwa kusan zan iya cewa RAYYERN KHALID yafi kowa sanin tsarinmu, ya kuma san yadda muke bin signal, ya san yadda muke tsara convoy, ya san yadda muke ɗaukar mataki idan an yi mana barazana." AJMAAL dake gefe ya yi shiru yana kallon hoton Rayyern kawai. Wani jami'i ya ce, "Amma me ya sa jami'inmu zai koma babban criminal irin haka duk da cewar ba wannan bane karo na farko da hakan ke faruwa ba?" Wani ya amsa masa da "Wataƙila kuma ba shi ba ne gizo ne kawai ya masa." Na farkon ne ya ɗan girgiza kansa tare da cewa, "Vice President ya tabbatar da cewar shi ne." Cike da daukar zafi da ɗumi wani daga cikin jami'an ya furta. "Idan kuwa shi ne... shin da gaske kenan zaluntar sa aka yi?" Haka kowa yaji saukar kalmar kamar an jefa dutse cikin ruwa.

Wani jim Director yayi har kusan na mintoci fiye da goma kafin ya sharce wata zufar dake goshinsa yana mai furta cewan. "Media ta riga ta san sunan Kind Dada tun tuni! Tun kafin mu gano wanene shi. Wanda hakan ba shi ke nufin cewar wannan shikenan wannan case ba zai ci gaba da ɓoyewa ba. Dole mu yi aiki da gaskiya guda ɗaya tak, duk inda aka kama Kind Dada, ba za a sake yi masa treating kamar tsohon jami'inmu ba." Ya tsaya yana kallon su ɗaya bayan ɗaya kafin ya furta, "Idan aka kama shi kuma ya yi resisting, a harbe shi."Kalmarsa ta ƙarshe ta yi wani irin nauyi a cikin dakin da wasu zukatan. AJMAAL kuwa har lokacin bai ce komai ba, sai dai idanunsa sun sauka kan hoton Rayyern, kamar yana kallon wani mutum ne da ya taɓa sani sosai amma yanzu aka tilasta masa ya dube shi a matsayin abokin gaba.

General Director ya kalli Ajmaal kai tsaye tare da ambatar sunan sa da.

"AJMAAL."

" Yes Sir."

"Daga wannan lokacin, wannan case naka ne." Kowa dake wurin babu wanda bai dago kai ya kalle Shugaban nasu ba, kallo irin na son gano anya lafiyansa kuwa. Kafin su dawo daga cikin wannan duniyar mamakin suka sake jin saukar maganarsa kamar tsawa. "Ba na so kace zaka bi shi kamar kana bin wani ordinary criminal ne. A Ahh ina son ne ka farauce shi kamar yadda ake farauta a dawa, saboda kafi kowa sanin yadda yake tunani, ka fi kowa sanin salon aikinsa, ka kuma fi kowa sanin inda zai iya fara wasa da inda zai iya ƙare shi. Saboda haka kai ne zaka nemo min RAYYERN KHALID as KIND DADA" Wani irin shiru AJMAAL yayi, kafin ya ɗago kansa da furta. "Yes Sir." Kafin Director din ya sake dubanshi da wani irin kallo mai zurfi da furta. "Ka san abin da hakan yake nufi."

AJMAAL ya juya ya kalle shi tare da sara masa yana amsawa da "Na sani Sir." Wani ɗan murmushi mara daɗi na kufce masa ya bayyana a gefen bakinsa da sake furta. "...zan yi amfani da duk salon da shi ne ya horas dani wajen nemo shi."

*KIND DADA *

Wani kayatacce kuma tsararren babban garden ne dake dauke da wani irin shiru, shirun da shi ne abinda wanda ke zaune a wurin yafi bukata sama da komai. Yana zaune zama irin na waɗan da suka isa har ma suke jin sun gama tumbatsa, baki daya wurin kawace yake da wani irin tsari na musamman, gefe da gefen wurin bishiyoyi ne suna rangaji a hankali saboda sanyin iskar daren dake kadawa, sai fountain dake can gefe yana fitar da ruwan da sautin sa ke fita a slow. Yana zaune cikin wata irin nutsuwar da kamar babu wata damuwa a duniya da ta taɓa samun hanyar zuwa gare shi. Ƙafar nan ɗaya saman ƙaramin table din dake gabansa, yayin da ɗayar kuma take sauƙe a ƙasa, hannunsa ɗaya rike da wani glass cup din dake dauke da Red Wine, ɗayan kuma taba ce ke tsakanin yatsunsa, yana kurɓa giyar a hankali yana jan hayaƙin taban ya fesar da hayaƙin a sama subi duniya. RAYYERN KHALID ke nan, mutumin da yanzu duniya ke nema ruwa a jallo, mutumin da sunansa ya girgiza duniyar DSS, mutumin da aka ba da umarnin a harbe shi idan aka kama shi ba kai tsaye. Amma gashi zaune a nan hankali kwance cikin wata irin nutsuwa yana kallon ruwan dake sauka a slow cikin yanayin dark duhun daren dake gabansa. Wani kalan yin baya da kansa yayi, tare da saka ƙafarsa ya tura table ɗin dake gabansa hadi da lumshe idonsa. Tamkar wanda ake jiran ya lumshe idon kuwa sai ga wani hoto ya fado masa, Prison, ƙofar da aka saka shi shi kadai din sa, hannunsa daure cikin sarkar ƙarfe. Muryoyin dubban mutane daban daban a saman kansa. Cikin wani irin duhun daren da yaki tausaya, taurari da hasken farin wata suna kin bayyana tamkar suma suna nadamar kallon abinda zai faru a cikin wannan tsohon daren ne, kafin hoto na biyu ya sake bayyanar masa, hoton Mahaifinsa cikin jini. Wani irin shegen masifaffen zafi mai tsananin ne yaji kamar zai tsaga kirjinsa, wani irin buɗe idanunsa da ƙarfi yayi tare da sakin wata uwar kara...

"AAAAHH!"

Haka ƙarar ta kubce masa daga ƙasan zuciyarsa, hannunsa ya kai kan glass cup ɗin da ke rike a hannunsa ya damƙe shi da dukkan ƙarfinsa har sai da glas cup din ya fashe a tafin hannunsa, jini ya fara fita tsakanin yatsunsa yana digowa ƙasa, amma bai sam sam shi bai damu da hakan ba, idanunsa sun yi wani irin ja kamar wanda aka dawo da shi cikin wani wurin da ya shafe shekaru yana son ƙoƙarin binnewa. Kafin a natse ya kalli jinin dake diga daga tafin hannunsa zuwa kasa, wani irin murmushi mai kona zuciya na kufce masa mara dadi da dadin gani. Kafin a bayyane ya furta, "Dan kun saka a harbeni hakan ba komai bane, tun da har kuka iya sanja labari daga inda yake ku juya inda alkamin ba bai dosa ba, Kun kashe ni kun kuma binne sunana wannan ba komai bane, bare dan a karo na biyu kun sake bada umarnin a har be ni..." Yay maganar tare da mikewa tsaye idonsa na kallon sararin samaniya. Ya ɗan yi shiru na wani lokacin kafin ya sauke idanunsa kan hannunsa mai jini wani irin murmushi na sake bayyana a saman fuskarsa tare da ɗaga bottle na giyar dake gabansa ya kafa kansa bai dire ba sai daya tabbatar ya shanye ta tass yay wurgi da kwalban tana tarwatsewa a wurin.

ꨄ Washe gari da safe.

Kowa ka gani masu zaman jinya da kuma ma'aikatan lafiyan dake asibitin kowa ka gani shige da ficensu kawai suke suna sabgogin gabansu. Yayinda da wasu kuma ke zaune a gefen dakunan suna jiran sakamakon abin da ya shafi yan uwansu. A can gefe guda ma Baba Gaje ce da tayi zuwan dare ita da Sadiya suna zaune kusa da juna, dukkaninsu babu wanda yake magana, domin tun bayan data bata labarin kudin jinyar Nadiyan da aka bukata ita ma hankalin ta ya riga ya tashi. Shi ne dalilin daya saka Sadiya arar waya anan wurin masu zaman jinyar ta kira lambar mijinta inda da kyar ma ta samu ya yarda ya kaima Baba Gajen har ta samu ta maganar kudin, tace don ALLAH a nemo ko nawa idan ta dawo ko kayan ɗakin tane zata sayar ta biya, haka Baba Gaje tayi ta shige fice a ƙauye amma ba'a wani dace ba, haka tazo daga ita sai wata dubu biyunta a hannu wanne itama dan jarin tane da take yin kokon safe na saida wa ta tarkato ta taho dashi, wannan abu shi ya saka hankalin Sadiya tashi ta bar Baba Gaje a daren ta kutsa zuwa garin nasu magribar fari, haka tayi ta zagayen dangin da suka rage musu, da duk mutanen data sani ta roƙi da koda aro ne a ara mata amma ba'a dace ba, duk inda ta juya sai dai ta dawo da hannu babu komai. Haka ta debo kafa ta dawo tana zama kusa da Baba Gaje a matukar wahalce da gajiye. Kafin da kyar ta iya buɗe wata ƙaramin jaka da ta kasance tare da ita, ta fara zaro duk abin da take ganin za su iya sayarwa ko su samu wani abu a kansa, amma su din ma duk ba'a dace din ba, inda koda ace an dace din ma to ba su kai komai ba idan aka kwatanta da adadin kuɗin da ake nema. Baba Gaje kuwa tana kallonta ne kawai zuciyarta cike da tausayawa, kafin Sadiya ta fara haɗa kan kuɗin da suka samu gaba ɗaya a gabanta. Ɗaya bayan ɗaya haka ta shiga ƙirga kuɗin, ta sake ƙirgawa karo na biyu kamar ba ta yarda da abin da idanunta suka gane mata ba ne, kafin daga ƙarshe ta ɗago kai tana kallon Baba Gaje cikin wata irin sarewar dake nuni da nakasa ko kasawarta, cikin wata irin magana marar ƙarfi tace, "Dubu goma sha huɗu da ɗari tara..." Ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta gyara ta ƙara ƙirgawa, "Kusan dubu goma sha biyar kenan." Baba Gaje ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, domin ita ma ta san abin da ke gabanta, kuɗin da ake nema sun yi nisa sosai da wannan. A kuma daidai wannan lokacin ne wata nurse ta fito daga bangaren da Nadiya take, tana nufo inda suke kai tsaye hannunta rike da wasu takardu. Sadiya ce ta yi saurin mikewa tana zuwa gareta, "Yaya yanayin ƴar uwar tawa?" Nurse ɗin ta amsa mata cikin nutsuwa, "Yanayinta yana nan yadda yake, amma har yanzu tana buƙatar kulawa." Sadiya ta ɗan yi murmushi na dole tana cewa, "Mun yi ƙoƙarin samo kuɗin sai dai bamu kai ga samu duka ba ga dai iyaka abin da muka samu kafin a jima na koma ƙauye na daga kayan ɗakina na sayar IN SHA ALLAHU zuwa yamma zan kawo kudin." Nurse ɗin ta kalli kuɗin sannan ta kalli Sadiya, kafin ta girgiza kai a hankali. "Hajiya bama irin haka, don da ace ana irin haka din da tuni asibitin bata kai labari ba, don haka ba zamu sake taɓa yar uwar kiba har sai lokacin da kuka shirya kudin ku baki daya..." Kalmar data saka murmushin Sadiya daukewa kenan yana guduwa daga fuskarta. "Na sani..." ta furta a hankali, "amma wannan shi ne duk abin da muka samu kuna amsar uziri irin haka, saboda kamar ku mutanen dake cikin birni yawanci baku san irin ƙalubalen rayuwar da na ƙauyuka suke zamu ba" Nurse ɗin ta yi ɗan shiru kamar ba zata tanka mata ba, amma zuwa can tace, "Kin ga Malama wannan wahalar rayuwar da kike gani babu inda bata zaga ba, idan nace zan baki asalin yadda rayuwa tayi dani tun daga farko har zuwa nan da baki ce haka ba, so dan haka ki ringa iya kanki and kuma kuyi ƙoƙarin ganin kun biya, domin har sai kun biya kafin a ci gaba da kulawa da ita, duk da na fahimci halin da kuke ciki, amma akwai tsarin asibitin ne" Sadiya ta ɗan ja da baya, hawaye suka cika mata ido. "Don ALLAH! kada ku bar ta haka saboda ba mu da kuɗi." Nurse ɗin ta ɗan taɓa baki da ɗage kafadarta sama tace "Ku yi ƙoƙari kawai kafin nan kafin yamma don wllh kuna wuce yammar har gadon da take kai ma sai an fitar da ita, gasu can sauran marasa lafiyar da aka kawo su tare su har su biya tu jiyan." daga haka ta juya tayi tafiyar ta tabar Sadiya kuma tsaya cak tana kallonta har ta ɓace ma ganinta.

Baba Gaje ta miƙe a hankali ta ƙaraso kusa da ita. "Sadiya..." Amma Sadiya ta girgiza kai, hawaye suka gangaro mata. "Baba Gaje, daga ina za mu samo sauran? Mun yi duk abin da muka iya." Ta kalli kuɗin dake hannunta. "Dubu goma sha biyar ne kawai..." Ta yi wani ɗan dariya irin mai ciwon nan, kafin ta ɗora da fadin. "Baba Gaje maganar fa rayuwar Nadiya ake, mu kuma muna nan muna ƙirga kuɗin da bai kai ko kusa da abin da suke nema ba." Baba Gaje ta kama hannunta tana cewa, "Ki yi haƙuri, za mu samu mafita IN SHA ALLAHU." Sadiya ta sunkuyar da kanta, "Nadiya ce kullum take taimaka mana Baba Gaje... sau nawa ta hana kanta abin da take so saboda ta samu ta kawo mana? Yanzu ita ce ke cikin hali na naiman taimako da buƙatarmu amma mun gaza! Kai innalillah wa'inna ilaihi raji'un ubangiji ka raba mu da rayuwar da tafi karfinmu..." Muryarta ta karye gaba ɗaya kafin ta rufe fuskarta da hannayenta kawai.... Ko kafin su sake yunkurin cewa komai suka jiyo ƙarar wasu takalma, wanda har sai da duk suka juya suna kallo, zaratan jami'an sojoji suna gani, wanda dama sai dai su din kenan irin wannan taku haka. Cikin wasu daga cikin jami'an tsaro ne suka shigo cikin asibitin, suna tafiya a zafafe cikin tafasar jini suna yi suna duba wurare daban-daban, ba don suna neman wani abu ba sai dai an turo rukuninsu ne domin duba lafiyar waɗanda suka samu raunuka daga harin da kuma tabbatar da tsaron wurin. Haka suka wuce su Safiya duk inda suka wuce girma kawai ake basu, daki daki suke bi suna duba marasa lafiya, bayan sun nemi ganin wadanda aka kawo daga Kurman Rafi. Bayan Ɗaya daga cikinsu ya tsaya na ɗan lokaci yayin da idanunsa suke kan wata gadon da ke can gefe, haka kawai yaji zuciyarsa ta motsa wanda ya jawo hakan ya sake saka shi sake matsowa gaban gadon. A daidai lokacin da ya kalli Nadiya dake kwance, take yaji wannan abun da yaji na sake motsa masa a rai. Cak haka ya tsaya yana kallonta na ɗan lokaci kafin ya gane ita ce yarinyar da ya taɓa gani a ranar da aka tura su garin, komai bai ce ba daga haka ya juya ya ci gaba da tafiyar sa. Sai ga wata nurse nan su biyu suna nufo dakin daya fito, cikin kamar muryan faɗa fada haka ya jiyo muryan ɗaya daga cikin su tana cewa. "Gadon da take kai kawai zamu mayar da ita, ita kuma tun da har yanzun yan uwanta sun gaza biyar kudin mu mai da ita dayan dakin har sai lokacin da suka samo suka kawo..." Cak haka yaja ya tsaya bayan ya gama tabbatar da cewa wacce suke magana din akai Nadiya din ce, don har sun bude dakin ma sun shige sai kuma ga karar wani gado nan ana gangarowa alamar dai itan ake nufi, ai bai ma san lokacin daya isa room emergency din ba, sai ganin kawai mutum sukayi a kansu amma dai yayi kokari kwarai da gaske wajen daidaita yanayinsa. "Nawa ne kuɗin ita ma gadon din?" haka suka ji saukar muryan nasa daya saka su saurin kallonsa, baki daya daburcewa suka so yi har sai da ya ɗan daka musu tsaiwar daya saka Nurse Halima faɗa masa adadin kuɗin, wallet nashi ya zaro yana miƙa musu da faɗin cewa suje su chaji duk abinda suke ganin zai isa har zuwa lokacin da za'a sallameta. Cikin abinda bai wuce kiftawar ido da buɗewa suka chaji kudin yana wucewarsa bayan ya sake juyawa ya mata kallo ɗaya ya fice daga room ɗin.

Baba Gaje da Sadiya kuwa suna can zaune zuciyoyinsu a kulle, har sai da nurse ɗin ta dawo ta ce musu, "An biya." Wanda jin hakan ya saka Sadiya saurin ɗago kai tace. "An biya kuma?.... To waye... ?" Nurse ɗin ta gyada kai. "Eh tabbas an biya duk abin da ake da bukata yanzun haka." Sadiya ta kalli Baba Gaje, ita ma Baba Gaje ta kalle ta, babu wacce ta fahimci daga ina kuɗin suka fito. "Wa ya biya?" Sadiya ta sake jefa mata da tambayar farki. Nurse ɗin ta ce, "Wani jami'i ne." "Wane jami'i?" "Ban san sunansa ba." Ta juya tana nuna musu inda ya bi, amma lokacin da suka kalli wajen babu shi tuni har ya ɓace ma ganinsu. "Ya riga ya fita ma." nurse din ta fadi tana juyowa don zuwa kan Nadiya domin ci gaba da gudanar mata da aikinta, Sadiya kuwa da har lokacin take tsaye tana kallon ƙofar da aka ce ya fita, idonta taf da ruwan hawaye kafin ta sauke numfashi mai nauyi. "ALLAH ya saka masa da alheri..." ta furta a hankali. Shi kuwa Baba yana can gida Sadiya da zata tafi ta tafi dashi ganin Baba Gaje tazo.

Washe gari kuwa lokacin da wannan jami'in ya sake dawowa domin duba marasa lafiyar da aka samu daga harin, Baba Gaje tana zaune a wajen corridor na dakin da aka sake dawo da Nadiya ne, inda kai tsaye idanunta suka sauka a kansa shi da nurse din jiya domin yaje dakin take ce masa ai an sauya mata daki ne, ai kuwa nan take ta gane shi. Wani irin firgici ya kama ta har ta miƙe da sauri ta koma bayan kujera tana cewa, "Ya subhanallahi don girman ALLAH kayi min rai! Me ya kawo ka nan kuma? Jikata au yata na kawo zaman jinya ne, ba Bon zan dasa muku a cikin asibitin ba!" Cak haka Jami'in ya tsaya yana kallonta, kafin wata yar dariya ta kubce masa, don sai yanzun yake gano ta tabbas itace wacce ya gani da Nadiya har tayi fitsari a wando. "Goggo..." ya furta yana karasa isowa gare daya saka Baba Gaje ta ƙara ja da baya, "Kar ka zo kusa da ni!" da hannu yake mata alamar kwantar da hankali yana karasa isowa tare da kama hannunta a hankali yana cewa, "Babu komai, ki daina tsorona. Ni jami'i ne." Daidai nan kuma nurse din ke sanar musu da shi ne ma wanda ya biya duka kudin jinyar Nadiya din. Ta kalle shi sosai kafin ta gane babu wata alamar barazana a tare da shi tare da masa godiya, itama Yaya Sadiya ta matso tana masa godiyan sosai yana cewa babu komai. Tare dasu ya wuce don sun ce an hana musu ganinta, bayan sun je sun dawo har zuwa lokacin bata farfado ba ya fita babu jimawa yaje ya dawo musu da uwar sayayya ta kayan bukata. Ya kuma basu dubu ashirin yace saboda da zirga zirga aikuwa Baba Gaje harda kwallarta.

DSS HEADQUARTERS ABUJA

Sosai maganar bayyanuwar Rayyern Khalid ta sake daukar dumi fiye da jiya, saboda yau din ma tun farar safiya babban dakin taron ya sake cika, amma wannan karon babu wani yanayi na taron yau da kullum, domin duk wanda yake cikin dakin yana sane da cewa sunan da ke gabansu ba sunan wani ordinary criminal bane. A saman screen ɗin an sake haskaka hoton RAYYERN KHALID, tsohon jami'in DSS da ya taɓa zama abin koyi ga jami'ai da dama. K Mashi yana tsaye kusa da teburin yayin da AJMAAL yake zaune yana kallon bayanan da ke gabansa, wanda sai yau aka gama shirya file a kan sa, amma babu wanda zai iya cewa hankalinsa yana kan abin da ke screen ɗin saboda tun daga lokacin da aka ambaci sunan Rayyern yake cikin wani irin shiru.

General Director ya ɗaga kansa yana kallon su. "Duk inda Kind Dada ya shiga, ya bar mana tambaya fiye da amsa. Amma yanzu mun san abu guda." Ya nuna hoton. "Mutumin nan ya sanmu." Wani jami'i ya ce, "Sir, idan da gaske shi ne Rayyern Khalid, to wannan yana nufin duk wani tsarin da za mu yi zai iya zama yana hannunsa tun kafin mu fara gabatar dashi ." General Director ya kalle shi. "Exactly." Ya juya zuwa AJMAAL. "Shi yasa na ba ka wannan case din." AJMAAL ya ɗaga kai. "Sir." saurin katse shi director din yayi yana cewa. "Ka san abin da yake tunani. Ka san yadda yake aiki. Ka san abin da yake kira da mistake da abin da yake kira da trap. Ka san inda zai iya barin sawu da kuma inda ba zai taɓa barin shi ba." AJMAAL ya sauke idanunsa kan hoton. "Sir, dole akwai alamar tambaya a cikin wannan abin daya faru, nake kuma tunani daban. Taya Rayyern kwatsam zai bayyana mana kansa? Alhalin na battar duk wani mai aikata laifi a kullum kwanan duniya sake ɓoye wa daga huka yake, idan har abinda nake hasashe gaskiya kenan yabar VP ya gane shi ne, to kuwa tabbas akwai yiwuwar ya yi hakan ne saboda yana son mu san cewa shi ne KIND DADA..." K Mashi ne ya kalle shi. "Kana nufin ya gayyace mu cikin wasan kenan?" AJMAAL ya ɗan yi wani murmushi mara daɗi. "A'a Sir. Ina nufin... tuni har mun shiga cikin wasan ma." Daga haka wani irin shiru ya mamaye dakin.

A hankali AJMAAL ya miƙe ya nufi screen ɗin, idanunsa na sauka a kan hoton tsohon malaminsa. "Yanzu case ɗin ya canza. Ba muna farautar Kind Dada bane kawai." Ya ɗan tsaya. "Muna farautar RAYYERN KHALID ne.Mutumin da ya san yadda za mu fara farautarsa tun kafin mu yanke shawarar farautarsa." General Director ya gyada kai. AJMAAL ya ɗaga idanunsa kamar alamar mai tunani "Saboda haka zan fara daga inda ya fara koya min yadda ake ɓoye gaskiya."

....Rayyern yau kam sanye yake cikin wasu kaya na kwasar magana, don gaba daya shigar idan har ka ganshi da su babu abinda zai saka baka kira shi shege a cikin shegu ba, ga kan sa da a wayewar yau din ya ma wani dan iskan aski na kwasar maganar shi ma, wata ash vest ce a jikinsa irin mai makalewar nan a tsakigar gadon bayan mutum, tun daga dokin wuyarsa vest din ta makale ta Lafe a jikinsa, sai wani short wando amma burgujeje, gaba ɗaya dantsen hannuwansa a bayyane, daga gefen wuyarsa wani kyakkyawan hoton EAGLE ne, mai girma, dantsensa daya kuma kan LION sai sauran zanan nakin tattoo din da da ya bi wasu wuraren yana zane su da ababuwa maban banta. Yana zaune cikin wata mayyar close rug wacce ya lume a cikin ta, daga nan bakin gidan gefe da pool din dake wurin. Wannan hannun da ranar yaji masa rauni an rufe shi da wani ɗan farin bandeji, wanda da dukkan alamu wannan din ba aikin kowa bane na mark ne. Daga yadda yake zaunen yana yawan duba time a hannunsa dake daure da agogon fata zai baka tabbacin kamar akwai wani abu da yake jira ne. A hankali ya ɗaga kai lokacin da wata mota ta tsaya a bakin wurin, wani basamuden mutum ya fito daga cikin motar bai yi wata magana ba, sai ya ƙaraso ya ajiye wata ƙaramar jaka a gabansa, da wani kamar cakudadden yare ya masa magana wanda ya saka a karo na farko babban criminal irin Kind Dada yayi wata dariya da ambatar sunan. "AJMAAL?" a bayyane. Wanda cikin wannan mugun yaren mutumin nan gyada masa kai yana cewa "Shi ne aka ɗora ma alhakin wannan case."

Wani irin shiru ya biyo baya ne ya biyo baya kafin Rayyern ya ɗauki taba ya kunna ta, ya kai bakinsa tare da jan hayaƙin a hankali ya wani furzar da shi sama. "Na sani." ya furta yana sake zukar tabar wani smile na bayyanuwa a saman fuskarsa. "Idan suka tura wani daban, da na fara damuwa."Yay magana din tare da ɗaga bottle na Red Wine ɗin dake gabansa ya kurɓa kaɗan.

"AJMAAL ne ya kamata ya zo din dama" Ya wani lumshe idanunsa yana dage ƙafarsa daya zuwa saman table ɗin dake gabansa, gefensa jarkar ruwan Mr. V ne da har abada ba'a raba shi dashi kamar yadda har abada ba'a taba raba shi da red wine da kuma cigarettes. "Saboda akwai wasu darussa da malami ba ya koya wa ɗalibi sai ranar da ɗalibin ya zo ya yi ƙoƙarin kayar da shi..." Ya ɗaga kansa yana kallon mutumin, "Ku bar shi ya zo." saurin kallonsa mutumin yayi da faɗin.

"Amma Boss?"

Rayyern ya yi wani ɗan murmushi da girgiza masa kai "Kar ku taɓa shi, kada kuma ku masa komai har sai ya gano abin da nake so ya gano din." Daga nan ya koma yana sake jingina da kujerarsa, yana kallon ruwan swimming pool din dake gabansa...

BY AMMEY LAYLERH ✍🏻

***

༺𝙂𝙐𝘿𝙐𝙉 𝘿𝘼 𝘽𝘼𝘽𝙐 𝙏𝙎𝙄𝙍𝘼༺

Kᴡᴀɴᴄɪʏᴀ ᴛᴀ ғɪsʜɪ

𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.